Da SunanSa Mad'aukaki Amincin Allah ya tabbata ga Annabi da Alayensa
SAK'ON ANNABI MUHAMMAD (s.a.w) "Ba mu aiko ka ba sai don rahama ga talikai" (Anbiya: 107). Rahamar Allah ita ce abu na farko da ya bayyana ga bayinsa bayan bayyanar sunansa Allahu, don haka ne ma rahamarsa ta yalwaci kowane abu. Rahamar Allah a nan ta mamaye dukkan janibin halitta a samuwarta, da kuma tsarin rayuwarta da aka fi sani da Shari'a.
Shi rahama ne a Shari'a da ma'anarta mai fad'i da ta shafi siyasa, tattalin arziki, zaman tare, tsaron al'umma, yalwar al'umma , rayuwar auratayya, hak'k'ok'in yara da na mata, da raunanan mutane, hukunce-hukuncen ibadoji da mu'amaloli, kawar da talauci da fatara daga cikin al'umma, ilmantar da al'umma gaba d'aya ta yadda ba za a samu jahili ko da d'aya ba, samar da mazauni da matsuguni ga kowane mutum. Rahama ce ga dukkan talikai da tsarin da zai samar da adalci a cikin al'ummu duk duniya baki d'aya, da ta yalwaci kowane abu, balle kuma d'an Adam mai k'ima da daraja. Don haka ne yayin da duniya ta kasance cikin duhu sai garinta ya waye da wanda Isa d'an Maryam (a.s) ya yi wasiyya da zuwansa Muhammad (s.a.w).
Rahamar ba ta tafi ba don wafatinsa, domin rahama ce mai fad'i da ta yalwaci kowane abu har alk'iyama ta tashi, don haka ne ma ya zab'a mata mahalli har goma sha biyu da zasu kasance bayyanar rahamar bayan wucewarsa. Ita siffa ce mafificiya ga Manzon Allah, Suna ne da Allah ya tsaga shi daga gareshi ya yafa masa shi, don haka ne ya zamanto rahama ga dukkan talikai da rahmaniyyarsa, rahama ga muminai da rahimiyyarsa da ta tsattsago daga rahamaniyyarsa.
Sai ya kasance yana da fifikon da babu wani mahaluki da ya taka shi, wannan matakin shi ne matakin "Hamd" wanda alaminsa shi ne "Tutar Hamd", sai ya sanya mai rik'on wannan tutar shi ne wasiyyinsa Ali (a.s), yana cewa da shi: "Kai ne mai rik'on tutata duniya da lahira". (Duba Kanzul Ummal na Muttak'i Hindi, Bahanife: J 13, Hadisi: 36476). Sai Manzon Allah ya taka matsayin "Hamd", Alinsa kuwa yana kan "Tutar Hamd", don ya yi nuni da cewa ga k'ofarsa nan da duk wani da ya wuce ba ta nan ba, to ba zai iso gunsa ba.
Kasancewarsa rahamar Allah ga bayi, kuma wanda ya taka mataki mafi girma na "Hamd= Godiya", don ya kasance mai yawan godiya ga Ubangijinsa, ibadarsa ba don tsoron wuta ko kwad'ayin aljanna ba, wannan ita ce ibadar bayi da masu kwad'ayi, amma ibadarsa ta kasance don godiya ce ga Allah. Sai ga tsokar jikinsa Zahara (a.s) take nanata cewa da Ubangiji ya azabtar da ita a wutarsa, da ta rik'i tauhidinta a hannu.
Imam Ali (a.s) kuwa wanda yake rik'e masa "Liwa'ul Hamd = Tutar Godiya" yana munajati da Allah yana cewa: Kuma wallahi! da ka sanya ni a cikin azaba tare da mak'iyanka, ka had'a ni a wuta a tsakanin wad'anda bala'inka ya fad'a wa, na rantse da girmanka ya madogarata jagorana, ina mai rantsuwa mai gaskatawa, matuk'ar ka bar ni ina magana, to zan d'aga murya zuwa gareka tsakaninsu -'yan wuta- da muryar masu buri, kuma wallahi sai na kira ka ina kake ya masoyin muminai, ya matuk'ar burin masana, ya mai taimakon masu neman taimako, ya masoyin zukatan masu gaskiya, ya Ubangijin talikai! (Muhasabutun Nafs: Kaf'ami; S: 187).
Da matakin: "Abd" ne ya taka matakin "Hamd" domin k'arshen matakin "Abd" zai kai ga matakin "Hamd" sai Allah ya kasance Hameed shi kuwa Muhammad. Yayin da ya taka matakin "Hamd" sai ya siffantu da rahamar Ubangiji, don haka ne bayan gode wa Allah sai kirarin rahamarsa kamar yadda ya zo a surar Fatiha.
Sai ya gadar da wannan rahamar ga wasiyyai, da wannan ne sayyidi Ali (a.s) yake cewa: "Ni bawa ne daga bayin Muhammad" (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449). Sai wad'ancan haskaka goma sha biyu da 'yarsa Zahara (a.s) suka kasance feshi daga rahamar Allah ta hannun Muhammad (s.a.w) bawansa, Rininsu da saninsu na Allah ne. (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449).
"Rinin Allah waye ya fi Allah iya rini, kuma mu masu bauta ne gareshi" (Bak'ara: 138). Sai Allah ya runa su da shiriyarsa da rahamarsa, sai suka runa mu da shiriyar da Allah ya yi musu, don haka ne Muhammad (s.a.w) ya kasance rahamar Allah ga talikai baki d'aya, a bayansa kuma Littafin Allah da Alayensa (a.s).
Sai aka wajabta salati gareshi tare da wad'annan Alayen nasa goma sha uku, sai aka yi masa ni'imomi da babu wanda ya same su. Mataki ne na "Hamd", da wajabcin yi masa salati. Da wasu ni'imomi kuma da babu mai samun su sai ya rok'a kamar yadda aka yalwata masa k'irjinsa, aka sanya masa Ali d'an'uwansa wasiyyinsa mai k'arfafarsa... "Shin ba mu yalwata maka k'irjinka ba" (Sharh: 1). Amma Annabi daga Ulul azm kamar Musa (a.s) bai isa ya samu ba sai ya rok'a. "Ya ce: Allah ka yalwata k'irjina... ka sanya mini mataimaki daga ahlina, d'an'uwana Harun…" (Taha: 25 - 35).
Sak'on Manzo Muhammad (s.a.w) Babu wani addini da ya zo da rahama ga al'umma fiye da wannan addini na k'arshe, domin wanda aka aiko da shi yana d'auke da rahamar Allah (s.w.t) tare da shi. Don haka ne ma "... Ba mu aiko ka ba sai rahama ga talikai..." (Anbiya: 107). Da wannan ne zamu ga addinin nan mad'aukaki na musulunci ya zo da lamunin rayuwar dukkan d'an Adam wacce ba ta keb'anta da musulmi ba. Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo game da d'aukar nauyin al'amuran al'umma da zamu kawo wasu kamar hakan:
Daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ni ne na fi cancanta da kowane mumini fiye da kansa kuma Ali (a.s) shi ne ya fi cancanta da shi bayana". Sai aka ce da shi Imam Ja'afar Sadik' me wannan yake nufi? Sai ya ce: Fad'in Annabi (s.a.w) wanda ya bar bashi ko kaya to suna kaina, wanda kuwa ya bar dukiya to ta magadansa ce"(Tafsiri Nurus sak'alain: mujalladi 4, shafi: 240).
A wata ruwaya ta Ali bn Ibrahim ya kawo a tafsirinsa daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Babu wani wanda yake bin bashi da zai tafi da wanda yake bi bashi wajen wani jagora na musulmi kuma ta bayyana ga wannan shugaban cewa ba shi da shi, to sai shi wannan talakan marashi ya kub'uta daga bashinsa kuma bashinsa ya koma kan jagoran musulmi da zai biya daga abin da yake hannunsa na dukiyar musulmi" .
Bayan Imam Sadik' ya fad'i wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: "Babu wani dalili da ya sanya mafi yawan yahudawa musulunta sai bayan wannan magana ta Annabi (s.a.w), kuma sun yi imani da su da iyalansu" .
A wata ruwayar Sheikh Mufid ya karb'o daga majalisinsa da sanadin da muka ambata daga Imam Ja'afar Sadik' (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya hau kan mimbari sai fuskarsa ta canja kuma launi ya juya sannan sai ya fuskanto da fuskarsa ya ce: "Ya ku jama'ar musulmi! Ni an aiko ni ne kusa da alk'iyama … -har inda yake cewa- ya ku mutane wanda ya bar dukiya to ta iyalinsa ce da magadansa, amma wanda ya bar wani nauyi ko rashi to yana kaina a zo gareni" .
Haka nan ya karb'o daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Wanda yake da wata dukiya kan wani mutum da ya karb'a kuma bai ciyar da ita a b'arna ko sab'o ba sai ya kasa biya, to wanda yake binsa dole ne ya jira shi har sai Allah ya arzuta shi sai ya biya shi, idan kuwa akwai jagora mai adalci to yana kansa ne ya biya masa bashinsa, saboda fad'in Manzon Allah (s.a.w) cewa: "Duk wanda ya bar dukiya to ta magadansa ce, kuma wanda ya bar bashi ko wani rashi to yana kaina ku zo gareni, don haka duk abin da yake kan Annabi (s.a.w), yana kan jagora. (Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 492).
Da wd'annan dokokin da ire-irensu masu yawa da ba mu kawo su ba ne Musulunci ya sanya talauci ya kawu daga dukkan daular da take kusan fad'in kwata na duniya gaba d'aya a wancan zamanin. Talauci ya kawu ta yadda kusan idan ka ga mai rok'o to zai kasance abin mamaki, musulunci ba ya son zama cikin k'ask'ancin rok'on mutane, don haka ne ya kawar da talauci, ya sanya dokokin lamunin rayuwar al'umma. Duba mamakin da Imam Ali ya yi yayin da ya ga wani yana bara a kwararon birinin Kufa.
Hurrul amuli ya ambaci cewa: Imam Ali (a.s) yana tafiya a cikin lungunan garin Kufa wata rana, sai ya ga wani mutum yana rok'on mutane, sai ya yi mamaki sosai, sai ya juya da shi da wad'anda suke tare da shi suna tambayarsa Mene ne haka? Sai ya ce: Ni tsoho ne kuma kirista na tsufa ba na iya aiki kuma ba ni da wata dukiya da zan rayu da ita, sai na shiga bara. Sai Imam Ali (a.s) ya yi fushi ya ce: Kun sanya shi aiki yana saurayi sai da ya tsufa zaku bar shi?! Sai ya yi umarni a sanya wa wannan kirista wani abu na albashi daga Baitul-mali da zai rik'a rayuwa da shi (Wasa'ilus Shi'a).
Wanan k'issa tana nuna cewa; Talauci ya kawu gaba d'aya har sai da ya kasance ba shi da wani mahalli a daular musulunci. Hatta Imam Ali (a.s) da ya ga talaka guda d'aya mai bara kuma ba ma musulmi ba sai da ya yi mamakinsa, ya gan shi wani abu bare da bai dace da al'ummar musulmi ba. Sannan ya yi umarni da a sanya masa albashi da zai rayu da shi tare da cewa shi kirista ne da ba ya rik'o da musulunci, domin kada a samu talaka a k'asar musulmi ko da kuwa mutum d'aya ne. Kuma domin duniya ta san abin da musulmi suke a kai na yak'i da talauci: da cewa kuma hukumar musulunci ita ce take yak'i da talauci ta kuma d'aukaka matsayin talakawa ba kawai musulmi ba, har da wasunsu matuk'ar suna k'ark'ashin daular.
Haka nan musulunci ya d'auki d'an Adam da k'ima matuk'a ko da kuwa bai musulunta ba, sai dai duk wanda ya tab'a musulmi ya kashe su to shi kad'ai ne musulunci ya yarda musulmi su tab'a, don haka ne zamu ga a rayuwar Manzon Allah (s.a.w) bai tab'a kai hari kan mutanen da ba su suka fara kai masa hari ba. Kuma idan mutanen wani gari suka kai masa hari to bai tab'a yak'ar wasunsu na wani garin daban ba ko da kuwa addininsu d'aya ne, sai dai ya rama kan wad'annan dai da suka kai masa hari kawai.
Duk da a rayuwar musulunci an samu yak'ok'i masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga mak'iya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zab'ar b'angaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame. Don haka ne ma adadin wad'anda ake kashe wa b'angarorin biyu ba su da yawa a dukkan yak'ok'insa tamanin da wani abu. Wad'anda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu d'aya da d'ari hud'u ba. (Littafin Tafarkin Rabauta: Fasalin; Aiko Annabi Mai Daraja (s.a.w).
Musulunci bai tab'a yarda da zaluntar wani mutum ko wani mai rai ba, kai hatta da b'arnar abinci da lalata wuri da lalata k'asa ya hana balle azabtar da d'an Adam ko kashe shi, ya kuma sanya kalma mai dad'i da zaka gaya wa d'an'uwanka mutum ya yi farin ciki a matsayin sadaka. Don haka ne ya soki mai lalata kayan gona da dabbobi, ya kira shi mai yad'a fasadi da b'arna, balle kuma mai isar da cutarwa ga mutum. Saboda haka ne ma muka samu dukkan matsalolin da muke ciki a yau musamman a k'asashenmu sun taso daga rashin fahimtar musulunci ne, sai d'an Adam ya kasance ba shi da wata k'ima.
Mun rasa ilimi ta yadda yawancin mutanenmu suna rayuwa a matsayin masu k'arancin ilimi ko ma ba su da shi saboda kawai yarenmu ba a yarda ya zama yaren ilimi ba, sai wannan k'arancin ilimin da rashin lamunin rayuwar suka haifar mana da rashin ganin k'imar d'an Adam. Muna iya ganin yadda aka kashe mutane babu imani, ko tausayi, ko hankali, kamar yadda Aljazira ta nuna a rikicin da ya faru a Maiduguri, ta yadda aka kashe mutanen da su ba "Yan boko haram" ba ne, (kai ko da ma su ne ya kamata a kai su kotu domin doka ta zartar musu da hukuncin da ya dace ne). Har ma mai harbin ana gaya masa kada ya lalata bulet, kuma ya bar kai domin ana buk'atar hular, wannan lamari mai ban takaici ya yi nuni da cewa; hatta da alburushi da hula sun fi d'an Adam k'ima.
Sai ga ma'aikacin da aka d'auka aiki domin ya kare al'umma yana harbe su ba su ji ba su gani ba, ana biyansa albashi da kud'in al'umma domin ya kare ta, amma sai ga shi hatta da raunanan mutane kamar guragu yana kamowa yana harbewa. Kuma idan dai ba a d'auki mataki kan wad'anda suka yi wannan ba, to tabbas wata rana shi wanda ya sanya su yin hakan zasu yi wa danginsa ko shi ma ta fad'a kansa. Domin idan rashin hankali, da rashin imani, da k'ek'ashewar zuciya, da rashin tausayi, da rashin doka, suka yi jagoranci, to babu makawa zasu shafi kowane mutum ne. Idan rashin tsoron Allah da tunawa da cewa za a mutu a koma ga Allah ya yi hisabin dukkan abin da muka yi ya mutu murus, to sakamakon da za a samu kenan.
Musulunci ya sanya lamunin rayuwa ta hanyoyi masu yawan gaske, sai ya shimfid'a dokokin da zasu wadatar da d'an Adam kamar zakka, humusi, sadaka, Baitul mali, kyauta, da ayyukan jin k'ai, sannan ya yi matuk'ar gaba da jahilci da ba a tab'a samu ba a rayuwar d'an Adam, sai ya tilasta neman Ilimi ko da kuwa a k'asar Sin ne. Musulunci ya yi gaba da rashin ganin k'imar d'an Adam matuk'a, har ma ya 'yanta bawa saboda ubangidansa ya yanke masa al'aura. Kai hatta da iradar yara da 'yan mata yayin zab'in wanda zasu aura ya ba ta kariya. Sannan a fili yake hatta da addini bai tilasta kowa rik'o da shi sai wanda ya ga dama.
Sannan musulunci bai tab'a yarda da zubar da jinin mutum ya tafi a banza ba, don haka ne ma muke kira da gwamnati da ta biya diyya ga iyalan wad'annan mutanen da aka kashe wad'anda ba su ji ba su gani ba, kai hatta da kisan k'are dangi da aka yi wa musulmi da sunan bak'i a Jos a watan Safar 1431 muna neman a biya su diyyar wannan bala'in da ya fad'a musu. Jinin mumini ba ya fad'uwa haka banza ya wuce sai an biya diyyarsa, kuma ya hau kan gwamnati ne ta mik'a diyya ga danginsa, duba wannan misali mai zuwa da zai nuna maka matuk'ar k'ima da sak'on Muhammad (s.a.w) yake bai wa d'an Adam kamar haka:
Kulaini ya karb'o daga Hasan ya ce: Yayin da Sayyidi Ali (a.s) ya rusa rundunar d'alha da Zubair (r) sai mutanen suka gudu suna ababan rusawa, sai suka wuce wata mata a kan hanya ta firgita daga garesu ta yi b'ari saboda tsoro, kuma d'an nata ya fito rayayye sannan sai ya mutu, sannan sai uwar ta mutu. Sai Imam Ali (a.s) da sahabbansa suka same ta an jefar da ita da d'anta a kan hanya, sai ya tambaye su me ya same ta?. Sai suka ce: Tana da ciki ne sai ta ji tsoro da ta ga yak'i da rushewar mutane da gudunsu. Sai ya tambaya: Waye ya riga mutuwa a cikinsu?. Sai suka ce: d'anta ya riga ta mutuwa.
Sai ya kira mijinta baban yaro mamaci ya ba shi gadon sulusin diyyar d'ansa, sannan sai kuma ya gadar da uwar sulusi, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wacce ta gada daga d'ansa sannan sai ya ba wa makusantan matar ragowar gadonta, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wato dirhami dubu biyu da d'ari biyar, sannan sai ya ba wa makusantanta rabin diyyarta wato dubu biyu da d'ari biyar na dirhami, wannan kuwa saboda ba ta da wani d'a banda wannan da ta jefar da shi -b'arinsa- ya mutu. Ya ce: Wannan kuwa duka ya bayar da shi ne daga Baitulmalin Basara. (Biharul anwar, mujalladi 32, shafi: 214. Da Mustadrikul wasa'il, mujalladi 17, shafi: 446).
Haka nan ne musulunci ya sanya Baitulmali domin amfanin al'ummar musulmi da biyan buk'atunsu, da bayar da hak'k'ok'insu. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa: Hak'k'in mutum musulmi ba ya fad'uwa banza. (Manla yahaduruhul fak'ih, mujalladi 4, shafi: 100). Wani hadisin ya zo cewa: Jinin mutum musulmi ba ya tafiya banza. Da wannan ne musulunci ya yalwata wa al'umma da yalwa da arziki, da lamunce rayuwa, da adalci.
Musulunci ya zo da tsarin da ba shi da misali: ya haramta, ya wajabta, ya kwad'aitar, ya karhanta, ya halatta. Duba abubuwan da aka wajabta a musulunci guda: 115, da kuma wad'anda aka haramta guda: 97, da wasu: 112, da munanan halaye guda: 95, da kuma kyawawan halaye: 83, a littafin Tafarkin Rabauta. Duba ci gaban mak'alar a bayani mai suna: Musulmin Duniya.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Thursday, March 11, 2010