AIKIN KWADAGO
Hafiz Muhammad Sa’id hfazah@yahoo.com
Yin K'wadago (K'odago) Kwadago ko kuma Kodago shi ne mutum ya yi aikin lada, kamar ya yi aikin gini domin a biya shi wani kudi a matsayin ladan aikinsa bisa yarjejeniyar gwargwadon kudi da yanayin aiki da yawansa ko girmansa ko adadinsa wani lokaci da lokacisa. Ubangiji madaukaki yana fada game da hakan: "Shin su ne suke raba rahamar ubangjijinka mu ne muka raba arzikinsu a tsakaninsu a duniay kuma muka muka fifita su a kan wasu da darajoji domin wasu su riki wasu 'yan aiki, kuma rahamar ubangjinka ita tafi daga abin da suke Tarawa"[1]. Da kuma fadinsa game da Annabi Musa (a.s) "Dayarsu ta ce ya baba ka dauke shi aiki domin fiyayyen wanda zaka dauka aiki shi ne mai karfi amintacce"[2]. Da wannan muna iya sanin cewa lamarin yin kwadago ko aikin lada -aikin kudi- wani abu ne wanda yake sananne tun kafi musulunci, kuma musulunci ya zo ya zartar da shi a matsayin daya daga cikin hanyoyin rayuwar mutane.
Ayoyin da suka gabata suna nuna mana cewa; Allah ya hore wa wasu mutane wasunsu, wato akwai alakar ubangida da yaronsa a tsakanin mutane ko dan kwangila da mai aiki, da shugaba da dan aiki da makamantan hakan, kuma wannan alaka ba ta iya nuna fifiko a tsakinnsu a wurin Allah sai dai tana nuna mana yadda ya sanya sassabawar mutane ta fuskanci hore musu abin duniya da zai iya kaiwa ga tsarin rayuwarsu da samun alakoki tsakaninsu, da kuma neman abin rayuwar juna daga junansu, don haka babu wani alfahari da mai kwangila zai nuna wa dan kwangila, ko kuma mai aiki ya nuna wa dan aiki, ko mai gidan haya ya nuna wa dan haya, ko mai motar haya kamar mai tadi da zai nuna wa dan tadi ko kuma fasinja ba shi da wani alfahar ko fifiko da zai nuna a kan direba. Ita wannan alaka an sanya ta ne domin a tsara musu rayuwarsu a tsakaninsu babu dadi babu ragi, don haka ne ma ake neman girmama juna a cikin wannan lamarin domin dadada alaka da kyautata ta, da kuma cika alkawura da yarjejeniyar juna.
Ta wani bangaren kuma muna ganin yadda daya ayar ta yi nuni da cewa idan zaka dauki mai aiki to ka dauki wanda yake da ilimi kan aiki da karfin yin aikin da kuma rikon amana kamar yadda aka yi nuni da ya kasance amintacce. Wadannan sharudda suna da muhimmanci a cikin aiki, kuma muna iya ganin abin da ya rusa kasashenmu na Afurka da wasu nahiyoyinma yana komawa zuwa ga wadannan lamuran, ta yadda akan dauki mai aiki domin sanayya ko dangantaka ko nasaba ko kuma ta cin hanci da rashawa, sai a sanya wadanda ba su cancanta ba a wurin wadanda suka cancanta kuma wannan tabbas yana dukusar da kasa ya lalata ta, ya kuma karya kashin bayan tafiyarta, sai aikin da ya kamata a yi shi cikin shekaru takwas ya dauki shekaru talatin ko sama da hakan, domin duk sa'adda aka yi ba daidai ba, to wannan yana nufin maimakon a yi gaba an yi baya, maimakon a yi gyara an yi barna kenan, kuma maimakon a samu ci gaba an samu ci baya kenan, da haka ne sai komai ya tsaya cik.
Ina iya bayar da misalin cewa: idan aka ba wa dan kwangila aikin yin titi, sai mai kwangila a matsayinsa na gwamna ko ciyaman, ko kuma mai kula da kwangila ta bangaren gwamnati ya kasance maciyin amana wato ba amintacce ba ne, haka ma dan kwangila wanda zai yi aikin sai shi ma ya kasance maciyin amanar kasarsa ko al'ummarsa, idan aka yi wannan aikin na ha'inci, mu kaddara an yi shi a matsayin Naira miliyan goma daga dukiyar al'umma, sannan kuma ya kamata ne titin ya yi shekara talatin bai lalace ba idan an yi mai kyau, sai ya lalace a cikin shekara biyu kawai, wannan yana nuna maimakon a sanya wannan miliyan goma a wani abu daban kamar lafiya ko ilimi ko tsaro ko walwala da sauransu to bayan shekaru biyu kacal yana nufin ana bukatar ware wasu miliyan goma kenan domin sake yin titin. Da haka ne maimakon kasa ta ci gaba sai ta samu ci gaban shekaru hamsin cikin shekaru biyar kacan ko kasa da hakan.
Don haka ne ma wasu suke ganin yadda sama da shekaru talatin duk wanda ya hau takarar shugaban kasa ko gwamna ko ciyaman yana maganar zai samara da wutar lantarki da ruwan sha, da tsaro da aminci, da lafiya da walwala, da gyara titina da kwatami da magudanar ruwa, babban abin mamaki koyaushe al'ummarsa zata yi tunanin cewa to fa wane ya zo ya yi maganar kuma bai cika ba, wanda wannan yana nufin gurfanar da shi da binciken me ya sanya shi rashin cika alkawarin, kuma ina kudaden da ya ware don hakan, wannan magana ce wacce a tarihin rayuwar kasarsa babu wani batu kan hakan, kuma abu ne wanda ya sha ruwa kenan, kuma koda kuwa an dago maganar sai ka ji maganar beli, kamar dai wanda ya yi wa laifi wato al'ummar ita ba ta da hakki, kamar belinsa yana nufi wanda ya ba shi beli wato; alkali shi ne aka yi wa laifi, kuma wani abin mamaki babu wanda zai tayar da wannan magana har kiyama ta tashi.
Domin a samu tsarin rayuwa ya yi kyau sai Allah ya sanya sassabawar samuwarmu da lamurranmu da ayyukanmu domin a samu tafiyar tsari mai kyau, kuma wasu su mori wasu ta hanyoyi mabambanta, muna iya ganin yadda babban dalibin Manzon Allah (s.a.w) kuma kofar birnin iliminsa Imami kuma sayyidi Ali (a.s) yake cewa game da fadin Ubangiji madaukaki "Mu ne muka raba musu arzikinsu". Yana cewa: Ubangiji ya gaya mana cewa yin aikatau -kamar aikin kwangila, da na gwamnati kamar koyarwa ko aikin ofis, da na lada kamar na hayar kai domin yin wani aiki kamar noma ko gini- daya daga hanyoyin rayuwar mutane ce, yayin da Ubangiji da hikimarsa ya bambanta himmomin mutane da nufinsu da sauran halayensu, kuma ya sanya wannan hanyar rayuwar mutane ce, wani ya dauki wani aiki… da ya zamanto dole ne ga daya daga cikinmu ya yi gini ga kansa, ya yi kafinta, kuma ya sana'anta abubuwa daban-daban a komai… da rayuwar duniya ba ta daidaitu ba, dab a su samu yalwatuwa ba, da sun gajiya sun kasa, sai dai shi madaukaki ya kyautata tafiyar da duniya da sassaba himmominsu, da dukkan abin da ake neman sa wanda himmominsu suke karkata gareshi na abin da wasu suke yi wa wasunsu, kuma domin sashensu su wadatu da sashensu a bangaren halayen rayuwarsu wacce da ita ne al'amuransu suke daidaita[3].
A nan muna iya gani a fili Imam Ali (a.s) yana nuna mana cewa ganin da muke yi na sassabawar ayyuka ya taso ne sakamakon sassabawar iradoji da himmomin mutane, kuma abisa dabi'ar mutum kuma bisa dokar canjin lamurra sakamakon canjin asalinsu da madogararsu dole ne a samu canji da sassabawa da cancanjawa tsakanin ayyukan mutane sakamakon rashin himmomi da iradoji iri daya. Wannan kuwa Ubangiji ya yi hakan ne domin ya tsara mana rayuwarmu kamar yadda ta dace, saudayawa dayanmu yakan so ya yi wani abu amma sai ya samu cin karo da canji a cikin iradarsa da nufinsa, kuma himmarsa ta yi rauni game da shi sai ya fasa.
Amma abin tambaya a nan shi ne; idan aka samu zabi tsakanin shagaltuwa da kasuwanci ko kuma aikin kwadago wannan ne ya fi cancanta a yi? A bisa tsarin musulunci ya zo cewa kana da zabi ka yi daya daga ciki ta nahiyar halacci a mahangar fikihun musulunci kenan, amma ta nahiyar tattalin arzikin musulunci bisa tsarinsa ya fi son ka yi kasuwanci da ka yi aikin lada, kuma wannan wani lamari ne wanda hakikanin rayuwar mutane take nuni da shi, kuma ma'abota tajriba ta rayuwa da suka jarraba abubuwa mabambanta sun yi furuci da hakan.
Don haka ne a fi karfafa hukumomi su sanar da mutane sana'o'i da kasuwanci sai kuma su bude musu shaguna da kantuna bayan sun koya musu sun iya, kuma su taimaka musu da jari, sai a samu karancin zaman kashe wando ka zaman banza da rashin aiki da yake addabar mutane, domin gari yana dada yawa da fadi, al'umma kuma tana dada bukatuwa, don haka yawan mutane baya iya kawo talauci, sai dai rashin tsari da rashin ba wa komai hakkinsa ya kawo talauci, kuma rashin fetuu a kasashe ba ya kawo talauci domin ga Japan ba su da mai amma suna daga cikin kasashen da suka fi kowa arziki a duniya, kamar yadda Amurka ba ta hako manta amma ta fi kowa tattalin arziki mai karfi a duniya.
Sannan wannan zai yi maganin al'umma ta yi rubdugu kan arzikin kasa sai kasa ta rushe, domin tattalin arzikin kasa idan albashi ya yi masa yawa sai ya fadi ya yi kasa saboda albashi yana cinye shi sai a samu karancin kudin yi wa al'umma ayyuka. Don haka ne ma sai musulunci ya kwadaitar da yin ayyukan zasu ba mu arziki ta hanyar kasuwanci da sana'o'i da kuma wani lokacin ayyukan kwadago. Muna iya cewa; wasu kasashen kamar Faransa sun gwammace su rika ba wa marasa aiki yi albashi duk wata, sai wannan ya yi wa kasar nauyi a arzikinta alhalin kuma duk da hakan wannan abin da ake bayarwa ba ya isa, maimakon su dauki samfurin da musulunci ya zo da shi na agazawa 'yan kasar ta hanyar koyar da su sana'o'i da kasuwanci da agaza musu don dorewa kan abin da suka koya sai suka dage kan tsarinsu domin maganin wannan tsaka mai wuya da suka fada har ta jawo kone-kone da asarar biliyoyin daloli tsawon watanni sakamakon haka.
Don haka ne wadanda suka yi ilimi koda ba su samu aikin gwamnti ba to gwamnatoci suna iya agaza musu da tirenin din kasuwanci da sana'o'i domin su dogara da kansu. Kuma wasu kasashe a wadannan kwanakin kamar kasar Sin domin su yi maganin raunin tattalin arziki sun raba wa mutanen kauyuka kowane mutum gona da jari da iri domin a habbaka noma, kuma a yi maganin rushewar tattalin arziki.
Duba ka ga kasashe masu rauni irin su Itopia da Zimbabe masu dazuzzuka korra shar, amma suna fama da yunwa da talauci mafi muni, kuma babu gonaki domin babu mai kudin mallakar filayen da zai yi noma, kamar yadda kakan samu irin wannan yanayi a kasashen yammanci Afurka, don me ya sanya hukumomin ba zasu su ba su gonaki da filaye da kayan noma da iri da jari ba domin su ceci kasar daga mummunan halin da take ciki. Sau da yawa kakan samu mutane da rashin wannan ne kawai matsalarsu, da yana da gona babba, da iri da jari da an ga abin mamaki a rayuwa, da an samu habakar arzikin nahiya guda da albarkacin samuwarsa.
Don haka ne musulunci ya zo da tsarin lamunin rayuwar al'umma, kuma ya aikata hakan a aikace, har dukiya ta bunkasa da bunkasa mai yawa da tarihin dan Adam bai taba samun irinsa ba.
Ya zo cewa imam Ali (a.s) ya aika da wani gwamna Afrika, bayan wani lokaci sai ya aiko masa da wasika yana cewa dukiya ta yi yawa gun mu me zamu yi da ita? Sai imam Ali (a.s) ya ce masa ka ba wa talakawa ita domin su wadata, sai ya sake aiko da wata wasika wani lokaci zuwa ga imam (a.s) cewa talakawa sun wadatu kuma har yanzu akwai dukiya mai yawa me zamu yi da ita? Sai imam Ali (a.s) ya aiko masa da cewa ka aurar da gwagwarensu da wannan dukiya, sai ya aurar da gwagwarensu sannan sai ya aika da ragowar dukiya zuwa ga imam (a.s).
Haka ne yayin da tunanin Ali da aikin Ali ya yi hukunci da koyarwar Ali to al'umma zata rayu rayuwa mai dadi, domin aikinsa aikin Manzon Allah ne da ilimin da Allah da Manzonsa suka ba shi, kuma shi imam Ali shi tafarki ne madaidaici kuma hujjar Allah a kan mutane gaba daya da koyarwar da Annabi (s.a.w) ya yi wa al'ummarsa.
Kuma kamar yadda hukuma take daukar nauyin gina mutane su samu tsayuwa da kafafunsu haka nan ne su ma mutane aka karfafe su da idan ta samu matsalar tattalin arziki sai su agaza mata domin kada ta yi rauni ta rushe alhalin da ita ne tsarin al'umma yake kafuwa ya tasyu. Wani lokacin mukan ji maganar rage ma'aikata daga wata kasa ko gwamnti ko kampani ba tare da an maye musu da wata sana'a ko wani aiki ko kuma kasuwanci ba, wannan wani abu ne mai matukar muni matuka, musulunci bai yarda da hakan ba, domin wannan tozarta dan Adam ne, sannan kuma a bisa tsrin da Obama yake yi wa Amurka a kwanan nan sai na gani jiya ta intanet cewa; zasu kirkiro aiki na dan lokaci -part time- domin tallabar rashin aikin yi da ya fara yawa a kasar, da sauran matakai da kasashe sukan dauka.
A bisa hakika tsarin karfafa dogaro da kai wani abu ne daga sirrin tattalin arzikin al'umma da walwalarsu, sannan kuma jikan Imam Ali (a.s) wato Imam sadik (a.s) ya yi nuni da hakan a yayin da Ammarus Sabadi ya tambaye shi cewa; "Mutumin da yake kasuwanci amma idan ya yi aikin kwadago sai a ba shi abin da yake samu a kasuwanci, sai ya ce: kada ya yi aikin kwadago, sai dai ya nemi Allah madaukaki ya arzuta shi ya yi kasuwanci, domin idan ya yi kwadago sai ya hana kansa arzikin"[4].
Sannan kuma an hana mutum ya karbi aiki bai yi komai ba sai ya ba wa wani kuma ya ci riba a kai, don haka idan yana son ya samu riba a kai dole ne shi ma ya kasance ya yi wani abu ko yaya ne a cikin aikin kamar yadda zamu iya ganin hakan a koyarwar alayen Annabi (s.a.w) yayin da aka tambayi dayansu (a.s) game da mutumin da yake karbar aiki kuma sai ya ba wa wani ya yi shin zai iya cin riba a cikinsa, sai ya ce: a'a, sai dai idan ya yi wani aiki a cikinsa shi ma[5].
Kuma an tsananta matuka kan wanda yake zaluntar dan aiki kuma ya hana shi ladan aikinsa kamar yadda wata ruwaya daga fiyayyan halitta take cewa; Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya zalunci dan kwadago to Allah zai shafe aikinsa kuma ya haramta masa kanshin aljanna, kuma hakika kanshinta ana jin sa tun daga nisan tafiyar shekaru dari biyar"[6]. Da fadinsa cewa; "Zaluntar dan aiki hakkinsa yana daga manyan zunubai[7].
Haka nan an hana jinkirta ba wa dan aiki ladansa kamar yadda fiyayyen manzanni yake cewa: "Ku ba wa dan aiki ladansa kafin guminsa ya bushe, kuma ku sanar da shi ladansa yana cikin aikinsa"[8]. Amma game da yarjejeniya kuwa to dalibinsa Imam Ali (a.s) yana cewa ne: "Manzon Allah ya hana daukar mutum aiki har sai an sanar da shi ladan aikinsa"[9].
Amma tsarin albashi musulunci yana zuwa ga cewa; a ba wa kowane mutum abin da zai ishe shi rayuwa daidai gwargwadon halin da yake ciki da kuma nauyin da yake kansa, wannan kuma tsari ne da duk fadin duniya tun bayan Manzon Allah da hukumar Imam Ali ba a sake samun wanda ya yi aiki da wannan tsarin ba a hukumance.
Hafiz Muhammad Sa'id Kano,
hfazah@yahoo.com
Cibiyar Al'adun Musulunci
2/13/2009
---------------------------------
[1] Zukhrufi: 32.
[2] Kasas: 26.
[3] Wasa'ilus shi'a: 13/244/3.
[4] Alkafi: 5/90/3.
[5] Alkafi: 5/273/3.
[6] Amalis saduk: 347/1.
[7] Albihar: 103/170/27.
[8] Kanzul ummal: 9126.
[9] Alfakih: 4/10/4968.