Hakikan Mutuwa
Ayatullahi Ja'afar Subhani
Ya bayyana cewa hakikanin mutum ba jiki ba ne, sannan sakamakon kasantuwarsa ya nisanta daga duk wasu siffofi na jiki (kamar abin da ya shafi lalacewa, rarrabuwa, da makamantansu) zai kasance wanzanje tare da izinin Ubangiji bayan mutuwar jiki. Daga wannan abin da muka fada a sama zamu iya fahimtar ma'anar mutuwa, domin kuwa hakikanin mutum shi ne ruhinsa wanda yake madawwami. Hakikanin mutuwa ba wani abu ba ne sai rabuwar ruhi da jiki sakamakon wasu sharudda da suke faruwa. Wato ruhin mutum zai kai wani mataki na kammala wanda ba ya bukatar jiki, wato zai kai wani mataki wanda zai iya ci gaba da rayuwar da ta dace da shi ba tare da jiki ba.
Kasantuwar ruhi bayan mutuwa wani abu ne wanda aka tabbatar a cikin falsafa da ilimin kimiyya, manyan malaman falsafa kamar su Sukrat, Filato da Aristo duk sun tabbar da wanzuwar rai bayan mutuwa a cikin falsafar Kasar Girki. Haka Ibn Sina da shehul Ishrak da Sadrul muta'allihin wadanda suke masana falsafa ne na duniyar musulunci duk sun tabbatar da wannan al'amari ta hanyar dalilan hankali. Sannan yau a kasashen yammacin duniya an sanya shi cikin abin da ake bincike a cikin ilimin kimiyya.
Idan a karni na sha tara an karkata zuwa ga wannan duniya ta jiki, da mantawa da abin da yake bayan wannan duniyar kamar Allah, mala'ika da ruhi, da sauran abubuwan da suke a duniyar gaibu, ta yadda suke shakku a kan samuwarsu. Amma farkon karni na ashirin koma kafin nan sakamakon kokarin wasu wadanda suke da imani da samuwar wannan duniya sun sake bude wata sabuwar kofa ta shiga wannan duniya ta gaibu. Ta yadda duniyar ruhi da wanzuwarsa bayan mutuwa ta samu karbuwa wanda muka yi bayani kamar yadda aka gani a bahsimmu da ya gabata.
Kur'ani Da Wanzuwar Ruhi
Kamar yadda ya zamana tushen bincikemmu a wannan magana shi ne Kur'ani da hadisan Manzo da magadnsa Ahlul baiti (a.s) dan haka tare da amfani da wadannan dalilai zamu ci gaba da binckemmu a kan wannan magana.
Ayoyi da dama a cikin Kur'ani suna bayar da sheda a kan cigaban rayuwa bayan mutuwa wadanda ba zamu iya kawo dukkansu ba a cikin wannan 'yar karamar kasida, saboda haka zamu takaita da kawo wasu daga cikinsu a matsayin misali:
1-Shahidai a tafarkin Allah:
Ayoyi da dama a cikin Kur'ani suna ba da shedar cewa shahidai zasu ci gaba da rayuwa bayan tsallaka gadar mutuwa da suka yi, saboda haka zamu yi nuni da ayoyi uku da suka yi magana a kan hakan:
A- "Kada ku ce wa wanda aka kashe a tafarkin Allah matacce, domin kuwa rayayye ne, sai dai kune ba ku fahimtar hakan".
Ba tare da kula da jumlar "sai dai ku ne ba ku fahimta ba" wacce ta zo a cikin wannan aya, zai iya yiwuwa a yi tunanin cewa ana nufin rayuwarsu ta zamantakewa, domin kuwa kasantuwar sadaukantarwar da suka yi, zai zamana kodayaushe suna raye a cikin zukatan al'umma, ta yadda kodayaushe za a rika tunawa da sunayensu, sannan sadaukarwarsu zata zama rubutun zinari a cikin Littattafan tarihi. Amma abin da ya zo bayan wannan aya yana kore wannan tunanin, domin kuwa idan da ana nufin rayuwarsu ta hanyar tunawa da su da ake yi a cikin al'umma, wannan ba zai zama wani boyayyen abu ba ga al'umma wanda sai Allah madaukaki ya ce, "sai dai ku ne ba ku fahimta"domin kuwa wannan rayuwar kowane mutum yana iya fahimtar hakan.
B-"Kada ku yi tsammanin wanda aka kashe a tafarkin Allah ya mutu, domin kuwa rayayye ne ana azurta shi a wajen Ubangiji".
C-Suna farin ciki da abin da Allah ya ba su na daga falala, kuma suna albishir ga wadanda ba su riske su ba wadanda zasu daga baya, da cewa kada su ji tsoro ko bakin ciki". "Suna albishir da abin da Allah ya yi musu ni'ima da shi na falala, kuma lallai Allah ba ya tauye ladan muminai".
Wadannan ayoyi na sama suna daraja ta musamman wajen bayyana wannan ma'ana. A cikin wadannan ayoyi ba kawai Allah ya nuna cewa Shahidai suna raye ba ne, ya nuna yadda suke amfanuwa da abubuwan rayuwa, domin kuwa ya nuna yana azurta su kuma sunacikin farin ciki, wanda wannan ya nuna abubuwan da suke nuna rayuwar mutum ta jiki da ta ruhi.
2-Muminin da ya yi magana bayan mutuwa cikin surar Yasin: Annabi Isa (a.s) ya tura wasu mutane guda uku zuwa wani gari domin su isar da sakon Allah. sai mutanen wannan gari suka yi inkarin wadannan mutane, sai wani mutum guda kawai daga cikin mutanen wannan gari ya karba wannan kira, sai kuwa mutanen wannan gida suka yo ca a kansa, bayan sun kashe shi ga abin da yake cewa:
"Ni na yi imani da ubangijinku, ku saurare ni. Sai aka ce ma sa ka shiga al'janna, sai ya ce ina ma mutanena sun sani. Dangane da gafarar da Allah ya yi mini, sannan ya sanya ni a cikin manyan mutane".
Abin da kuwa ake nufi da wannan aljanna wacce aka shigar da shi, aljannace ta barzahu, ba wai aljannar da za a shiga ba a ranar kiyama, wannan kuwa ana iya gane shi ta hanyar abin da yake fata yana cewa ina ma mutanena sun san gafarar da Allah ya yi mini ya kuma sanya ni cikin manyan mutane. Wannan fata tashi ba tana nuna cewa ba mutanensa sun san halin da yake ciki kamar yadda yake a lahira ana yaye duk wani hijabi ga mutane, ta yadda kowa zai san halin da kowa yake, Saboda haka wannan rashin sanin halin da mutum yake ciki a lahira yana faruwa ne a wannan duniya, ta yadda mutanen wannan duniyar ba su san abin da yake faruwa ba a waccan duniyar, sannan ayoyi da dama suna bayyana wannan ma'ana.
Bayan wannan abin da muka yi bayani a baya, ayoyin da zamu ambata a nan gaba zasu bayyana mana cewa bayan mutuwa da gafarta masa bayan ya shiga aljanna, zai zamana fitilar rayuwar mutanensa zata mutu sakamakon wata tsawa daga sama, Kamar yadda Kur'ani yake cewa: "Ba mu aiko wa mutanensa runduna daga sama ba bayan rasuwarsa, kuma ba zamu yi hakan ba. Babu wani abu da ya kasance sai tsawar bazata sai ga su dukkansu suka kasance matattu".
Wadannan ayoyi guda biyu da muka ambata a sama suna nuna mana cewa, bayan shahadarsa da shiga aljannarsa, mutanensa sun kasance suna rayuwa a cikin wannan duniya kwatsam sai mutuwa ta riske su, saboda haka wannan aljanna da ake ambata a baya ba wata aljanna ba ce sai aljannar barzahu.
3-Za a gabatar da Fir'auna da mutanensa ga wuta
Za a gabatar da Fir'auna da mutanensa ga wuta safiya da marece, Sannan lokacin da kiyama ta tsaya za a ce musu ya ku mutanen Fir'auna ku shiga cikin matsananciyar azaba".
Tare da kula da bangarori guda biyu na wannan aya zamu iya fahimtar kasantuwar Fir'auna da mutanensa a cikin rayuwar Barzahu, kamar haka:
Kafin zuwan ranar kiyama sun kasance ana bijiro su ga wuta safiya da yamma, Sannan bayan kiyama ta tsaya za a shigar da su a cikin matsananciyar azaba.
Idan da bangare na biyun wannan aya bai zo ba (Sannan ranar kiyama za a shigar da su cikin matsananciyar azaba) da ba za iya fahimtar haka da sauki ba, amma tare da kula da wannan bangare na aya, zai bayyanar mana da cewa akwai azaba a barzahu, domin kuwa idan ba haka ba ne babu ma'anar a kawo batun cewa sannan idan kiyama ta tsaya za a shigar da su azaba mai tsanani.
4-Mutanenn Annabi Nuhu Sun Shiga Cikin Azaba Bayan An Nutsar Da Su A Cikin Ruwa
"Sakamakon kura-kuren da suka yi aka nutsar da su a cikin ruwa, sakamakon haka ne suka shiga a cikin wuta, sannan ba su samu wani ba sabanin Allah wanda zai taimaka musu".
Mai yiwuwa a yi tunanin cewa mai yiwuwa saboda shigarsu wuta wani abu ne wanda babu shakku a cikinsa shi ya sa aka yi amfani da shudadden aiki, wato aka ce sai aka shigar da su a cikin wuta. Amma wannan fassara sakamakon rashin dalili a kan yinta kuma ta saba wa zahirin ayar.
Domin kuwa da ana nufin cewa sai ranar kiyama ne zasu shiga cikin wuta, wato tsakanin nutsewarsu da shiga wutar, wato da an yi nuni da hakan kamar a ce; sannan zasu shiga wuta, amma ba a yi nuni da hakan ba.
Sannan kuma dole mu yi tawili a inda ake cewa, "sannan ba su sami wanda zai taimaka musu ba"wato sai mu yi tawili da cewa tunda wannan al'amari haka zai faru shi ya sa aka yi amfani da lokacin da ya wuce a cikin wannan jumla, wannan tawili kuwa ba shi da wani dalili, don haka wannan tawili ba ya inganta a nan.
Saboda haka a nan zamu wadatu da wannan, don mu kauce wa tsawaitawa a kan haka sai mu yi cikakken bayani a inda ya dace.
Rayuwar Barzahu A Cikin Hadisi
Dukkan abin da muka ambata dangane da abin da ya shafi rayuwar barzahu daga Kur'ani mai girma yake, amma a cikin maganganun Manzo da Ma'asumai (a.s) an yi cikakken bayani a kan hakan, wanda a kan haka manene a ka kebance babi-babi a kan bayanin rayuwar barzahu a cikin Littattafan hadisi da na akida. Saboda haka a nan zamu tsakuro wani abu ne daga cikinsu a matsayin misali:
1-Manzo (s.a.w) ya kasance a karshen rayuwarsa yakan ziyarci makabartar baki, sannan yakan yi magana da mutanen da suke rufe a wannan makabarta kamar haka:
"Amincin Allah ya tabbata a gareku ya gidan muminai, kun kasance kun rigaye mu, amma muma munanan zamu riske ku, kuma muna yi muku murna a kan ni'imar da kuke a cikinta".
2-Lakantawa mamaci kalmomi da ake yi yana daga cikin abubuwan da aka sallama a kansu a cikin fikihun musulunci. Sannan wannan yana nuna wani nau'in rayuwa da mamaci yake a cikinta, Mai lakanta wa mamaci yakan yi amfani da sunansa da siffofinsa yana kiransa da murya sama, yayin da yake cewa, yayin da mala'ikun mutuwa suka zo maka daga Allah, sannan suka tambaye ka dangane da Ubangiji da addini da annabinka da imamai, sai ka ce musu: "Na yarda da Allah a matsayin ubangijina, sannan na yarda da musulunci a matsayin addinina, kuma na yarda da Muhammad (s.a.w) a matsayin annabina, kuma na yarda da Ali (a.s) a matsayin Imamina.
Dukkan wannan yana nuni ne da cewa mutuwa ba wani abu ba ne sai kawai fita daga wannan duniyar da shiga wata sabuwar duniya, ta yadda mamaci a waccan duniyar yana ji yana gani kamar yadda yake a wannan duniyar, harma yakan yi magana da magadansa.
A nan kawai zamu wadatu ne da fassarar lakantawar da AhlusSunna suka kawo a cikin littafansu kamar haka:
Marubucin (al-fikhu ala mazahibul arba'a) yana rubuta cewa; mustahabbi ne bayan an rufe mutum kuma an baje kasar kabarinsa a lakanta masa wadannan kalmomin da zasu zo a kasa, mai lakanta wadannan kalmomi dole ya ambaci sunan mamaci da sunan mahaifiyarsa, idan kuwa bai san sunan mahaifiyarsa ba sai ya ambaci sunan 'Hauwa'sannan sai ya kira shi ya ce: ka tuna da alkawarin da ka bar duniya da shi, wannan kuwa shi ne shedawa da cewa Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, sannan da shedawa da manzancin Manzo Muhammad (s.a.w) Sannan ka sheda da cewa aljanna da azabar lahira gaskiya ne, sannan ka sheda da cewa kiyama zata tsaya, sannan Allah madaukaki zai tayar da kowa, kuma ka yi imani da Allah da gaskiyar addinin musulunci, sannan ka amince da Manzo Muhammad da Kur'ani mai girma, sannan ka yarda da alkiblar ka'aba, da imani da 'yan'uwantakar sauran muminai.
Sannan Gazali a cikin Ihya'ul ulum yana cewa: mustahabbi ne a yi wa mutum talkini yayin da ya rasu. Sannan sai ya ruwaito wannan hadisi kamar haka:
"Sa'id Bn Abdullah yana cewa, a lokacin da Abu Imam Bahili zai rasu na kasance a bisa shinfidarsa, sai ya yi mini wasiyya da cewa, kamar yadda Manzo ya yi umarni, in yi masa "talkini" yayin da ya rasu. Manzo ya ba da umarni cewa duk lokacin da kuka gama rufe wani a cikin kabari wani ya tsaya a saitin kansa ya kira sunan shi da na mahaifiyarsa, domin kuwa yana ji amma ba shi iya mai da amsa. Sannan ku mai -mai ta wannan aiki har sau uku, ku ce masa: "ka ambaci abin da ka fita duniya tare da shi, kace ka shaida babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma Manzo Muhammad ma'aikinsa, sannan ka yarda da cewa Allah shi ne ubangijinka, kuma ka yarda da musulunci a matsayin addininka, ka kuma shaida Muhammad (s.a.w) annabin Allah ne, ka kuma shaida da shugabancin Kur'ani". Sai ya kara da cewa, a wannan lokaci sai mala'ikun tambaya zasu ce wa junansu ta shi mu tafi kawai domin kuwa duk abin da muke so mu tambaya an gaya masa.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, May 21