Imam Sadik
  • Take: Imam Sadik
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 5:25:50 13-7-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Ja'afar Sadik (a.s) Imami Na Shida: Imam Ja'afar Sadik Dan Muhammad (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Ja'afar dan Muhammad dan Ali dan Husaini dan Ali dan Abi Dalib (a.s). Mahaifiyarsa: Ummu Farwa 'yar Kasim dan Muhammad dan Abubakar. Alkunyarsa: Abu Abdullah, Abu Isma'il. Lakabinsa: Assadik, Assabir, Alfadil, Addahir, Alkamil, Almunji. Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul awwal 83H.
Inda aka haife shi: Madina. Matansa: Fadima 'yar Husaini dan Ali dan Husaini (a.s), sauran matansa kuyangi ne. 'Ya'yansa: 1-Isma'il 2-Abdullah 3-Musa 4-Ishak 5-Muhamma-d 5-Abbas 6-Ali 7-Ummu Farwa 8-Asma'u 9-Fadima. Tambarin hatiminsa: Allahu waliyyi wa Ismati min khalkihi.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 65. Tsawon Imamancinsa: shekara 34. Sarakunan zamaninsa na Umayyawa: Abdulmalik dan Marwan da Walid dan Abdulmalik da Sulaiman dan Abdulmalik da Umar dan Abdulaziz da Walid dan Yazid da Yazid dan Walid da Ibrahim dan Walid da Marwan Al-himar.
Na lokacin Abbasawa: Abul Abbas Assaffah da Abu Ja'afar Al-Mansur Addawaniki.
Tarihin shahadarsa: 25 Shawwal 148H. Inda ya yi shahada: Madina. Dalilin shahadarsa: Guba da ya sha a lokacin Mansur dawaniki. Inda aka binne shi: Makabartar Bakiyya a Madina.

Shi ne Ja'afar Sadik dan Muhammad (A.S) kuma babarsa ana yi mata kinaya da "Ummu Farwa" an haife shi a Madina ranar juma'a sha bakwai ga Rabi'ul awwal, ranar da aka haifi Annabi (S.A.W) wannan kuwa a shekara ta tamanin da uku bayan hijira, kuma ya shahada da guba ranar litinin ishirin da biyar ga shawwal shekara ta dari da arba'in da takwas, shekarunsa a lokacin sittin da biyar sai dansa Imam Musa Kazim (A.S) ya yi jana'izarsa, ya binne shi a Bakiyya a gefen mahaifinsa Bakir (A.S) da kuma kakanninsa Sajjad da Mujtaba (A.S).
Ya kasance yana da ilimi da daukaka da hikima da fikihu da zuhudu da tsantseni da gaskiya da adalci da baiwa da karimci da jarumtaka da sauransu.
Sheikh Mufid yana cewa: Ba a karbo hadisai masu yawa ba daga Ahlul Baiti (A.S) kamar yadda aka karbo daga gareshi kuma ba, babu wani mutum da aka karbo ruwayoyi daga gareshi kamar yadda aka karbo daga Ja'afar Sadik (A.S), sun tara sunayen wadanda suka ruwaito daga gareshi sai ga su sun haura mutane dubu hudu…
Abu hanifa ya kasance daga cikin dalibansa (A.S) kai tsaye, kamar yadda sauran malaman mazhabobi suka kasance dalibansa da wasida, kuma mafi yawan ma'abota sababbin ilimomi kamar kimiyya da pizik da ilimin kasa da yanayi da taurari da ilimin gano ma'adinai fitar da taskoki da albarkatun kasa da sauransu, Imam Ja'afar Sadik (A.S) ne ya assasa asasinta.
Ya dauki damar nan ta tawayen abbasawa a kan umayyawa wajen assasa makarantarsa da tarbiyyar dalibai wadanda ya bayyana musu koyarwar musulunci da kuma shari'a kuma ya yi musu bayanin fikirori da kuma rushe shubuhohi da ake jifan addini da su har sai da ya karfafa ilimin shari'a, kuma an san shi da sunan shugaban mazhabar ja'afariyya wato Shi'a, don haka ne maka ake cewa da mabiyan Ahlul Baiti (A.S) Shi'a ja'afariyya.
Daga zahudunsa ya kasance yana shan kunu da mai kuma yana sanya riga mai kauri mai kaushi, saudayawa yakan sanya mai rasha-rasha, kuma yana aikin gonarsa da kansa.
Daga ibadarsa ya kasance yana salla da yawa, saudayawa ya kan suma a cikin salla, wata rana Mansur ya kira shi a wani dare. Sai mai hidima ya ce: na same shi a cikin dakinsa sai na samu ya sanya kumatunsa a kasa yana mai kaskantar da kai yana addu'a, duk fuskarsa da kumatunsa sun yi kura.
Ya kasance mai yawan kyauta, mai kyawawan halaye, mai taushin magana, mai kyawun mazauni, da kyawun zamantakewa.