HAKKIN UBA
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babu karfi sai da Allah".
A nan saboda girma da muhimmancin hakkin iyaye a kan 'ya'yansu babu wani abu da zamu ce sai dai; Duk abin da kasan zaka yi in dai bai saba wa shari'a ba don faranta masu rai to wannan abin ka yi shi, idan kana da da zaka iya gano sirrin haka, duba ka ga danka da wahalar da kake sha a kansa, wannan kuwa bai kebanta da mai da ba domin hankali yana iya fahimtar wahalar rayuwa da iyaye suke sha a kan 'ya'ya.
Akwai hadisai masu yawa da suka zo game da girmama iyaye da kuma biyayya a gare su kamar haka;
1-Wanda ya yi kallo zuwa ga iyayensa kallo na rahama Allah zai rubuta masa ladan aikin Hajji .
2- Wanda ya kalli iyayensa kallo na wulakanci Allah ba zai karbi sallarsa ba koda kuwa sun kasance suna masu zaluntarsa ne .
3- Umarnin iyaye ana gabartar da shi a kan wajibi kifa'i .
4- Kada a daga sauti kan sautin iyaye ko gabata gaba gare su .
Imam Ali (a.s) yana cewa: "Da yana da hakki kan uba, kuma uba yana da hakki kan da, daga hakkin uba a kan da, ya bi shi a komai sai dai cikin sabon Allah, kuma hakkin da a kan uba shi ne ya kyautata sunansa, ya kyautata ladabinsa da koyar da shi Kur'ani" .
Amma girmama 'ya'ya da kyautata musu ba ya nufin mutum ya bari su kai shi ga fadawa cikin fitina da kaucewa ra'ayi na gari. Sau da yawa wani lokacin maimakon iyaye su yi wa 'ya'yansu tasiri sai lamarin ya juye akasin haka. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Zubairu bai gushe ba tare da mu Ahlul-bait har sai da dansa Abdullahi mai shu'umi ya girma" .
Don haka ne ake son kyautata tarbiyyar yara domin su samu 'ya'ya nagari wadanda zasu kawo gyara ba kawai a gidajensu ba, har ma da a cikin al'ummarsu. Domin neman samun albarkar masu albarka zan so kawo takaitacciyar nasihar nan ta sayyidina Ali (a.s) ga 'ya'yansa domin mu ga misalin yadda 'ya'ya sukan zama nagari sakamakon samun tarbiyya mai kyau daga iyaye.
Sayyidi Ali mijin nana Fatima (s.a) yana yi wa 'ya'yansa Imam Hasan da Husain (a.s.) wasiyya da gargadi a lokacin da tsinanne Abdurrahman dan Muljam ya sare shi da takobi yana mai cewa:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Ina muku wasici da tsoron Allah da kuma shawartarku da kada ku rusuna ga (jin dadin) duniya ko da kuwa tana bin ku, sannan kuma kada ku yi bakin ciki a kan wani abu na duniya da aka hana ku. Ku fadi gaskiya da yin aiki don lada. Sannan ku kasance masu tsanani ga azzalumai, kuma masu taimakon wanda aka zalunta.
Ina muku wasici, da sauran dukkan 'ya'yana da iyalaina da dukkan wanda rubutuna ya isa gare shi, da jin tsoron Allah da tsara al'amuranku, da kuma kyautata alaka tsakaninku, don kuwa na ji kakanku (Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Kyautata (alaka) tsakanin (juna) ya fi salla da azumi".
Ina hada ku da Allah cikin al'amarin marayu, kada ku bari su shiga cikin wahala, sannan kada a cutar da su a gabanku.
Ina hada ku da Allah cikin al'amarin makotanku, don kuwa sun kasance wasiyyar annabinku, Ya kasance yana yawan magana a kansu har sai da muka tsammanci zai ba su wani sashi na gado.
Ina hada ku da Allah cikin lamarin Kur'ani, kada ku bari waninku ya wuce gabanku wajen aiki da shi.
Ina hada ku da Allah cikin lamarin salla, don kuwa ita ce jigon addininku.
Ina hada ku da Allah dangane da Dakin Ubangijinku (Ka'aba), kada ku kaurace masa matukar dai kuna raye, don kuwa idan aka bar shi ba zaku tsira ba.
Ina hada ku da Allah kan jihadi saboda Allah da dukiyoyinku, kawukanku da harsunanku.
Ina gargadinku da kiyaye zumunci da biyan bukatun al'umma, sannan kuma ku nisanci nesantar juna da kuma yanke zumunci. Kada ku bar umurni da ayyukan alheri da kuma hani da munana, don sai mafiya sharrin cikinku su doru a kanku, kuma ku yi addu'a a ki karba.
Daga nan sai ya ce:
Ya ku 'ya'yan Abdul Mudallib!: Ba na kaunar in gan ku kuna zubar da jinin musulmi kuna masu cewa: "An kashe Amirul Muminin". Ku kula kada ku kashe wani saboda ni in ba wanda ya kashe ni ba.
Ku hakura, idan har na cika daga wannan sara da ya yi mini, to ku sare shi kamar yadda ya sare ni, amma kada ku lalata jikinsa (gabobinsa), don na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Ku guji lalata jiki ko da kuwa jikin mahaukacin kare ne.
Mu duba mu ga wannan wasiyya mai ratsa jiki da take kunshe da mafi girman kyawawan halaye. Bayan nan akwai wata gajeriyar wasiyya mai amfanarwa ga al'ummar wannan duniya a yau wacce ita ma ya yi ta ne ga 'ya'yansa Imam Hasan da Husaini (a.s.) Jim Kadan kafin shahadarsa yana mai cewa:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Wasiyyata gareku ita ce: Kada ku hada Ubangiji (Allah) da kowa wajen bauta, sannan kada ku yi watsi da sunnar Manzon Allah Muhammadu (s.a.w). Ku tsayar da wadannan jiga-jigai guda biyu da kunna wadannan fitilu guda biyu, sai ku tsira daga sharr.
Jiya na kasance sahibinku (tare da ku), a yau kuma darasi gare ku, sannan gobe kuma zan rabu da ku. Idan har na saura (idan har ban rasu ba), to ni zan dau fansar jinina (in rama ko in yafe), idan kuwa na cika, to daman mutuwa abar riska ce. Idan na yafe, to hakan abin kusanci (ga Allah) ne gare ni, sannan a gare ku abu mai kyau, don haka ku yafe" . "…shin ba ku son Allah Ya gafarta muku" .
Wallahi, wannan mutuwar da ta zo min ba ta kasance abin ki gare ni ba, ko kuma hatsarin da ba na so ba. Ni ban kasance ba face kamar matafiyin dare wanda ya kai ga gacinsa, ko kuma mabukacin da ya cimma manufarsa "...kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alheri ga barrantattu" .
Magana kan kimar uba ta riga ta gabata a cikin magana kan hakkin uwa, don haka ba zamu tsawaita magana kan wannan lamarin ba a nan.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Tuesday, May 31, 2011