Cigaban Rayuwa Bayan Mutuwa
  • Take: Cigaban Rayuwa Bayan Mutuwa
  • marubucin: Ayatullahi Subhani
  • Source:
  • Ranar Saki: 8:56:43 2-10-1403

Cigaban Rayuwa Bayan Mutuwa

 

Ayatullahi Ja'afar Subhani

Mun Tabbatar Da Asali Guda Biyu A Bahsoshin Da Suka Gabata
1-Hakikanin dan Adam shi ne ruhinsa.
2-Mutuwa ba shi ba ne karshen rayuwa, kawai wata kofa ce domin shiga wata duniya, sannan mutum bayan mutuwa zai rayu har abada. Sannan sai asali na uku wanda kuma ya fi sauran muhimmanci a cikin wannan Bahasi, wanda yake shi ne alakar da take akwai tsakanin rayuwar barzahu da rayuwar wannan duniyar. Domin kuwa ana iya yin tunani cewa akwai wani abu wanda ya kare mutane daga gani ko jin abin da yake faruwa a barzahu.
Idan aka tabbatar da wannan asali, zamu iya mantawa da abin da mutanen yammacin duniya suke fada dangane da al'amarin ruhi, domin kuwa mai yiwuwa ya zamana wasu abubuwan da suke fada ba a bin dogara ba ne. Kawai zamu yi Bahasi ne a kan wannan magana tare da amfani da Kur'ani da sunnar Ma'aiki da magadan Manzo (a.s).
Ayoyin Kur'ani zasu yaye mana hijabi, yadda alakar mutane take da wadanda suke rayuwa a barzahu, saboda haka a nan zamu kawo wasu daga cikin wadannan ayoyi da suka yi bayani a kan haka, ta yadda zamu gane ya wannan alaka take tsakanin mu da wadanda suka tsallaka zuwa wata duniya ta hanyar gadar mutuwa, kuma ta yaya ne har yanzu alakarmu da su ba ta yanke ba. (Duk da cewa wannan al'amari koda bai hade kowane mutum ba, amma tabbas akwai wadanda suke da wannan alakar).
1- Salih (a.s) yana magana da ruhin mutanensa
Ayoyin da suke ba da sheda a kan yadda mutane suke da alaka da mutanen da suka wuce, wannan aya mai zuwa tana nuna mana yadda Annabi Salih yake magana da mutanensa wadanda aka hallakar, yana cewa: "Suka soke taguwa suka saba umurnin ubangijinsu, sannan suka ce: Ya Salihu idan har kai annabi ne to ka zo mana da azabar da kake yi mana alkawari da ita". "Sai girgizar kasa ta kama su sakamakon tsawar da Allah ya yi musu, suka wayi gari a cikin gidajensu a mace". "A wannan lokaci sai ya nisance su, kuma ya ce musu yaku mutane lallai na isar muku da sakon Allah, sannan na yi muku nasiha amma ba ku son nasiha". A kula da kyau dangane da abin da wadannan ayoyi guda biyu suke magana a kansa:
Aya ta farko tana nuni a kan yadda mutanen annabi Nuhu (a.s) suka roki a aiko musu da azaba. Aya ta biyu kuwa tana nuni a kan zuwan azaba da yadda suka halaka. Aya ta uku kuwa tana nuni ne a kan yadda Annabi Salihu (a.s) ya yi kira ga mutanensa bayan sun halaka, inda yake ce musu: Na isar da sakon Allah amma kun kasance ba ku son mai nasiha. Abin da kuwa yake nuni da cewa Annabi Salihu (a.s) ya yi magana da mutanensa bayan sun mutu abubuwa ne guda uku kamar haka:
1-Tsarin yadda ayoyin suka zo.
2-Harafin "fa" da ya zo a kalmar "fatawalla" wanda yake nuni a kan jeri, wato wannan kalma tana ba da ma'ana a kan kasantuwar abu daga wannan sai wannan wato bayan halakarsu, sai ya juya fuskarsa ya ce musu:
3- "Sai dai ku ba ku son mai nasiha". Wannan yana nuna yadda suka yi nisa a wajen bijirewa Ubangiji, wanda bayan mutuwarsu ma suna da wannan siffa ta yadda ba su son mai fada musu gaskiya.
Wannan aya tana nuna yana magana ne da ruhunan mutanensa, sannan ya nuna bayan mutuwarsu ma suna cikin wannan hali na suna rashin son nasiha.
Tambaya: Maganar da annabi Salihu ya yi ba wai yana nufin da gaske yake ba, kawai yana magana ne kamar yadda mawaka sukan yi da bango ko kofa?
Amsa: Idan mutum ya yi amfani da halin da yake a ciki yayin da ya yi wannan magana, sannan sai ya ce, ai Annabi Salihu ya yi magana ne kamar yadda mawaki yake magana da kofa da bango, to lallai mutum ya yi tafsiri ne kawai da ra'ayinsa, sannan wannan tafsiri bai inganta kuma kuskure ne a bayyane. Hakikanin tafsiri da ra'ayi shi ne mutum kafin ya fassara wata aya ya zamana yana da wata akida, saboda ya kare wannan akidar tasa sai ya yi tawilin zahirin aya ta yadda zata yi dai-dai da akidarsa, domin kuwa wanda yake da wannan ra'ayi saboda ba shi da imani da alakar da take akwai tsakanin wannan duniyar da rayuwar barzahu, babu makawa sai ya yi irin wannan tafsiri.
Manzo (s.a.w) ya yi magana a kan wadanda suke irin wannan aiki yana cewa: "Duk wanda ya fassara Kur'ani da ra'ayinsa, to ya tanaji wurin zamansa a cikin wuta".
Tambaya: Annabi Salihu ya yi magana ne da mutanen da suka yi saura, wato wadanda suka yi imani da shi, sakamakon haka ne suka tsira.
Tsammanin haka mai rauni ne, sannan ba shi da ma'ana, domin idan yana magana ne da masu imani wadanda suka yi saura daga cikin mutanensa, to me ya sa a gaba yake cewa: Sai dai ku ba ku son nasiha".
2- Shu'aib, inda yake magana da ruhin mutanensa
"Girgizar kasa ta kama su, suka wayi gari a cikin gidajensu suna halakakku". "Su ne wadanda suka karyata Shu'aibu sun kasance kamar ba su rayuwa ba a ciki, Wadanda suka karyata Shu'aibu sun kasance sun yi asara". "Sai ya juya musu sai ya ce: Yaku mutane ku sani na isar muku da sakon Ubangiji, sannan na yi muku nasiha, to yaya zan ji tausan mutanen da suke kafirai"? Yanayin kafa hujja da wannan aya ya yi yanayi daya da yadda aka kafa hujja da shi a cikin magana a kan Salihu (a.s).
3-Manzo (s.a.w) ya kasance yana magana da ruhin annabawa
"Ka tambayi wadanda muka aika kafinka daga manzanimmu, shin mun sanya wani bayan Rahaman a matsayin abin bauta"? Zahirin wannan aya tana nuna cewa Manzo yana iya magana da annabawan da suka gabata, kuma suke rayuwa a wata duniya, ta yadda zai tambaye su, ta yadda yana nuna rashin hanuwa a kan hakan ta hanyar hankali, saboda haka babu wani dalili da zai sanyamu ki yin amfani da zahirin wannan aya.
Tambaya: Abin da ake nufi da wannan aya shi ne ana tambayar yahudawa da nasara ne, kamar yadda a wata aya yake cewa: "Idan kana shakku a kan abin da muka aiko maka, ka tambayi wadanda suke karanta littafin da aka saukar kafinka, tabbas gaskiya ta zo maka daga ubangijinka".
Amsa: wanann tsammani yana da rauni kwarai da gaske saboda:
Na farko: Tafsirin aya da wata aya yana zama daidai yayin da aya ta farko ta zamanto ba a bayyane take ba, amma idan ayar ta kasance ba ta da wani kokwanto ko rashin bayyana, ba bu wani dalili da zai sanya a dauki hannu daga zahirinta a yi tawilinta, ta yadda zamu ce: ai ma'ana shi ne a nan tambaya ne ga malaman yahudu da nasara, domin kuwa babu wani wanda zai hana Manzo ya tambayi dukkan wannan gungu guda biyu, domin kuwa musamman aya ta farko tana magana ne da Manzo in da take nuna cewa ya tambayi annabawan da suka gabata, amma aya ta biyu tana magana ne da al'ummar Manzo inda take nuna su tambayi malaman yahudu da nasara.
Sannan abin da yake shaidawa a kan wannan ma'ana a bayyane shi ne, Allah madaukaki ya sanya hanyoyi guda biyu a gaban Manzo (s.a.w) a aya ta uku mai zuwa inda take nuna hanya ta uku yana cewa:
"Kuma lallai mun bai wa Musa (a.s) alamomi guda tara bayyanannu, sannan ka tambayi Bani Isra'ila yayin da ya zo Musa ya zo musu, sai Fir'auna ya ce masa lallai Musa ina ganinka dandabo". A cikin wannan aya maganar ta zo ne daga su Bani Isra'il ba wai wasu gungun malamai ba wadanda suke karanta littafai. Saboda haka ba tare da wata hujja ba babu yadda zamu yi tawili dangane da aya ta uku.
Na biyu: Aya ta farko tana nufin cewa a tambayi dukkan annabawa da suka gabata, hada da Nuhu da Ibrahim… Amma aya ta biyu kuwa tana magana ne a kan malaman yahudu da nasara, ta yadda ta hanyar karatun da suke suna iya amsa tambayar Manzo dangane da umurnin da Allah ya bai wa manzanninsu, ta yadda zasu gabatar da wannan ga Manzo da al'ummarsa. Saboda haka a nan ba mu da hakkin da zamu takaita ma'anar wannan aya ta farko ga malaman yahudu da nasara kawai. Wato; alkawarinsu ya takaita ne kawai ga annabawansu ba hada ba da sauran annabawa.
Na uku: Aya da ake magana a kanta, ta zone a cikin surar Zukhruf, wannan sura kuwa kamar yadda malaman tafsiri suka hadu a kan cewa ta sauka ne Makka, haka nan ma'anarta ma tana tabbatar da hakan. Saboda haka a garin Makka a wannan lokaci babu wasu malaman yahudu da nasara ko wasu gungun mutane masu yawa ta yadda Manzo zai tambaye su.
Rayuwar Barzahu A Cikin Hadisai
Bahasimmu a cikin Kur'ani dangane da wannan magana ya kawo karshe. Alakar kuwa da take akwai tsakanin wannan duniyar da duniyar barzahu hadisai da dama sun zo da bayanin hakan, saboda haka a nan saboda mu takaita zamu wadatu da wasu tabbatattun hadisai a matsayin misali a kan hakan:
1-Manzo (s.a.w) ya yi magana da wadanda aka kashe a yakin "Badar"
Bayan yakin Badr ya kawo karshe, a lokacin kafiran kuraishawa aka kashe musu mutum saba'in aka kuma kama wasu saba'in din a matsayin bursunonin yaki, saura kuwa suka ranta a cikin na kare. Manzo mai girma (s.a.w) ya bayar da umarni, aka zuba wadanda a kashe daga kuraishawa a cikin wata rijiya, a lokacin da a ka zuba su a cikin rijiya sai Manzo ya kira kowane daya bayan daya da sunansa ya ce: Ya kai Utba, Shaiba, Umayya, Abu Jahl…shin kun samu abin da Allah ya yi muku alkawari?! Ni kam na samu abin da Allah ya yi mini alkawari ya kasance kuma gaskiyane. A wannan lokaci sai sai wasu gungu daga cikin musulmai suka ce wa Manzo, kana kiran wadanda suka mutu ne?! Sai Manzo ya amsa da cewa: Ai ba ki fi su jiba Amma su ba su iya amsawa.
Ibn Hisham yana cewa: A lokacin nan sai Manzo ya kira wadanda aka kashe daga kafiran kuraishawa ya ce: Ku wadan ne irin mummunan dangi kuka kasance ga Manzo?! Kuka karyata ni, a lokacin da wasu suka gasgata ni, lokacin da wasu suka ba ni mafaka, amma ku kuka yake ni, amma sai wasu suka taimake ni. Shin abin da Allah ya yi muku alkawari kun same shi?!
Wannan magana da Manzo ya yi da wadanda aka kashe daga cikin kafiran kuraishawa wani abu wanda dukkan bangarori guda biyu suka kawo, wato malaman Shi'a da Sunna sun ruwaito wannan al'amari. Sannan a kan wannan zamani ma sun ruwaito wannan abu a cikin wakokinsu.
Hassan Bn Sabit ya kasance daya daga cikin mawakan wannan zamanin da aka aiko Manzo (s.a.w) wanda yake bayyanar da abubuwa ta hanyar waka a wannan lokaci, sannan ta haka ne ya kasance yana taimakon musulunci da musulmi. Sannan kuma zuwa yanzu an buga diwaninsa, sannan a cikin wannan diwani nasa ya yi magana dangane da yakin Badr a cikinta akwai bayani wannan abin da muke magana a kan shi. Ga abin da yake cewa a cikn wannan kasida ta shi:
"Lokacin da muka saka a cikin rijiya bakin dayansu, sai Manzo ya ce musu: Shin ba ku sadu da maganata ba a matsayin gaskiya, ta yadda umarnin Ubangiji yake kama har zukata. A lokacin ba su yi magana ba, da a ce zasu iya yin magana, zasu ba da amsa ne da cewa: Gaskiya abin da kake fada shi ne dai-dai.
Babu wata jumla wacce tafi wannan jumla wajen bayyanar da wannan al'amariin da yake cewa: Ai ba ku fi su ji ba, sai dai su ba su iya amsawa. babu wani bayani da zai fi wannan bayyana, ta yadda Manzo ya kira daya bayan dayansu da sunansa, sannan ya yi magana da su kamar lokacin da suke a raye.
Babu wani musulmi da zai yi inkarin wannan alma'ari wanda yake a cikin tarihi saboda wata akida ta shi da ta yi rigaye, ta yadda zai iya cewa ai tunda wannan al'amari bai yi dai-dai da wannan karamin hankalin nawa ba to bai inganta ba!
Ga Matanin abin da Manzo yake cewa: Yayin da aka jefa su a cikin rijiya, sai Manzo (s.a.w) ya ce: "Ya ku ma'abuta kafirci sun kun sami abin da Allah ya yi muku alakwari da shi gaskiyane? Lallai na sami abin da Allah ya yi mini alkawari da shi gaskiya ne, sai sahabbansa suka ce masa: Ya manzon Allah kana magana ne da mutanen da suka mutu? Sai ya amsa musu da cewa: Lalli sun gane abin da Allah ya yi musu alkawari da shi gaskiya ne…"
2-Lakanta wa mamaci kalamomin shahada
Lakantawa mamaci kalmomin shahada wanda muka yi maganarsa a baya, bayan nuninsa ga cewa mamaci bayan ya bar duniya yana ci gaba da rayuwa ta har abada, yana kuma nuna alakarmu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Batun alakar da take akwai da wadanda suka mutu kasancewar wani abu ne bayyane, kamar yadda Bukhari yake ruwaitowa daga Anas Bn malik daga Manzo (s.a.w) cewa; wanda aka rufe yana jin karar takalman wadanda suke kai shi kabari.
Sannan maganganun Abubakar da Imam Ali (a.s) zuwa ga Manzo (s.a.w) yayin da ya yi wafati yana daga cikin abin da yake tabbatar da samuwar alaka tsakanin mutum da wata duniya ta daban.
Ibn Hisham yana rubutawa a cikin littafinsa na tarihi: Lokacin da Manzo (s.a.w) ya yi wafati, abubukar ya zo a kan shinfidar mutuwarsa ya yaye abin da aka rufe fuskarsa da shi ya sumba ce shi, sannan ya ce masa: Ubana da Uwata fansa gareka, amma dangane da mutuwar da Allah ya rubuta maka yanzu ka hadu da ita, amma ba zaka sake haduwa da mutuwa ba. Sannan ya sake rufe fuskar Manzo (s.a.w)
Haka nan lokacin da Manzo ya yi wafati, bayan Imam Ali (a.s) ya yi masa wanka ga abin da yake ce masa: Ubana da uwata fansa a gareka! Tare da mutuwarka wahayi da manzanci wanda sakamakon mutuwar wani ba ya yankewa amma yanzu ya yanke. Saboda haka tunda yanzu babu shi sai mu ci gaba da hakuri wanda ka kasance kana kirammu zuwa gare shi a kan abubuwan da ba su da dadi, kamar yadda na zubar da hawaye dangane da mutuwarka har ta kasance kwalla sun bushe daga inda suke bubbugowa. Amma bakin cikimmu a kan wannan hanya zai ci gaba. Uwa da uba fansarka ya Manzo! ka kasance kana tunawa da a wata duniyar ta daban. !
Wace jumla ta fi wannan bayyana inda Imam yake cewa ka tuna da mu a wajen Ubangiji ka kula da mu.
Wannan hadisi da kuma wasu hadisai masu yawa suna bayyana mana yadda mutum yake da alaka da wata duniya kuma wannan alakar tana ci gaba.
Rayuwar Barzahu A Bakin Malaman Hadisi Da Fikihu
Rayuwar barzahu tana daga cikin tushen akidar al'ummar musulmin duniya, Sannan manyan malamai wadanda suka yi rubutu a kan akida sun kawo wannan magana a cikin littafansu, sannan mu dauki wannan magana ta rayuwar barzahu wani abu ne wanda aka sallama a kansa. A nan kasa zamu yi nuni da wasu daga cikin maganganun wasu malamai da suka yi a kan hakan:
1-Ahmad Bn Hambal yana cewa: Azabar kabari gaskiya ce, Sannan zatambayi mutum a kan addini da Ubangijinsa, Sannan zai ga makomarsa aljanna ce ko wuta a cikin rayuwar barzahu. Sannan tamabayar kabari wacce mala'iku guda biyu zasu gabatar gakiya ce.
2-Abu Ja'afar Dahawi (ya rasu a shekara ta 321) yana rubuta cewa: Mu mun yi imani da azabar kabari dangane da wanda ya cancanci hakan, haka nan dangane da tambayar da mala'iku guda biyu zasu yi wa mamaci a cikin kabari, dangane da Allah, addini da annabi, kamar yadda ya zo daga Manzo (s.a.w)
3-Abu hasan al-ash'ari (ya rasu a shekara ta 324) yana rubutawa a wata risala da ya yi dangane da akida, yana cewa: Mun yi imani da azabar kabari, tafkin alkausara, da mizani, siradi, tayar da matattu.
4-Bazdawi (ya rasu a shekara ta 331Bh) yana rubuta cewa: Tambayar kabari gaskiya ga AhlusSunna sannan mumini yana iya amsa wannan tambaya.
5-Imam razi a cikin tafsirin ayar da take cewa"suna albishir ga wadanda ba su riske su ba) yana ccewa: wannan tana ba da sheda a kan rayuwar mamaci a barzahu kafin ranar tashin kiyama. Haka Manzo yana cewa: Kabari lambu ne daga cikin lambunan aljanna, ko kuma rijiya ce daga cikin rijiyoyin gidan wuta, wannan shi ma wani dalili ne a kan hakan.
Sannan yana karawa da cewa: Hadisan da suka zo dangane da tambaya da azabar kabari kusan mutawatirai ne.
6-Ibn Taimiyya (ya rasu ashekara 726) yana cewa akwai hadisai ingantattu wadanda suke nuni da dawowar rai yayin tambayar kabari.
7-Taftazani (ya rasu a shekara ta 791) yana cewa wadannan ayoyin na kasa suna nuni ga rayuwar barzahu su ne kamar:
A- "Ana bijiro wa mutanen Fir'auna da wuta a gare su safiya da yamma".
B- "Mutanen Nuhu sakamakon laifinsu suka nutse a cikin ruwa sannan aka shigar da su cikin azaba".
C- Ya Ubangiji ka kasha su sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu".
Rayawa ta farko ita ce bayan mutuwa a cikin kabari, rayawa ta biyu kuwa ita ce bayan busa kaho. Wato; dukkan wadanda suke rayuwa a barzahu zasu rasu kafin ranar kiyama, sannan zasu rayu bayan busa kahon kiyama.
A nan mun kawo maganganun mashahuran Malaman Ahlus-Sunna dangane da wannan magana. Dangane da malaman Shi'a kuwa wannan wani abu ne wanda yake an sallama a kan ingancinsa. Sannan ya wadatar don kuwa misalin Sheikh Saduk da Sheikh Mufid duk sun rubuta wannan a cikin akidojin Shi'a.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, May 21, 2012