Yin Ceto1
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Ceto Ko Yaye Zunubbai
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Ceto wani asali ne wanda Kur'ani da sunnar Ma'aiki suke tabbatar da shi, sannan dukkan kungiyoyin musulmai sun amince da shi ba tare da wani shakku ko kokwanto ba. Hakikanin ceton waliyyan Allah kuwa shi ne, sakamakon matsayin da suke da shi a wajen Allah, a cikin wani yanayi na musamman sai su roki Allah ya gafarta wa wasu daga cikin bayinsa laifukan da suka yi a kan takaitawarsu.
Waliyyan Allah ba kowane mutum mai sabo ne zasu ceta ba, zasu ceci mutumin da kawai ya kasance alakar imaninsa da Ubangiji ba ta yanke ba, haka nan alakarsa da wadannan waliyyan Allah ba ta yanke ba. Da wata ma'ana shi ne idan ya kasance bai nisanta ba daga halayen kwarai na ruhi, ta yadda mutum zai kai wani matsayin da ba zai yiwu ya sake komawa mutumin kirki ba.
Batun ceto kasantuwar yadda yake abu tabbatacce a tsakanin musulmai ta yadda duk wani malami ko masani na musulunci ka tambaya zai ba ka amsa da cewa ai ceto yana daya daga cikin akidun musulunci. Sannan kodayaushe a cikin addu''o'i nuni ga wadannan masu ceto na hakika. Mafi yawancin mutune suna cewa: Ya Allah ka sanya Manzo a matsayin mai cetommu, kuma ka sanya cetonsa a gare mu karbabbe ne!
Gudanar falalar Ubangiji ta hanyar ceton masu ceto
Duniyar halitta ta kafu ne a kan tsari na dalili da sanadi (wato duk abin da zai faru yana da dalili da na sanadi a kan faruwarsa) Sannan bukatocin danAdam na duniya suna samuwa ne ta hanyar wasu daga cikin bayin Allah tare da izinin Ubangiji. Falala da ni'imar ruhi ma ba ta fita ba daga cikin wannan tsari, Shiryarwa da gafarta zunubbai duk suna daga cikin kwarar ni'imar Ubangiji, kuma suna karkashin wannan tsari.
Misali nufin Allah wanda yake mai hikima ya tsara cewa kwarar ni'imarsa zata biyo ne ta hanyar manzanninsa zuwa ga sauran mutane, domin babu wani mutum ban da su annabawa da ya cancanci sauraren sakon Allah kai tsaye daga gare shi.
Tare da kula da wannan babu wani abu wanda zai hana cewa kwarar ni'ima a wata duniyar ma zata kasance kamar haka bisa wannan tsari. Wato gafarar Allah zata bi ta hanyar ruhin tsarkakan bayin Allah zuwa ga bayin masu sabo wadanda suka cancanci su sami wannan falalar, kamar yadda ya ksance shiryarwar Ubangiji a wannan duniya tana biyowa ne hanyar annabawa da manzannin Allah madaukaki zuwa sauran al'umma.
Babu shakka wannan ni'aimar Ubangiji tana iya gangarowa kai tsaye daga Allah bat re da ta biyo ta hanyar wani daga cikin waliyyan Allah ba zuwa ga masu sabo da zunubi. Amma nifin Allah wanda yake cike da hikima ya yi rigaye a kan cewa wannan falala ta ruhi a waccan duniya sai ta biyo ta hannun wasu daga cikin bayin Allah masu tsarki. Amma me ya sa haka?
Wannan kuwa ya kasance domin waliyyan Allah da bayinsa na kwarai da mala'ikunsa na sama da masu daukar al-arshi, wadanda suka gabatar da dukkan rayuwarsu wajen bin Allah madaukaki, sannan ba su taba ketare iyakar Allah daga bautarsa ba, don haka sun cancanci yabo da girmamawa, daya daga cikin alamar girmamasu kuwa shi ne, karbar addu'arsu dangane da masu sabo, wannan kuwa yana kasancewa ne a cikin yanayi na musamman,
Ceton waliyyan Allah ba haka nan yake a sake ba, wato babu wani sharadi. Waliyyan Allah bazasu iya ceto ba tare da izinin Allah ba, wato ya zamana su ne suke da ikon yin hakan daga kawunansu, alhali duk al'amura a ranar kiyama suna hannun Allah, kamar yadda kowane lokaci muke karantawa a cikin sallolimmu cewa; "Shi kadai ne mai mulikin ranar sakamako", amma duk da haka wanda yake da wannan cikakken iko zai bai wa wasu daga cikin bayinsa izini ta yadda zasu iya gudanar da wannan aiki.
Ceto Wani Nau'i Ne Na Tsarkakewa
A mahanga Kur'ani mutuwa ba ita ce karshen rayuwa ba, mutuwa wata kofa ce domin shiga wata duniya da ake kira barzahu inda rayuwarta ta sha bamban da rayuwar wannan duniyar, yayin da wasu daga cikin mutane suna cikin azaba wasu kuwa suna cikin ni'imar Ubangiji.
Wasu gungu daga cikin masu zunubi wadanda ba su yanke alakarsu ba da imani da Allah madaukaki, sannan sun kiyaye alakarsu da masu ceto a wajen Allah, to wadanda zasu hadu da sakamakon wasu daga cikin ayyukansu a cikin rayuwar barzahu, wannan kuwa zai kasance ne a matsayin tsarkake su daga zunubban da suka aikata, wadannan mutane yayin da zasu jefa kafarsu a filin tashin kiyama, sakamkon nau'i na tsarkakewar da aka yi musu arayuwar barzahu, zasu samu cancantar samun gafarar ubangijin talikai, a mahangar wadanda suka dauki al'amarin ceton masu matsayin tabbataccen al'amari, wani abu ne na tsarkake dukkan wata sauran daudar zunubi da ta rage na masu sabo, ta yadda ruhinsu zai tsarkaka daga dukkan wata tsatsar da ta bata shi da zunubi.
Bambancin Ceto Da Kamun kafa A Rayuwar Duniya
Sakamakon wasu maganganu ya sanya wasu mutane da ba su fahimci al'amura ba, suna tunanin cewa, ceton waliyyai kamar kamun kafa da wani mutum ne a duniya wajen cimma wani abu da yake bukata, wato amfani da wanda ka sani ko nuna bambanci domin cimma wani abu, don cire wannan matsala daga kunnuwan mutane, zamu bayyanar da bambanci tsakanin ceto da kamun kafa a rayuwar duniya ta hanyoyi guda uku kamar haka:
1-Ceto a ranar lahira yana hannun Allah madaukaki ne, wato komai zai samu tushe ne daga gare shi, wato shi ne zai tayar da mai ceto sakamakon matsayi na musamman da yake da shi zai ba shi izinin yin ceto, ta yadda Allah zai gudanar da rahamarsa da jinkansa ga bayinsa ta hanyar shi wannan bawa nasa, amma a duniya abin sabanin haka yake, domin kuwa mai laifi ne zai tayar da wanda zai shigar masa tsakani, idan da bai sanya wanda zai shigar masa ba, shi da kansa ba zai yi tunanin yin hakan ba. Idan har Kur'ani yana ba da umarni ga wadanda suka yi zunubi da su je wajen manzon Allah a nan duniya, domin ya nema musu gafarar Allah, don haka wannan ma zai samo asali ne daga shi Allah madaukaki, domin kuwa zai bai wa masu zunubi umarni da su yi wannan aiki, domin idan da bai bayar da wannan umurnin ba, to da babu yadda za a yi su je wajen Manzo (s.a.w) idan kuwa har ma sun tafi ba tare da umurnin Allah ba to da zuwansu ba zai yi wani tasiri ba.
2-A cikin ceto na gaskiya mai ceto yana karkashin inuwar rububiyya ne, amma a cikin ceton na bata, mai karfi zai tasirantu da maganar mai ceto ne, sannan shi kansa mai ceto ya tasirantu da maganar mai laifi ne.
3-A cikin ceto na duniya nuna bambanci ne kawai a cikin dokoki, ta yadda karfin mai ceto zai yi tasiri a cikin mai kafa doka ko mai tafiyar da doka ya rinjaye shi, ta yadda mai karfi kawai zai iya gudanar da dokarsa a kan raunana. Amma a ceton lahira babu wani wanda zai gwada wa Allah karfi ya rinjaye shi ko ya tilasta shi, sannan babu wanda zai iya hana a gudanar da doka. Ceton rahamar Ubangiji wanda yake mai fadi ya samo tushe ne daga shi kansa Allah madaukaki mai tausayi, yana so ne ta wannan hanyar ya tsarkake wasu daga cikin bayinsa wadanda suka cancanci hakan kuma zasu iya karbar wannan tsarkakewar.
Amma gungun da ba zasu samu ceto ba, ba ya nufin cewa ba akwai nuna bambanci a cikin dokokin Ubangiji, wannan yana nufin cewa su wadannan ba su cancanci samun wannan rahama mai fadi ba ce ta Allah ta'ala, don haka ne zasu yi saura a cikin wannan hali da suke ciki. Rahamr Ubangiji ba kamar akwatin banki ko na wani dan kasuwa bane, ta yadda zai iya karewa, rahamar Allah ba ta karewa sai dai ya zamana wanda za a ba bai cancanci ya karbi wannan falalar ba, balantana ya samu wannan rahama.
Idan Allah yana cewa: "Allah ba ya gafarta wa Mushrikai" , wannan ya samo asali sakamakon cewa zuciyar mushrikai kamar wani jarka ce a rufe, idan da za a saka shi a cikin kogi guda bakwai ruwa ba zai taba shiga a cikinsa, ko kuma kamar kasar da ba ta yin noma mai gishiri, duk yadda aka yi ruwa babu wani abu wanda zai faru sai dai ta jike ko kaya ta fito daga gareta.
Idan Kur'ani yana Maimaita cewa, ceto a ranar kiyama zai kasance daga wadanda Allah ya amince wa, kamar yadda yake cewa: "Babu wanda zai yi ceto sai dai wanda muka yardar mawa" . Wannan ya faru ne sakamakon ya san cewa wane ne daga cikin bayinsa ya cancanci baiwar Allah madaukaki da wanda bai cancanci wannan baiwar ba. Ba wai kawai mushirikai ba zasu rahamar Allah da ceton waliyyan Allah ba, har da wadanda saboda tsananin zunubinsu ba zasu cancanci samun wannan gafarar ubangijin ba, don haka ceton bayin Allah ma ba zai kai zuwa garesu ba.
Dalilai Daga Kur'ani Dangane Da Ceto
Ayoyin da suka zo dangane da ceto manyan bayin Allah sun fi gaban mu kawo dukkansu a cikin wannan bahasi, don haka zamu kawo wasu daga cikinsu ne, domin mai karatu ya samu cikakkiyar masaniya dangane da batun ceto da sharuddan da suke tattare da yin hakan, wanda muhimmi daga cikinsu shi ne izinin Allah madaukaki. Saboda haka za a ambaci wani asali tabbatacce duka da yake ba za a kawo sunayen masu ceto ba, amma za a kawo siffofinsu das sharuddansu wannan ya wadatar, kamar haka:
A nan zamu ambaci ayoyi guda biyar idan muka kula da kayu zasu tabbatar mana da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:
A-Ceto a ranar kiyama ya samo tushe ne daga Kur'ani.
B-Wasu mutane suna da hakkin yin ceto wadanda suke da wasu siffofi na musamman.
Ga matanin wadannan ayoyin kamar haka:
1-"Wa zai iya yin ceto ba tare da izininsa ba" .
Zahirin wannan aya yana nuna cewa babu wanda zai iya yin ceto sai tare da izini daga Ubangiji, amma ta wata fuska wannan aya tana nuna mana cewa akwai wadanda zasu yi ceto a ranar kiyama tare da izinin Ubangiji.
2-"Babu wani mai ceto sai bayan izininsa" .
3-"Babu wanda ya mallaki ceto daga abubuwan da suke bauta wa sai wanda ya riki wani alkawari da Allah" .
Wato wasu ne kawai daga cikin mutane suke iya yin ceto, wato wadanda Allah ya yi wa alkawarin yin ceto, Allah madaukai zai bayar da alkawarin ceto ga wasu daga cikin wadanda ake bauta wa wato wadanda suka kadaita Allah madaukaki kamar irin annabi Isa (a.s) wanda kiristoci suke bauta wa.
4-"A wannan ranar ceto ba ya amfani sai dai wanda Allah mai rahama ya bai wa izini ya kuma yarje masa magana" .
5-"Babu wanda cetonsa zai yi amfani sai wanda Allah ya bai wa izini" .
Mala'iku Da Ceto
A ayoyin da suka gabata ba a ambaci sunayen masu ceto ba, kawai an ambaci siffofinsu ne, amma a wasu ayoyin an ambaci sunayen masu ceto. kamar haka:
"Da yawa daga cikin mala'iku a sama cetonsu ba ya wadatar da komai, sai bayan Allah ya bayar da izini ga wanda ya so ya kuma yarje masa" . A cikin wannan aya an yi nuni da wasu mala'iku a sama wadanda zasu yi ceto a cikin yanayi na musamman.
Ceton Masu Matsayi Abin Yabo
Kur'ani mai girma yana bayyana Manzo a matsayin abin yabo, sannan ruwayoyi suna fassara wannan da cewa, wannan makamin na ceto ne. Dangane da haka ne Kur'ani yake cewa:
"Don gabatar da sallar dare ka ta shi wani bangare na dare, da sannu Allah zai tayar da kai matsayi abin yabo" .
Zamakhsahri yana rubuta cewa: Matsayi abin yabo, wacce wannan aya take ambata, yana nuni ne da matsayin da Manzo zai samu na wanda yarda da shi, duk wanda ya ga Manzo a wannan matsayi zai yabi Manzo a kan samun wannan matsayi, wane matsayi wanda ya fi na ceto wanda dukkan wadanda suka halarci tashin kiyama zasu yabi Manzo a kansa?
Sheikh Tabarasi yana cewa: Dukkan malama tafsiri sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da wannan matsayi abin yabo shi ne mukamin ceto da Manzo zai samu a ranara kiyama, sakamakon haka ne zai samu yabo daga dukkan halitta. Sannan dukkan annabawa zasu kasance karkashin wannan tuta ta Manzo, shi ne kuma farkon wanda zai yi ceto kuma farkon wanda za a karbi cetonsa.
Ruwayi mutawatir suka zo domin bayyana hakikanin wannan aya suna cewa: Abin da ake nufi da wannan matsayi abin yabo shi ne makamin ceto da Manzo zai samu ranar kiyama, Suyudi a cikin Durrul Mansur, Bahraini a cikin tafsirin burhan sun ruwaito hadisai daga shugabannin addinin musulunci, domin mu takaita ba zamu samu halin kawo su ba a nan.
Manzo Da Ba Shi Kyauta Har Ya Amince Da Ita
A wata aya ana bayanin cewa Allah madaukaki zai bai wa Manzo kauta har sai ya yarda, kamar yadda aya take cewa:
"Lallai lahira ta fi maka wannan duniya. Da sannu Allah zai ba ka kyauta har zai ka aminta" .
Aya ta biyu tana da rikitarwa ta fuska guda biyu kamar haka:
Na daya: Ba a bayyanar da inda Allah zai bayar da wannan kyauta ba, ta wace hanya aka san cewa ranar kiyama ne zai faru?
Na iyu: Ba a bayyanar da abin da Allah zai bayar ba, watakila abin da za a bayar wani abu ne ba ceto ba.
Amma rikitarwa ta farko ana warwareta ta hanyar kula da abin da ya gabaci wannan aya, domin kuwa Allah ya yabi lahira kuma ya fifita ta a kan duniya, sannan bayan wannan ne yake cewa: "Allah zai ba ka har sai ka yarda". Idan muka hada wadannan ayoyi guda biyu zamu gane cewa wurin da za a bayar da wannan kyauta na wannan duniyar ba ce wata duniya ce ta daban.
Babban matsayin Manzo wanda shi rahama ne ga dukkan halitta, yana wajabta masa a wannan rana mai ban tsoro ya tuna da al'ummarsa, ta yadda sakamakon gafarta wa da yawa daga cikinsu ya yi farin ciki da haka. Tare da kula da wannan asali za a kawar da rikitarwa ta biyu a cikin wannan al'amari cewa, ceton al'umma ake nufi da wannan kyauta wanda zai sanya Manzo (s.a.w) ya amince.
Abin da kuwa yake tabbatar da wannan ma'ana shi ne ruwayoyin da suka zo a kan cewa abin da ake nufi da wannan kyauta wacce za a bai wa Manzo har sai ya yarda, shi ne ceton al'ummarsa.
Zuwa nan mun fa'idantu daga Kur'ani dangane da asalin ceton, sannan hadisai da suke Maganakan ceto saboda yawansu sun fi gaban muka kawo su duka a nan, saboda haka daga wadannan ruwayoyi wadanda suke sama da dari zamu takaita ne kawai da wasu daga cikinsu.
Manzo (s.a.w) yana cewa: "An ba ni abubuwa guda biya…kuma an ba ni ceto sai na yi tanadinsa ga al'umma ga duk wanda bai yi shirka da Allah ba".
Sannan Manzo yana cewa: "Nine farkon wanda zan yi ceto kuma farkon wanda za a karbi cetonsa" .
Abu Zar yana cewa: Manzo (s.a.w) ya yi salla a wani dare, Sai ya karanta wata aya har zuwa asuba yana ruku'u da sujjada da ita, Wannan aya ita ce: "In ka yi musu azaba, lallai su bayinka ne, idan kuwa ka yi musu gafara, lallai kai mabuwayi ne mai hikima". Yayin da asuba ta yi sai ya ce wa Manzo (s.a.w) ba ka gushe ba kana karanta wannan aya har asubahi ta yi, kana ruku'u kana sujjada da ita, Sai ya ce: Lallai na roki Allah ta'ala ne a kan ceton al'ummata, kuma ya ba ni shi, insha Allah zata kasance ga duk wanda bai yi shirka da Allah ba a kan komai.
A nan zamu takaita da wadannan ruwayoyi daga Manzo (s.a.w) a cikin tafsirin manshur Jawid wadanda muka rubuta shi ta fuskar maudu'ai na Kur'ani, muna kawo ruwayoyi fiye da dari da aka ruwaito daga Manzo da aimma (a.s) dangane da ceto, a cikin wannan littafi mun kawo sharuddan ceto da masu ceto da sharuddan wadanda za a ceta aranar kiyama da sakamakon ceton a bayyane.
Kamar yadda yake kowa ya yarda da asalin ceto har kuwa da Muhammad Bn Abdul wahab da malaminsa Ibn Taimiyya duk sun yarda da wannan magana, don haka a nan ba zamu tsawaita magana ba a kansa. Abin da yake muhimmi a nan shi ne, mas'la ta biyu, wacce wahabiyawa suke haramtawa, wannan kuwa shi ne neman ceto daga wadanda suka cancanci yin ceto na gaskiya. Don haka a kan wannan ne zamu yi cikakken bayani a fasali mai zuwa.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012