Imam Husain (A.S)
  • Take: Imam Husain (A.S)
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 5:57:57 13-7-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Husain Shahidi (a.s) shi ne Imami Na Uku: Imam Husain Shahidi (a.s) Dan Ali
Sunansa da Nasabarsa: Al-Husaini dan Ali dan Abi Dalib dan Abdul Mudallib. Babarsa: Fadima 'yar Manzon Allah (s.a.w). Alkunyarsa: Abu Abdullahi. Lakabobinsa: Arrashid, Addayyib, Assayyid, Azzakiyyi, Almubarak, Attabi'i limardatil-Lah, Addalil ala zatil-Lah, Assibd, Sayyidi shababi Ahlil Janna, Sayyidus-Shuhada'u, Abul ayimma.
Tarihin haihuwarsa: 3 Sha'aban 4 H, ko 5 Sha'aban. Inda aka haife shi: Madina. Yakokinsa: Ya yi tarayya da babansa a yakin Jamal da Siffaini da Naharawan kuma shi ne jagoran Askarawan Rundunar Alkawari da imani masu tsanani a kan kafirai da mabiya bata a al'amarin kisan kare dangi da aka yi wa Ahlul Baiti (a.s) a Karbala.
Matansa: 1-Shazinan 'yar kisra 2-Laila 'yar Murra Assakafiyya 3-Ummu Ja'afar Al-kada'iyya 4-Arribab 'yar Imri'ul Kais Al-kalbiyya 5-Ummu Ishak 'yar Dalha Attaimiyya.
'Ya'yansa: 1-Ali Akbar 2-Ali Asgar 3-Ja'afar 4-Abdullahi Addari'i 5-Sakina 6-Fadima.
Tambarin zobensa: Likulli ajalin kitab. Tsawon rayuwarsa: shekara 57. Tsawon Imamancinsa: shekara 11. Sarakunan zamaninsa: Mu'awiya da Dansa Yazid. Tarihin shahadarsa: 10 Muharram 61H. Inda ya yi shahada: Karbala.
Dalilin shahadarsa: An kashe shi yana mai kare addinin kakansa Muhammad (s.a.w) a gumurzun dauki ba dadin nan na Karbala a kan rundunar fasiki Yazid. Inda aka binne shi: Karbala.
Shi ne Husain dan Ali dan Abu Dalib (A.S) kuma babarsa Fadima 'yar Muhammad (S.A.W) kuma shi ne jikan manzon Allah kuma halifansa na uku, kuma baban imamai tara bayansa, kuma shugaban mutane bayan dan'uwansa Imam Hasan (A.S).
An haife shi a Madina mai haske uku ga watan sha'aba na shekara ta hudu bayan hijira, kuma an kashe shi abin zalunta da takobi a hannun bani umayyawa da umarin Yazid dan Mu'awiya a waki'ar ashura da ta shahara a ranar asabar goma ga watan Muharram, shekara ta sittin da daya daga hijira, ya tsayar da salla a wurin kuma a nan ne aka binne jikinsa mai tsarki da aka yanyanka da takubba tare da wadanda suka yi shahada tare da shi bayan kwana uku da yin shahadarsu. Dansa ne Imam Aliyyu Zainul abidin ya shirya shi ya binne shi inda kabarinsa yake a yanzu a Karbala mai tsarki inda wannan waki'ar ta auku a Karbala.
Falalarsa ba ta ambatuwa saboda yawanta, shi ne kanshin sanyin idanuwan manzon (S.A.W) wanda ya fada game da shi "Husain daga gareni yake kuma ni daga Husain nake" .
Kuma ya fada game da shi da kuma dan'uwansa Hasan (A.S) cewa: "su ne kanshina na duniya" . Kuma mai tsira (S.A.W) ya ce: "Hasan da Husain shugabannin samarin aljanna ne" . kuma ya ce: Hasan da Husain shugabanni ne sun tsaya ko sun zauna" .
Kuma ya kasance mafi sanin mutane kuma mafi bautarsu, ya kasance yana salla raka'a dubu kowane dare kamar babansa Imam Ali (A.S) kuma yan daukar gari a kafadarsa da dare yana raba wa talakawa har sai dai aka ga kufan wajen a bayansa bayan kashe shi, ya kasance mai yawan karimci da kyauta, mai girma da daraja ne, mai yawan hakuri, kuma mai tsanantawa idan aka sabi Allah.
Daga cikin baiwarsa: wani balarabe ya zo wajensa yana mai neman kyauta sai ya ce:
Babu wani yankewa daga kaunarka ko daga
'yancinka, a kofar gidanka majalisin bukata
Kai mai baiwa ne kuma kai madogara ne
Babanka ya kasance mai kashe fasikai
Ba domin abin da na farkonku suka yi ba
Da yanzu dukkaninmu jahannama ce makoma
Sai Imam Husain (A.S) ya ba shi dinare dubu hudu ya ba shi uzuri yana cewa:
Ka karbe ta daga gareni ina mai bayar da uzuri
Ka sani lallai ni mai tausayawa ne a gareka
Da a ce sanda ce ta wayi gari a hannunmu
Da ta zama mai maiko a gareka da maraice
Sai dai rikicewar zamani ma'abocin sabani
Ga shi tafina ta zama mai karancin amfani
Hakika ya raya shari'ar musulunci kuma addinin kakansa (A.S) a duniya da juyin da ba shi da misali ga irinsa a duniya, kai muna iya cewa ya raya dukkan duniya ne gaba daya har zuwa ranar kiyama, kuma shi ne shugaban shahidai, kuma mafificin mutane bayan dan'uwansa (A.S).