Yawi Shi'a Kage
  • Take: Yawi Shi'a Kage
  • marubucin: Sheikh Waili
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:7:12 1-9-1403

Yawi Shi'a Kage

SHEIKH WA'ILI
Babi Na Hudu

Wasu Daga Cikin Kage-kagen da Ake Yi wa Shi'a
A binciken da na gabatar a baya na yi kokarin in yi bayanin ra'ayin Shi'a jini da tsoka da kuma tunani, kuma tuni na riga na bayyana cewa lalle kissar Abdullahi dan Saba' tana taka rawa ta musamamn ta yadda duk wanda yake so ya rufe fuskar shi'anci ta ainihi yake labewa a bayan ta, don ma kada mai karatu ya ce lalle mas'alar Abdullah dan Saba' ba zai yiwu ta zama lamari na rudu ba, to a nan ma bari in ba shi wasu misalsali na kage-kagen da aka yi wa Shi'a har ya zama ya ga gaskiyar abin da muke da'awa da idaniyar sa.
Lalle wadannan lamuran da ambaton su sai zo da ma makamantan su suna bukatar kwakkomawa a kan abin da tarihin mu ya tattaro da kuma akidarmu, tare da kokarin gyara tsokacin abin da tarihin ke dauke da shi, domin wanzuwar wadannan gurbatacciyar ajiyar a cikin kundin tarihin mu zai wanzu yana taka rawar da tsutsa (wadda ke cin katako da kayan amfani, kamar zago dss) take takawa a can kasan tushen gini har sai wata rana ba zato ba tsammamni sai a ga kawai ginin ya fadi, kuma ba wanda wannan asarar zata wayi gari da shi sai musulmai a kan kansu, amma wanda ya rubuta wadannan abubuwan a tsara su a layi tuni ya ruga ya wuce zuwa rahamar Ubangijin sa kuma da sannu zai tsaya a gaban Mai hukunci adali, sai dai ya zame mana dole mu gyara yanayin da muke ciki kuma bai halattaba akaowane yanayi mu dura wa kan mu da `ya`yan maganin rigakafin cutar (tsakuwa ba ) alhali ba ya wanzuwa zuwa wani lokaci a jikin dan Adam, amma ba za mu yi wa kan mu riga kafin rarraba da daidaita ba, da kuma riga kafin mummunan tunanin wanda yake wanzuwa kuma tasirinsa ma yake wanzuwa har zuwa dogon lokaci ba. A yanzu kan lokaci ya yi da zan bayyana maka misalsalin wadannan kage- kagen.

Misali Na Farko: a Kan Auren Mata da Yawa
Hada tsakaninn mataye da kuma iyakance su, jamhurun masulmai sun tafi a kan cewa, bai halatta ga da ya hada mata sama da guda hudu ba saboda fadinsa madaukaki, "Ku auri wadanda suka yi muku na daga mata biyu-biyu da uku-uku da hudu-hudu) Nisa'i / 3. Kuma saboda Sunna madaukakiya wacce ta iyakance adadin mata zuwa hudu kamar yadda zai zo, kuma Shi'a ma a kan wannan kamar sauran musulmai suke ba sa halatta aurar mata sama da hudu, kama a wajen su ma da mutum zai saki daya daga cikin hudun bai halattaba a gare shi ya cike adadin su zuwa hudu ba har sai wadda ya saka ta gama iddah, kuma dukkanin Shi'a sun hadu a kan haka, kuma ga misalai na daga maganganun su zan kawo maka.
Na Daya: Shahid na farko yana fadi a cikin lum'a: Bai halatta ga da ya hada sama da `ya`ya guda hudu ba, ko kuma `ya`ya biyu da bayi biyu ko `ya`ya uku da baiwa daya, ko bawa ya hada sama da bayi hudu ko `ya`ya biyu ko `ya daya da biyi biyu. Kuma ba a halatta masa bayi uku da `ya guda daya ba.
Na Biyu: Mikdadus Suyuri ya na fadi a cikin Kanzul irfan takaituwa a kan mata hudu da kuma rashin halaccin yin kari a kan haka ga aure dauwamamme, abu ne da aka hadu a kan sa kai har ma auren wani lokaci a wajen da yawa daga cikin malaman mu, saboda fadin Manzo (s.a.w) ga Gilan yayin da ya Musulunta, alhali yana da mata 10, : Ka riki hudu ka rabi da sauran. Ai ragowar su, kuma saboda fadin Imam sadik, bai halatta ga rowan namiji ya gudana a cikin mahaifar sama da mata hudu `ya`yaye ba, kuma mai karato zai iya komawa kowane irin littafi na fikihu daga cikin litattafan imamaiyya ya duba babin aure domin ya gain ko in mas'alar aure tana daga cikin mas'alar da take ijma'i ce a wajen su ko kuwa, amma tare da haka saurari, ka ji abin da sashin malaman musulunci suke fadi daga cikin Ahlus-sunna wadanda ya wajaba su zama abin koyi a wajen amana da gaskiya.
A- Ibn Hazam yana cewa ba a saba a kan cewa bai halatta ga wani ya auri sama da mata hudu ba: Daga cikin musulmai ba, amma wasu daga cikin Rafidhawa sun sabawa wannan, wadanda bai halatta a kira su da sunan musulmai ba,
B- Muhammad dan Abdulwahid wanda aka fi sani da Hammamul Hanafi, yana cewa: Rafidhawa sun halarta tara daga `ya`yaye, sannan ya ciratto daga Nakh'i da Ibn Abi Laila- halaccin mata tara- kuma khawarij sun halatta 18, kuma an hakaito daga sashin mutane halaccin kowane adadi mutum yake so ba tare da iyakancewa ba:
Fuska ta farko: Cewa ya bayyana adadin da ya halarta da lafazin, biyuwa, ukuwa, da kuma huduwa, da harafin jam'i, wannan kuma zai bada adadi tara ke nan. Fuska ta biyu kuma shi ne kalmomin (musna wa sulasa wa ruba'a) ababan kidanyawa ne daga adadi mai hauhawa kamar dai yadda aka sani a larabci, sai adadin ya zama 18 ke nan. Fuska ta uku kuma shi ne gamewa kamar ayar: Ku auri wadanda suka yi muku daga mata don haka lafazin biuwa ukuwa adadi ne na dabi'a ba kaidi ba ne, kamar yadda ake cewa: Ka debe abin da kake so daga cikin kogi tulu daya ne ku guda biyu ko uku. Amma na farkon sun kedanta da cewa Manzo ya auri tara kuma asali rashin kebancewa in ba da wani dalili ba, har dai zuwa karshen abin da ya kawo, sannan ya fara gabatar da dalilai a kan takaice mata zuwa hudu.
Abubuwa biyu sun fita a sarari daga fadin Hammam: Na daya danganta halaccin zuwa Imamiyya, kuma wannan tsantsar kuskure ne, kuma muna yin fito na fito da duk wanda zai iya gaya mana masdari daya na Shi'a da ya tafi a kan hakan. Na biyu: Daga cikin Ahlus-sunna akwai wadanda suka tafi a kan auren mata tara kamar yadda Hammam kan sa ya kawo.
C- Muhammad abu Zuhra yana cewa a cikin Ahwalish Shakhsiyya: Sashin Shi'a sun halatta aurar mata tara `ya`ya, saboda ma'anar fadinsa madaukaki "biyu biyu da uku uku da hudu" yana nufn biyu da uku da hudu, irin wadannan maganganun na abu Zuhra misalsalin su na da yawa, iya sani na da shi mutum ne mai sakaci a wajen abin da yake danagantawa zuwa wasu, baya yin ihtiyadi a waien nakaltowa, amma dai tattaunawa a kan wannan yana da nasa lokacin domin fagage da wuraren yin sakacin sa suna da yawa, kuma suna bukatar yin wani aiki na musamman da kuma fagen tattaunawa.
Bayan abin da na ambata maka, da sannu zan zayyano maka dalilai a kan cewa wannan ra'ayin a wajen Ahlus-sunna yake ba a wajen Shi'a ba kamar yadda ya gabata a gare ka.
1. Kasani Ala'uddin yana fadi a cikin Albada'i'u: Bai halatta ba da ya auri sama da mata hudu ba, daga `ya`yaye a wajen dukkanin malamai, wasun su kuma sun ce an halatta masa ya hada tsakanin tara, wasu kuma su ka ce an halatta masa ya hada 18, kuma suka kafa hujja da zahirin fadinsa mdaukaki "Ku auri wadanda suka yi muku daga mata". Na farko sun ce lalle ya ambaci wadannan adadodin ne da harafin jam'iwanda shi ne wau, kuma gaba ki daya zai kama guda tara, kuma suka kafa haujja da abin da Manzo ya aikata shi ne cewa ya auri mata tara, kuma shi ne abin koyi ga Al'umma. Na biyun kuma suka ce lalle (musna) ninikin biyu ne, sulas kuma ninkin uku ne ruba'a ninkin hudu ne, gabaki dayan su kuma sha takwas ne, har dai izuw karshin abin da ya ambata, kuma zahirin maganar sa lalle wadannan ra'ayoyin na Ahlus-sunna ne, domin da Shi'a suna da wani ra'ayi a nan da ya kawo shi kamar yadda ya saba yi.
2. Ibrahim dan Musa Garnadi Ashshadibi ma'abocin littafin mawafakat a cikin littafinsa Al'i'itisam, yana cewa sannan sashin wadanda suka jinginawa wasu bandgarori daga cikin wadanda suka kuskure- saboda kuskuran- tawilin littafin Allah bisa cewa ya halatta auren mata sama da hudu, zaka samu kodai ya zama saboda ya yi ku yi da Annabi bisa rayawar sa, gama cewa an halatta masa sama da haka, tare da rashin waiwayawa zuwa ijma'in musulmai na cewa wannan abu ne da ya kebance shi, ko kuma saboda jirkita ma'anar fadinsa madaukaki" ku auri wadanda ku ne so). Sai ya halatta hada tsakanin guda 9, sai ya zamana ya zo da bidi'a, ya yada ta a cikin al'umma. Abin da Shadibi ya fadi wannan abu ne da yake cikin Ahlus-sunna, da a ce a cikin Shi'a yake da ya zo da nassin hakan, na farko ken an, na biyu: Da ya canja salon maganar sa, domin salon maganar wanann mutumin kan Shi'a zan bar maka bayanin yadda salon yake bayan da kaji da kunnen ka, saurari abin da yake fadi: "Ya ce: An hakaito daga Shi'a cewa Manzo ya dauke wa ahlin gidansa da duk wadanda suke nutse a cikin son su dukkanin ayyuka, kuma babu wani taklifi a wuyan su sai abin da suka ga dama suka yi na daga nafila, kuma dukkanin haram halal ne a gare su, kamar alade da zina da giya da sauran alfasha, kuma suna da mata da ake kira masu wakilci wadanda suke yin sadaka da farjojin su, ga mabukata da kuma neman lada, kuma suna aurar wadanda suka so daga yan'uwa mata da `ya`ya da iyaye, babu wani laifi a kan su haka ma a wajen yawaita mata. Daga cikin wadannna akwai Abidiyya wadanda suka mulki Misra da Africa, daga cikin abin da ake hakaitowa daga gare su cewa lalle mace ta kan kasance tana da mazaje uku ko sama da haka a cikin gida daya kuma suna haihuwa da ita sannan kuma ana jingina dan zuwa kowane daga cikin su" wannan ne karshen maganar sa. Wanda ya yada wannan littafin ya dan yi tsokaci a kan wannan maganar ta sa a hashiyar littafin da fadinsa; Kadai yana nufin sashin bangarorin Shi'a na boye wadanda suka fita daga musulunci. Ina kiran mai karatu da ya sa hannun sa a kan hancin sa domin kada ya shaki wannan mushen, bayan haka sai ya rufe zancen sa da cewa:
Na Daya: Lalle Abidiyya da makamantan su ba sa daga cikin Shi'a imamiyya duk da cewa na yi imani da rashin ingancin abin da ya jingina zuwa gare su, la'akari da abin da ya jingina zuwa wasun su, alhali ba abu ne da ya inganta ba.
Na biyu: Ba mu ne wadanda muke halatta auren makusanta ba, kuma hukunci wanda ya aukawa daya daga cikin makusantan sa a wajen mu kisa ne, ka koma kowane littafi daga cikin litattafan Shi'a a babin haddodi, Kadai Imam Abuhanifa ne yake fadin cewa lalle wanda ya auri Babarsa ko `yar'uwar sa ko `yarsa ya na mai sani kuma da gangan kuma ya yi dukhuli da ita, ba za a tsayar masa da haddi ba, kadai za a yi masa ta'aziri ne domin daura auren ya haifar da shubuha.
Ke nan ba mu ne wadanda mu ke yin sakaci wajen keta haram ba, kamar yadda ba so muke mu saka Abu hamifa a cikin rikici ba, abin dai da muke so mu nuna ana shi ne ra'ayin sa a kan dabbaka ma'anar shubha a kan wannan daurin auren kuskure ne, domin makusanta ba mahallin da ake iya daura aure da su ba ne tun asali.
Na uku: Ina rokon Allah ya sanya sakamakon wannan maganar a a kan mizanin Shadibi a ranar da zai gamu da shi, kuma da sannu zai tambaye shi a kan wannan domin Allah madaukaki yana cewa: "Duk wanda ya aikata misalin kwayar zarra na alheri zan ganshi kuma wanda ya aikata misalign kwayar zarra na sharri zai gan shi" 7.8 Daga surar Zilzilz: Na dan kawo magana ne a kan wannan mas'alar, alhali ya kusata a kirata daya daga cikin badihan abubuwa, domin in dan tsankayar da kai a kan gejin amanar wasu mutane, ban san da mai wadannan za su iya kawo hanzari ba, alhili ga litattafan Shi'a nan a tare da su, cike da labarori. Shin sun zayyana mana wani littafi guda daya da ya zo da hallacin naman alade ko shan giya? lalle wadanda suka fadin wannan wasu ne ba mu ba.
Koma tafsirin fadinsa Madaukaki "Daga cikin `ya`yan itaciya dabino da na Inibobi, kuna yin giya da su, kuma arziki ne mai kyau, (su) lalle a cikin wannan akwai aya ga mutane masu hankali". Surar Nahli/ 67. A cikin tafsiran Ahlus-sunna don ka ga ra'ayin Imam Abuhanifa a kan tsimi, ra'ayinsa sannane ne, bari in gaya maka daya daga cikin fatawoyin sa wacce zata bayyana maka ra'ayin sa a kan wannan lamarin, Abuzuhra yana cewa a cikin Littafinsa Falsafatul Ukubah.
Dalili a kan sakacin Abuhanifa a kan lamarin sashin abubwan da suke sa maye shi ne cewa ya tabbata a gare shi a wasu ruwayoyi cewa wasu daga cikin sahabbai suna shan wadannan abubuwa, don haka sai ya ki haramta ta su har kai a tuhumci sashin sahabbai da yin sado, a kan wannan ne ma yake ciwa: Da zasu nutsar dani a cikin Furata don nace haram ce, ba zan aikata ba. Har kada na fasikantar da sashin sahabbai, kuma da zasu nutsar dani a cikin Furat domin in sha digo daya daga cikin ta ba zan aikata ba, lamarin a wajen Abuhanifa ihtiyadi ne saboda girmama sahabbai da kuma yin ihtiyadi ga addinin sa, na kasa fahaimtar ma'anar ihtiyadi a nan, domin haram, haram ne ga sahabbai da ma wasunsu, lalle wannan sakamakon da abu Zuhra ya fitar ba zai taba karbuwa ba akowane hali, kuma yaya gaskiya da ya kira littafinsa falsafar Ukuba, lalle shi falsafa ce maras ma'ana a wasu lokuta.
3. Ra'ayi na uku da yake nuna cewa lalle hada sama da hudu a wajen wadanda ba Shi'a ba, abin da Ibn Kudama ya fada a cikin Mugni ta'aliki ne a kan abin da matanin ya zo da shi.
Da ba shi da hakkin hada sama da mata hudu, dukkanin ma'abota ilimi sun hadu a kan wannan kuma ba mu san wanda ya sabawa wannan ba sai wani abu da ake hakaitowa daga Ibn Kasim dan ibrahim cewa ya halallta tara, saboda fadinsa madaukaki "Ku aura wadamda kuke so". Kuma (wau) din nan na jam'i ne. Kuma saboda Manzo ya rasu ya bbar mata tara, kuma wannan ba wani abu ba ne saboda abune da ya ketre iyaka sannan ya fita Sunna, Manzon Allah ya ce da Gilan dan Salma, a lokacin day a musulunta alhali akarkashin sa akwai mata goma, ka riki hadu ka rabi da da sauran daga wannan ne zai bayyanar maka cewa Shi'a ba su da wata magana a cikiin wannan mas'alar, ban san daga ina aka samo wanda yake daganta Shi'a da wannan maganar ba.
Wannan cakudedeniyar ta Shadubi da makamancinsa ta kara wa miyar malaman yamacin duniya zaki, wadannan da suke karfafa cewa lalle Shi'a da sufawa suna sarayar da shari'a kuma suna haramta haram ya yin da suka isa zuwa gaskiya.
Misali Na Biyu: Shakku a Kan Annabta
Idan har sashin kage-kagen da aka yi wa Shi'a sun mutu murus kuma sun zama babu, sashin su kuma an fade su amma ba su zama shahararru ba kamar yadda lamarin yake a kan misalin farko da ya gabata mun ambace shi, to lalle wannan kagen da zan ambaca a yanzu haka yana nan a raye kuma an ma tambaye ne a kan ta a duk inda naje. Duk da sharhin da na yi ta yi wa wadanda ya tambaye ne cewa karya ne, ina kudurce cewa ba ta kau daga kwakwalwar su ba, lalle abin da mutum ya tsufa a kan sa baya daga cikin abin da ya ke iya rabuwa da shi ba ta sauki, wannan mas'alar ita ce cewa: Lalle Shi'a su na kudurce cewa lalle wahayi Allah ya nufaci Ali dan Abi Dalib da shi, sai dai Jira'il ne ya yi ha'inci ko ya yi kuskure sai ya kaiwa Annabi wahayin, a takaice wannan ne sharrin da ake dangata shi da Shi'a, kuma lalle an kirkiro wannan kagen na ta bakin Sha'abi Amir dan Sharahil, a cikin wata makala da ya gabata na ambace wani bangare daga cikin ta, kuma karyar lamarin ta bayyana a sarari, amma a yanzu zan ambata maka kirjin wannan kalmar da abin da yake tattare da ita.
Ibn Shahin Umar dan Ahmad, a cikin littafinsa Alludfu fis Sunna, kamar yadda dan Taimiyya ya ambace shi a cikin Minhajus Sunna, ya ce: Muhammad dan baban Kasin dan Harun ya zantar da mu, Ahmad dan Walid alwasidi ya zantar da mu, Ja'afar dan Nasirul Dusi ya zantar da mu, daga Abdurrahman dan Malik dan Magul daga babansa ya ce: Sha'abi ya ce dani: Ina tsoratar da ku daga ma'abota son rai, masu batarwa daga hanya kuma mafi sharrin su ita ce Rafidha, ba su shiga musulunci ba ba don kwadaya ko don tsoron ba, har zuwa inda ya ce: Kaga Yahudawa suna kin jibra'il kuma suna cewa shi makiayin mu ne a cikin mala'iku, haka ma Rafidhawa suna cewa: Jibrilu ya yi kuskure a wajen kai sakon ga Muhammad, har zuwa karshe, lalle wannan fuskar da ta bayyana da sunan Sha'bi, Ibn Hazam ya yi amfani da ita a cikin laittafin sa Alfasalu fil milal wal nihal, sai ya jingina ta zuwa wata firka daga cikin gullat wacce ya kira da Gurabiyya. Saboda sun ce Ali yana kama da Muhammad sama da yadda hankaka yake kama da hankaka, saboda haka ne ma Jibra'ilu ya yi kuskure, a wajen wahayi sai ya tafi wajen Muhammad da shi, alhali wajen Ali aka aika shi kuma babu wani zargi a gare shi tun da kuskure ya yi, sashin su kuma suna zaginsa kuma su na cewa da gangan ya yi, haka Ibn Hazam ya Ruwaito. A yayin da Razi a cikin littafinsa, i'itikadat firakul islamiyya a kan cewa: Sun ce kuskurewa ya yi ba da gangan ya yi ba , kuma ka riga ka san cewa tushen ruwayar Sha'abi. La'akari da mihimmancin maudu'in zan bibiyi wannan ruwayar kuma in ambata maka kuma in fitar maka da shirmen da ke cikin ta, da kuma cewa lalle wadanda suka kirkiro ta ba su lura da abin da ke cikin ta ba na daga tuba- tubai.
A- Farkon abin da za a iya cewa shi ne lokacin da sha'abi ya ke yin gwajejeniya tsakanin Yahudawa da Shi'a ya ambaci Shi'a da sunan Rafidawa, kuma wannan ne lafazin da ya ambaci Shi'a da shi kuma tuni muka warware rashin ingancin sa, malam tarihi na Sunna sun ambaci cewa a karshen rayuwar Zaidu dan Ali ya faru cewa akwai wusu daga cikin daidaikun mutane a cikin rundunar sa, a yayin da suka nemi da ya barranta daga Halifofi biyu sai ya ki sai wasu mutane daga cikin su suka ki bin sa (yi rafadhin), sai aka kira su da Rafidhawa, wanann ita ce ruwayar wannan lakabin, kuma wannan waki'ar ta kasance shekarar da a ka kashe Zaid, ma'ana, 124, bayan hijira, a yayin da Sha'abi an haife shi a shekara ta Ishirin ko talatin bisa wata ruwayar, don haka bambancin da ke tsakanin samuwar sa da wannan ruwayar shekara goma sha takwas ne, saboda a shekara ta dari da biyu, amma kasanyuwar lafazin rafidha ya zo kafin wannan lokacin wani adu ne da ruwayoyi ba su tabbabtar da shi ba, ko kuma wannan kissar kirko ta a ka yi, kuma wannan ne yafi inganta.
B- Lalle mazajen sanadin wannan ruwayar ko dai wanda ake tuhuma kamar Abdurrahaman dan Malik dan Magul, domin lalle litattafan tarihin maruwaita sun ce shi rarrauna ne, makaryaci, makikirin hadisi, kuma Nisa'i ma yana fadi game da shi cewa ba amintacce ba ne.
Da kuma wanda ya jahilci lamarin kamar Muhammad dan Bahili, wannan Muhammad din ji sunansa a cikin lisanil mizan ko Tarihi bagdad da makamancin su ba,
C- Ya gabata mun yi bayanin cewa lalle Sha'abi ana jifan sa da shi'aci, wannan kuma ba gaskiya ba ne, kowanne daga Ibn Sa'ad da Shahristani da ya yi nassi a kan shi'ancinsa, sannan hankali ba zai karbi a ce dan Shi'a ne zai fadi wannan maganar ba.
D- Idan muka kaddara cewa wadannan maganganun gaske ne, su waye wadannan gurabiyya din, su nawa ne? kuma a ina suke? shin akwai su a sararin samuwa, mafi kyan zato shi ne, suna cikin katangar nan da aka kirkiri Abdullahi dan Saba a cikin ta da ainihin hadafin da ya sa a ka halicce shi.
E- Wanda yake da'awar Annabtar wani mutum babu makawa da wannan Annabin ya kasance abin jinginawa zuwa wani ubangiji, a nan za a iya cewa, wannan ubangijin da ya aiko Mazonsa zuwa Annanbinsa, shin ya riga ya san cewa dan sakon ya kasance wawan da ba ya iya bambance tsakanin wanda aka aika shi zuwa gare shi, da waninsa ne ko kuwa, idan ya kasance shi Ubangijin bai sani ba, to ke nan bai cancanci ubangijintaka ba, idan kuma ya sani kuma ya aika shi, to wane ubangiji ne kuma wannan wanda zai aiki wanda baya zartar da umarnin sa, ko kuma ya yarda da abin da Jabail ya yi sai ya zama ba mishikila ke nan a wannan lokacin.
F- Ashe Kur'ani mai girma bai fadi game da Jabra'il ba! "Mai biyayya ne sannan kuma Amintacce ne". Takwir/21. Kuma yana fadi game da Manzo (s.a.w) "Kadai shi Manzon Allah ne kuma cika makin Annabawa". Al'ahzab/40. kuma Shi'a musulmai ne suna karanta Kur'anitsakar dare da kuma gefen rana, ta yaya baza su fahimci wannan ba, sai dai in a ce kamar yadda aka fadi cewa lalle su na ganin an jirkita Kur'ani, kuma mun warware wannan maganar da abububwan da muka gabatar na daga nassosi cewa yana daga cikin abin da ya tabbata tsakanin musulmai fadin Annabi (s.a.w) babi Annabi a baya na, kuma musulmai sun ji wannan daga gare shi.
G- Duk wanda yake da masaniya a kan tarihi, ya san mutukar biyayyar Imam Ali (a.s) ga Annabi (s.a.w) da kuma jihadinsa a gaban Manzo, ta yaya wannan zai hadu tare da sanin sa da cewa ya kwace masa Manzanci, sai dai in a ce bai san cewa wannan Mnazancin nasa ba ne.
H- Masdarin shari'a na farko kuma asasi shi ne Kur'ani mai girma, a wajen dukkanin musulmai, kuma daga a cikin su akwai Shi'a, to idan has Kur'ani ya sauka ga mutumin sa ya ke sakarai, mara kirki, maha'inci, to wane aminci ne zai saura bayan wannan.
I- Ashe dubban manarori da masallatan da Shi'a suke da su wadanda dare da rana suke shelanta ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, wanda su ke, hujjoji ne a kan cewa wannan kissa ce da aka kirkiro, kamar dai sauran `yan'uwanta ba?
J- Lalle litattafan akida da na fikihun Shi'a a cike suke da duniya shi akwai abin da ya ke yin nuni zuwa wannan kagen, a cikin wani liattafi guda daya daga cikin litattafan su, kuma mun yarda ma ya kasance koda ma daga wadanda suka karkace hanya ne na daga abin da muke ganin daga sauran bangarori. Lalle muna neman wani masdari guda da wandannan suka dogara da shi a ciki nakalto abin da suka nakalto, idan har ammawa suna nakalto maganganun mazajen da suka yarda da tunanin bisa karba da yarda duk yadda tunanin na su ya kasance, mai kuma zai sa wayayyu za su zama bisa irin wannan tunanin? kuma miye amfanin ilimi idan har bai daidaita tunanin dan Adam ba? kuma wai har yaushe kuma wace rana ce musulmai zasu fitar da abin da aka sa a cikin cikkunan su? ina ma dai wadannan mutanen suna fitowa fili su gaya mana cewa lalle suna da wasu maslahohi a cikin wanzuwar wannan rudanin, da sun hutar da tsatso bayan tsatso, kuma da sun zama wadanda suka yi gaskiya tare da kawukan su, kamar yadda Marwan dan Hakam ya aikata a wani lokaci daga cikin lokuca da zuciyar sa take a farke, a ya yi da a ka tambaye shi a kan matsayin Imam Ali (a.s) daga tawayen da a ka yi wa Usman, sai ya ce: Ba wani mutum da ya kare Usman kamar Ali, sai aka ce da shi to don me kuke zagin sa a kan mimbari? Sai ya ce: Lamiri ba zai taba daidai ta a gare mu ba sai da haka, kuma da alamun cewa sashin mutane ba za su gasgata cewa sashin wadannan kirkire-kirkiren ba su da tushe ba, domin a karkashin gasgatawar sa ga wannan akwai kubutarwa ga Rafidhawa, kuma wannan yana nufin a kyale wasu mutane ba tare da an samar musu da aiki yi ba, lalle ba na shakka cewa da yawa daga cikin mutane, ba bu wata maslaha da suke da ita a cikin misalin wadannan tuhumce-tuhumcen, sai dai ba abu ne mai sauki ba mutun ya kubuta daga wani abu da rai yake kunshe da shi wanda ya tashi da shi a cikin matakan sa na rayuwa ba, sai dai wannan kuma na zai kubutar ba daga laifin dagewa a kan kuskure ba.
K- Lalle Allah Madaukakin Sarki yana cewa: "Ba mu aiku wasu ba gabanin ka face mazaje" kuma alokacin da aka aiko Manzo Ali yaro ne dan shekara 7 ga shi kuma ayar ta zo da nassin Annabta cewa bata kasancewa sai ga Namiji.
Kuma a karshen wannan fasalin yana da kyau muyi nuni zuwa, abin da gwarazan malaman Shi'a su ka rubuta a cikin litattafan Shi'a na Akida dangane da Annabta da kuma shi kansa Annabi (s.a.w). Na kwakkoma duba zuwa Aka'idul Saduk, da kuma Awa'ilil Makalat na Mufid, da Shariful Murtahda a kan tsarkakar Annabawa da makamancin su, amma zan wadatu da fikira guda biyu kawai.
Na daya: Sayyid Muhsin Amin Amuli yana cewa: Wanda ya yi kokwanto a kan annabtar Annabi kuma ya sauya masa abokin tarayya a cikin Annabata lalle wannan ya fita daga addinin musulunci.
Na biyu: Ridhal Muzaffar yana fadi a cikin aka'idul imamiyya cewa: Muna kudurce cewa lalle ma'abocin manzancin musulunci shi ne Muhammad dan Abdullah, kuma shi ne cikamakin Annabawa kuma shuwagaban Ma'iaka kuma mafificin su, gaba daya, kamar yadda shi ne shugaban Mutane baki daya, ba wani ma'abocin fifici da ya kai kwatankwacin sa afalala, kuma ba wanda ya kai kusa da shi a gima, kuma shi ne ma'abocin madaukakan halaye.
?
Misali Na Uku: Jifan Shi'anci Da Kabilanci
Kabilanci shi ne: Tayayyar al'ummu, wato danganta abu da wata kabila ko al'umma, wani lokacin a kan yi amfani da ita da ma'anar dabi'ar nan ta gaba da larabawa suke da ita. Wannan fassarar ta biyu kirkirarren masdari ne da ake amfani da shi. Shu'ubi a wata fassarar, yana nufin wanda yake daidaitawa tsakanin balarabe da wanin sa kuma baya fifita balarabe. Kuma an cirato wannan sunan ne daga aya mai girma" Ya ku wadanda kuka yi imani, lalle mun halicce ku daga namiji da mace kuma muka sanya ku kabilu ko al'ummu domin ku yi saneneniya lalle wanda ya fi girma a cikin ku a wajen Allah shi ne wanda ya fi ku takawa" Hujurat/13. wannan kuma saboda musulman da ba larabawa ba, sun yi kira zuwa daidaita tsakanin juna kuma wannan ayar ta kasance daya daga cikin shelar su, kuma daga cikin shelar su akwai hadisin Annabi (s.a.w) Babu fififci ga balarabe a kan ba'ajame, dukkanin ku daga Adam kuke Adam kuma daga kasa yake, sannan sai larabawa suka fadada su ka yi amfani da kalmar shu'ubi ga wanda yake wulakanta larabawa, daga baya sai suka dada fadada ta suka yi amfani da ita a kan zindiki da mulhidi, suna la'akari da cewa zindikanci da mulhidanci abu ne da yake damfare da kin larabawa saboda gaba ne da addinin su, sannan bayan haka sai suka yi amfani da su a kan mawali.

Dalilan somi-somin Kabilanci:
Dalilan sun kasu zuwa kaso biyu:
Kaso Na Farko:
Na daya Aiki ne, na biyu kuma sakamakon aikin, a takaicen takaicewa, Larabawa sun kasance a lokacin jahiliyya a daidaice ba wani abu da yake hade su kuma daula ta kasance ga wanin su, sai musulunci ya zo ya hade kansu kuma ya dora su a kan kujerar mulkin Kisra da Kaisar, a lokaci guda sai suka duba suka gan su sun zama wata al'umma mai girma a hannun su akwai sama da makamai da kuma karfin da al'ummu suke jin tsoro, kuma mutane suna kallon su kallo na girmamawa, la'akari da cewa ita ce al'ummar da aka yi wa bushara da musulunci kuma suke dauke da koyarwar sa, sai jiji-da-kai ya samo tushen sa a cikin su, sai suka rika yin mu'amala da al'ummar da suka bude garururuwan su mu'amlar da ke cike da dagawa da jin fifici da ya wuce iyaka kuma suka ki su daidaita kan su da su, kuma suka hana mawali auren larabawa, kuma suke kiran wanda aka Haifa ta wannan auren da (hajin) mai aibi ko wanda jinsi kala biyu suka haifo, dss, kuma sun kasance idan balaraben kauye ya sauka a wata unguwa daga cikin unguwoyin su, yana daga cikin abin kunya ya siyar masa da abinci, sai dai a bashi sabani mawali, Jariri mawaki yana cewa: A lokacin da ya sauka bako a wajen Bani Ambar sai ya zamo ba su karbi bakuncin sa ba, kuma saka siyar masa da abincin bakunci siyarwa.
Ya kai Malik dan Dafir hakika siyarwar ku ga*
*Abinci ga baki yana bata addini har ma salla.
Sun ce zamu sayar muku da shi siyarwa sai nace da su*
*Ku dai sayar ga mawali ku ji kunyar larabawa.
Kuma Ibn Abdu Rabbihi ya fadi a ciki Akdul farid cewa: Larabawa sun kasance suna cewa bai mai yanke salla sai dayan abubuwa uku: Jaki, ko kare, ko maula (wanda ba balarabe ba).
Kuma sun kasance ba sa yi wa maula kinaya kuma ba sa tafiya tare da shi a lokaci zafi, kuma ba sa yi masa ta yi, sai dai ya tsaya a kan su idan kuma har suka yi tarayya da shi a cikin abinci sai su kebe masa waje na musamman, don ya san cewa shi maula ne, kuma al'ummar ta kasance bata neman aure daga babansa da dan'uwan sa, sai dai daga wajen shugaban ta kuma sun kasance a lokacin yaki suna hawan doki su bar mawali a kasa.
Bisa gaskiya wannan dabi'ar ta larabawa a kan lamari maula, sakamakon aikin da ya gabata ne, na yanayin yadda rumawa da farisawa suka kasance suna ma'amala da larabawa, kuma abin da muka yi nuni akan sa na maula wannan bisa matakin sauran mutane ke nan amma matakin masu mulki ba ma yadda za'a yi kaga ma'amalar ta yi kusa da hanyar inda dan Adamtaka, musamman ma sarakunan Umayyawa kamar irin su Hajjaj wanda ba ya dage jiziya daga wadanda suka musulunta daga ahlul zimma, kuma shi ne wanda ya yanke hannayen mawali ya mayar da su kauyuka yayin da suka yi hijira zuwa birane , dukkanin wadannan abubuwa sun ingiza wadannan mawalan bisa ginuwa a kan shi'arin Musulumjci da kuma kira zuwa daidaita tsakanin juna don hak sai aka ambace su da ma'abota daidaitawa, sannan sai wasu yanayoyi suka shude da suka kai ga kawar da sha'anin mawali musamman ma a kwanakin Umar dan Abdul'azizda abin da ya biyo bayan sa, sai suka zaburo domin tabbatar da samuwar su, sai lamarin ya ci gaba bayan wannan har zuwa lokacin da sakamakon aiki ya fara tsananta har ya kai ga wulakanta larabawa.
Amma Ta Bangare Na Biyu:
Wanda shi ne ci gaban ga karnonin da suka gabata a yayin da larabawa suka kasance a kwanakin kisrori da kaisarori, ba su da wani matsayi da za iya ambata, kuma wannan madubar ta buyu ga larabawa bayan lokaci mai tsawo bayan da musulunci ya mulki wadannan al'ummu, sai dai kuma daga baya sai suka dawo da girman su na da saoda dalilai masu yawa da babu damar da zan kawo su a nan saboda, abin da ya taimaka a kan haka shi ne cewa su mawalin daga al'ummomi ne ma'abota ci gaba tun a baya, kuma tun daga wasu daga cikin al'ummu sun ci gaba a cikin mabambantan sha'anonin mulki da na ilimi don hak sai suka taka rawa mai girma, a cikin fagage daban-daban na al'umma, kari a kan cewa lalle daular abbasiyya ta dogara a kan su saboda abubuwa biyu:
Na farko: Saboda bukatuwar su zuwa ga tsara lamuran daula, da kuma yin amfani da kwarewar wadannan al'ummun a wajen gudanarwa da kuma kafuwa da tabbatuwa da su ke da su a kan wannan, da kuma yin koyi da su a wajen holewa da jin dadi,
Na biyu: Domin a yi amfani da su a wajen karya karfin larabawa, domin sun tsorata da larabawa musammam ma da suka ga karkatar larabawa ga Alawiyyawa, kuma farisawa da turkawa sun taka mummunar rawar a wajen karya kayar larabawa da kuma cimma manufar abbasawa, a cikin wannan, amma kuma daga bayan sai sika gama da halifancin abbasawa, hattama a matsayin ta na daular larabawa, sai suka maida Bagdada wata mu'assasa da aka shafe al'umun larabawa a cikin ta, bayanin da nan ba mahallinsa ba ne.
Mabayyana Kabilanci
Fagagen da kabilanci ya bayyana a cikin su, mafi mihimmancin su su ne: Adabi da zube, tun daga kwanakin Umayawa har lokacin Abbsawa, kuma wasu ruwayoyi sun bayyana a tarihi wadanda suke kaskantar da matsayin larabawa, kuma suke daukaka wadansun su, da kuma wasu abubuwan da suka kunshe da raya ibadodi da al'adu da akidun da suka kasance a wajen sashin al'ummomin da suka shiga musulunci, kai hatta ma yanayin zamantakewar sarakuna da 'yan kasa a wajen cin abinci da da tufafi da kuma tsarin dabi'u na zamantakewa wata kalar daban, sun bayyana da wasu alamomi ba na larabawa ba. Kuma abu ne na dabi'a ga wasu alamomi na da ciratowa daga wasu, da a ce zai takaitu ga hakan, sai dai wannan koyi ne da ke tattare da razanin da kuma alfahari da wannan yanayin, tare da shafe alamomin larabawa da kuma gusar da yanayin yadda suka saba zamantakewa da rayuwarta.

Alakar Al'ummu Da Shi'anci
Bayan wadannan 'yan takaitattun jimlolim a kan kabilanci zamu iya tambaya a kan cewa, meye alakar wannan kabilancin da shi'anci? Kuma daga ina zargin shi'anci da kabilanci ya samo asali, lamarin da ya ingiza Dr. Ahmad Amin har ya sami damar cewa: Amma shi'anci ya kasance shekar bangaranci wadda suka kasance suna fakewa zuwa gareta kuma ya zama mayafin da suke lulluba da shi.
Hakika jifan Shi'a da kabilanci abu ne mai ban ta'ajibi da mamaki, babu wata alaka tsakanin shi'anci da bangaranci, kuma da sannu zamu yi kokarin iyakance da kididdige lamuran da suke su ne alama ko kuma sababin kabilanci, domin mu ga ina matsayin Shi'a daga wadannan lamuran, daga baya kuma, wai shi miye matsayin wannan tuhumar:
1- Tushen da ba na Larbawa ba
Shi'a da wadanda suke yin biyayya a gare su ba su kasance daga cikin na gaba-gaba ba, ta bangaren mawali, da ma kowane irin jinsin da ba jinsin larabawa ba, kamar yadda muka gabatar da wannan kuma mun yi wannan bayanin dalla-dalla a cikin abin da ya gabata daga wannan littafin babu bukatar in maimaita shi,
2- Matsayin Shi'a game da bangarencin larabci
Mawallafa da masu tunani na Shi'a sun tsaya a gaban bangarancin larabci, da kuma larabawa matsaya madaukakiya a cikin girmama larabawa da kuma girmama tunanin larabci tare da shiryarwa da kuma ba da gudummuwarsa wajen hidimar shari'a suna masu kafa hujja kan cewa Allah madaukaki ya girmama larabawa ta hanyar dora musu wannan sakon kuma ya sanya harshen su shi ne yaren Kur'ani mai girma, kuma ya kalli kasar su a matsayin mashimfidar fara kira kuma makiyaya daga tafkokin ta, kuma tuni mun rigata mun yi bayanin matsayar mu game da yaren larabci, da kuma bangarencin larabci na halifa da makamancin wannan dalla-dalla.
3- Matsayar su a kan ci gaban larabawa:
Shi'a ba su da wani mummunar matsaya game da ci gaban larabawa, balle ma akasin haka shi ne daidai, Shi'a su ne `yan gaba-gaba a wajen hidimtawa domin ci gaban larabawa a cikin mabambanta sassanta, kuma ga wasu jama'u nan daga cikin jigajigan su wadanda suka yi hidima a cikin fagagen wayarwa da al'adu kyawawa daga cikin gwaraza a cikin ilimin Sira da tarihi akwai Abdullahi dan Abi Rari'I ma'abocin littafin Tasmiyatu man shahida ma'as sahaba ma'a Ali (a.s), da kuma Muhammad dan Ishak ma'abocin littafin Siratun Nabawiyya, da kuma Jabiru dan Zaidul Ja'afi. Daga cikin manya a ilimin nahawu akwai Abu Aswadun Du'ali da khalil dan Ahmad shugaban basarawa, da Muhammad dan Hasan Alrawasi, shugaban Kufawa da kuma Ustaz Kisa'i da Fara'a da Ada'u dan Aswad aldu'ali da Yahayal Mibrad dan Ya'amarud dawani da Yahaya dan Ziyadu da Bakir dan Muhammad abu Usmanul mazini da Muhammad dan Yazid abu Abba salmibrad, da Sa'alabatu dan Maimun abu Ishak al'nahawi da Muhammad dan Yahya abu Ishakas Suli da Abu aliyul Farisi Alhasan dan Ali da kuma Al'ahfash na farko Ahmadu dan Umran da kuma Muhammad dan Abbas Abubukar Alhawarizmi, wanda Sa'alabi yake fadi game da shi a cikin Yatimatul Dahri: Fitaccen zamani kuma kogin adabi, ilamin wake da zube masani daukaka da fifici, ya kasance ya na hada tsakanin fasaha da balaga, kuma yana bada leccar labaran larabawa da kwanakin su kuma yana koyar da litattafan luga da nahawu da wake, da kuma Tanuhi Ali dan Muhammad da Marzabani Muhammad dan Imrana ma'abocin, Tasaniful Ra'I'ah fi ulumil Arabiyya, da sarkin malaman nahawu Hasan dan Habida Ma'azul Harra'u mawallafin Ilumul tasrifi, da kuma Usman dan Jani Abul Fatahi da Abbanu dan Usmanul Ahmar da Ya'akub dan sikkit ma'abocin Islahul mandik, da kuma Abubukar dan Durad ma'abocin Jamhara, da kuma Muhammad dan Imrana Almarzabani ma'aboci littafin alfaslu fi ilmil bayan da kuma Safiyyud Dinul Hilli ma'abocin kafiya fi bada'i'i, da kuma Khalai'in Nahawi Husain dan Muhammad Ma'abocin littafin Sin'atul shi'iri.
Haidar Center for Islamic Propagation
Face Book: Haidar Center
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012