Adalcin Allah Da Sharhi Kan Halayyar Dan'adam Mu'assasar Al-Balagh Tsarawa: Hafiz Muhammad
Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
Adalcin Allah Madaukaki Adalci siffa ce, cikin siffofin Allah (S.W.T.). Muna iya ganin gurabun adalcinSa a dukkan bangarorin samammu, kamar fagen halitta da samarwa da fagen dabi'a da halittar mutum da dabba da tsiro, haka kuma muna ganin wannan adalcin cikin shari'a da dokokin Ubangiji.
"Lalle Allah Na yin umurni da adalci da kyautatawa". (Surar Nahli, 16: 90) Haka ma adalcin Ubangiji ya bayyana cikin abin da Yake hukumtawa da kaddarawa kan halittunSa na hukumci da kaddara, da cikin abin da Ya shar'anta na shari'u da sakonni. Kamar yadda yake bayyana a fagen lahira, ranar hisabi da sakamako. Zai sakantawa mai kyautatawa da kyautatawar, mai mummunan aiki kuwa da irin aikinsa.
"Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa". (Surar Kahf, 18: 49)
"Sa'an nan kuma a cika wa kowane rai abin da ya sana'anta". (Surar Bakara, 2: 281) "Allah ba Ya kallafawa rai face ikon yinsa, yana da ladan abin da ya aikata, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatawa...". (Surar Bakara, 2: 286)
Bisa wannan tsarin ne musulmin farko suka tafi wajen fahimtar alakarsu da Allah (S.W.T.) da fahimtar halayyar 'yan Adam da ayyukansu. Daga bisani sai falsafa ta shigo ga kuma ra'ayoyin ilmin tauhidi dukkansu masu sassabawa juna. Hakika wadannan sun tsirar da ra'ayoyi uku kan fassarar ayyukan mutane da alakarsu da iradar (nufi) Allah Madaukakin Sarki.
Wadannan ra'ayoyi kuwa su ne:
1. Jabru (Tilastawa).
2. Tafwidhu (Sakarwa).
3. Babu Jabru ballantana Tafwidhu.
Hakika wadansu kungiyoyi da mazhabobi sun yi mummunan fahimta wa zahirin wadansu ayoyin Alkur'ani, kamar fadinSa (S.W.T.) cewa: "Zahirinsu ya sanya irin wannan kungiya suka yarda da Jabru. Abin da wannan ra'ayi yake nufi shi ne dan'Adam ba ya mallakar nufi kuma ba shi da zabi, shi ba kome ba ne face bigire da gurin saukar kaddararrun abubuwa daga Allah (S.W.T.). A bisa wannan ra'ayi, mutum abin tilastawa ne, ba shi da wani zabi cikin al'amurransa. Masu irin wannan ra'ayi ana kiransu da sunan Mujabbira.
Ra'ayi na biyu kuwa shi ne mai cewa an sakar wa dan'Adam ikon zabi wajen ayyukansa, da kuma nufinsa babu nufin Allah a cikin ayyukansa. Kai suna ganin ma cewa Allah ba Ya iya hana mutum yin abin da ya yi nufin yi ko sabo ne kamar kisan kai, zalunci, shan giya, ko kuwa ayyukan biyayya ne kamar su adalci, kyautatawa, salla da dai sauransu. To da wannan, dan'Adam yana da 'yanci ga barin Allah (S.W.T.), wannan kuwa shi ne ra'ayin Mu'utalizawa.
To Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi raddi wa wadannan ra'ayoyi guda biyu, sun nuna bacinsu gaba daya. Kowanne daga ra'ayoyin nan biyu sun saba da abin da Alkur'ani ya zo da shi, akidar tauhidi kuwa ta kafu kan tushensa ne. su Imamai (a.s.) sun fayyace mana cewa akwai bayyananniyar alaka tsakanin irin yadda ake fahimtar halayyar mutum da imani da adalcin Allah. Suka ce lallai abin da ra'ayin cewa mutum ba ya mallakar wani nufi ko zabi sai dai shi abin tilastawa ne kurum, yana janyo tuhumtar Mahalicci Mai girma da Daukaka da zalunci da kore adalci daga gare Shi, lallai kuwa Ya girmama daga hakan. Saboda ma'anar wannan shi ne Allah Ya tilastawa mutum aikata sharri sannan kuma Ya yi masa ukuba dominsa, haka nan Ya tilasta masa aikata alheri sannan kuma Ya hana shi ladansa. Domin haka ne Imamai (a.s.) suka kakkabe wannan
mumunan fassara wanda da yawan musulmi suka fada ciki a dalilin gurguwar fahimtar da suka yi wa zahirin wadansu ayoyi kamar cewa: "Yana batar da wanda Ya so, Yana kuma shiryar da wanda Ya so".
Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi wa matsalolin shiryarwa da batarwa tafsiri bayyananne mai dacewa da adalcin Allah (S.W.T.). Bayanin wannan yana tafe.
Haka nan kuma Imamai (a.s.) sun yi watsi da ra'ayin masu cewa an sakarwa mutum akala sai yadda ya ga dama zai yi, ba tare da Allah Yana iya hana shi ba. Sun bayyana cewa wannan ra'ayi karkatacce da cewa tuhumar Allah ne da rashin cikakken iko kan bayinSa da gajiyawarSa kan hakan. Alhali kuwa Allah (S.W.T.) Mai cikakken iko ne, kuma Mamallakin dukkan halittunSa.
Imamai (a.s.) suna da matsaya matsakaiciya dangane da al'amarin da ya shafi adalcin Ubangiji. Wannan matsaya tana kore Tilastawa da Sakarwa, tana cewa: (Nufin mutum baya iya rabuwa da nufin Allah). Sun bayyana wannan alakar da take tsakanin nufin mutum da nufin Ubangiji bayani cikakke a akidance. Nan gaba za mu kawo ruwayoyinsu masu nuna wannan ra'ayi.
Kafin mu kawo wadannan ruwayoyi, bari mu yi dan sharhi kan batutuwan da mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bambanta da masu ra'ayoyi kan mas'alar adalcin Allah, bisa abubuwa guda uku na asasi:
Dan'Adam yana da nufi da ikon zabin duk aikin da zai yi, ko na alheri ko na sharri, haka kuma kin aikata shi. Mutum yana iya kisan kai ko sata ko zalunci ko karya, da wannan nufin da ikon da yake da shi. Haka kuma yana da daman tsai da adalci da aikata aikin kwarai da yin salla da barin haramtattun abubuwa, da wannan nufi nasa da iko.
Hakika Allah (S.W.T.) Yana da ikon hana mutum kowane aiki, kamar yadda yake da ikon sa mutum aikata kowane aiki ba tare da zabin mutum ya sami tasiri ba. Sai dai Allah ba Ya tilastawa kowa aikata alheri ko sharri.
Amma Shi Allah, domin tausayinSa da jin kanSa, Yana shiga tsakanin bawan da ya cancanci taimakonSa wajen aikata mummunan aiki, domin jin kai. Haka ma Yana taimaka masa wajen aikata alheri idan ya cancanci taimakon.
1. Wani abin da yake da dangantaka da adalcin Ubangiji kuma shi ne: Allah Yana sakantawa kowane mutum ranar kiyama da abin da ya aikata, alheri ko sharri. Sai dai kuma wata kungiyar ta musulmi tana ganin cewa mai yiyuwa ne Allah Ya shigar da mai kyautata aiki cikin wuta, mai mummunan aiki kuma aljanna, suna kuma dogara ne, bisa kuskure da mummunan fahimta, kan wannan aya mai girma: "Ba a tambayarSa ga abin da Yake aikatawa, alhali kuwa su ana tambayarsu". (Surar Anbiya, 21: 23)
Wasu jama'a daga cikin musulmi sun dogara da wannan ayar ne bisa tafsiri na kuskure, suka ce ba ya wajaba kan Allah (S.W.T.) Ya cika alkawarin sakayya da Ya yi a ranar kiyama. Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun mai da martani kan wannan zance da cewa, wannan ya sabawa gaskiyar Allah Ta'ala da adalcinSa.
Wancan ra'ayin yana daidaita mai kyautatawa da mai mummunan aiki, hakan kuwa yana rusa kimar kallafawa bayi da kuma sanya shari'a. Ingantaccen zance dai shi ne babu wani aikin da ba shi da sakamako, ko kuma mai daukar laifin yinsa, kamar yadda aya ta ce:
"To wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai ganshi. Kuma Wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
2. Ra'ayoyin sashin musulmi sun tafi a kan cewar ya dace ga Allah (S.W.T.) Ya kallafawa bayi abin da yafi karfinsu, wannan kuwa sun fade shi ne domin dogara kan fahimta ta kuskure da suka yi wa wannan aya mai girma:
"Ya Ubangijinmu Kada Ka sanya mu daukar abin da babu iko gare mu da shi". (Surar Bakara, 2: 286)
Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kore wannan fahimta suna masu bayanin cewa ta saba da adalcin Allah da kuma bayyanannen fadi na Alkur'ani mai girma, cewa: "Allah ba Ya kallafa wa rai face abin da zai iya dauka". (Surar Bakara, 2: 286). To yanzu za mu kawo sashen ruwayoyi da tattauna-war Ahlulbaiti (a.s), masu mana sharhin wadannan ginshikai na asali da fassara halayyar mutum da alakar da ke akwai tsakanin nufin mutum da ta Allah (S.W.T.). Wadannan ruwayoyi suna kulla tafsiri da sharhin halay-yar mutum da tushen adalcin Allah domin su karfafa mana dayantaka (ta Ubangiji) fahimta da tunani da kuma i'itikadi cikin sakon Musulunci. A lokaci guda sun bata ra'ayin Jabru da Tafwidhu da ma dukkan sauran tunace-tunace da kirdado wadanda suka fice daga tafarkin Alkur'ani.
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Allah Ya halicci halittu Ya kuma san makomarsu. Ya umarce su (da ayyukan biyayya) Ya hane su (ayyukan sabo). Kuma bai umarce su da abu ba face Ya sanya musu hanyar barin abin. Ba su zamowa masu riko (da umarnin) ko masu bari face da izinin Allah( )".
Yayin da Imam Ali bn Abi Dalib (a.s.) ya tafi kasar Sham (Syria), domin yakar Mu'awiyya a Siffin, wani daga sahabbansa ya tambaye shi cewa: "Ya Amirul Muminina! Ka ba mu labarin wannan tafiya tamu, shin da hukumcin Allah ne ko da kaddararSa?" sai ya amsa masa da cewa: "Saurara dattijo, na rantse da Allah ba kwa hawan wani tudu ko ku gangara cikin wani kwari face bisa hukumcin Allah da kaddararSa".Sai Dattijon ya ce: 'Ga Allah nake neman ladar wahalata, Ya Amirul Muminina'. Sai Imam Ali (a.s.) ya ce da shi:"Kaiconka! Ta yiyu kana zaton hukumci lizimtacce da kaddara yankakkiya! Da haka al'amarin yake da sakamako da horo sun baci, kuma da alkawari da narko sun warware. Allah (S.W.T.) Ya umarci bayinSa bisa zabinsu, Ya hana su domin gargadi, Ya kallafa musu sassauka bai kallafa musu mai tsanani ba, Yana biyan kadan da mai yawa. Ba a saba masa domin rinjaya, ba a tilastawa don a yi maSa biyayya. Bai aiko Annabawa don wasa ba, kuma bai sauko da Littafi wa bayi haka a banza ba. Bai kuwa halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu a banza ba; "Wannan shi ne zaton wadanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta daga wuta( )".
An ruwaito daga Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s.) cewa an ambaci Jabru da Tafwidhu a gabansa, sai ya ce: "Shin ba zan sanar da ku wata ka'idar da ba za ku sassaba a cikinta, kuma duk wanda ya yi jayayya da ku sai kun rinjaye shi ba?Sai muka ce: 'E, a sanar da mu', sai ya ce:"Allah Mai Girma da Daukaka ba a biyayya gare Shi domin tilastawa, ba a saba masa don rinjaya, ba ya sake da bayinSa cikin mulkinSa. Shi ne Mamallakin abin da Ya mallakar masu, Mai iko kan abin da Ya ba su ikonSa. Idan bayinSa sun yi biyayya gare Shi, ba zai tare ko Ya hana su ba. Idan kuwa suka zabi su saba masa, in Ya ga damar tare su sai Ya yi, idan kuwa bai tare su ba suka aikata sabon, to ba kuwa Shi Ya jefa su ciki ba". Daga nan sai ya ce: "Wanda duk ya kiyaye wannan maganar, to lallai zai rinjayi mai sabawa da shi( )".
A cikin littafin Sharh al-Aka'id na Shaikh Mufid an ce:
"An ruwaito daga Abul Hasan na Uku (a.s.) yayin da aka tambaye shi batun ayyukan bayi; shin halittattu ne daga Allah Ta'ala? Sai ya amsa da cewa: "Da Shi Ya halitta su da bai barranta da su ba, alhali Yana cewa: 'Lalle ne Allah Barrantacce ne daga masu shirka'. Barrantan nan ba ta shafar zatinsu, Ya dai barranta ne daga shirkarsu da munanan ayyukansu( )".
A cikin littafin Kitabul Tauhid na Muhammad bn Ajlan, ya ce: "Na tambayi Abu Abdullah (a.s.) cewa: 'Shin Allah Ya sakar wa bayi al'amarinsu ne?', sai ya ce: "Karimcin Allah ya wuce gaban Ya saki al'amurransu gare su", sai nace: 'To kenan Allah Ya tilasta wa bayi aikata ayyukansu kenan?, sai ya ce: "Adalcin Allah Ya wuce gaban tilastawa bawa yin wani aiki sannan kuma Ya azabta shi a kan wannan aiki( )".
A ruwaito cikin Uyunul Akhbar al-Ridha (a.s.) wajen fadar Allah Ta'ala cewa: "Kuma Ya (Allah) bar su a cikin duffai, ba su gani". (Surar Bakara, 2: 17)
Abu Abdullah (a.s.) ya ce: "Ba a siffanta Allah da bari kamar yadda ake siffanta halittunSa, sai dai yayin da Ya san cewa ba su dawowa ga barin kafirci da bata ba, sai Ya hana su taimako da ludufi (tausayi), Ya bar su da zabinsu( )".
Har ila yau ya zo cikin wannan littafin wajen tafsirin Imam Ridha (a.s.) kan fadin Allah (S.W.T.) cewa: "Allah Ya sa rufi a kan zukatansu".
Sai ya ce: "Abin da ake nufi da 'Khatam' shi ne 'al-Dab'u' watau rufi a kan zukatan kafirai domin yi musu ukuba kan kafircinsu, kamar yadda Allah (S.W.T.) ya ce: "A'a Allah ne Ya rufe a kansu (zukatansu) saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan( )". (Surar Nisa', 4: 155)
To haka ne tafarkin Ahlulbaiti (a.s) yake fayyace manufar shiriya da bata da kuma cewa Allah (S.W.T.) bai halicci mutane suna batattu ko shiryayyu ba. Sai dai Ya bar musu zabi, Ya ba su nufi, Ya kuma bayyana musu hanyar alheri tare da gargadi kan hanyar sharri da halaka, Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle ne Mu, Mun shiryar da shi (mutum) ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai kafirci". (Surar Insan, 76: 3).
Kuma Yana cewa: "Kuma Muka shiryar da shi ga hanyoyi biyu". (Surar Balad, 90: 10). Watau Mun sanar da shi hanyar alheri da ta sharri, zabi kuma na gare shi.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fassara ayar da cewa: "Su dai hanyoyi ne guda biyu, hanyar alheri da hanyar sharri. Kada hanyar sharri ta fi soyuwa gare ku bisa hanyar alheri( )".
Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) ya zabi ra'ayi tsarkakakke na bayani kan halayyar dan'Adam na alheri ko sharri, da wata ka'ida: "Babu Jabru ba tafwidhu, sai dai al'amari ne tsakanin al'amurra biyu, watau mataki tsakanin matakai biyu".
Yayin da aka tambayi daya daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s), shin akwai wani mataki tsakanin tilasta-wa (jabru) da sajarwa (tafwidh)? Sai ya amsa da cewa:
"Abin da yake tsakaninsu ya kai fadin tsakanin sama da kasa".
Wannan shi ne takaitaccen bayanin tafarkin Ahlul-baiti (a.s) kan batun Jabru da Tafwidh, haka ne kuma akidar musulmin da suka yi koyi da tafarkinsu take.