Imam Sajjad
  • Take: Imam Sajjad
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 15:6:20 1-10-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Ali Sajjad Dan Husaini (a.s) Imami Na Hudu: Imam Ali Sajjad Dan Husaini (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Aliyyu dan Husaini dan Ali dan abi Dalib (a.s). Babarsa; ita ce Shazinan 'yar Yazdajir dan Shahribar dan Kisra an ce sunta Shahri Banu. Alkunyarsa; Abu Muhammad, Abul Hasan, Abul Husaini, Abul Kasim. Lakabobinsa: Zainul Abidin, Sayyidul Abidin, Assajjad, Zussafanat, Imamul Muminin, Almujtahid, Azzahid, Al'amin, Azzakiyyi. Tarihin haihuwarsa: 5 Sha'aban 38 H. a wata ruwaya 15 Jimada Akhir.
Inda aka haife shi: Madina. Matansa: An rawaito cewa ya auri mata bakwai, Ta farko ita ce: Ummu Abdullahi 'yar Al-Husaini (a.s) amma sauran duk Kuyangi ne.
'Ya'yansa: 1-Imam Bakir (a.s) 2-Abdullahi 3-Al-Hasan 4-Al-Husaini 5-Zaid 6-Umar 7-Al-Husainil Asgar 8-Abdurrahman 9-Sulaiman 10-Ali 11-Muhammad Asgar 12-Khadija 13-Fadima 14-Aliyya 15-Ummu Kulsum.
Tambarin zobensa: Wama taufiki illa bil-Lahi. Littattafansa; Sahifatus sajjadiyya da Risalatul hukuk.
Tsawon rayuwarsa: shekara 57. Tsawon Imamancinsa: Shekara 35. Sarakunan zamaninsa: Mu'awiya da Yazidu dan Mu'awiya, da Mu'awiya dan Yazidu dan Abi Sufyan, da Marwana dan Hakam, da Abdulmalik dan Marwana, da Walida dan Abdulmalik.
Tarihin shahadarsa: An yi sabani a kan hakan amma an ce 12 Muharram ko 18 ko 25 ga Muharram, haka nan shekara an ce 94 ko 95 H. Inda ya yi shahada: Madina.
Dalilin shahadarsa; Guba da aka ba shi a lokacin halifancin Walid dan Abdulmalik. Inda aka binne shi: Makabartar Bakiyya Madina.
Shi ne Imam Ali Zainul'abidin, Sajjad, Sayyidul abidin (A.S) dan Husain, babarsa ita ce Shahar banu 'yar sarki Yazdajir, kuma ana cewa da shi dan masu alheri biyu, saboda fadin Manzo (S.A.W) cewa: Allah yana da masu alheri zababbu biyu daga bayinsa, zababbunsu daga larabawa kuraishawa, daga ajamawa kuwa farisawa, a kan haka ne ma abul aswad ya yi waka yana mai cewa:
Wani saurayi ne tsakanin Kisira da Hashim
Mafi girman wanda aka alakanta masa kamala
An haife shi a Madina mai haske ranar alhamis biyar ga watan sha'aban mai girma a shekara ta talatin da takwas daga hijira, kuma ya yi shahada ta hanyar shan guba ranar asabar ishirin da biyar ga watan Muharram shekara ta casa'in da biyar hijira yana da shekaru hamsin da bakwai kuma dansa Imam Muhammad Bakir (A.S) ne ya shirya janajarsa, kuma ya binne shi gun kabarin amminsa Mujtaba (A.S) a Madina mai haske a Bakiyya.
Ya kasance ba shi da kama a ilimi da ibada da fifiko da tsantseni da taimakon masu rfashi, kuma malamai sun rawaito addu'a da wa'azozi da karamomi da yawa daga gareshi.
Ya kasance yana fita da duhun dare sai ya dauki gari a bayansa kuma da jakunkuna na dinare da dirhami kuma yakan dauki abinci a bayansa ko itace har sai ya zo kofa kofa yana kwankwasawa sannna sai ya ba wa wanda ya fito, ya kasance yana rufe fuskarsa domin kada talaka ya gane shi, yayin da ya mutu sai mutanen Madina suka gane shi suka san cewa shi ne mai raba gari.
Hada da abubuwa da yawa da ayke yi na ba wa maraya da miskinai da raunanan abinci da kuma ci tare da su.
Yana daga kyawawan halayensa (A.S) ya kasance yana kiran masu yi masa hidima kowace shekara sai ya ce: Wanda yake son aure daga cikinku zan aurar da ita, idan tana son a sayar da ita zan sayar da ita, idan tana son 'yanci zan 'yanta ta.
Ya kasance idan mai bara ya zo masa yakan ce: maraba da wanda zai dauki guzuri na zuwa lahira.
Ya kasance daga tsananin tsantsenninsa yana salla a wuni da dare raka'a dubu, idan lokacin salla ya yi sai fatar jikinsa ta tashi kuma ya yi yalo ya rika makyarkyata, kuma daga lakabobinsa akwai mai saba saboda kufai na sujada a goshinsa da tafinsa da gwiwarsa.
Wani mutum ya zage shi wata rana ya gaya masa bakar magana shi kuma (A.S) yana shiru bai yi magana ba, bayan wani lokaci sai ya zo wajen sa, sai mutanen da suke nan suka yi tsammanin ya zo ne ya rama, sai ya karatanta ayar nan: "Da masu hadiye fushi kuma masu rangwame ga mutane kuma Allah yana son masu kyauttawa" .
Sannan sai ya tsaya kan wannan mutumin ya ce: ya dan'uwana ka tsaya a kaina da zu ka ce kaza da kaza, idan abin da ka fada akaina haka ne to ina neman gafarar Allah, amma idan abin da ka fada ba haka ba ne to Allah ya gafarta maka .