Imam Ali
  • Take: Imam Ali
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 6:37:59 13-7-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
IMAM ALI AL-MURTADHA (a.s) Imami Na Farko: Imam Ali Al-Murtada Dan Abi Dalib (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Ali dan Abu Dalib dan Abdulmudall-ibi dan Hashimi dan AbdulManafi. Mahaifiyarsa: Fadima 'yar Asad dan Hashim dan Abdul Manaf Al-kunyarsa: AbulHasan, AbulHusaini, Abus-Sibdaini, Abur Raihanataini, Abuturab. Lakabinsa: Amirulmuminin, Sayyidul muslimin, Imamul muttakin, Ka'idul gurralmuhajjalin, SayyidulAusiya, Sayyidul Arab, Al-Murtada, Ya'asubuddini, Haidar, Al-Anza'al Badin, Asadul-Lahi…
Ranar haihuwarsa: 13 Rajab shekara talatin bayan shekarar giwa wato bayan haihuwar Annabi (s.a.w) da shekara talatin. Inda aka haife shi: Makka cikin Ka'aba.
Yakokinsa: Ya yi tarayya a yakokin Manzo (s.a.w) gaba daya banda yakin Tabuka da Manzo ya umarce shi da ya zauna a Madina domin tafiyar da al'amuranta, amma yakokin da ya jagoranta da kansa a lokacin halifancinsa su ne: Jamal, da Siffaini, da Nahrawan.
Matansa: 1-Fadimatuz Zahra (a.s) 'yar Manzon Allah (a.s) 2-Amama 'yar Abil Asi 3-Ummul banin Alkilabiyya 4-Laila 'yar Mas'ud 5-Asma'u 'yar Amis 6-Assahba'u 'yar Rabi'a (Ummu Habib) 7-Khaula 'yar Ja'afar 8-Ummu Sa'ad 'yar Urwa 9-Makhba'a 'yar Imru'ul Kaisi.
'Ya'yansa: Masu Tarihi sun yi sabani kan yawan 'ya'yansa amma suna tsakanin 25 ne zuwa 33 a ruwayoyi daban-daban, sai dai mu zamu ambaci fitattun cikinsu ne: (1-4) Al-Hasan da Al-Husaini da Zainabul-Kubura da Zainabus-Sugura (a.s) su ne 'ya'yan Zahra (a.s) 5-muhammad Al-ausad 6-Al-Abbas 7-Ja'afar 8-Abdullahi 9-Usman dan Ali 10-Muhammad dan Hanafiyya 11-Muhammad Al-Asgar (Abubakar) 12-Yahaya 13- Umar dan Ali 14-Ummu Hani 15-Maimuna 16-Jumana (Ummu Ja'afar) 17-Nafisa.
Tambarin zobensa: Al-mulku lil-Lahil wahidil kahhar. Tsawon rayuwarsa: Shekar 63. Tsawon Imamancinsa: Shekara 30. Tarihin shahadarsa: 21 Ramalana 40H. Wurin da ya yi shahada: Masallacin Kufa.
Dalilin shahadarsa: Saran takobin nan na la'ananne Abdurrahman dan Maljam yana mai sujada a mihrabin masallacin Kufa. Inda aka binne shi: Yankin Gariyyi a Garin Najaf.
Shi ne Ali dan Abu Dalib (A.S) kuma babarsa ita ce Fadima 'yar Asad (A.S) shi dan ammin Manzon Allah ne kuma mijin 'yarsa kuma wasiyyinsa halifansa a kan mutane bayansa wato; Amirul muminin mahaifin imamai (A.S).
An haife shi a Ka'aba mai girma a Makka ranar juma'a daren sha uku ga watan Rajab bayan shekaru talatin da haihuwar Annabi (S.A.W) kuma ya yi shahada daren juma'a a masallacin Kufa a mihrabi da takobin ibn muljam muradi -daga cikin hawarijawa- wannan kuwa a daren sha tara ga watan Ramadan ne kuma bayan nan da kwana uku ne a daren ishirin da daya na Ramadan ya yi wafati yana da shekaru sittin da uku, Imam Hasan da Husain (A.S) sun shirya janazarsa kuma suka binne shi a Najaf inda kabarinsa yake yanzu da wasiyyarsa (A.S) domin ya kubuta daga sharrin hawarijawa da Hajjaj daga tone kabarinsa, kuma wannan ya amfane shi , kuma Imam Ja'afar Sadik da Imam Musa Kazim (A.S) su ne suka nuna wa mutane inda kabarinsa yake (A.S).
Yana da falaloli da darajoji da ba zasu kirgu ba, ya kasance farkon wanda ya yi imani da Manzon Allah (S.A.W) kuma bai yi shirka da Allah ba koda sau daya, bai yi sujada ga gunki ba, don haka ne ma ake ce wa da shi; Allah ya girmama fuskarsa. Kuma yana tare da nasara a dukkan yakokinsa, bai taba gudu ba koda sau daya, shi mai kai hari ne ba mai gudu ba, bai taba ba wa yaki bayansa ba, bai taba gudu ba, kuma kyakkyawan hukuncinsa ya kai matuka har Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafi iya hukuncinku shi ne Ali (A.S) .
Kuma saboda yawan iliminsa ne Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Ni ne birnin ilimi Ali kuwa shi ne kofarta" . Kuma saboda lizimtarsa ga gaskiya ya ce: "Ali yana tare da gaskiya kuma gaskiya tana tare da Ali" .
Ya kasance mai adalci ne a jagorancinsa ga al'umma, mai rabawa mutane arziki da daidaito, mai nisantar kwadayin duniya. Ya kasance yakan zo Baitulmali sai ya duba abin da ya taru cikinta na zinare da azurfa yana cewa: "ya ke yalo! Ya ke fara! Ku yaudari wanina" . Sannan sai ya rarraba wa mutane har sai babu abin da ya rage, yana tausaya wa miskinai, yana zama da talakawa, yana biyan bukatu, yana fadar gaskiya, yana hukunci da adalci, yana hukunci da abin da Allah ya saukar.
Yana aiwatar da hukunce-hukuncen Allah, yana kuma tafiyar da ayyukan Manzon Allah (S.A.W) har sai da alheri da albarka da yalwa suka mamaye kowa, da dukkan kasashe da dukkan garuruwa.
A takaice, ya kasance kamar Annabi (S.A.W) a dukkan siffofi da kyawawan halaye sai dai a wahayi da annabta, don haka ne Allah ya sanya shi kamar Annabi yake a komai banda annabta kamar yadda ya zo a ayar nan ta mubahala .