Imam Jawad
  • Take: Imam Jawad
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 15:38:2 1-9-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Muhammad Jawad (a.s) Imami Na Tara: Imam Muhammad Jawad Dan Ali Ridha (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Ali da Musa dan Ja'afar (a.s). Babarsa: Kuyanga ce sunanta: Sukaina Al-marsiyya, an ce sunanta Al-khaziran. Alkunyarsa: Abu Ja'afar Assani da Abu Ali. Lakabobinsa: Al-jawad, Attakiyyi, Azzakiyyi, Al-kani'u, Al-murtada, Al-muntajab. Tarihin haihuwarsa: 10 Rajab shekara 195H. Inda aka haife shi: Madina. Matansa: Kuyanga ce mai suna Sumana da Ummul fadli 'yar ma'amun. 'Ya'yansa: 1-Imam Al-Hadi (a.s) da 2-Musa 3-Fadima 4-Amama. Tambarin zobensa: Ni'imal kadir Allah.
Tsawon rayuwarsa: shekara 25. Tsawon Imamancinsa: shekara 17. Sarakunan zamaninsa: karshan hukuncin Al-amin da Al-ma'amun da Al-mu'utasim. Tarihin shahadarsa: karshen Zul'ki'ida shekara 220H. Inda ya yi shahada: Bagdad.
Dalilin shahadarsa: Shan guba a lokacin halifa Al-mu'utasim. Inda aka binne shi: An binne shi a makabartar Kuraishawa a Al-Kazimiyya kusa da kakansa Al-kazim (a.s).
Shi ne Muhammad Jawad dan Ali (A.S) babarsa sayyida Sabika (A.S), an haife shi a juma'a goma ga watan Rajab shekara ta dari da casa'in da biyar a Madina kuma ya yi shahada a bagadaza a karshen zul'ki'ida a shekara ta dari biyu da ishirin hijira, kuma dansa Imam Ali Hadi (A.S) shi ne ya shirya janazarsa kuma ya binne shi a makabartar kuraishawa da take gefen kakansa Imam Musa dan Ja'afar (A.S) a kazimiyya inda kabarinsa yake a yau.
Ya kasance mafi ilmin mutanen zamaninsa kuma mafificinsu, kuma mafi baiwarsu, mafi dadinsu mazauni, kuma mafi kyawunsu kyawawan halaye, kuma mafi fasaharsu harshe, ya kasance idan ya hau sai ya dauki zinare da azurfa, kuma wani mutum ba ya tambayarsa sai ya ba shi, kuma duk wanda ya tambaye shi daga ammominsa ba ya ba shi kasa da dinare hamsin, kuma wacce ta tambaye shi daga ammominsa mata ba ya ba ta kasa da dinare ishirin da biyar.
Daga cikin abin da ya nuna iliminsa ga mutane: kusan malamai tamanin daga malaman kasashe sun taru waje daya gunsa bayan sun dawo daga hajji, suka tambaye shi mas'aloli daban-daban sai ya amsa musu. Kuma haka nan mutane masu yawa sun taru gunsa suka tambaye shi mas'aloli dubu talatin a majalisi daya (wato mu'utamar na kwanaki) kuma ya amsa musu duka (irin wannan a yau ana kiran su mu'utamar na wasu kwanaki, amma duk ya amsa gaba daya).
Kuma wannan ya faru ne yana da shekaru tara, sai dai wannan ba wani abin mamaki ba ne ga Ahlul Baiti (A.S) wadanda wahayi ya sauka ga kakansu, kuma zababbu bayansa (A.S) musamman bayan Kur'ani ya yi bayanin ba wa Isa (A.S) littafi da annabta yana cikin tsumman haihuwa.
Sannan halifa ya aura masa 'yarsa bayan ya jarraba shi da mas'aloli masu muhimmanci da ya amsa su duka -a wani labari mai shahara-.