Ziyarar Kabari1
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
FASSARA: YUNUS MUHMMAD SANI
DUBAWA: HAFIZ MUHAMMAD SA'ID
[Al'adar Mutunce Kuma Sunnar Ubangiji]
Makabarta wani wuri ne babba a cikin birni da kauye inda yake dauke da babba da yaro mai iko da talaka daga magabata wadanda suke cikin barci mai zurfi wanda kamar ba za a farka ba.
Ziyartar wannan wuri Wanda yake nuna gajiyawar dan Adam, sannan yana da rawar da yake takawa wajen gusar da duk nuna iko ko kwadayin abin duniya ga mutum. Mutum mai hankali yayin da ya ga wannan wuri mai ban tsoro, zai fahimci rashin tabbatuwar duniya daga kusa, sannan ya fara tunani akan mafita sakamkon fahimtar manufar halittar duniya da ya yi zai sanya ya fita daga cikin magagin dimuwa da son kai, sannan ya fara tunanin neman abin zai taimaka masa wajen rayuwar da ba ta da iyaka. Manzo (s.a.w) a kan wannan al'amari domin tarbiyyantar da al'umma yana cewa: "Ku ziyarci kaburbura domin zasu tuna muku ranar karshe". Sannan a wani wurin daban yana cewa: "Ku ziyarci makabarta domin kuwa akwai darasi gareku a cikin yin hakan".
Sannan akwai wasu daga cikin mawakan zamani kamar Marigayi Sayyid Sadik Sarmad yayin ziyarar Kasar misra da kuma ziyarar Kaburburan fir'aunoni, sai ya yi wata a kan haka wadda take fassara hadisin Manzo (s.a.w) a kan hakan:
Ziyartar Kaburburan Masoya
Mutanen da suka rasa wani masoyinsu sakamakon alaka ta jini da soyayyar da take tsakaninsu ba zasu manta da shi ba, zaka ga kodayaushe suna yin taruka domin tunawa da shi sannan suna yin kokari wajen girmama shi. Yayin da mutuwa ta kare su daga saduwa ta jiki, sai suka koma bangaren guda wato ta hanyar ruhi suna saduwa da shi, don haka ne zaka ga suna zuwa wurin da aka rufe shi ta hanyar daidaiku da cikin jama'a domin su ziyarce shi sannan suna yin taruka domin tunawa da shi din. Taron mutuwa da ziyartar kaburburan wadan suka rasu wata al'ada ce wadda ta hade ko'ina a cikin al'ummar duniya, ta haka ne zamu iya cewa wannan al'amari yana da alaka da halittar mutum. Sakamkon soyayyar da take tsakanin mutane da danginsu wadda take janyo su da su zo domin su ziyarce su yayin da suke da rai, wannan shi yake janyo su ziyarci kaburansu yayin da ba su da rai. Musamman kamar yadda yake a musulunci cewa ruhin mutum sabanin jikinsa ba ya lalacewa. Ba ma haka ba kawai yakan kara samun karfi na musamman a wannan duniyar sannan yana jin dadin kulawar da masoya suke yi masa ta hanyar ziyartarsa da yi masa addu'a kamar karanta masa fatiha da makamantanta, ta yadda suke kara masa nishadi da karfi.
Don haka bai dace ba mu sha kan mutanen a kan gudanar da irin wannan al'ada wadda take wani nau'in halittar mutum ce, Abin da ya kamata shi ne mu nuna musu yadda ya kamata su aiwatar da hakan, ta yadda sakamakon soyayya ga masoyansu kada su kai zuwa ga sabon Ubangiji.
Ziyarar Kaburburan Malamai
Abin muka yi Magana a kan shi a sama ya shafi ziyarar sauran mutane ne da suke da alaka ta jini da take tsakanin mamaci da mai ziyararsa. Ta yadda sakamakon wannan ziyara zai biya bukatun wanda ya ziyarta ta hanya kulawar da ya yi masa, ta yadda masu ziyara zasu tsabtace kabarinsa har ma su sanya wa kabarin turare da sauransu.
Amma a cikin wadannan masoya akwai wadanda suke malamai ne da wadanda suka kawo gyara a cikin duniya wadanda suke da wani matsayi na musamman wanda ya sha bamban da wadanda suka gabata. Wadannan sun kasance tamkar kamar kyandir ne wanda ya kone kansa domin ya haskaka wa waninsa, haka suma suka haskaka wa mabiyansu ta yadda suka yi rayuwa a cikin kunci, amma suka bai wa mabiyansu taskar ilimi madawwamiya. Sakamakon haka ne suka cancanci yabo da girmamawa. Musamman malamai wadanda suka koyar da al'umma littafin Allah da Sunnar Manzo (s.a.w) ta yadda suka bai wa al'umma abin da zai kai su zuwa ga cin nasarar rayuwar duniya da lahira kuma madawwamiya. Don haka halartar kabarin irin wadannan malaman yana nufin girmama wadanda suke cikin kabarin ne, Sannan kuma sakamakon abin suka yi na yada ilimi ne ya janyo soyuwar al'umma zuwa gare su ta yadda suka yi hidima da kare wadannan ayyuka na su (Littattafai da makamantansu kamar kaburburansu). Hakika duk al'ummar da suke girmama ilimi da malamai ba zasu taba shiga cikin tarkon kuncin ilimi ba.
Ziyarar Kaburburan Shahidai
Haka nan ziyartar kaburburan Shahidai wadanda suka bayar da jininsu domin kare al'ummarsu da addinin Allah shi ma yana da matsayi na musamman wanda ya fi na sauran mutanen da ba su ba.
Ziyartar kaburburan shahidai wadanda suka rasa rayukansu a kan tafarkin Ubangiji, bayan tasirin da yake ga ruhin mutum, sannan yana nuna rikon alkawari a kan tafarkin da suka bayar da jininsu a kai. Wato mai ziyara kamar yana cewa ne yana nan kan tafarkinsu sannan zai yi kariya a kan wannan abin mai tsarki da suka bayar da jininsu. Domin mu kara fahimtar abin da kyau bari mu ba da wani misali wanda yake raye a halin yanzu:
Mutumin da ya ziyarci Dakin Allah kafin ya yi dawafi yakan yi wa Hajrul Aswad sallama ya kuma sanya hannu ya shafe shi da ma'anar cewa yana yin bai'a ne ga Annabi Ibrahim (a.s) gwarzon tauhidi, da nufin cewa tauhidi shi ne abu na gaba a wajensa. Ta yadda zai yi iya kokarinsa wajen yada shi, amma tunda yanzu ba zai iya kai hannunsa ba zuwa ga Annabi Ibrahim ta yadda zai yi masa bai'a wajen daukar alkari domin wannan aiki shi ne sai ya kai hannunsa ga abin da shi Annabi Ibrahim (a.s) ya bari ta yadda zai gabatar da bai'arsa ta hanyar wannan abin da ya bari. Ya zo a cikin hadisi cewa yayin da mutum yake mika hannunsa zuwa ga Hajrul Aswad yana cewa ne: "Na mika amana da alwakarin da na dauka, sannan na jaddada bai'ata ka sheda a kan hakan".
Ziyartar shahidan Badar da Uhud da Karbala da sauran masoyan da suka bayar da jininsu a tafarkin Allah yana bayyanar da wannan al'amari. Masu ziyarar wadannan wurare masu tsarki sukan yi wa masu wannan wuri sallama da mika gaisuwa zuwa ga ruhinsu tsarkaka, sannan suna daukar alkawari ne a kan cigaba da hanyarsu.
Da wani kalamin muna iya cewa ziyarar kabarin wani nau'i ne na girmama su. Sakamakon an kashe shahidi a kan wani abu mai tsarki da yake girmamawa, duk wanda ya ziyarci shahidi ya girmama shi, a hakikanin gaskiya ya girmama wannan akidar ne wadda a kanta ne aka kashe shi, sannan yana daukar kansa wanda yake biyayya akan wannan hanya.
Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)
Ziyarar Kabrin Manzo mai girma (S. A.W) ko kuma Magjinsa mai tsarki (a.s) bayan girmama su a kan abin da suka yi na sadaukar da rayukan su wajen shiryar da al'umma zuwa ga hanyar Allah, Shi ma yana da hukuncin yi musu bai'a. Imam na takwas (a.s) a cikin maganganunsa dangane da ziyarar kaburburan ma'asumai (a.s) yana cewa: Kowane Imami yan da alkawari tsakaninsa da mabiyansa ziyar kabarin Imamai daya daga cikin wannan alkawarin ne".
A hakikanin gaskiya yayin da mutum yake ziyartar kabarin Manzo (s.a.w) ko na Imamai kamar yana yin bai'a da alkawari da su ne cewa ba zai taba bin wata hanya ba a cikin rayuwarsa sai hanyar da suka bari.
Ga abin da mai ziyar kabarin Manzo yake cewa: Idan Muhajirun da Ansar wadanda suka halarci yakin Hudaibiyya sun yi maka bai 'a a kan kariya ga addini (Fathi: 18), Sannan idan matan Makka sun yi maka bai'a a kan gujewa daga yin shirka da sabon Allah (Mumtahna: 12), Idan har Muminai masu sabo sun samo umarni a kan cewa su zo wajenka domin ka nema musu gafa, ni ma ya manzon Allah ya mai ceton al'umma sakamakon halartata zuwa haraminka da sallama zuwa ga kabarinka ina mai yi maka bai'a a kan cewa zan yi kariya ga addininka sannan in yi nesa daga shirka da sabon Allah, sannan sakamakon haka ina rokonka ka neman mani gafara a wurin Allah.
A nan dole mu fahimci cewa ziyarar kaburburan bayin Allah ya sha bamban da yawon shakatawa domin kuwa yana da manufarsa da ta sha bamban da yawon bude ido. Masu yawon bude ido suna zuwa wuri ne domin su more wa idanunsu, suna neman wurare masu kyau ko na tarihi domin su gane wa idanunsu, Saboda haka gurinsu shi ne shakatawa da hutawa, duk da cewa idan wannan bai kasance tare da sabon Allah ba, to musulunci ba ya hani da wannan. Amma masu ziyarar kaburburan bayin Allah suna yi ne domin kara samun alaka da masoyinsu da kuma jaddada alkwarinsu da shi, don haka duk wata wahala da zasu hadu da ita wajen isa zuwa gare shi koda kuwa zai kai ga su dunga gudu a cikin daji da kafafunsu ne da taka kayoyi suna iya jure wa duk hakan.
Dan yawon bude ido yana neman abin da zai biya bukatunsa na kasantuwarsa mai rai ne shi, amma mai ziyara yana kokarin ya shayar da ruhinsa ta hanyar saduwa da masoyinsa, domin kuwa ba zai iya isa zuwa ga masoyinsa ba, sai ya mika hannunsa zuwa ga kabarinsa wanda yake dauke da kanshi da launinsa.
Tarihi yan nuna cewa: Bayan wafatin Manzo Allah (s.a.w) wani bakauye ya shigo garin Madina sai ya zauna a gefen kabarin Manzo sai ya karanta wannan aya wadda take cewa: "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo a gareka suka nemi gafarar Allah Sannan Manzo ya nema musu gafara da sun sami Allah mai karbar tuba mai rahma".
Sai wannan bakauyen balarabe ya ce: Ya kai manzon Allah gani na zo a wannan wuri domin ka nema mani gafara ina mai neman cetonka zuwa ga Allah". A lokacin yana cikin kuka sai ya karanta wannan baiti na waka inda yake cewa:
Ya mafificin mutumin da aka bisne jikinsa a wadannan kasashe,
Kanshinsa ya bice tudu da kwari na wannan yanki.
Ina gabatar da kyautar raina zuwa ga wannan kasa wadda ta boye fiyayyen haliitta.
Bayan ya gama wannan baiti na waka sai ya nemi gafara ya tashi ya tafi abinsa.
Wannan balarabe da muka ambata ya fahimci ma'anar ziyarar kabarin Manzo daga cikin zuciyarsa tsarkakka, saboda haka ne ya taso ya zo domin ya ziyarci shugaban halitta. Wannan ita ce hikimar ziyartar kaburburan 'yan'uwa, masoya, malamai, shahidai a tafarkin Allah da shugabannin addini (a.s) wanda hankali da shari'a suke tabbatar da ingancinsa.
A nan dole ne mu yi bincike ta mahanga daban-daban a kan ziyarar kabari kamar haka:
1-Ziyarar kabarin muminai a mahangar Kur'ani da Sunna.
2-Mata da ziyarar kabari.
3-Ziyarar kabarin Manzo a mahangar manyan malaman musulunci.
4-Ziyarar kabarin Manzo a mahangar Kur'ani da Sunna.
A nan gaba zamu yi bahasi ne a kan wadannan abubuwa guda hudu da muka ambata a sama:
Ziyarar Kabarin Muminai A Mahangar Kur'ani Da Sunna
Ziyarar kabarin muminai musamman wadanda suke da alaka ta jini da mutum, wani abu ne wanda duk mutanen duniya sun hadu akan yin hakan domin kuwa ya dace da halitta mutum, sannan muna iya fahimtar haka daga wannan aya: "Kada ka sallaci kabarin wanda ya mutu dag cikinsu har abada, Sannan kada ka tsaya akan kabarinsa domin kuwa lallai sun kafirce wa Allah da manzonsa, Sannan sun mutu alhalin suna fasikai".
Wannan aya mai girama tana bai wa Manzo umurnin abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Kada ya yi salla ga wadan suka mutu daga cikinsu. " Har abada kada ka sallaci daya daga cikinsu idan ya mutu.
2-Kada ya je a kabarinsu, domin yi musu addu'a ko makamancin haka. (kada ka tsaya akan kabarinsa).
Bangare na biyu na wannan aya yana da muhimmanci na musamman a gare mu, wannan kuwa shi ne, shin tsayuwa a kan kabari yana nufin yayin rufewa ne ko kuwa yana da ma'ana fiye da hakan? Amma masu tafsiri suna karfafa ma'ana ta biyu ne, wanda zamu yi bayani dangane da abin da suke cewa kan hakan.
Bidhawi yana cewa: Ma'anarsa kada ka tsaya a kan kabarinsu yayin rufewa ko ziyara.
Shi ma Suyudi a cikin tafsirul jalalaini ya tafi a kan wannan ra'ayi, Sannan Arif Bursi a cikin tafsirin Ruhul Bayan da Alusi Bagadadi a cikin ruhul ma'ani ya kawo wannan.
Saboda haka Allah madaukaki yana hani ga Manzo a kan ya tsaya a kan kabarin munafukai yayin rufewa ne ko kuwa domin ziyara. Wannan yana nuni ne a kan cewa Manzo ya kasance yana halartar kabarin muminai yayin rufewa ko kuwa lokacin ziyara, sannan yana yi musu addu'a. Domin kuwa idan ba haka ba, babu ma'ana a yi masa hani a kan wannan al'amari.
Saboda haka idan haka ne ma'anar wannan jumla zata kasance kamar haka: Har abada kada ka tsaya a kan kabarin Munafukai.
Sakamakon haka ne zai zamana munafukai sun rasa wannan falala su kuwa muminai suna rabauta daga wannan falala, domin kuwa Manzo yana iya halartar kabarin muminai lokacin rufe su ne ko kuwa lokacin ziyara domin ya yi musu addu'a.
Ziyarar Kabari A Cikin Sunnnar Manzo
Bayan ruwayoyi guda biyu da muka kawo farkon wannan bahasi wadanda suke nuna hikimar ziyara, dole a nan mu kara fadakarwa a kan cewa, Manzo da kansa ya kasance yana zuwa makabartar "Bakiyya" domin ziyartar kaburburan musulmi. Sannan a kasa tarihi ya tabbatar da hakan kamar haka:
1-Musulim a cikin sahih dinsa yana cewa: An ruwaito daga A'isha cewa duk karshen dare yakan tafi makabarta domin ziyara, duk lokacin da ya shiga wannan wuri yana ce musu:
"Amincin Allah ya tabbata gareku ya gidan mutane muminai kun samu abin da ake alkwari da zuwansa a gaba, Kuna rayuwa tsakanin mutuwa da tashin kiyama, mu ma zamu hadu daku, Ya Allah ka gafarta wa wadanda suke a cikin" Bakiyya".
2-Muslim a cikin Sahih dinsa ya ruwaito daga A'isha tana cewa Manzo ya ce mata: Jibril ya sauka zuwa gareshi ya ce masa Allah yana ba da umarni da cewa ku tafi ziyarar mutanen "Bakiyya" Sannan ku nema musu gafara.
A'isha tana cewa: Sai na tambayi Manzo cewa, yaya za yi musu addu'a? Sai Manzo ya ce ki ce: "Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku mutanen wannan gida daga muminai da musulmai, Allah ya jikan wadanda suka riga mu da wadanda zasu zo bayanmu daga cikinsu, Mu ma insha Allah muna nan zuwa mu hadu da ku".
3- Muslim yana ruwaitowa daga Buraida cewa: Manzo (s.a.w). ya kasance yana koyar da Sahabbansa cewa yayin ziyara ga abin da zasu ce: "Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku mutanen wannan gida muminai muna nan zamu hadu da ku, Muna rokon Allah da ya ba mu lafiya tare da ku.
Mata Da Ziyarar Kabari
Mata suna da hukunci guda ne da maza dangane da ziyarar masoyansu da waliyyan Allah, domin kuwa hukuncin maza da mata a cikin musulunci duka abu guda ne, sai kawai wurin da aka bambanta maza da mata a wasu wurare na musamman tare da dalili.
Manzo (s.a.w) Yana kira zuwa ga musulmi da cewa: "Ku ziyarci kaburbura domin suna tuna muku lahira".
Sannan a wani hadisi daban yana cewa: "Ku ziyarci makabarta domin akwai darasi a cikin yin hakan. "
Gaskiya ne wadannan kira tare da lura da yadda aka amfani lamirin maza kamar ya nuna cewa da maza ake, amma kamar yadda muka tunatar cewa kusan dukkan kira da ake yi a cikin Kur'ani da hadisi kamar ana kira ne zuwa ga maza, saboda haka dukkan ayoyin da aka yi amfani da su wajen umartar mutane a kan yin salla da azumi da wannan sigar ne wato an yi amfani da lamirin maza ne, amma wannan umarni ya kunshi mata kamar yadda ya kunshi maza. Kamar yadda yake cewa: Ku tsayar da salla ku bayar da zakka duk abin da kuka gabatar domin kawunanku na alheri to zaku same shi a wajen Allah"
Wannan umarni bisa lura ga ka'idar larabci kamar yana fuskantar maza ne, amma wannan hukunci ya kunshi duka maza da mata ne.
Saboda haka kiran da a aka yi a cikin dukkan wadannan hadisai guda biyu da cewa"ku ziyarci kaburbura"duk da cewa ya fuskantar maza ne amma sakamakon haka ya hada maza da mata ne.
Bayan wannan hadisi kuma a kawai wasu ruwayoyi da suke nuni da halascin ziyarar kabari ga mace, saboda haka a nan zamu ambaci wadannann hadisai kamar haka:
1-Muslim yan ruwato a cikin sahih dinsa daga Manzo cewa: Jibril ya sauko zuwa gare ya ce ma ni: Ubangijinka yana ba da umarni da a ziyarci kaburburan mutanen "Bakiyya" Sannan ka nema musu gafara a wajen Allah"
Sai Manzo ya tashi daga bisa shimfidarsa ya tafi Bakiyya domin ziyara, sai A'isha ta bi Manzo (s.a.w). daga baya, sai ta fahimci umarnin da Allah ya aiko wa Manzo. A lokacin sai ta tambayi Manzo cewa to yaya zan ziyarci mutanen baki?
Sai Manzo ya ce: "Ki ce amincin Allah ya tabbata ga nutanen wannan gida daga musulmai da muminai, Allah ya gafarta wa wdan da suka riga mu da wadanda zasu zo bayammu.
Wurin da ake kafa dalili a nan shi ne wajen koyar da A'isha yadda ake ziyara, saboda haka idan ya zamana mace bai halitta ba ta ta ziyarci makabarta, a nan babu ma'ana Manzo ya koyar da matarsa.
Sannan bugu da kari A'isha ta kasance tana gaya wa sauran mata dangane da abin da ya auku, saboda haka da wannan zamu iya gane cewa ya hada kowa da kowa cewa ziyarar baki daya ta halatta ga mace da namiji. Domin kuwa matar Manzo da sauran mata duk daya suke a wajen hukuncin Allah.
2-Fadima (a.s) 'yar Manzo (s.a.w) kuma daya daga cikin mutanen mayafi (wadanda aka saukar da aya ta 33 suratul ahzab a kansu) Bayan wafatin Manzo ta kasance tana ziyartar kabarin amminta wato shahidin Uhud inda take yin salla raka'a biyu sannan ta yi kuka a kabarinsa.
Hakim Nishaburi bayan ya ruwaito wannan ruwaya yana cewa: wadanda suka ruwaito wannan ruwaya dukkansu amintattu ne kuma adalai, ta wannan fuskar ba su da bambanci da maruwaitan Bukahri da Muslim.
3-Tirmizi ya ruwaito daga Abdullahi Bn abi malika yana cewa: Lokacin da Abdurrahman Bn Abibakar ya rasu a wani wuri da ake kira da (Hubsha) Sai aka dauki jana'izar shi zuwa Makka a ka rufe shi a can. Bayn wani lokaci sai A'isha wadda take 'yar uwa ce a gare shi ta zo Makka domin ziyarar kabarin Abdurrahaman dan'uwanta, Sannan ta yi wasu wakoki guda biyu wadanda suke nuna tsananin damuwarta a kan rashinsa.
4-Bukhari yana rubuta cewa: Wata rana Mnazo ya ga wata mata gefen wani kabari tana kuka, sai ya ce mata "Ki mallaki kanki sannan ki yi hakuri a kan rasa wani naki da kika yi".
Amma bukhari bai ruwaito cigaban wannan hadisi ba, amma Abu Da'ud a cikin sunan dinsa ya cigaba da wannan hadisi ga abin yake kawowa: Wannan mata ba ta gane Manzo ba, sai ta kalubalanci Manzo ta ce: Me ya dame ka dangane da abin da musibar da ta same ni?
A wannan lokaci sai wata mata da take gefenta ta ce mata kin gane kuwa wannan kowane ne?, Manzon Allah ne (s.a.w).
A wannan lokaci wannan matar domin ta gyara abin da ta yi wa Manzo sai ta tafi gidan Manzo ta ce masa: Ya manzon Allah ka yi hakuri ban gane kai ne ba. Sai Manzo ya amsa mata da cewa: Hakuri a cikin musibar da ta samu mutum shi ne abin da ya dace.
Idan da ziyartar kabarin 'yan uwa ya kasan ce wani aiki ne daya haramta, mai makon Manzo ya umurce da yin hakuri zai ce ma ta ne ke wannan aiki naki ya haramata a fili, amma sai ya umurce ta da yin hakuri a kan abin da ya same ta ba wai ta nisanci kabarin ba.
Amsar wasu tambayoyi guda biyu
Wasu sun haramta ziyarar mata zuwa kaburbura, suna kafa hujjarsu ne kuwa da wadannan hadisai guda biyu kamar haka:
1-"Allah ya la'anci mata masu ziyarar kabari"
Amsa:
Wannan Hadisi ya rasa sharuddan da ya kamata ya kasance yana da su kafin a iya kafa hujja da shi. Domin bisa ga dogara da dalilai da aka ambata a baya dole ne mu dauka wannan hadisi an shafe shi, Sannan cikin sa'a wasu daga cikin malaman hadisi na Sunna sun dauki wannan hadisi matsayin shafaffe. Tirmiz maruwaicin wannan hadisi yana cewa: Wannan hadisi an shafe shi lokacin da kafin halasta ziyartar kabari ne, amma lokacin da Manzo ya halasta ziyarar kaburbura wannan hukunci ya hade mace da namiji babu bambanci.
Kurdabi yana cewa: Wannan hadisi yana Magana ne a kan matan da suke bayar da dukkan lokacinsu a makabarta ne, ta yadda sakamakon haka ba su bayar da hakkokin mazansu da ya hau kansu. Kuma sheda a kan haka shi ne Manzo ya yi amfani da kalmar "Zuwwar" wadda take da ma'anar kambamawa, wato wadanda suke yi yawaita ziyara.
2-Ibn maja yana ruwaito daga Ali Bn Abi Dalib cewa: Manzo (s.a.w). Ya fito sai ya ga wasu mata a zaune, sai ya tambaue su me ya sa suke zaune? sai suka ce: Muna jiran jana'iza ne.
Sai ya ce zaku yi wa jana'izar wanka ne?
Suka ce: A'a.
Sai ya ce: zaku dauki gawar ne?
Suka ce: A'a.
Ya ce: zaku saka gawar kabari ne?
Suka ce: A'a.
Sai Manzo ya ce: ku koma gida kuma su masu sabo ne ba masu neman lada ba.
Amsa:
Wannan hadisi ta fuskar ma'ana da isnadi ba a bin dogaro ba ne da za a iya kafa hujja da shi, saboda sanadin wannan hadisi (maruwaita hadisin) akwai Dinar Bn Amru ya shiga a cikinsu, ta fuskar masu ilimin ruwaya suna cewa ba a san shi ba, kuma mutum ne mai karya mai sabo kuma wanda ake bari.
Shin ana iya dogara wajen kafa hujja da irin wannan hadisi wanda maruwaicinsa yake da wadannan siffofi na rauni?
Mu dauka ma dangane wannan hadisi yana da inganci, sam ba shi da alaka da ziyarar kabari, domin kuwa Allah wadai din da Manzo ya yi ya shafi matan da suka fito domin kallon janaza, ba tare da wani aiki da zasu yi ba wajen kai jana'zar. Saboda haka wannan bai shafi batun ziyarar kaburbura ba.
A nan dole mu yi tunatar wa akan wani al'amari shi ne, addinin musulunci addini ne wanda ya dace da halitta mutum, kuma mai sauki, Manzo yana cewa: "Akidun musulunci akidu ne tabbatattu duk wanda zai shiga cikinsu ya shiga tare da dalilai na hankali".
Mu dauka cewa mahaifiyar mumini sai ta rasa danta aka kuma rufe shi a karkashin kasa, sai ta damu a kan hakan, abin da kawai zata iya yi a nan shi ne ta ziyarci kabarinsa. A nan idan aka hana ta yin wannan aiki wanda ya dace da hankali kuma dukkan mutanen duniya sun tafi a kan hakan, wannan zai haifar da muguwar damuwa ga zuciyar uwa. Shin musulunci zai yi hani da irin wannan aiki sannan kuma ya zama addini mai sauki?
Kai asali ma ziyarar kaburbura wani darasi ne kuma mai sanya mutum ya rika tunawa da lahira wanda kuma ya kunshi karantawa wadanda aka ziyarta fatiha. Ta yaya za a hana mata dangane da samun wannan falala?
Da wani kalamin kasantuwar hikimar ziyarar kaburbura tana kunshe da daukar darasi da tunawa da lahira, ta yaya za a kebance maza kawai ban da mata a ciki?
Kasantuwar ziyarar kaburbura ya nisanta da duk wani sabo, idan muka dauka haka kuma sai aka hana mata a wancan lokaci, to kila sakamakon cewa ba su kiyaye sharuddan da suka kamata ne.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012