Manufar Takiyya
SHEIKH WA'ILI
Takiyya Da Hukunce- hukuncenta
Yana daga cikin abin da a ke kallafawa Shi'a kuma ya wayi gari daga cikin abin da ba ya wufinta daga gare su idan har suke zo cikin kwakwalwa, kai ka ce wata gaba ce daga gare su banda sauran Musulmai, ita ce: Takiyya, abin da ya taimaka a kan haka shi ne a tsawon tarihi Shi'a sun kadaita da fuskantar matsin da ya wuce kima domin wannan yana kamanta fagen fama a daidai lokacin da fito na fito bai da wata ma'ana in ba gaba da kiyayya ba, ba kamar yadda ake fahimtar lafazin fito na fito ba a wannan zamanin kuma lalle yana daga cikin abin da yake a zaune cewa zasu sha raraka da azaba daban daban, kuma ya zama dole su kare kansu daga kawarwa daga doron kasa baki daya, don haka sai suka rabe a bayan takiyya, la'akari da cewa ita wata aba ce da shari'a ta zo da ita domin tsare kai ta hanyar ta yayin larura kuma sun ruwaito wa takiyya madogararta ta shari'a daga cikin Kur'ani da Sunna kuma kamata ya yi a yabe su a kan wannan domin sun yi amfani da abin da mai shari'a ya yi umarni da shi, domin kare kai daga hadari.
Kuma domin kada lamarin ya kai su ga dayan abubuwa biyu wato karar da iri ko kuma tarwatsewa da kuma wayar garin a cikin kwaryar azzalumai kamar yadda wanin su ya aikata na daga wanda ya fake a karkashin inuwar mulki da kuma masu mulkin, kuma ya wayi gari yana ci yana sha a karkashin su kuma yake rayuwa a karkashin kulawar su, kuma yake ta fama kirkiro dalilai domin ra'ayin su ya zama ya dace da shari'a kamar yadda Ibn Khalkhan ya fadi dangane da tarihin Abu Yusif alkali, ya ce: Zubaida matar Harunar Rashid ta rubuta zuwa Abu Yusif Alkali cewa me kake gani a kan lamari kaza kuma mafi soyuwar a gare ni shi ne gaskiya ta kasance a cikin kaza, sai ya bata fatawa da abin da take so, sai ta aiko masa da kumbon zinare a cikinsa akwai wasu kanana rufaffu kuma a cikin kowacce akwai kala-kala na turare, a cikin wani kofi kuma akwai dirhamomi da, a tsakiyar kumbon kuma akwai wani kofin a cikin sa akwai dinarori, dss.
Shi'a sun kasance ababan yabo saboda juriyar da suka yi a kan zalunci da cutarwa da zalunci' kuma ba su da wata alaka ta shiri da abota da masu mulki. Tabbas sun ki kulla alaka da su kuma sun tsaya kyam domin kare asasin addinin su, in ba a wasu matsananta yanayoyi ba.
An lura da cewa akwai wani bayyanannen yanayi da ya zama mahallin yin nazari a kai. Shi ne cewa tun lokacin da Shi'a suka sami kansu tsamo tsamo a ciin zalunci suka kulla abota da takiyya bisa gwargwadon yanayin da suka sami kansu a ciki (tsanani da sauki). Amma ba su yi riko da takikayya riko na aikin ibadar da ake yi yau dakullum ba, (larura ke sa a yi takiyya). Balle ma ba wanda ya kai Shi'a sadaukarwa a aikace kuma duk mai bukata zai iya komawa ya karanta matsayar Shi'a tare da ma'awuya da ma wasunsa na daga sarakaunan Umawuyya da sarakunan Abbasiyya, dauki misalin Hijir dan Adiyu, Maisamal Tammar da Rashidul Hijiri da Komail dan Ziyad da daruruwan makamancin wadananan, haka ma irin matsayar Alawiyyin tsawon tarihi da kuma tawayen da fito na fito din da suka yi ta yi ba iyaka.
Bisa wannan zan iya cewa lalle takiyya ba Shi'a ne kawai suka kadaita da ita ba, matsayar su kamar ta sauran nmusulmai ce, kuma wannan abu ne da yake a sarari bisa sharhin ayoyi masu girma da hadisan da suka zo musamman a kan wannan lamarin. Daga cikin ayoyi masu girma da suka zo a kan wannan bugire: Akwai fadinsa madaukaki: "Kada muminai su riki kafirai majibinta lamari ba muminai ba kuma lalle wanda ya aikata wannan ba ruwan Allah da shi, sai dai in takiyya kuka yi kuma Allah na gargadar ku daga fushin sa kuma makoma tana gare shi". Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa madaukaki "In ba wanda aka tilasta ba, alhali zuciyar sa tana cike da imani" Nahal/106.
Amma hadisai daga ciki akwai wanda Buhari ya ambata a cikin sahihin sa a cikin littafin adab a babin mu'amala da mutane daga manzo (s.a.w) Lalle mu mukan yin murmushi ga wasu mutane alhali zuciyar mu tana la'antar su.
Da kuma kamar fadinsa: An dage (yafewa) wa Al'umma ta kuskure da mantuwa da abin da aka tilasta su a kai. Kuma ibnil Arabi ya ambaci wannan a cikin tafsirin aya ta 106 suratun Nahli, da kuma kamar fadin Manzo (s.a.w): Ga Muhammad dan Maslamata tare da wadanda suke tare da shi ya yin da ya tura su, su yaki Ka'abu dan Asraf, sai suka ce ya ma'aikin Allah shin kayi mana izinin mu fadi bakar kalma a kan ka? Sai ya yi musu izini, kuma a mahangar wannan ayar da wadannan nassosin da kuma abin da suka kunsa musulmai sun kasu zuwa kasu mai yawa, wasu daga ciki suna ganin cewa ya halatta da baki amma banda a aikace, wasu kuma suka halatta duka, amma kuma sun yi sabani a kan wajabcin ta kai tsaye. Ko kuma madlakin halaccin ta, ko kuma rari da rabi tsakanin su. Ya zama ke nan tana wajaba a wani lokaci, kuma tana halatta a wani lokacin. Kuma a babai na ga ba zan amfanar da kai labari a kan ra'ayin wasu daga cikin malaman musulunci, domin ka zamo cikin masaniya a kan wannan lamarin, bayan da na yi maka wata yar shimfida a kan kwanduwar lamarin.
Ma'anar Takiyya
Malaman tafsiri sun ta'arifin takiyya da cewa ita ce : "Boye akida domin jin tsaron fadawa cikin hallaka da kuma mu'amala ta sarari tare da makiyin da ake da sabani da shi tare da cewa zuciya na cike da gamsuwa a kan cewa akwai gaba da kiyayya a tsakani da kuma sauraron gushewar abin da ya hana a raba gari". Kuma shehul Mufid ya yi ta'arifin ta a cikin littain sa Almakalat da cewa: "Boye gaskiya da kuma boye akida da kuma boyuwa daga idanun abokan sabani da rashin bayyanar musu da abin da zai jawo cutuwa a duniya da lahira" duka dai duk ma'anar daya ce a cikin wadannan ta'arifofin guda biyu.
Bayan da muka yi ta'arifin takiyya bari mu koma zuwa ra'ayoyin malaman mazhabobin musulunci a cikin hukunce- hukuncen takiyya daban-daban.
Maganganun Bangarorin Musulmai A Kanta
1. Mu'utazilawa:
Mu'utazila sun halarta yin takiyya yayin bijirowar wani hadari da abin da ke hallaka mutum ko ya ke jin tsoron rasa ransa, a kan wannan ne abu Hazaifil Ilaf yake cewa: Lalle wanda aka tilasta idan har bai iya yin shagube ko tauriya a kan abin da aka tilastashi ba, zai iya yin karya kuma an yafe masa zunubin karyar
2. Khawarijawa:
Kwarijawa a kan takiyya sun kasu zuwa kaso uku; kaso na farko wadanda ake kira Al'azrikah mabiya Nafi'u dan Azrak, sun hana yin takiyya hani mai stanani ga wanda yake yin ta sannan kuma sun kafirta wandanda ba sa yin fito na fito da zalunci da azzalumai. Akan wannan ne nafi'u yake cewa: Takiyya bata halarta ba kuma kin yakar zalunci kafirci ne na sarari saboda fadinsa Madaukaki " Sai ka ga wani shashi daga cikin su suna jin tsoron mutane kamar tadda suke jinn ntsaron Allah koma sama da haka" suarar nisa'I 77. da kuma fadian sa madaukaki "Su na yin jihadi a tafarkin Allah kuma ba sa jin tsoron zargin mai zargi"Ma'ida /55.
Ka so na biyu kuma su ne: Najidat, mabiyan Najidata dan Uwaimir; sun halatta takiyya a cikin magana da kuma aiki koda kuwa hakan zai kai ga kashe ran da Allah ya haramta.
Kaso na uku kuma su ne Sufriyya: Sun kasance masu matsakaitan ra'ayi tsakanin wadannan bangarorin guda biyu, don haka su sun halarta ta a magana amma banda aiki kamar yadda Shahristani ya ruwaito daga gare su, kuma dalilan su mahallin tattaunawa ne a kai amma yanzu ba a kan wannan nake magana ba.
3. Ahlus-sunna:
A wajen Ahlus-sunna takiyya ta halarta a wajen magana banda a aikace kuma wadansun su sun tafi a kan wajabcin ta don haka ma ya tafi a kan wajabcin ta a wasu yanayoyi, kamar su Gazali a yayin da yake cewa a kan wannan: Kare jinin musulmi wajibi ne don haka duk yayin da a ka nufi zubar da jinin musulmi yin karya a kan haka ta wajaba . Hakika shashinsu sun takaita a kan yin rangwame da yin takiyya, idan musulmi ya kasance a tsakanin kafirai ta yadda ya zamo yana jiwa kansa ko dukiyar sa tsoro. Daga cikin wadanda suka tafi a kan yin rangwame a bisa yin takiyaya; Razi mai tafsiri da Dabari, kuma ya zo ma cikin tafsirin na ayar "Sai dai in takiyya kuka yi musu ". A yayin da wasu daga cikin malaman suka tafi a kan cewa takiyya tana damfare da kowane yanayi, ba sai tsakanin musulmai da kafirai ba, balle ma hatta ma idan musulmi ya kasance a tsakanin musulman da halayyar su ta yi kama da ta kafirai ai a yanayin da ba shi da ikon iya bayyana mazhaba a tsakanin musulman na daga sauran mazhabobin, kuma daga cikin wadanda suka tafi a kan wannan ra'ayin akwai Shafi'i da Ibn Hazam azzahiri.
Kuma hukuncin takiyya wanzanjejje ne kamar sauran hukunce-hukuncen har zuwa ranar alkiyama, sabanin wandanda suka takaice shi daga lokacin da musulunci yake da rauni, saboda haka ne ma malamai suke cewa:
Takiyya ta halatta ga mausumi har zuwa ranar alkiyama suna masu jingina zuwa ga fadin Manzon Allah (s.a.w) ga Ammar dan Yasir yayin da ya cewa Annabi (s.a.w) ba su kyale ni ba har sai da na fadi bakar magana a kan ka, sai ya ce da shi idan suka kuma, kai ma ka kuma fadar abida ka fada. Baidhawi ya ambaci wannan a cikin tafsirin sa ga aya ta 106 na suratun nahali ka koma cen.
4. Ra'ayin Shi'a a kan takiyya:
Shi'a ba su da sabanai da Sunnan a kan takiyya domin ita a wajensu hanya ce da shari'a ta yi nuni zuwa gare ta domin kare rayukan da ya wajaba a kare su. Haka ma domin kare sauran abubuwan da shari'a ta yi umarni da a kare su. Kacokaf wandannan ne manufar takiyya a wajen su. Ba a kamar yadda wasu suke fadi ba cewa Shi'a sun yi riko da takiyya a matsayin wani makami na yaudara da rabewa jirkita kama, domin yin boyayyun kungiyoyi na yaudara masu rusa al'umma.
Takiyya a wajen Shi'a tana sabawa ne bisa gwargwadon matsaya, ta yiwu ta zama wajibi ko kuma halal ko kuma haram don haka ne ma za ka ga cewa a maganaganun malaman Shi'a suna bayyana wadannan yanayoyin guda uku, Ibn Babawaiahil Kummi yana cewa: Akidarmu a kan takiyya shi ne cewa ita wajibi ce kuma wanda ya karyata kamar wanda ya bar wajibi ne kamar wajabcin salla kuma wanda ya bar ta kafin bayyanar Imam Mahadi (A.J) to ya fita daga addinin Allah da Annabin sa da Imamai, a yayin da shehul Mufid Muahammad dan muhammad dan Nu'uman ya ke cewa:
Takiyya halal ce yayin ji wa kai tsoron halaka, kuma tayiyu ta halatta bisa yanayin da bai kai ga hakan ba, yayin jin tsaron hallakar dukiya, dama dai sauran masalahohi, ina mai karawa da cewa wani lakoci ma tana iya zama wajibi ba tare wajabcin ta ba, kuma ina mai tabbatar da cewa halal ce, a cikin dukkanin magana ko zance amma bata halatta a cikin wani abu daga aiki na kashe mumini da abin da barnar sa tafi rinjaye a cikin addini.
A yayin da wani malamin Shi'a na zamani yake cewa a kan ta: Takiyya tana da hukunce- hukunce, ta dangaren wajabci da da kuma rashin wajabci bisa gwargwadon sabawar yanayi ko matsayar da ake jin tsaron cutarwa, ba wajibi ba ce a kowane hali ba, balle ma ta yiwu ta halatta ko ta wajaba sabanin wasu lokuta, kamar idan ya zama bayyanar da gaskiya da fito da ita file taimako ne ga addini, kuma hidimtawa musulunci ne da kuma yin jihadi a tafarkin Allah, lalle a wannan lalkacin dukiya bata da kima kuma rayuka ba su da daraja, kuma ta yiwu yin takiyya ya haramta a cikin ayyukan da suke kai ga a kashe rayuka masu kima, ko kuma yaduwar fasadi ko barna a cikin addini ko cutarwa mai tsanani ga musulmai ta hanayar batar da su ko kuma yaduwara zalunci a cikin su, har dai inda yake cewa: Lalle akidarmu a kan takiyya wasu daga cikin wadanda suke son su suki Shi'a Imamiyya sun yi anfani da ita sai suka sa ta saga cikin abubuwan da ake sukan Shi'a da isu, kai ka ce ba abin da zai gamsar da su ya kawar da kishirwar su, idan har ba a gabatar da wuyayin su -Shi'a- domin a kawar da su daga doron kasa ba.
Daga wadannan yan kalmomin da na ambata zaka fahimci cewa takiyya ta na damfare da yanayoyi da kuma waje, kuma tana kasancewa mahallin da hukunce- hukuncen da a kan ambata suke sauka, bisa sabanin yanayoyi. Kuma tuni ya gabata mun jiro dalilan Shi'a a kan yin takiyya daga cikin Kur'ani da Hadisi, saboda haka ne ma Imam Sadik ya kasance yana cewa: "Takiyya addini na ce kuma addini iyayana" musaman ma a zamanin sa da takobi ta zama ita ke magana guda daya, kuma sashin su sun so su yi wa matsayar Imam Sadik tawili da kuma matsayar Shi'a a kan takiyya da cewa ita tana mangance musu abubuwa biyu ne:
a. Shi ne cewa lalle yin shirunm imamai daga neman hakkin su da kuma kyale azzalumai ta wannan bangaren, da kuma cewa sune iamaman da ya wajaba a yi musu biyayya, lalle wannan yanayin zai haifar da cin karo da tanakudi a cikin maganganun guda biyu, da ba mafita daga hakan sai da takiyya, Razi ya fadi wannan a cikin littafinsa Muhassili Ara'al Mutakaddimina wal Muta'akhkhirina, haka ma Maldiyyu a cikin littafinsa Attanbih wal Raddi ala Ahlul Ahwa'i wal Bida'i .
b. Lamari na biyu shi ne: Abin da yake a bayyane na sabanin da imamai suke yi a junansu a maganaganu da kuma a cikin maganganun Imam guda daya a matakai daban-daban na daga abin da yake kawo alamar tambaya, domin su kawar da wannan sai su ka fake da takiyya har kada wata matsala ta saura daga hakan. Mai littafin Dirasatun fil firaki wal Aka'id ya fadi abin da wannan zancen nasu yake kunshe da shi.
Da dukkanin alamu wannan mai binciken yana so ya suranta cewa lamarin takiyya ya rikirkice masa, wannan kuwa saboda mahangogin nan guda biyu da ya ambata kadai suna daga cikin mahallin da ake dora takiyya a kan su ne ba wai saboda su aka shar'anta takiyya ba, wannan ke nan, tare da cewa wannan mai binciken wanda shi ne Dr. Arafan yana daga cikin wadanda suka fi kowa yi wa Shi'a adalci daga cikin mutane, a bisa abin da ya rubuta akan su, idan aka auna shi da wanin sa, amma kalli abin da yarubuta a kan su. Kuma da yawa daga cikin murubuta suna ganin cewa akwai rauni a cikin matakin da Imam Sadik (a.s) ya dauka na tsanantawa a kan yin takiyya, a yayin da Imam da wannan matsayar ta sa ne ya kare sahabbansa daga munanan farmakai na kan mai uwa da wabi farmakin da babu wata magana tattare da shi sai takobi da wuka, a irin wadannan yanayoyin babu makawa da a sa hankali da hikima, bari in dan baka kadan daga yadda surar yanayin ya kasance:
Khadibul bagadadi yana cewa da sanadinsa daga baban Ma'awiyata na shiga wajen Harunar Rashid sai ya ce da ni: Na so na kadamar wa kuma in gama da duk wanda yake tabbatar da khalifanci ga Ali, Abu Ma'awiya ya ce sai ya yi shiru sai ya ce da ni kayi magana, sai nace: Ka yi mini izini? sai ya ce kayi magana, sai nace: Ya amirul muminin kabilar taim sun ce a cikin mu akwai halifan Manzo, kabilar Addi sun ce a cikin mu akwai halifan manzo, kuma Banu Umayyata sun ce a cikin mu akwai halifofi to ku banu hashim meye raban ku, wallahi baku da wani rabo im ba Ali dan Abi Dalib ba, sai ya yi shiru , mutumin ya san ta inda zai shiga da ta inda zai fita, a nan zamu iya cewa idan har zai kaddamarwa wanda yake fadin hakkin Ali a kan halifanci, to ina kuma ga ra'ayin wadannan masu zubar da jinin wadanda suke rayuwa a zamanin jin dadi alhali wuta ba ta lashi fasakun su ba kuma karfe bai sjiga naman jikin su ba.
Kari a kan cewa akwai wani abu shi ne, shuwagabannin musulmai takiyya ta zame musu larura saboda yanayoyin da suka sami kan su a cikin, daga cikin wannan akwai abin da Ahmad dan baban Ya'akub wanda aka fi sani da Yakubi ya fadi, yayin da ya bijiro da matsayin Ahmad dan Habali a kwanakin jarrabawa da bisa fadin cewa Kur'ani abin halitta ne: Yayin da aka jarrabi ahmada dan Hambali da cewa Kur'aniabin halitta ne aka yi mishi `yan buloli, sai Ishak dan Ibrahim ya ce da Mu'utasim, ya Amiral Mu'minin, bar ni in yi munazara da shi, sai ya ce yi yadda kaga ya dace da shi, sai Ishak ya ce da Imam Ahamd mai zaka ce a kan halittar Kur'ani? Sai Imam Ahmad ya ce ni mutum ne da aka sanar da ni ilimi amma ba a sanar da ni wannan ba, sannan ya ce: Shi wannan ilimin da ka sani shi mala'ika ne ya saukar maka shi daga sama ko kuma ka san shi ne a wajen mazaje. sai Ahmad ya ce: Ina! na koye shi ne daga wajen mazaje, sai Ishak ya ce: Ka koye shi ne ahankali a hjankali, sai ya ce a, sai Ishak ya ce: Sai wani abu ya yi saura a gareka wanda baka san shi ba ko! Sai Ahmad ya ce a, sai ya ce to wannan yana daga cikin wanda baka san shi ba, sai Amirul mu'minina ya sanar da kai shi, sai Ahmad ya ce: Lalle ina kan abin da amirul muminina ya tafi a kan sa, sai Ishak ya ce a kan cewa Kur'ani abin halitta ne? sai Ahmad ya ce: A cikin cewa Kur'ani abin halittane, sannan ya shaida da hakan, sai ya kwance shi ya kuma sake shi ya koma dida.
Saboda wannan ne Jahiz a cikin tattaunawar sa tare da Ahlun Hadis bayan da ya ambaci jarrabar da aka yi wa Imam Ahmad dan Hanbali: Sahibinku wannan -yana nufin Imam Ahmad dan hambali- ya kasance yana cewa babu takiyya sai a gidan kafirci idan har abin da ya tabbabtar na cewa Kur'ani abin halitta ne ta fuskacin takiyya ne to shi ya aikata ta a gidan musulunci, idan kuma ya karyata kansa, idan kuma abin da ya tabbatar bisa inganci ne, to ba ku, ba shi, don gama ba zararren takobi ya gain, ba kuma wani dukan sa a ka yi da yawa ba. Ba a bulala shi ba face bulala talatin wacce a ka gutsier kayan marmarin ta, wacce aka daure gefen ta, har sai da ya fito fili ya yi ikrari ba sau daya ba, kuma ya kasance a kuntataccen waje ba ne, ba kuma a cikin mummunan halin yanke kauna yake ba, ba wata sarkar karfe aka sa masa ba, ba a karya zuciyar sa ba saboda tsananin razanarwa ba, ya kasance ana tambayar sa da tausassan harshe shi kuma yana amasawa da kakkausa, suna sa lamarin a ma'auni shi kuma yana yin ko oho, suna yin hakuri shi kuma yana harzuka.
Tare da cewa tarihin musulmai yana damfare da takiyya, tabba sakwai wasu abubuwa da wasu musulman ba sa tabbatar da samuwar su amma kuma sana faruwa a cikin su, dauki misalin wanzuwar kabarin Annabi (s.a.w), wahabiyyawa ba sa barin wani kabari a tsaye, kuma sun ruwaito a cikin sahihai daga abi Hayyaj Al'asadi ya ce: Ali dan Abi Dalib (a.s) ya ce da ne ashe bana aika ka akan abin damanzo Allah (s.a.w) ya aika ni akan sa ba, kada in bar wani tsayayyen kabari face sai na daidaita shi ko wani gunki face sai na kawar da shi, bisa wannan ruwayar ne wahabiyyawa suka jingina, ko kuma daya ce daga cikinn rawayoyin da suka dogara da su wajen rusa kaburbura, sai dai ba su iya kusantar kabarin Manzo ba tare da cewa ruwayar gamammya ce bata togace wani kabari ba, kuma wannan ba komai ba ne sai yin takiyya ga sauran musulmai. Ruwayar Ibn Hayyaj ta zama dalilin da ya sa dan Taimiyya ya sa wa Shi'a da zafi, tare da cewa a wajen su ruwayar bata tabbata ba ta ban garen sanadin ta. Kuma dan Taimiyya ya cika littafinsa da nau'o'in zagi wadanda koyarwar musulunci da ladabin Kur'ani ba su yarda da su ba, daga cikin irin wannan zagin akwai cewa duk inda ya shude da ambaton Allma Ibn Mudahharul Hilli, sai ya ambace shi da Ibn Munajjas (dan wanda aka najasta).
A yayin da Allama ya kasance a cikin jayayyar sa da malamai yana mutukar nuna ladabi kuma mai karatu zai iya komawa litattafan nan nasu guda biyu wadanda suka wallafa a tare sannan ya yi hukunci a kan salon tattaunawar su, domin ya gano bambancin da ke tsakanin su.
Zuwa nan nake fatan na riga na dan bawa mai karatu wata yar shimfida a kan takiyyya wacce za ta sa ya fahimci surar yadda take a dunkule. Kuma lalle yanayin zamanin da muke ciki ba zai taba wufinta daga takiyyar da ake gudanarwa tsakanin al'ummu ba.
Haidar Center for Islamic Propagation
Face Book: Haidar Center
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012