Imam Hasan (A.S)
  • Take: Imam Hasan (A.S)
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 6:43:19 13-7-1403

Imam Hasan Mujtaba (a.s) Imam Hasan Mujtaba (a.s) Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Hasan Mujtaba (a.s) Imam Hasan Mujtaba (a.s) Dan Ali (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: shi ne Al-hasan da Ali dan Abu dalibi dan Abdulmudallibi (a.s). Babarsa: Fadim Azzahara (a.s) 'yar Manzon Allah (s.a.w). Alkunyarsa: Abu Muhammad.
Lakabinsa: Attakiyyi, Azzakiyyi, Assibd, Addayyib, Assayyid, Alwaliyyi. Tarihin haihuwarsa: 15 Ramadan 3 H. a mash'huri, a wata ruwaya an ce shekara ta 2. Inda aka haife shi: Madina.
Yakokinsa: Ya yi tarayya a duk yakokin da aka yi wajan bude kasashen Afrika da kasashen Farisa tsakanin shekara ta 25 zuwa ta 30, ya kuma yi tarayya a duk yakokin da babansa ya yi na Jamal da Siffaini da Nahrawan.
Matansa: 1-Ummu Bashir 'yar Mas'ud Khazrajiyya 2-Khaulatu 'yar Manzur Alfazariyya 3-Ummu Ishak 'yar Dalha Attaimi 4-Ja'ada 'yar Ash'as.
'Ya'yansa: 1-Zaid 2-Al-Hasan 3-Amru 4-Al-Kasim 5-Abdullah 6-Abdurrahman 7-Al-husaini 8-Dalhat 9-Ummul Hasan 10-Ummul Husaini 11-Fadimatu 'yar Ummu Ishak 12-Ummu Abdullah 13-Fadima 14-Ummu Salama 15-Rukayya.
Tambarin hatiminsa: Al-Izzatu lil-Lahi Wahdah. Tsawon rayuwarsa: Shekara 47. Tsawon shekarun Imamancinsa: Shekara 10. Sarakunan zamaninsa: Mu'awiya dan Abi Sufyan.
Tarihin shahadarsa: 7 Safar 49H, an ce 28 Safar 50H. Inda ya yi shahada: Madina. Dalilin shahadarsa: Guba da Mu'awiya ya ba shi ta hannun matarsa Ja'ada 'yar Ash'as. Inda aka binne shi: Makabartar Bakiyya Madina.
Shi ne Hasan dan Ali dan Abu Dalib (A.S) kuma babarsa Fadima Zahra 'yar Muhammad (S.A.W) jikan Manzon Allah (S.A.W) mafi girma kuma na biyu a halifofinsa kuma Imami jagora ga mutane bayan babansa (A.S).
An haife shi a Madina mai haske ranar talata a rabin watan Ramadan a shekara ta uku hijira, kuma ya yi shahad da guba da Mu'awiya dan Abu Sufyan ya yi masa kaidinta ta hannun matarsa Ja'ada 'yar ash'as wannan kuwa a ranar alhamis bakwai ga watan safar , shekara ta hamsin hijira, kuma dan'uwansa Imam Husain (A.S) shi ne ya yi masa wanka ya binne shi a Bakiyya a Madina inda kabarinsa yake yanzu wanda abin takaici wahabiyawa suka rushe kubbarsa.
Ya kasance mafi bautar mutane ga Allah a zamaninsa kuma mafi iliminsu kuma mafificinsu, kuma ya fi kowa kama da Annabi (S.A.W), kuma mafi girman Ahlul Baiti a zamanisa kuma mafi hakurin mutane.
Ya kasance daga cikin karamcinsa, daya daga cikin kuyanginsa ta mika masa wani damki na turaren kamshi sai ya ce: ke 'yantacciya ce. Sai ya ce: haka nan Ubangijinmu ya tarbiyyantar da mu yayin da ya ce: "Idan aka gaishe da ku to ku amsa da mafi kyawu daga gareta ko kuma ku yi raddinta" .
Yana daga cikin hakurinsa cewa wani mutumin Sham ya gan shi yana haye da dabba, sai ya rika la'antarsa shi kuma Imam Hasan (A.S) ba ya yi masa raddi, yayin da ya gama sai Imam Hasan (A.S) ya zo wajensa ya yi masa sallama ya yi dariya ya ce: ya kai wannan tsoho ina tsammanin kai bako ne a wannan gari, ta yiwu ka yi batan kai, amma da ka… roke mu da mun ba ka, da kuma ka nemi shiryarwar mu da mun shiryar da kai, da ka nemi mu hau da kai da mun ba ka abin hawa, idan kuwa kana jin yunwa ne to sai mu ciyar da kai, idan kuwa kana da tsaraici ne to sai mu tufatar da kai idan kuma kana da talauci ne sai mu wadata ka, idan ka kasance korare ne sai mu ba ka wajen zama, idan kuwa kana da wata bukata ne sai mu biya maka .
Yayin da mutumin nan ya ji wannan magana sai ya yi kuka ya ce: na shaida kai ne halifan Allah a bayan kasa, Allah ne kawai ya san inda yake sanya sakonsa.