Hakkin Gani
  • Take: Hakkin Gani
  • marubucin: Imam Sajjad a.s
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:5:42 1-10-1403

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Hakkin Gani
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa:"Amma kuma hakkin gani shi ne ka rufe shi daga ganin abin da bai halatta ba, ka yi lura da gani da shi, ka bar wulkata shi kana mai kallon ko'ina sai idan gun darasi ne da zaka dauka, ko wani amfani na ilimi da shi, domin gani kofa ne na lura".
Ya wajaba a kiyaye gani daga haram musamman kallon namiji ga mace, Musulunci ya hana kallo mai tayar da sha'awa ko kuma da nufin tayar da sha'awa, kamar yadda ya hana kallon jikin mace ajnabiyya in banda fuska da tafuka koda ba tare da nufin sha'awa ba. Haka nan yana hana mace kallon abin da maza bisa al'ada sukan rufe shi na daga jikinsu, amma in ba haka ba, ba ya zama haramun.
Amma idan ya zama a matsayi na dole kamar a matsayi na magani da ba wani mai iyawa sai ajnabi to a bisa lalura ya halatta idan zai yiwu ta madubi ko ruwa, idan ba zai yiwu ba to a lokacin yana halatta da idanu .
Haka nan akwai abubuwan da ya halatta da wanda bai halatta ba a gani a telebijin da satalayet da bidiyo da hoto kamar tsaraici. Haka nan yana da kyau ga iyaye su kayyade wa yara lokacin kallonsu domin yakan hana su karatu, a wannan kwanaki an samu lissafi mai yawa a kasashen Yammacin duniya na kallon telebijin da ya sanya karatun yara ya yi rauni sosai.
Ganin haram kibiya ce daga kibiyoyin Iblis da yake farautar mutane da shi, da zarar wani ganin ya wakana yana iya tayar da sha'awa wacce take abu ce mai karya rai da tarbiyyarta. Wani ganin na haram yana faruwa daga nan ne sai so ya shiga, sai kuma magana da juna, sai alkawarin mahada, sai taba juna, sai faruwar haram. Don haka ne manzon rahama (s.a.w) yake cewa: "Duba -zuwa haram- kibiya ce mai guba daga kibiyoyin Iblis -shedan- wanda duk ya bar ta saboda tsoron Allah, to Allah zai ba shi wani imani da zai ji zakinsa a cikin zuciyarsa". (Ma'arijul Yakin fi Usuliddin: Muhammad Sabzawari; s 407).
Akwai wasu bayanai masu amfani game da idanuwa da yadda za a kiyaye shi da suka zo a wasu littattafai kamar haka. Yana da kyau a nisanci tsawaita lokaci ana amfani da ido musamman idan yana kallon abu mai haske ne, sai dai ana yi ana hutawa, haka nan ma ga masu wasu ayyuka kamar walda, da karatu, da kira. Kamar yadda ba a san karatu a mota ko kan wani abu da yake motsi yayin da yake motsawa. Sannan yana da kyau matuka a kula da lafiyar ido, kada a bari kuda ya rika taba shi, domin yana yada cututtukan ido. Sannan kada a bari haske mai karfi ya rika dukan takardar da ake karatu da ita, abin ya fi shi ne hasken ya kasance yana dukan bayan mai karatu ko ta saman kansa sannan sai ya hau takarda. Kuma yana da muhimmanci a rika yin abubuwan da suke kara karfin ido kamar kallo kore.
Game da amfani da tubarau domin rage karfin haske suna bayar da shawarar amfani da mai kalamr toka, amma idan domin kare idanu daga kura ne ko haki sai a yi amfani da yalo, amma yana da muhimmanci sanya tubarau ya kasance da umarnin likita ne. Ido shi ne mafi muhimmancin abu ga mutum, don haka sai a koma wa masu ilimin ido domin shawarar yadda za a kare shi.
Imam Ali (a.s) yana cewa: "Babu wata gaba a mariskai na zahiri da ya kai daukakar ido, don haka kada ku ba wa ido duk abin da yake so, sai ya shagaltar da ku daga ambaton Allah". Wannan ruwayar tana da muhimmanci musamman a wannan zamanin da kayana kallo suka yawaita, idan mutum ya ba wa idanuwansa ikon ganin duk wani abu da yake son gani to lallai kuwa zai yi asarar abubuwa masu yawan gaske, musamman idan wadannan abubuwan sun kasance na haram ne.
Idanuwa da kunnuwa a matsayinsu na hanyoyin riskar abu ta hanyar gani da ji, suna da matukar girma a cikin nassin addini, sannan addini ya yi nuni da cewa rashin yin amfani da su ta hanyar da ta dace shi ya kawo wa mafi yawan mutane asarar lahira. Ubangiji madaukaki yana cewa: "Hakika wadannan da suka kafirta babu bambanci a wurinsu, ka yi musu gargadi ko ba ka yi musu ba, su ba zasu yi imani ba, Allah ya yi wani rufi a kan zukatansu, da jinsu, da ganinsu, kuma suna da azaba mai girma".
A nan zamu ga wadannan ma'abota azaba an azabatar da su ne bayan an yi wa ganinsu wani rufi ta yadda ba zai iya ganin gaskiya ba koda kuwa ya duba ta. Kamar dai yadda yake cewa ne "Muka sanya yunki -marufi ko garkuwa da kariya- ta gabansa, da kuma wani yunki ta bayansu, sai muka rufe su ba sa iya gani". (Yasin: ). Sai dai kada wani ya yi tunanin haka kawai aka yi musu hakan, domin kafin Allah ya yi musu hakan su ne suka zabi hanyar da zasu kai ga wannan halin.
Sannan akwai bahasosi masu amfani game da gani wadanda suka shafi akida musamman game da lamarin ganin Allah da Ash'ariyya suka tafi a kansa, sauran musulmi suka yi musun sa. Ahlul-baiti (a.s) sun tafi a kan cewa babu wata hanyar da za a ga Ubangiji da idanuwa, domin duk wani abu da aka gani to jiki ne mai iyaka da yake dorantar mai ganin sa. Allah kuwa ya barranta daga wadannan siffofin na iyaka, kamar jiki, da mahalli, da wuri, da yanayi (kuality), da kala, da adadi (kuantity), da kewaye, da hali, da duk wani sharadi na abin da za a iya gani.
Wannan bahasi ne mai fadi idan muka shiga nassosin shari'a da suka zo a Kur'ani mai girma da hadisai masu daukaka, sai dai zamu yi dan nuni kadan da abin ta fuskancin Falsafa ne kawai. Duk wani abu da za a iya gani da ido dole ne ya kasance yana da wasu sharuddan abin da ake iya gani, wadannan sharuddan sun hada da iyaka, ta yadda zai iya kasancewa daura da abin da zai gan shi, amma idan bai tsaya daura da shi a wata iyaka ba ayyananniya babu wata hanyar da zai iya ganin sa.
Sannan ya kasance jiki ne, jiki shi ne duk abin da yake da kusurwoyi uku, sai dai zamu iya cewa wannan jiki ne na mandik (mathematical body, logical body) da yake ainihin zatin jiki ne (essence) wanda shi ma ba a iya ganin sa, sai idan jiki na dabi'a (natural body) wanda yake bujurowa (accident) ya bujuro masa.
Allah ba ko daya ne daga cikin su ba, domin shi ba kusurwowi ba ne da ma'anar jikin mandik, ba kuma jiki ne na dabi'a ba; domin da ya kasance jiki ne na mandik, da babu shi ke nan, sai ubangiji ya kasance surar kwakwalwa da tunani ne, kamar yadda da ya kasance jikin dabi'a da ya kasance daya daga cikinmu, sai ya nemi mai samar da shi, domin dabi'a wacce take mai motsi maras iyaka, da iyaka, da mahalli ba yadda za a yi tana da wadannan bukatun sai ta kasance ita tun azal akwaita a matsayin ba ta da farko!.
Wannan yana lizimta mana ken an dole ne Ubangiji ya kasance daya daga cikin dabi'a (nature) idan dai har zai yiwu a gan shi. Amma matukar shi ba dabi'a ba ne to babu wata hanyar ganin sa. Don haka ne ma imam Ali (a.s) ya gaya wa wani mai tambayarsa shin ka ga Ubangijinka? Sai ya ce masa: E, ban taba bauta wa ubangijin da ban gan shi ba. Amma domin gudun kada mai tambaya ya fada cikin halaka, sai imam Ali (a.s) ya gaggauta yin bayani don kada a dauka gani na ido ake nufi a halaka yana mai cewa: Idanuwa ba sa riskarsa da gani na kuru-kuru, sai dai zukata ne suke riskarsa da hakakanin imani. (Attauhid: 308).
Sannan mahalli ko wuri a falsafa da aka fi sani da cewa shi ne wurin da wani abu ya cinye, samuwarsa ta cike shi. Ko kuma mahalli da ma'anar da mutane suke fahimta sabanin na falsafa ta yadda zai kasance a kan wani abu, kamar kan kujera, ko kan tebur. Mahalli ko wuri da dukkan ma'anonin nan ba yadda zai kasance ga Allah mai kololuwar daraja maras iyaka a kamala da samuwa, domin babu yadda Allah madaukaki zai kasance abin dauka (mahmul), kamar yadda shi ba mai dauka ba ne da ma'anar daukar mahalli.
Sannan babu ma'ana ya kasance abin dauka da ma'anar falsafa kamar bayanin jumla (object ko predicate) kamar yadda ba yadda zai kasance mai dauka da wannan ma'anar ta falsafa balle ya kasance mafari a jumla (subject), don haka Ubangiji ba ya zama Mafarin Jumla (Subject) ko bayanin Jumla (Object).
Haka nan Allah ba shi da wuri, shi yana ko'ina, domin samun wuri zai komar da mu ga cewa shi abin dauka ne, alhalin mun yi nuni da cewa ba zai kasance abin dauka ba. kamar yadda tabbatar rashin kasancewarsa jiki ya kore masa samuwar wuri, domin duk abin da yake da wurin samuwarsa dole ne ya kasance jiki.
Haka nan Allah ba shi da yanayi (kuality), domin yanayi ko dai ya kasance na gani sai ya kasance kamar launi, ko ya kasance mai bujurowa jiki kamar girma da kankanta, ko ya kasance mai bujurowa rai, sai ya kasance ilimi, ko saken zuci, ko saken tunani, ko hankalta. Sannan akwai abubuwa da yawa da suke karkashin yanayi da suka hada da sanyi, da zafi, da bushewa, da danyancewa, da haduwa, da rabuwa, da kanshi, da wari, da ki, da so, da kyama, da sha'awa da wasu masu yawa.
Dukkan wadannan abubuwan da muka fada babu wanda Allah ya siffantu da shi saboda dalilai masu fadin gaske. Misali mu dauki launi, idan an tambaya Allah wace kala ce, zamu samu cewa wannan tambayar ba ta da ma'ana, domin launi yana bujurowa jiki ne, shi kuwa ba jiki ba ne. Sannan wannan yana nuna mana ba zai yiwu ba a ga Allah domin dan Adam ba ya iya gani sai ta cikin launi, idan kuwa babu launi babu gani, don haka Ubangiji ba abin gani ba ne.
Haka nan yawa (kuantity) ba ya samun ubangiji, domin yawa kala biyu ne, ko hadadde sai ya kasance jiki mai kusurwowi uku, ko ya kasance rababbe sai ya kasance adadi ke nan, kamar daya da biyu. Idan mun duba dukkan wadannan abubuwan babu yadda ubangiji zai siffanu da ko dayansu, domin shi ba jiki ba ne, ba kuma adadi ba ne, da ya kasance adadi da ya koma zuwa ga jiki ke nan.
Haka nan ubangiji ba shi da "kiyasin hali", kamar a ce samansa ko kasansa, ko kuma yana jirkice kamar yadda mutum yakan iya sanya kansa a kasa, kafafunsa a sama. Dukkan wani abu da ya danganci abubuwan da suke bujurowa ga samammu kamar yadda ake kiransu masu bujurowa to Allah sabaninsu yake. Don haka ya tabbata ke nan ba zai yiwu a ga Allah madaukaki ba.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Saturday, June 19, 2010