Auran Mutu'a
  • Take: Auran Mutu'a
  • marubucin:
  • Source:
  • Ranar Saki: 6:26:19 2-10-1403

A shar'ance Auren Mutu'a yana da sunaye da aka san shi da su, ana kiran sa "Aure Mai Iyaka" ko "Auren Jin Dadi", "Aure Mai Ajali".
 
Yardajjen Tunani
Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin kai
Duk wani addini da ya kasa warware matsalar dan Adam to wannan addinin ba cikakken addini ba ne, don haka ba shi da wani matsayi a wurin Allah madaukaki, haka nan ma duk wata mazhaba da ta kasa warware matsalar dan Adam to a bisa hakika wannan mazhabar ba ta da wata kamala, kuma ta rasa yarda daga wurin Allah madaukaki. Akwai bambanci matuka tsakanin a samu ra'ayin mazhaba ko addini mai kamala da cika, da kuma gazawar masu wannan mazhabar ko addinin.
Auren mutu’a yana daga cikin abin da yake iya warware matsalar dan Adam ta kawar da fasadi a duniya a cikin al’ummu, don haka mazhabin da yake da wannan fikira mai kima shi ne ya kamata ya yi magana game da warware matsalar dan Adam. Imam Musa Sadar yana cewa: "Musulunci shi ne addinin kadaita Allah madaukaki…". Kafin nan yana cewa: "Addinai sun kasance abu guda ta fuskacin cewa; dukkaninsu suna hidimar hadafi daya ne wadanda suka hada kira zuwa ga Allah da hidimar mutum, kuma wadannan abubuwa biyu fuska ne na abubuwa guda biyu" . Wannan yana nufin cewa; imani da Allah ba ya zama na gaskiya sai idan imani da cewa; addini ya zo ne domin hidimar mutane, ba mutum ne zai kasance domin hidimar addini ba, kuma duk wani addini da ba zai iya warware matsalar dan Adam ba, kuma ba zai iya daukaka kimarsa ba, to wannan addinin ba na Allah ba ne.
Aure Mai Iyaka, ko kuma Auren Jin Dadi, ko kuma Auren Mutu'a, Aure ne wanda yake daga mukullan kawar da fasadi a cikin kowace al'umma, sai dai magana kan hakan tana da tsawo. Sannan kuma aure ne wanda yana nan kan halaccinsa har abada, domin hadisi ya zo cewa: "Halal din Muhammad (s.a.w), halal ne har zuwa ranar kiyama, kuma haram dinsa, haram ne har zuwa ranar kiyama .
Saboda gobe ranar Laraba, ta yi daidai da ranar shahadar Imam Ja'afar Sadik (a.s), wato Imami na shida daga alayen manzon Allah (s.a.w) da aka sani da Ahlul-baiti (a.s), don haka ina mika ladan wannan rubutu zuwa gare shi!. 
Bayanin Aure
Aure alaka ce kebantacciya ta shari’a ko al’ada wacce ake kulla ta tsakanin mace da namiji, da lafazi na musamman, wacce take halatta wa kowanne daga bangarori biyu alaka mai karfi ta musamman tsakaninsu. Shari’ar musulunci ta nisantar da mutane daga zaman gwagwarci, ta kwadaitar da su yin aure domin samun al’umma ta gari mai kame kai, da renon manyan gobe da zasu ci gaba da shiryar da na baya zuwa ga tafarkin tsira. Aure yana bayar da damar kusanci tsakanin namiji da mace, kuma shi kadai ne hanyar hakan sai dai a zamanin da ya zama akwai bayi da aka fi sani da ababan mallaka  shari'a ta bayar da wannan damar tsakanin mai mallaka da baiwarsa.
Aure ya kasu gida biyu ne a shari’ar musulunci, ya hada da Aure maras iyaka  da aka fi sani da "Da’imi” da kuma aure mai iyaka da aka fi sani da "Mutu’a”, dukkan wadannan biyun shari’a tana da hikima, kuma an sanya musu sharudda, sannan aka kwadaitar da yin su. Yawancin aure maras iyaka yakan kasance don hada gida da tara iyali, da renonsu, da samar da al’umma ta gari wacce zata gaji na baya. Amma aure mai iyaka yakan kasance ne domin kariya daga zina, da fadawa cikin haramun; wannan yana da amfani matuka ga mutane mabambanta; muna iya kawo misalin matafiyi, da wanda ya kasa aure, ga shi kuma yana jin tsoron fadawa cikin zina, da maras ikon sama da mata hudu; ga shi kuwa yana iya fadawa fasadi, da sauran misalai masu yawa. Don haka ne imam Ali (a.s) ya ce: "Ba don Umar ya haramta auren mutu’a ba, da babu mai yin zina sai fasiki” .
Wannan lamarin kamar yadda yake ga maza, haka nan yake ga mata; sau da yawa macen da ba ta samun aure, sannan tana son kiyaye kanta daga zina da fada wa cikin sabon Allah madaukaki sakamakon ba zata iya kame kanta ba, ko kuma tana cikin yanayin rayuwa a al’ummar da ko dai ta fada wa fasadi, ko kuma ta zabi kiyaye dokar Allah. Sai dai wannan bayani ne kawai na wasu daga cikin hikimomin aure mai iyaka, amma ba su ne kawai dalilan sanya shi a shari’a ba, domin akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu. Allah yana da hikimomin da yakan sanya shi zartar da hukunce-hukuncensa da muna iya fahimtar wasu sashe daga ciki.
 
 
AUREN MUTU'A A MUSULUNCI
Dukkan musulmi sun yi ittifaki  a kan cewa auren mutu'a halal ne a farkon musulunci, kuma sahabbai sun aikata shi a lokacin Annabi (s.a.w) da lokacin halifansa na farko, da wani bangare na shugabancin Umar bn Khaddabi, sannan sai Umar ya hana. Har ma daga baya wasu suka yi da'awar an shafe shi. Amma sahabbai masu yawa sun saba wa Umar kan wannan hanawa da yi, wasu kuma suka goyi bayansa, wasu suka yi shuru.
Amma Ahlul-baiti (a.s) duk sun tafi a kan halarcinsa da hadisai da suka kai matsayin tawaturanci (masu yawa) kuma ga shi Kur'ani yana goyon bayan halarcinsa har zuwa yau.
Da akwai mas'aloli da yawa da duniyar musulmi ta shagaltu da sabani game da su, irin wadannan mas'aloli sun hada da kamar magana kan farkon wanda ya musulunta, da shafa kan kafafu a alwala, da ayyana halifa ta bangaren Annabi (s.a.w), da auren mutu'a. Sau da yawa irin wadannan mas'aloli a zahiri ko da sun shafi mas'alar fikihu ne, amma daga karshe wasunsu sukan tuke zuwa ga Akida ne.
Wani abu kuma da zamu sani shi ne: Sau da yawa masu kare auren mutu'a da dukkan karfinsu ba don su suna son yin mutu'ar ba ne, ko wani abu makamancin haka, abin da yake nufinsu shi ne kare addinin Allah daga jirkita domin maslaha tana cikinsa. Don haka ba ya kan wani mutum ya tambaya cewa: Me ya sa kuke kare auren mutu'a alhalin yawancinku ko kuma malamanku ko ma imamanku ba sa muhimmantar da yin sa?!
A nan sai mu ce; Shi dai aure kowane iri ne ganin dama ne, sannan abin da ya sanya mu kare wannan aure shi ne: Kasancewarsa shari'ar manzon Allah (s.a.w) ce wanda ya zo da addini cikakke daga Allah, da ba shi da wata tawaya balle a yi ragi ko a yi kari a cikinsa. Sannan kuma duk wata maslaha ta dan Adam tana cikin koyi da abin da Annabi ya zo da shi kai tsaye ba tare da wani jayayya ko neman sauyi daga gare shi ba.
Mene ne Auren Mutu'a?
Auren mutu'a shi ne mace mai cikakken hankali, 'ya, ko baiwa bisa izinin Ubangijinta, haka nan budurwa bisa izinin Uba ko Kaka na wajen Uba, ta yi aure da wani mutum zuwa wani lokaci ayyananne, da wani lafazi na musamman da shari'a ta sanya, a kan wani sadaki da aka ambata, da sauran sharuddan da suka zo a littattafan fikihu dalla-dalla. Kuma dukkan sharuddan aure da'imi suna cikin auren mutu'a, sai dai a wasu abubuwan kamar gado idan ba an shardanta shi ba, kuma idan aka mance ba a ambaci mudda ba, to ya koma na da'imi.
Sharuddan Auren Mutu'a
Shari'ar Musulunci tana da tsari da ta doru a kansa, kuma kowane lamari yana da nasa tsarin da ya hana da dalilansa, hukuncinsa, sharudansa da sauransu. Auren Mutu'a ma a matsayinsa na hukuncin shari'a yana da sharuda da ya doru a kansu da suka hada da;
1.    Yardar bangaren biyu, wato namiji da mace.
2.    Sadaki: wannan hakki ne na mace, ba ya saraya sai da yardarta ko ta yafe.
3.    Ambaton muddarsa, ko da kuwa awa daya ce, ko shekara goma, ko makamancin hakan.
4.    Kada wani abu ya hana kamar dangantaka ta jini ko ta shayarwa, ko ta auratayya da sauran abubuwan da sukan haramta auren mace.
 
Bambancin Auren Mutu'a da na Da'imi
Akwai bambanci tsakanin Auren Mutu'a da na da'imi da zamu iya kawo mafi muhimmancinsu kamar haka;
•    Na mutu'a yana da lokacin ayyananne da zai kare.
•    A mutu'a ba saki sai dai a yafe ragowar mudda komai yawanta kuwa, ko kuma idan mudda ta kare.
•    A auren mutu'a; da dayan ma'aurata miji ko mata zai mutu, to da babu gado tsakaninsu, sai dai idan sun shardanta hakan yayin aurensu.
•    Wasu sun kara da cewa a Auren Mutu'a dole ne a ambaci sadakin mace sabanin Auren Da'imi.
Auren Wata Al’umma
Idan auren wata al’umma da ba musulma ba ya kasance sabanin na musulunci to shari’ar musulunci ta zartar da aurensu, don haka wannan matar tana da hurumin cewa tana da aure kuma dole ne kiyaye dukkan hurumin da mace me aure take da shi game da wannan matar. 
Amma a mas’alar yaki wani abu ne mai bambanci da wannan mas’alar, domin yaki yana nuni da cewa al’ummar da ta kawo hari tana son kashe jama’ar musulmi ne gaba daya, don haka ne shari’a ta halatta daukar irin wadannan mutane masu hadari a matsayin ribar yaki, matansu kuwa a matsayin bayi da ya halatta a kusance su bayan ribace su a yaki. Sai dai a yau wannan mas'alar tana da abin lura duba ga cewa babu Waliyyul Amr ga musulmi a nahiyoyinsu musamman Imami halartacce a cikinsu.
Sannan kana iya samun sabani tsakanin su kan su musulmi, ta yadda wani yana da fatawa a mazhabinsa da ta saba da ta wani. A nan ma dukkan mazhabobi sun tafi a kan cewa; Auren da yake bisa ijtihadin malaman wata mazhaba haka ma saki da yake kan wata fatawa ta wata mazhaba dukkaninsu sun inganta.
Misalin da zan so bayarwa a nan shi ne; Idan wani mutum da yake bin mazhabar Maliki, ya saki mace ba tare da shedu biyu adalai ba, a waccan mazhabar ta Malikiyya sakin ya yi, amma a mazhabar Ahlul-bait (a.s) wannan ba saki ba ne, domin ya rasa daya daga cikin sharuddan da suka zo a cikin Kur’ani mai girma. Amma tun da a waccan mazhabar saki ne, don haka ya halatta ga wanda yake bin mazhabin Ahlul-bait (a.s) ya aure ta bayan ta gama idda; Akwai misalai masu yawa irin wannan a tsakanin mazhabobin musulunci.