Ziyarar Kabari3
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Ziyarar Kabarin dukkan musulmai da musamman ziyarar kabarin Manzo wani abu ne Wanda yake mustahabbi mai karfi a cikin musulunci. Sannan malaman hadisai daga Sunna da Shi'a sun ruwaito hadisai da dama a kan mustahabbancin ziyarar kabarin Manzo wadanda wasu daga cikinsu sun gabata a cikin bahasin da ya gabata ta yadda babu wani malami daga cikin malaman musuluncin da ya ba wa kansa damar yin shakku a kan mustahabbancin ziyarar Manzo. Wannan kuwa ya hada har da Muhammad Bn Abduh wanda yake da wasu masatlolin dangane da abin da ya shafi annabawa, a nan ba kawai ya yi shiru ba ne, sai dai ya yi magana a kan mustahabbcin ziyarar Manzo (s.a.w). Sannan mun kawo abin da yake cewa dangane da hakan a bahasimmu na baya.
Tare da la'akari da kasantuwar mustahabbicn ziyarar Manzo, amma msulmi sun kasu akan wannan kyauata ta Ubangiji:
1-Mazauna Madina
Mazauna Madina sakamakon makwabtaka da suke da ita da Manzo (s.a.w). Suna iya ziyartarsa ba tare wata wahala ba don aiwatara da wannan mustahabbi.
1-Mazauna sauran wurare a cikin duniya
Mazauna sauran sassan duniya dole ne su yi tafiya domin su damar yin sallama ga kabarin Manzo Su ce"Amincin Allah ya tabbata a gareka ya manzon Allah"
A nan tambayar da zata shi ne menene hukuncin wannan tafiya a shari'a?
Jawabain wannan tambaya kuwa a fili yake domin wannan amsa tana matsayin gabatarwa ce domin aiwatar da aikin mustahabbi, saboda haka a akidar wasu malamai tana matsayin mustahabbi, wasu kuwa suna cewa tana hukunci "Mubah" ne. Duk yadda ta kama kasantuwar wannan tafiya domin aiwatar da mustahabbanci ce ba zata taba zama haramun ba. Domin kuwa ba zai inganta ba a hankali Allah madaukaki ya umurce mu da aikin mustahabbi na ziyartar Manzo sannan ya haramta abin da yake matsayin gabatarwa ne domin aiwatar da wannan aikin. Saboda haka daga nan muna iya gane cewa hukuncin wannan tafiya domin aiwatar da wannan aiki ta halitta.
Kamar yadda yake a tarihi shi ne musulman da suke rayuwa a sauran sassan duniya wato ba wadanda suke rayuwa ba a garin Madina sukan taure kayansu domin tafiya zuwa ziyarar kabarin Manzo mai girma a nan ga wasu misalai a kan hakan:
Bilal wanda yake mai kiran salla ne na Manzo kuma Manzo ya kasance yana kaunarsa. Bayan tafiyar Manzo ya zabi ya tafi wani wuri yiwa musulunci hidima, sakamakon haka ne ya yi hijara daga garin Madina. Wani dare sai ya ga Manzo a cikin mafarki yana ce masa: Wannan wane irin rashin kulawa ne Bilal? Yanzu lokaci bai yi ba da zaka ziyarce ne?
Lokacin da Bilal ya tashi daga barci yana cikin bakin cikin da ya mamaye masa zuciya, sai kawai ya tanaji abubuwan bukata domin yin tafiya kuma ya tafi zuwa Madina. Lokacin da Bilal ya shiga a cikin Raudar Manzo yana kuka da murya mai karfi a wannan hali ya dinga goga fusakarsa a kan kabarin manazo. A nan haka sai kwatsam abin kauanar Manzo wato Hasan da Husain (a.s) sai suka yi wajensa sai ya kama su ya runguma, sai suka ce masa, Muna tsananin son mu ji muryar kiran sallarka, kiran sallar da kake yi wa kakanmu manzon Allah (s.a.w).
Bilal lokacin sallar Asubahi sai ya hau wurin da ya kasance yana kiran salla a zamanin Manzo (s.a.w). ya kira salla.
A lokacin da kira sallarsa ya mamaye Madina Ya girgiza garin Madina a wannan lokaci. A lokacin da ya yi kalmar shahada a cikin kiran sallarsa sai duk mutane suka daga murya suna kuka, a lokacin da kuwa ya yi shahada a kan manzancin Manzo (Ashhahadu anna Muhammadar Rasulullah) ai sai duk mutanen Madina suka yo waje suna kuka, kamar yadda ake rubutawa bayan ranar da Manzo ya yi wafati madina ba ta taba ganin irin kukan da ta gani ba a wannan lokaci.
2-Umar Bn Abdul Aziz ya kasance yana hayar mutane domin su taho daga Sham zuwa madina domin su yi masa sallama ga Manzo.
Subki a cikin Futuhus Sham yana rubuta cewa: Lokacin Umar Bn Abdul Aziz ya yi Sulhu da mutanen Kods sai Ka'abul Akhbar ya shigo wajen kuma ya musulunta, a wannan lokaci Umar ya ji dadi kwarai da musuluntarsa.
Sai Umar ya ce masa: Kana iya bi na mu tafi madina mu ziyarci kabarin Manzo ta yadda zamu fa'idantu da ziyararsa?
Sai Ka'ab ya amsa wa khalifa abin da ya nema daga gareshi, ya yi shirin tafiya tare da khalifa. A lokacin da Umar ya shiga garin madina, farkon abin da ya fara yi shi ne ya shiga masallacin Manzo ne domin ya yi wa Manzo sallama.
Duk da yake ba mu da bukatar mu kafa sheda a nan da irin wadannan misalai, domin kuwa al'ummar musulmi duk tsawon karnoni sha hudu sun dauki wannan al'amari na ziyara Manzo a matsayin mustahabbi kuma suna tafiya Madina domin su aiwatar da wannan mustahabbi.
Subki dangane da tafiyar ayari-ayari zuwa ziyarara Manzo ya yi maganganu da dama akan hakan, ya kara da cewa masu ziyara bayan sun gama aikin hajji suka kama hanyar Madina ne domin su kai wa Manzo ziyara, ya kara da cewa: wata sa'a sakamakon fahimtar ladar da yake cikin yin hakan sukan dauki hanyar da tafi nisa zuwa Madina, domin su samu lada mai yawa a kan haka. Sannan ya cigaba da cewa, wadanda suke tunanin cewa dalilin da ya sa mutane suke tafiya madina shi ne domin su ziyarci masallacin Manzo kuma su yi salla a ciki wannan kuskure ne, domin kuwa abin masu ziyarar suke fada ya saba wa wannan tunanin. Domin manufarsu a kan wannan ziyara shi ne su ziyarci kabari Manzo, sannan wannan shi ne gurinsu na ziyarar Madina.
Domin kuwa idan manufarsu a kan wannan tafiya shi ne ziyartar masallaci me ya sa ba su tafiya Kods domin su ziyarci masallacin baitil mukaddas wanda yin salla a cikinsa bai gaza wa yin salla a masallacin Manzo ba?
Kamar yadda yake haduwar malamai a kan wani hukunci yana nuna ingancin wannan hukunci a shari'a haka nan haduwar dukkan musulmi a kan wani aiki yana nuna mafi daukaka kasantuwan wannan abin a cikin shari'a.
Masu Haramta Tafiya Don Ziyarar Manzo
Har zuwa karshen karni na bakwai malamai sun hadu a kan wannan al'amari cewa tafiya domin aiwatar da wani aiki na mustahabbi koda ba ta zama mustahabbi ba to alal akalla ta halasta. Amma a farkon karni na takwas, Sai Ibn Taimiyya ya yi riko da hadisin Manzo wanda Abu Huraira ya ruwaito ta yadda ya saba wa dukkan malamai da suka hadu a kan wannan al'amari. Wannan ruwaya kuwa da Ibn taimiyya ya yi mafani da ita, an ruwaito ta ne ta fuska guda uku, amma abin da yake iya tabbatar wa Ibn taimiyya da manufarsa ya zo da fuska biyu ne kamar haka:
1-Kada a yi nufin tafiya sai zuwa masallatai guda uku: Wannan masallaci nawa, masallacin ka'aba da Masallacin Kods.
2-Ana yin tafiya ne kawai zuwa ga masallatai guda uku.
Ibn taimiyya ya yi riko ne da zahirin wannan hadisi domin tabbatar da manufarsa, ta yadda ya yi da'awar cewa domin aiwatar da ayyukan ibada masallatai uku ne kawai mutum zai iya zuwa domin yin hakan. Saboda haka ziyarar Manzo wanda yake matsayin ibada ba ya daya daga cikin wadannan abubuwa guda uku.
Wannan kafa hujja ta Ibn Taimiyya kuwa idan muka lura da kayu zamu iya gane rashsin ingancinsa, domin kuwa ba shi da kafafuwa masu karfi.
Domin kuwa mun san cewa jumlar da take kebewa tana ginuwa daga sassa guda biyu kamar haka:
1-Jumlar da ake kebewa daga gareta: "Ba wanda ya zo wurina"
2- Jumlar da a ka kebance "Sai Ali"
Hadisin da ya gabata ya ginu ne ta hanyar jumloli biyu ne.
1-jumla ta farko jumlar da aka kebance daga gare ta "Kada ku yi tafiya".
2-Jumla ta biyu kuwa, wadda a ka kebance. "Sai masallatai uku".
A jumlar ta farko abin da aka kebance bai fito ba a fili, bisa la'akari da ka'dar larabci a nan dole mu kadda wata jumla, wadda zata iya zama daya daga cikin wadannan jumloli guda biyu kamar haka:
1-Mai yiwuwa ka iya cewa "masallaci" ne. (Wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku)
2-Mai yiwuwa ana nufin "wuri" ne (kada ka yi tafiya zuwa wani wuri sai masallatai guda uku).
Saboda haka bisa ga tsammani na farko, zai zama ma'anar jumla zai zama haka, wato kada ka yi tafiya zuwa kowa ne masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata.
Saboda haka idan muka dauki wannan ma'ana zai zama cewa Manzo yana Magana ne a kan masallatai, wato don mutum ya yi salla kada ya yi wahala don tafiya kowane masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata. Saboda haka a nan ziyarar Manzo ba ta cikin abin da aka hana a cikin wannan hadisi domin ba a kansa ake Magana ba. Sannan dalilin da ya sa aka yi hani tafiya wani masallaci domin yin salla domin sauran masallatai hukunci guda garesu babu wani wanda ya fi wani daraja daga cikinsu. Saboda haka yayin da mutum yake da damar yin salla a daya daga cikin masallatai me zai sanya ya sha wahala domin ya tafi waninsa. Misali kamar idan akwai masallacin jumma'a a wani gari me zai sanya mutum ya tafi wani gari domin ya yi sallar jumma'a a can, domin kuwa ladar da zai samu a wancan masallacin ba ta dara wadda zai samu ba a wannan na garinsu. Amma dangane da wadancan masallatai uku abin ba haka yake ba. Domin salla a cikin daya daga cikinsu ya fi salla a cikin sauran masallatai.
Saboda haka tare da kula da cewa a cikin wannan hadisi an yi magana ne kawai a kana masallatai, don haka tafiya zuwa wasu wurare bai shafi wannan hani na hadisi ba, saboda haka ba ya Magana a kan halasci ko haramcin yin hakan.
Amma idan muka dauki ma'ana ta biyu ma'anar wannan hadisi zata kasance kamar haka: kada ka yi tafiya sai zuwa wurare guda uku (masallatai guda uku da muka ambata)
Idan muka dauki wannan ma'ana dogaron Ibn Taimiyya yana iya zama dai-dai. Amma tare da lura da yadda tarihin musulmai ya tafi a kan mustahabbacin tafiya zuwa kabarin Manzo (s.a.w). Domin ziyara tana nuna mana rashin ingancin wannan hadisi.
Na farko kamar yadda muka gani a cikin hadisin da ya gabata, ana iya tsammanin wata ma'ana daban, sakamakon wannan ma'ana kuwa ba za a samu wani fito na fito ba a hadisai da ayoyi da kuma tarihin musulmi da suke nuni a kan halascin ziyarar Manzo. Kuma tare da daukar ma'anar farko musamman kasantuwar mu dauki cewa kalmar da zamu iya kaddarawa ita ce masallaci, domin kasantuwar dacewarta da abin da ya zo a cikin jumlar, kuma shi ne abin da ya fi dacewa ya kuma fi karfi. Saboda haka wannan hukunci wanda Ibn Taimiyya ya dauka zai zama sam ba shi da ma'ana a nan.
Haka nan idan muka dauki ma'ana ta biyu wato muka dauka cewa ai a nan ana nufin "wuri" wato bai halitta ba mutum ya tafi wani wuri sai wadannan wurare guda uku, wannann kuwa zai bayar da ma'anar da ba ta dace ba, sannan fitowar wannan kalma daga mai hikima musamman Manzo ba zai yiwu ba. Wato ya zama an hana zuwa kowane wuri sai wadannan wurare guda uku (Masallacin ka'aba, Kudus da Masallacin Manzo). Alhalin musulunci ya halatta wasu tafiye-tafiye da dama a cikin musulunci, wasu daga cikinsu ma mustahabbi ne. Misali kamar tafiya domin neman ilimi, ko tafiya domin kasuwanci, ko tafiya don sada zumunci, tafiya don yawon bude ido, tafiya domin jihadi da dai sauran tafiye-tafiye da suke halas wadansu ma mustahabbi a musulunci.
Saboda haka a nan dole ne mu dauki ma'ana ta farko wato masallaci, cewa kada mutum ya yi tafiya domin ya je wani masallaci sai masallatai guda uku, domin kuwa su ne su kafi sauran masallatai matsayi. Da wannan ne zamu fitar da batun tafiya domin ziyarar Manzo domin ba ita ake Magana ba a cikin wannan hadisi.
Bayan dangane da ingancin wannan hadisi koda an dauki ma'ana ta farko, a akwai shakku a cikinsa. Domin kuwa yana nufin wannan Magana ta fito daga bakin Manzo inda take nuni da cewa tafiya zuwa kowane masallaci ba ta inganta sai masallatai guda uku. Alhali kuwa ruwayoyi sun zo a kan cewa Manzo (s.a.w)asu ranakun Asabar yakan tafi kasa wata sa'a bisa abin hawa domin ya je masallacin "Kuba" domin ya yi salla raka'a biyu a wajen. Wannan masallaci a zamanin da Manzo yake a raye yana da tazarar kilo mita 12 tsakaninsa da Madina.
Ziyarar Masallatai Guda Bakwai
A sassa daban-daban na garin Madina akwai wasu masallatai guda bakwai wadanda mahajjata sukan ziyarta yayin da suka je Madina, Idan ma muka kara da (masallacin Raddi shams, da na Bilal da na Ijaba) Yawansu zai wuce bakwai.
Mahajjata suka yi salla raka'a biyu a wadannan masallatai musamman sukan fi ba da muhimmanci akan masallacin Imam Ali (a.s) Yanzu tambaya zata iya zuwa cewa: Idan har yin salla a wadannan masallatai ba shi da wani fifiko a kan sauran masallatai, to me ya sa mahajjata suke zuwa ziyarar wadannan masallatai sannan su yi salla a cikinsu, alhali kuwa wannan bai zo ba a cikin shari'a? Saboda haka wannan zai zama "Bidi'a" kenan a cikin addini.
Amsar wannan tambaya kuwa a fili take:
Tafiya domin ziyarar wadannan masallatai ba wai don ya zo a cikin shari'a ba ne, ko kuma yin salla a cikin wadannan masallatai yana da wani fifiko na musamman, sam ba haka ba ne manufar tafiya zuwa wadannan wurare sai daya daga cikin biyu ne kamar haka:
1-Tunawa da musulman farko wadanda suka kasance cikin mawuyacin halin yakin Khandak amma a cikin wannan hali ne suka gina wadannan masallatai don su yi salla kuma suka cigaba da yakinsu. Domin kuwa wasu daga cikin wadannan masallatai suna wuraren da aka gwabza tsakanin sojin tauhidi da na shirka yayin da aka kashe gwarzon shirka (Amru Bn Abdu wud) kuma sakmakon haka ne gwamnatin dagutu ta kawo karshe. Halartar musulmi a wadannan wurare tana tuna musu da wannan abubuwa da suka faru a wannan wuri. Sannan yana kara karfafa alakarsu da wadanacan musulman farko.
2-Amma ma'ana ta biyu kuwa da zata iya zama dalilin da ya sa musulmai suke zuwa wadannan masallatai ita ce, domin neman tabarraki daga wadannan wurare, domin jinanan shahidai a kan hanyar tauhidi a wadannan wurare ne ya zube, Saboda haka wannan wurare sun sheda kai da kawon shahidan musulunci, sannan kuma wuri na kai-da-kawon manyan musulmai.
Wadannan manufofi su ne suke sanya musulmi suna tafiya zuwa wadannan wurare da makamantansu, kamar wurin da aka yi yakin khaibar da Fadak, duk sun samo asali ne daga wadannan manufofi guda biyu.
Amma yin salla a wadannan wurare bayan musulmi sun shiga wadannan masallatai domin aiwatar da umarnin Ubangiji cewa duk yayin da mutum ya shiga wani masallaci to ya gabatar da salla raka'a biyu a matsayin gaisuwa ga shi masallacin. Saboda haka ba wannan ba ne hadafinsu na zuwa wadannan masallatai ba domin su gabatar da salla a wajen. Wannan niyya tana zuwa ne bayan sun shiga masallatan.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012