Imamancin Imamai Mun yi imani cewa Imamanci wato; halifancin Annabi (S.A.W) yana daga cikin Usuluddin shika-shikan addini wadanda imani ba ya cika sai da kudurcewa da su, kuma bai halatta a yi takalidi da iyaye da dangi da malamai a cikinta ba komai girmansu da darajarsu kuwa, abin da yake wajibi shi ne a nemi sani a yi bincike a game da shi kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.
Atakaice sauke nauyin da yake kan baligi da aka wajabta masa ya dogara ne a kan imani da imamanci tabbatarwa ko korewa, koda mun kaddar cewa imamanci ba ya cikin shika-shikan addini da ba ya halatta a yi takalidi a cikinsu, duk da haka ya wajaba a yi imani da ita ta fuskacin cewa sauke nauyin da Allah ya dora wa baligi –karbar ayyukansa- ya wajaba a hankalce, kuma dukkaninsu ba ba sanannu ba ne ta hanya tabbatacciya yankakkiya, saboda haka wajibi ne muka wa wanda muka san mun sauke nauyin da yake kanmu ta hanyar biyayya gareshi, ko ya zamanto imami (A.S) a mazhabar imamiyya ko waninsa a wasu mazhabobin.
Kamar yadda muak yi imani da cewa annabci tausasawa ce daga Allah, kuma ba makawa a kowane zamani ya kasance akwai imami mai shiryarwa da zai maye gurbin annabi a ayyukansa na shiryar da ‘yan Adam da dora su a kan abin da yake maslaha a Sa’adar duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancanta daga mutane baki daya shi ma ya cancance ta, domin tafi da al’amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da ketare iya daga tsakaninsu. A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin da ke wajabta aiko da Annabawa da Manzanni shi ne yake wajabta sanya Imami bayan Manzo (S.A.W).
Saboda haka ne muke cewa: Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah a bisa harshen Annabi ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata. Imamanci ba zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba al’amarinsu ba ne da idan suka so zasu nada wanda suka son nadawa ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan ba tare da Imami ba. Ya zo cewa: “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwa irin ta jahiliyya” kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a Hadisi ingantacce.
Akan haka bai halatta ba wani zamani daga zamanoni ya kasance ba tare da imami ba da yake wajibi a yi masa biyayya wanda yake ayyananne daga Allah (S.W.T) shin mutane sun ki ko ba su ki ba, sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, yana rayuwa a cikinsu ne ko kuwa yana boye ne daga idandunan mutane, domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W) ya boyu daga ganin mutane kamar yadda ya boyu a cikin kogo da shinge haka na yake game da imami (A.S), kuma a hankalce babu bambanci tsakanin gajeriyar boyuwa ko mai tsayi[32]. Madaukakin sarki ya ce:
“Kuma ga kowace a’lumma akwai mai shiryarwa”. Surar Ra’ad: 8.
“Kuma babu wata al’umma face sai mai gargadi ya zamanto a cikinta”. Surar Fatir: 22.
Ismar Imami Mun yi Imani da cewa wajibi ga Imami ya zama katangagge daga dukkan munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da gangan ko da rafkanwa kamar yadda annabi yake. Haka nan wajibi ne ya zama katangagge daga rafkanwa da kuskure da mantuwa, domin Imamai su ne masu kare shari’a, masu tsayar da ita, halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin kuwa da ya hukunta mana imani da ismar annabawa shi ne ainihin dalilin da ya hukunta mana imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci ba. Ba wani abu ba ne a wajan Allah ya sanya duniya a abu daya.
Siffofin Imami Mun yi imani cewa imami kamar yadda annabi yake, wajibi ne shi ma ya zama mafificin mutane a siffofin kamala, kamar jaruntaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al’amura, da hankali da hikima da kuma kyawon dabi’a, dalilinmu na wannan siffofi ga Annabi shi ne dalilinmu na siffantuwar wadannan siffofi ga imami.
Amma game da iliminsa kuwa, shi yana samun ilmi da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukan saninsa ta gurin Annabi ne ko kuma Imamin da ya gabace shi, Idan kuma aka sami wani sabon abu to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhama da karfin kwakwalwar da Allah ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al’amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure, kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka ko koyarwar malamai, duk da yake iliminsa yana iya karuwa, shi ya sa Annabi (S.A.W) a addu’arsa yake cewa: “Ubangiji ka kara mini ilmi”[33]. Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayyar dan Adam cewa kowane mutum yana da wata sa’a ayyananniya ko wasu awowi a rayuwarsa da yakan san wani abu da kansa ta hanyar kaifin fahimta wanda shi a kan kansa reshe ne na ilhami, saboda abin da Allah ya sanya masa na karfin yin haka. Wannan karfi yana sassabawa da sabawar mutane a karfinsa da rauninsa da yawansa da karancinsa. Sai kwakwalwar mutum ta kai ga sani da ilmi ba tare da ya bukaci wani tunani ba da kuma kawo mukaddima da hujjoji na hankali ko kuma koyawar malamai ba, kuma saudayawa mutum kan sami irin haka a kan kansa a rayuwarsa, Idan kuwa al’amarin haka yake to ya halatta mutum ya kai ga kololuwar daraja da kamala a karfin tunaninsa na sanin ilhami, wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da da na yanzu suka tabbatar da shi.
Karfin ilhama a gun imami ana cewa da ita “kuwwa kudsiyya” wato karfi daga Allah, da take mafi kamalar kololuwar darajar ilhama, sai mai wannan siffa a kowane lokaci a kuma kowane hali ya so ya san wani abu sai ya san shi ba tare da mukaddima ba ko koyarwar wani malami, sai ya koma wa wannan abin domin saninsa sai ya san shi tare da taimakon wannan karfi da Allah ya ba shi, sai ilimi da wannan abu ya bayyana gareshi tamkar yadda bayyanar surar abu take bayyana a tsafatataccen madubi. Wannan kuwa abu ne bayyananne a tarihim Imamai (A.S), su a wannan fage kamar Annabi suke ba su taba yin tarbiyya ko neman ilmi a hannnu kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwanu shekarun balaga, karatu ne ko kuwa rubutu, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu duk kuwa da cewa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa Kuma ba a taba tambayar su wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar (ban sani ba) daga bakinsu ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu, alhali kuwa ba za ka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba sai ka ji an ambaci wanda ya tabiyyatar da shi ya koyar da shi, da kuma wadanda ya karbi ruywaya ko ilimi a hannunsu, da kuma dakatawarsu a wasu mas’aloli ko kokwantosu a mafi yawa daga ilimomi kamar yadda yake a kowane zamani da kowane guri.
Biyayya Ga Imamai Mun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul’amri” Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarkin zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar ilminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa kamar yadda Taurarin suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W). A wani hadisin yana fada: “Misalinsu a cikin wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa ba sa rigonsa da magana kuma su da umarnninsa masu aiki ne”. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa.
Mu mun mun yi imani da cewa umarninsu umarnin Allah ne, haninsu hanin Allah ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba Masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne. kuma ya wajaba a mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu.
Saboda haka mun yi imani da cewa hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta ba sai daga garesu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun nutsuwa da cewa ya bayar da wajibin da aka dora masa sai ta hanyarsu. Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S) ne duk wanda ya hau ya tsira wanda kuwa ya jinkirta ya bar su ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makale da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da’awowi da jayayya.
Bahasin imamanci game da tabbatar da cewa su ne halifofi na shari’a kuma masu shugabanci da izinin Allah a wannan zamanin ba shi ne muhimmi ba, wannan al’amari ne na tarihi da ya wuce, kuma tabbatar da shi ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari’a ba.
Abin da yake muhimmi shi ne abin da muka ambata na wajabcin komawa zuwa garesu wajan karbar hukunce-hukuncen shari’a, da kuma sanin abin da manzo (S.A.W) ya zo da shi kamar yadda ya zo da shi ta fuska ingantacciya. Kamar hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu kuma ba sa neman haskakawa daga haskensu to nisanta ne daga tafarkin daidai a Addini. Kuma baligi ba ya taba samun nutsuwar cewa ya sauke nauyin takalifin da ya hau kansa daga Allah, domin tare da samun irin wannan sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a, sabanin da ba a sa ran yin dacewa a kansa, to fa babu wata dama ga baligi ya zabi mazhabar da ya ga dama ko ra’ayin da ya zaba, dole ne ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda ya hakikance cewa da ita ce zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abin da ake da yakinin wajibcinsa yana lizimta wajabcin samun yakinin sauke nauyinsa.
Dalili tabbatacce da yake nuna wajabcin koma wa Ahlul Baiti (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) sun hada da fadinsa (S.A.W): “Hakika Ni na bar muku abin da idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, Assakalaini, dayansu ya fi dayan girma; su ne littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Zuriyata Ahlin gidana, ku saurara ku ji, ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tabki”[34]. Ka zurfafa tunaninka game da wannan hadisi mai girma zaka samu abin da zai gamsar da kai ya kuma girgiza ka a wannan hadisin a ma’anarsa a fadinSa (S.A.W): “Matukar kun yi riko da shi ba ku taba bata ba a bayana har abada” abin da ya bar mana su ne sakalaini tare ya kuma sanya su abubuwa guda biyu, bai iso da riko da daya ba, ba tare da dayan ba, da riko da su ne ba zamu taba ba har abada. Duba kuma ma’anar fadinsa (S.A.W) cewa: “Ba zasu taba rabuwa ba har sai riske ni a tabki” da nunin cewa wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su a hade ba to ba zai taba samun shiriya ba har abada, don haka ne suka zama su ne; “Jirgin ruwan tsira” kuma “Aminci ga mazauna kasa” da duk wanda ya ya bar su to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan da ma’anar soyayya gare su ba tare da riko da maganganunsu da bin tafarkinsu ba gudu ne daga gaskiya da ba abin da ke kaiwa ga hakan sai bakin ra’ayin jahiliyya, da gafala daga tafarki madaidaici a fassarar bayanan zancen Larabci mai fasaha.
Son Ahlul Baiti (A.S) Madaukakin sarki ya ce: “Ka ce ni ba na rokon ku wani lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai”. Surar Shura: 23. Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko da Ahlul Baiti (A.S) wajibi ne a kan kowane musulmi ya dabi’antu da sonsu da kaunarsu domin a ayar da aka ambata an takaita abin da ake nema daga mutane da nuna soyayyar makusantansa (A.S). Ya zo ta hanyoyi masu yawa da cewa; son su alamar imani ne kin su kuma alamar munafinci ce, kuma duk wanda ya so su ya so Allah da ta manzansa wanda kuma ya ki su to ya ki Allah da Manzonsa (S.A.W).
Hakika son su wajibi ne daga laruran addini da ba ya karbar jayayya ko kokwanto. Domin dukkan musulmi sun hadu a kan hakan duk da sabanin mazhabobinsu da ra’ayoyinsu, in ban da kadan daga wasu jama’a da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda aka sanya musu sunan “Nawasiba” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyara Annabi (S.A.W), don haka ne ma ake kirga su a cikn masu inkarin abin da yake wajibi na addinin Musulunci tabbatattu, wanda kuma yake karyata larurar Addini ana kirga shi a cikin masu karyata ainihin sakon Musuluncin koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada, saboda haka ne kin Ahlul Baiti (A.S) ya zama daga alamomin funafunci son su kuma ya zama daga alamomin imani kuma don haka ne kinsu ya zama kin Allah (S.W.T) da Manzonsa,
Kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai wajabta son su ba sai don su sun cancanci soyayya da biyayya ta bangaren kusancin su da Allah da Manzonsa da tsarkinsu da nisantar su ga shirka da sabo da kuma dukkan abin da yake nisantarwa daga karimcin ubangiji da yardarsa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa Ubangiji ya wajabta son wanda yake aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa domin shi ba shi da wata kusanci ko abotaka da wani, mutane a gurinsa ba komai ba ne sai bayi ababan halitta masu matsayi daya, kadai mafificinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoronsu gareshi. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafi takawarsu, kuma mafi darajarsu baki daya, ba don haka ba kuwa to da waninsa ya fi cancantar wannan soyayyar, kuma da ya kasance kenan Allah yana fifita wasu mutane a kan wasu a wajabcin so da biyayya haka nan kawai ko da wasa ba tare da cancanta ko daraja ba.
Imamai Tsarkaka (A.S) Ba ma imani ga Imamanmu (A.S) da abin da ‘Yan gullatu[35] da ‘Yan Hululiyya[36] suka yi ba, “Kalmar da take fita daga bakunansu ta girmama”. Surar Kahf 5.
Imaninmu game da su shi ne cewa su mutane ne kamar mu suna da abin da yake garemu kuma abin da ya hau kanmu ya hau kansu sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa Allah ya kebance su da karamarsa kuma Ya so su da soyayyarsa, domin sun kasance da karamarsa ya kuma ba su wilayarsa, domin su suna kan mafi daukakar daraja da ta dace da dan Adam na daga ilimi, da takawa, da jarumta da karimci, da kamewa, da dukkan kyawawan dabi’u mafifita na da sifofi abin yabo, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abin da aka kebance su da shi.
Da wannan ne suka cancanci su zamo Imaman kuma masu shiriyarwa kuma makoma bayan Annabi a cikin duk abin da yake na addini na bayani da shar’antawa da kuma abin da ya kebanta da Kur’ani na daga tafsiri da tawili.
Imaminmu Ja’afar Assadik (A.S) Ya ce: “Duk abin da ya zo muku daga gare mu daga abin da ya halatta bayi su siffanta da shi ba ku kuma san shi ba, ba ku fahimce shi ba, to kada kuyi musun sa ku mayar da shi gare mu, amma abin da ya zo muku daga garemu wanda bai halatta bayi su siffantu da shi ba, to ku yi musun sa kada ku mayar da shi zuwa gare mu.
Imamanci Sai Da Nassi Mun yi imani cewa lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah madaukaki a harshen Manzonsa ko harshen lmamin da ya aka sanya shi ta hanyar nassi idan yana son ya yi wasiyya da lmamin bayansa, hukuncin lmamanci a nan tamkar hukuncin annabci ne ba tare da wani banbanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah ya ayyana mai shiryarwa da ga dukkan mutane, kamar yadda ba su da hakkin ayyana shi ko kuma kaddamar da shi ko zabensa, domin mutumin da yake da tsarki da karfin daukar nauyin lmamanci baki daya da kuma shiryarwa ga ‘yan Adam gaba daya wajibi ne kada a san shi sai da shelantawar ubangiji, kuma ba a ayyana shi sai da ayyanawarsa.
Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da halifansa kuma shugaban talikai bayansa, sai ya ayyana dan amminsa Aliyyu Dan Abi Talib Amiri (A.S) ga musulmi, kuma amini kan wahayi, lmami ga halittu, ya ayyana shi a gurare da dama kuma ya nada shi ya kuma karba masa bai’a a kan shugabancin Muminai Ranar Gadir Ya ce: ‘‘A saurara a ji duk wanda na kasance shugabansa ne to wannan Ali shugabansa, Ya ubangiji! ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi ka tozarta wanda ya tozarta shi kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya’’.
Daga cikin wuraren farko da ya yi wasiyya da imamancin- -sa akwai fadinsa yayin da ya kira danginsa makusanta ya ce: “Wannan shi ne dan’uwana kuma wasiyyina kuma halifana a bayana ku ji daga gareshi ku bi shi”. A yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba. Kuma ya maimaita fadinsa dayawa da cewa: “Kai a gare ni tamkar matsayin Haruna ga Musa ne sai dai babu Annabi a bayana” Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar: "Kadai cewa Allah shi ne majibancinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka suna masu ruku’u". Surar Ma’ida: 55. Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya yi sadaka da zobe yana cikin ruku’u. Wannan dan littafin ba zai iya bin diddigin dukkan abin da ya zo na daga ayoyin Kur’ani da ruwayoyi ko bayan- -insu ba game da wannan maudu’i[37]. Sannan shi ma ya yi wasiyya da Imamancin Imam Hasan da Imam Husain (AS), shi kuma Husain (A.S) ya yi wasiyya da imamancin dansa Aliyyu Zainul Abidin (AS) haka nan dai Imami ke bayar da wasiyyar imamin da zai zo bayansa har zuwa kan na karshensu kamar yadda zai zo.
Adadin Imamai Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar Imamancin gaskiya su ne makomarmu a cikin hukunce-hukuncen shari’a wadanda Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da su da sunayensu gaba daya, sannan wanda yake gabata yana wasiyya da mai biye masa kamar haka: Adadi AI- kunya Suna Lakabi haihuwa Rasuwa 1 Abul Hasan Aliyyu Murtadha 23 K.H 40 H 2 Abu Muhammad Hasan Mujtaba 2 H 50 H 3 Abu Abdullah Husain Shahid 3 H 61 H 4 Abul Hasan Ali Sajjad 38 H 95 H 5 Abu Ja'afar Muhammad Bakir 57 H 114 H 6 Abu Abdullah Ja'afar Sadik 83 H 148 H 7 Abul Hasan Musa Kazim 128 H 183 H 8 Abul Hasan Ali Ridha 148 H 203 H 9 Abu Ja'afar Muhammad Jawad 195 H 220 H 10 Abul Hasan Ali Hadi 212 H 254 H 11 Abu Muhammad Hasan Askari 232 H 260 H 12 Abul Kasim Muhammad Mahadi 256 H Araye
Imam Al-Mahadi (AS) Shi ne Hujja a zamaninmu kuma boyayyen da ake sauraro, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukaka mafitarsa, zai zo domin ya cika duniya da adalci bayan an cike ta da zalunci.
Kudurcewarmu Kan Mahadi (A.S) Hakika albishir da bayyanar imam Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fatima (A.S) a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ta ruwayoyi masu yawa kuma dukkan musulmi duk da sabanin mazahabobinsu sun ruwaito hadisi game da shi.
Fikirar samuwar imam mahadi (A.S) ba wani sabon abu ba ne da Shi’a suka kago shi saboda izasu da yaduwar zalunci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarkin bayyanar wani wanda zai zo ya tsarkake kasa daga daudar zalunci kamar yadda wasu masu neman kawo rikici da rudani marasa adalci suka raya. Ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S) daga Annabi (S.A.W) ba ta yadda dukkan musulmi suka san ta kuma ta kafu a zukatansu suka yi imani da ita, da masu da’awar mahadiyyanci a karnonin farko kamar kaisaniyya da Abbasawa da wasu daga Alawiyyawa da sauransu ba su iya yaudarar mutane ba ta hanyar samun dama da amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci ba, domin sun sanya da’awar mahadiyyancinsu ta karya ta zama hanyar tasiri a kan jama’a gaba daya da kuma shiga rayukan jama’a.
Mu tare da Imaninmu da ingancin Addinin Musulunci, kuma cewa shi ne cikamakon addinan Ubangiji, kuma ba ma sauraron wani Addini da zai zo domin gyara dan Adam, hada da abin da muke gani na yaduwar zalunci, da yawaitar fasadi a duniya ta yadda ba zaka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashe duniya, tare da kuma abin da muke gani a fili na nesantar musulmi daga addininsu, da kuma ajiye hukunce-hukuncen Musulunci da dokokinsa a gefe guda a dukkan kasashen Musulmi da kuma rashin lizimtuwa- rsu da koda daya daga dubban hukunce-hukuncensa, amma duk da haka ba makawa mu saurari budi da farin ciki da dawowar Addinin Musulunci da karfinsa da iyawarsa wajan gyara wannan duniyar da ta dulmiya cikin takurawar zalunci da fasadi.
Sannan kuma ba zai yiwu ba Musulunci ya dawo da karfinsa da da jagorancinsa a kan dan Adam baki daya alhalin yana kan wannan halin da yake ciki a yau da gabanin yau na daga sabanin mabiyansa a dokokinsa da hukunce-hukuncensa da ra’ayoyinsa game da shi, tare da wannan hali da suka samu kansu a ciki a yau da ma kafin yau na bidi’o’i da canje-canje a dokokinsa da bata a cikin da’awoyinsu
Na’am ba zai yiwu ba Addini ya koma ga karfinsa sai dai idan mai gyara babba ya jagorance shi, yana hada kansu, yana kuma rushe abin da aka raba masa na daga bidi’o’i da bata tare da taimakon Ubangiji da ya sanya shi shiryayye mai shiryarw, wanda yake da matsayi mai girma na Shugabanci na gaba daya da kuma iko mai sabawa al’ada, domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
A takaice; dabi’ar yanayin fasadi a duniyar dan Adam ta kai matuka a baci da kuma zalunci, duk da kuwa imani da ingancin wannan addini da cewa shi ne cikamakon addinai, wannan al’amari ya hukumta sauraron mai wannan gyara domin tseratar da duniya daga abin da take ciki. Saboda haka ne dukkan bangarorin Musulmi suka yi imani da wannan sauraron, kai har da ma wadanda ba musulnli ba, sai dai kawai bambancin da ke tsakanin mazhabar Imamiyya da waninta shi ne, ita mazhabar imamiyya ta yi imani cewa wannan mai gyaran mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekara hijira ta 256 kuma bai gushe ba yana raye, kuma shi dan imam Hasan Askari ne mai suna “Muhammad” (A.S). Wannan kuwa saboda abin da ya tabbata daga Annabi (S.A.W) da kuma imamai (A.S) game da alkawarin zuwansa da haihuwarsa da boyuwarsa. Bai halatta ba Imamanci ya yanke a wani zamani daga zamuna koda kuwa Imami ya kasance boyayye ne, domin ya bayyana a ranar da Allah ya yi alkawari wanda kuma wannan yana daga cikin asiran Ubangiji da babu wanda ya san su sai shi.
Kuma rayuwarsa da wanzuwarsa ba komai ba ne sai mu’ujiza ce da Allah ya sanya domin ba ta fi mu’ujizar kasancewarsa imami ga mutane yana dan shekara biyar ba a ranar da mahaifinsa ya koma zuwa ga Ubangiji Madaukaki, kuma ba ta fi Mu’ujizar Annabi Isa (A.S) girma ba da ya yi magana da mutane yana cikin shimfida yana jariri, kuma aka aike shi Annabi ga mutane.
Tsawon rayuwa fiye da dabi’a fannin likitanci bai musanta haka ba, kuma ba ya ganinsa mustahili, sai dai shi likitanci bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba. Idan kuwa likitanci ya gajiya a kan haka to Allah mai iko ne a kan komai. Kuma tsawaita rayuwar Annabi Nuhu (AS) da wanzuwar Annabi Isa (AS) ya faru kamar yadda Kur’ani ya bayar da labari. Idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abin da Alkur’ani ya ba da Iabari game da shi to sun yi hannun riga da Musulunci. Yana daga abin mamaki musulmi ya tsaya yana tambaya game da yiwuwar haka alhali yana da’awar imani da Littafi Mabuwayi.
Daga cikin abin da ya zama dole mu ambace shi a nan shi ne cewa sauraron ba yana nufin musulmi su nade hannayensu ba ne game da al’amuran da suka shafi Addininsu ba ne, da kuma abin da ya wajaba na taimakonsa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Musulmi har abada abin kallafawa ne da aiki da abin da ya sauka na daga hukunce-hukuncen Shari’a kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon daidai yadda zai iya “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin kiwonsa.” Saboda haka bai halatta gareshi ba ya takaita wajibansa ba don yana jiran mai kawo gyara Imam Mahadi (A.S) wanda yake mai shiryarwa, wanda aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya saryar da takalifin da aka kallafa, ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama karazube kamar dabbobi.
Raja’a (Komowa Duniya) Abin da Mazhabar Ja’afariyya Imamiyya ta tafi a kansa da riko da abin da ya zo daga Ahlul Baiti (A.S) Shi ne cewa Allah (S.W.T) zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, sai ya daukaka wasu ya kuma kaskantar da wasu, ya dora masu gaskiya a kan marasa gaskiya, ya kuma sakawa ababan zalunta daga azzalumai, wannan kuwa zai faru ne yayin bayyanar Mahadi (A.S).
Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna sannan sai su sake mutuwa, daga baya kuma sai tashi, sai kuma samun sakamakon abin da suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuwa ukuba, kamar yadda Allah ya kawo a cikin Alkur’ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din wadanda suka sami fushin Allah suke yi domin a dawo da su dawowa ta uku ko sa gyara ayyukansu: “Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu to mun yi furuci da zunubanmu shin akwai wata hanyar fita”. Surar Mumin: 11. Na’am Alkur’ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya hadisai da dama sun zo daga Ahlul Baiti (A.S) game da hakan, kuma mabiya Ahlul Baiti sun yi ittifaki a kan haka in ban da ‘yan kadan daga cikinsu da suka yi tawilin abin da ya zo game da Raja’a da cewa ma’anarta ita ce komowar hukuma da Umarni da hani a hanuun Ahlul Baiti (A.S) da bayyanar lmamin da ake sauraro ba tare da komowar wasu ayyanannu mutane ba ko raya matattu.
Batun Raja’a kuwa a gurin Ahlussunna yana daga cikin abin ki da imani da shi ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja’a abin suka ga mai ruwaya kuma aibi gare shi wanda yake wajabta kin ruwayarsa da jefar da ita, tayiwu suna kirga ta a matsayin kafirci da shirka ne ko ma tafi muni, don haka wannan yana daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi’a da shi da aibata su da shi.
Babu shakka wannan wata barazana ce da kungiyoyin Musulmi a tsayin zamani suke amfani da ita domin sukar sashensu, kuma ba mu ga wani abu da zai halatta wannan ba domin imani da Raja’a ba ya rushe imani da tauhidi ko da Annabci, yana ma kara inganta su ne, domin Raja’a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya kamar yadda tashin kiyama da tayar da matattu suke. Raja’a tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wacce ya inganta ta zama mu’ujiza ga Annabinmu Muhammad (S.A.W) da Alayensa. Kuma ita tamkar mu’ujizar raya matattu ce wacca ta kasance ga Annabi Isa (A.S), kai ta fi ta ma domin ita tana kasancewa ne bayan matattun sun zama rididdigaggu. “Ya ce wanene zai raya kasusuwa alhali sun zama rididdigaggu? Ka ce wannan da ya fare su karon farko shi ne zai raya su kuma shi game da dukkan halittu masani ne”. Surar Yasin: 79-87.
Amma wanda ya soki Raja’a kuwa bisa dalilin cewa tana daga cikin “Tanasuhi[38]” wannan saboda shi bai fahimci bambanci tsakanin “Tanasuhi” da tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba ne, ita Raja’a wani nau’i ne na tayar da matattu da jikinsu ne, domin ma’anar Tanasuhi ita ce ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba, wannan kuwa ba ita ce ma’anar tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba ce, ma’anarsa ita ce komo da ainihin jikin da siffofinsa na kashin kansa da suka kebantu da shi, haka nan ma Raja’a take. Idan kuwa da “Raja’a” “Tanasuhi” ce to raya matattu ta hannun Annabi Isa (A.S) ma ya zama “Tanasuhi” ne, haka ma tayar da matattu da komo da ainihin jikkunansu ya zama “Tanasuhi’’ ke nan.
Saboda haka babu abin da ya rage sai tattaunawa game da “Raja’a” ta fuska biyu.
(1) Na farko: Cewar ita mustahiliya ce.
(2)Na biyu: Karyata hadisan da suka zo game da ita.
(1)A bisa kaddarawar cewa tattaunawar guda biyu daidai ne, to yin imani da ita ba a daukarsa a matsayin kyamar da masu gaba da Shi’a suka mayar da ita, kuma dayawa daga cikin abubuwan da suke mustahilai ne wasu bangarorin musulmi suka yi imani da su ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalai masu dama a kan hakan kamar: imani da yiwuwar rafkanwa ga Annabi (S.A.W) ko kuma aikata sabo, da kuma imani da rashin farko ga Alkur’ani, da kuma batun narkon azaba, da kuma imani da cewa Annabi bai yi wasiyya ba da halifa a bayansa ba.
Kuma wadannan munakashoshi biyu ba su da wani asasi na inagnci, amma batun cewa raja’a mustahili ce mun riga mun kawo cewa ita nau’i ce na tayar da matattu da jikkunansu, sai dai cewa tayarwa ce a nan duniya, kuma dalilin yiwuwar ta shi ne dalili akan yiwuwar tashin kiyama. Kuma babu wani dalili da sai ta zama abin mamaki sai dai kawai ita ba mu saba da ita ba ne a rayuwarmu ta wannan duniya, ba mu san kuma sabubbanta da abubuwan da suke hana ta ba da zasu sanya yin ikrari da ita ko mu kore ta. Tunanin mutum ba ya saukake masa yarda da abin da bai saba da shi ba cikin sauki, kamar wanda yake mamakin tayar da matattu yana mai cewa: “Wanene zai tayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. Aka ce masa: “Wanda Ya fare su a tashin farko shi ne zai raya su kuma shi a kan komai masani ne”. (Yasin: 78-79)
Na’am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali akai na tabbatar da shi ko kore shi, ko kuma mu ka raya rashin samuwar dalili to a nan ya zama dole a kanmu mu koma wa nassosin Addini wadanda suke su ne tushen wahayin Ubangiji. Kuma abin da zai tabbatar da yiwuwar Raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Alku’ani kamar dai mu’ujizar Annabi Isa (AS) ta raya matattu: “Kuma Ina warkar da Wanda aka haifa makaho kuma Ina rayar da matattu da izinin Allah”. Surar Ali Imran: 49. Da kuma fadin Ubangiji: “Ta yaya Allah zai raya wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah ya matar da shi Shekara dari sannan ya tayar shi”. Surar Bakara: 259. Da kuma ayar da ta gabata da ke cewa: “Suka ce Ya ubagijinmu Ka matar da mu sau biyu”. Surar Mumin: 11. Ma’anar wannan ayar ba za ta yi daidai ba, ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba duk da wasu daga masu tafsiri sun kallafa wa kawukansu yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba kuma ba zai tabbatar da ma’anar ayar ba.
(2) Tattaunawa ta biyu:- Ita ce da’awar cewa hadisai game da Raja’a kagaggu ne ba ta da asasi, domin Raja’a tana daga cikin al’amuran da suke na larura da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) na hadisai mutawatirai.
Bayan wannan ashe ba ka yi mamakin shahararren marubucin nan mai da’awar sani Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, da yake cewa; “Yahudanci ya bayyana a cikin Shi’anci ta hanyar imani da Raja’a”. Don haka ni nake cewa masa: “Ashe kenan Yahudanci ma ya bayyana a Kur’ani saboda da batun Raja’a” kamar yadda ya gabata game da ayoyin Alkur’ani mai girma da suka ambaci Raja’a. Kuma zamu kara masa da cewa: A hakika babu makawa wasu akidun Yahudanci da Kirintanci su bayyana a cikin da dama daga akidu da hukunce-hukuncen Musulunci, domin Annabi Mai girma (S.A.W) ya zo yana mai gaskata Shari’o’i da suka gabata duk da yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. Don haka bayyanar Yahudanci da Kirintanci a wasu abubuwan da Musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin Musulunci, wannan idan har an kaddar cewa Raja’a tana daga Akidojin Yahudawa kenan kamar yadda wannan marubucin yake da’awa.
Ko yaya dai Raja’a ba tana daga cikin shika-shikan Musulunci ba ce da ya wajaba a kudurce ta da yin bincike a kanta, imaninmu da ita bi ne ga hadisai ingantattu da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga karya, kuma tana daga cikin al’amuran gaibi da suka ba da labari game da ita kuma aukuwarta ba mustahili ba ne.
Yin Takiyya An ruwaito daga Imamus Sadik (A.S) a sahihin hadisi cewa: “Takiyya Addinina ce kuma Addinin iyayena ce” da kuma “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi”. Haka nan takiyya ta kasance taken Ahlul Baiti (A.S) wajen kare kai daga cutar da su da kuma mabiyansu da kare jininsu da kawo gyara ga halin da musulmi ke ciki da kuma hada kansu. Takiyya ba ta gushe ba a matsayin alama da ake sanin shi’a da ita tsakanin sauran bangarori na al’ummu kuma dukkan mutum idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yarda da abin da ya yi imani da shi ko kuma bayyanar da shi a sarari, to babu makawa ya boye ya kiyaye a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi’ar hankali ke hukunci da shi. Kuma sannanen abu ne cewa Shi’a da lmamansu sun sha nau’o’in jarrabawa da matsa lamba na tsawon zamani da babu wata jama’a da ta sha irinta. Wannan al’amari ya tilasta su a mafi yawan lokutansu su yi amfani da takiyya suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyanarwa da suturta akidunsa da ayyukan da suka kebanta da su saboda abin da yake biyo bayan hakan na daga cutuwa a addini da duniya, wannan shi ne ya sanya suka bambanta da takiyya aka kuma san su daita.
Takiyya tana da hukunce-hukunce ta fuskacin wajabcinta da rashin wajabcinta daidai gwargwado sassabawar wuraren tsoron cutuwa da aka ambata a babobinta a littattafan fikihu. Ita ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya zama hall ko saba mata ya zama wajabi ne a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga Addinin da hidima ga Musulunci da jihadi a tafarkinsa, to a wannan hali dukiya ba komai ba ce kuma ba za a fifita rai ba.
Takiyya tana iya zama haram a ayyukan da sukan iya kaiwa ga kashe rayuka masu alfarma ko yada karya, ko barna a Addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su ko kuma yada zalunci da ketare haddi a tsakaninsu. A kowane hali dai takiyya a gun Shi’a ba ta mayar da su wata kungiyar asiri ba ce domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi’a marasa fahimtar al’amura kamar yadda suke, suke surantawa kuma suka ki dora wa kansu nauyin fahimtar ra’ayi ingantacce.
Kamar yadda ba ta sanya Addini da hukunce-hukuncensa sun zama wani sirri daga asiran da bai halatta a bayyana su ga wanda ba ya imani da su ba, al’amarin bai zama haka alhalin littattafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu na fikihu da hukunce-hukunce da bahasosin Akida sun cika gabas da yamma sun ma wuce yadda ake tsammani daga kowace al’umma da take da wani addini. Akidarmu ta takiyya wadanda suke son aibata shi’a sun samu damar amfani da ita, suka sanya ta daga abubuwan da suke sukan su da ita, kamar dai sa iya kashe kishirwar gabarsu sai da fille wuyayensu da takubba da tumbuke asalinsu gaba dayansu a wadancan zamunan da suka gabata da ya isa a ce wannan dan shi’a ne ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Baiti (A.S) na daga Umayyawa da Abbasawa har da Usmaniyawa.
ldan sukan mai son suka ya dogara ne da abin da yake raya rashin shar’ancinsa a addini, to mu sa mu ce masa:
Na Farko: Mu masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S) kuma muna bin shiriyarsu ne, kuma su ne suka umarce mu da ita suka wajabta ta a kanmu a lokacin bukata, ita tana daga Addini a wajensu kuma ka ji fadin Imamus Sadik (A.S) da yake cewa: “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi.”
Na biyu: Shar’anta ta kuma ya zo a Alkur’ni mai girma, da fadarsa madaukaki: “Sai dai wanda aka tilasta shi alhalin zuciyarsa kuwa tana nutse da imani”. Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar Dan Yasir da ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan Musulunci. Da kuma fadinsa madaukaki: “Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya”. Surar Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa: “Kuma wani mutum daga mutanen fir’auna yana mai boye Imaninsa Ya ce”. Surar Gafir: 28.