WACE CE SAYYIDA FATIMA?
  • Take: WACE CE SAYYIDA FATIMA?
  • marubucin:
  • Source:
  • Ranar Saki: 6:48:10 13-7-1403

Bismillahir Rahamanir Raheem
Wa sallalahu ala Muhammad wa Alihid Dahireen

Ina farin cikin taya al’ummar musulmi baki daya murna da zagayowar watan haihuwar shugaban matan talikai baki daya, kuma shugaban matan Aljanna, ‘yar fiyayyen halitta Manzon Allah Muhammad (S).

Wannan diya ma’abociyar girma da daukaka, wacce Allah ya so ya zabeta ya sanyata ta zama shugaban dukkan matayen talikai baki dayansu duniya da lahira, wato Sayyida Fatima Azzahara (AS), wacce Allah ya sanya ta ta zama tsokar jikin Mahaifinta.

Mahaifinta : Annabi Muhammad (SAWA).
Mijinta : Imam Ali (AS).
Ita Kuma: Uwar Hasan da Husaini (AS).

Sananne abu ne cewa Fatima (as) it ace fiyayyiyar dukkan matayen talikai na zamanininta da na gabanin hakan. Kai! Ita ce fiyayyiya akan dukkanin wata halitta da Allah (T) ya yi ta a matsayin jinsin mace.

Kana iya tabbatar da wannan kuwa, idan ka koma ga wasu ruwayoyi da suke bayani sanka-sanka akan hakan a cikin littafin “Al-Kisal” shafi na 205. A babin da yake bayani akan shugabannin matayen Aljanna guda hudu ne, kuma Sayyida Fatima ‘Yar Manzon Allah Muhammad (S) ita ce fiyayyiyarsu.

In kana bukatar sanin ko wace ce wannan baiwar Allah mai girman daraja, dole ne ka ziyarci littattafan magabata ka karanta ruwayoyin hadisai da aka ruwaito dangane da girma da daraja da fifiko da isan wannan tsarkakakkiyar Uwa, ma’abociyar girma da matsayi da daukaka gami da fifiko matabbaci.

Ya ishe ta girman daraja da matsayi, ruwayar da aka samu daga jikanta Imamu Jafarus-Sadiq (AS), a cikin littafan “Al-Amali” na Sheikh Suduq, shafi na 592. Da kuma Ilalis Shara’ie, shafi na 178, da ke cewa:

“Ba don Amirulmuminin (ALI) ya auri (FATIMA) ba, da bata da abokin gamin aure a duk halittan Allah (T) a duk duniya har izuwa ranar Alkiyama…..”

Kai akwai ruwayar da aka ruwaito daga Shi Imam (AS) din, wacce ta ked a Karin cewa “….Tun daga Annabi Adamu (AS) har abin da ke gabaninsa (tsatsonsa gaba daya, har tashin alkiyama).”

A cikin Littafin Uyun-Akbarir-Ridha (AS), Juzu’I na 1, shafi na 225, an ruwaito Hadisil Qudisi, daga Amintaccen Allah Mala’ika Jibrilu (AS) yace; “Ya Muhammad (S)! Allah wanda girmanSa ya girmama yana cewa; ‘Ba don na halicci Ali (AS) ba, da Fatima (AS) bata da Kufu’I (sa’an aure) a duk doron kasa, tun daga Adamu (AS) har abin da ke gabaninsa.”

In ba ka san ko su waye ‘ya’yanta Sayyida Zahara (SA), sune Imam Hasan da Husaini (AS), wadanda Manzon Allah (S) yake fadi dangane da hakkinsu da darajarsu cewa:

Sune shugabannin samarin Aljanna.
Su shi ne, Shi su ne.
Su ‘ya’yansa ne, daga gare Shi suke, kuma duk abin day a cutar das u yana cutar das hi.
Kuma yake cewa su shugabanni ne a duniya da lahira.
Su jagorori ne (tare da sun rike mukami ko basu rike ba).

In kasan wadannan ‘ya’yan nata, to sai nace maka duk darajarsu da falalarsu da matsayinsu da duk wani girma da Allah (T) ya ba su. to Sayyida Fatima (SA) it ace Uwarsu, kuma ta fi su wannan matsayi da girma da daraja, ta fifita akansu a duk wata falala da daraja.

Imam Husaini (AS) ya na fadi ma ‘yar uwansa Sayyida Zainab (SA) a ranar Ashura cewa:

“…Babana (Ali) shi ne mafi alkairi akaina, Uwata (Fatima) ita ce mafificiya akaina, haka kuma Yayana (Hasan) Shi ne mafi alkairi akaina…..” yana fadan wannan ne a ya yin da yake bata hakuri, akan cewa duk abin nan da taga ya same su a wannan falale na Karbala, wadanda suka fi shi ma makamancin hakan ya samesu.

Kai! An ma samu ruwaya daga Imam Ali (AS) yana cewa: “Fatima Azzahara (SA) ta fi Imamai biyun nan; Hasan da Husaini.”

Haka kuma a cikin “Amali” na Sheikh Suduq: 437, an ruwaito daga Amirulmuminin (AS) ya na cewa: “Alhasan da Husaini sun kasance masu girman falala a Duniya da Lahira, amma kuma Mahaifansu (Ali da Fatima) sun fisu girman Falalar.”

Hakika Allah (T) ya girmama matsayin Sayyida Zahara (SA) a yayin da ya fifita zatinta birbishin na sauran dukkan matayen talikai, kuma ya sanya yunbunta daban da na sauran halittu baki daya baya ga Fiyayyen Halitta Muhammad (SAWA) da Amirulmuminin (AS).

An ruwaito a cikin littafin “As-Siradal Mustaqeem, Juzu’I na 1, shafi na 170, fasali na 5”, daga Annabi Muhammad (S) yana cewa:

“Lokacin da akai Isra’I da Ni, na shiga Aljanna, sai Mala’ika Jibril (AS) ya kawo min ‘Tuffah’ (Apple) na ci, sai ya narke ya zama Maniyi, FATIMA daga wannan (tuffah) din take. Duk lokacin da nai shaukin shakan kamshin Aljanna, nakan fuskanci Fatima (na shaki kamshin daga gareta).”

A cikin wani hadisin kuma daga Annabi (S) ya ce: “Ku sani wannan ‘tuffah (apple) din Allah (T) da kanSa ne ya halicce shi, sannan ya mallaka shi ga Annabinsa a yayin Mi’iraji.” – Tawilul Ayat; 241.

Kaga ita Sayyida Azzahara (SA) an samar da maniyinta ne daga abincin Aljanna. Kuma wani Karin falala ma, sai ya zama Allah (T) da kansa ne ya samar da wannan sinadarin da ya tarce kan cewa ta hanyar sa ne za’a samar da wanann tauraruwa mai albarka.

AMINCIN ALLAH (T) YA TABBATA A GAREKI YA KE SHUGABAR MATAN TALIKAI BAKI DAYA.

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua