MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Hakkin Hannu
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin hannunka shi ne kada ka shimfida ta kan abin da bai halatta gareka ba, sai ka samu azabar Allah a gobe -kiyama- da wannan shimfidawar da ka yi, ka kuma samu zargi daga mutane a gidan yau -duniya-. Sannan kada ka rike ta daga abin da Allah ya wajabta mata, sai dai ka kiyaye ta da rike ta daga mafi yawan abin da bai halatta gareta ba, da shimfida ta zuwa ga mafi yawan abin da bai zama wajibi a kanta ba, sai ta kasance ta yi hankali, ta daukaka a wannan gida -duniya-, sannan lada kyakkyawa ya wajaba gareta daga Allah a gidan gobe -lahira-".
Shimfida hannu da aka hana daga dukkan wani abu da bai halatta ba shi ne sanya hannu domin dauka ko karbar duk wani abu da bai halatta ba. Idan mutum ya dauki wani abu da ba nasa ba, alhalin babu izinin mai shi, ko ya bayar da wani abu da ba nasa ba wanda ba shi da hakki a kansa, to ya shimfida hannunsa inda bai halatta ba. Sannan sai Imam (a.s) ya yi nuni da cewa sakamakon hakan shi ne mutum ya fada cikin fushin Allah a ranar kiyama, sannan kuma ya samu suka da zargin mutane a ranar lahira.
Kamar yadda shimfida hannu zuwa ga abin da bai halatta ba yake laifi haka ma rike hannu daga aikta abin da yake wajibi yake laifi. Akasin haka kuma kamar yadda shimfida hannu zuwa ga abin da yake wajibi yake tilas, haka na rike hannun daga abin da yake haram ne yake wajibi. Saba wa duka wannan lamurran biyu yana iya kai mutum ga azabar Allah madaukaki a ranar kiyama, kuma mutane su zarge shi da muzantawa a wannan gida na duniya.
Sannan ba a son mutum ya yi duk abin da ya ga dama ko da halal ne, an fi so ya tsakaita a rayuwarsa, shi bai bai takaita ba, shi kuma bai yawaita da shige gona da iri ba. Sau da yawa shugabannin tarbiyyar kai suka takaita da abin da yake wadatar da su a rayuwa koda kuwa suna da yalwa.
Hannun a harshen larabci yana da ma'anoni masu yawa da wasu daga ciki an yi amfani da su a ayoyin Kur'ani mai daraja, yana da ma'anar karfi kamar a cikin fadinsa madaukaki "Ka ambaci bawanmu Dawud ma'abocin karfi…" . Kuma ta zo da ma'anar ni'ima a fadinsa "… sai dai hannayensa shimfidaddu ne yana ciyarwa yadda ya so…", Surar Ma'ida: 64. A hausa bahaushe yakan ce: "Wane yana da sakin hannu", idan yana da kyauta da baiwa ga mutane.
Amma a wannan ayar ma yana iya zama da ma'anar iko da karfi da kudura ne yahudawa suka ce: "Hannun Allah yana da kukumi…" Surar Ma'ida: 64, saboda abin da suke nufi a nan shi ne cewar; Allah ya riga ya saukar da hukuncin shari'a, kuma ba zai iya shafe shi ya kawo wani ba. Da wannan ne ya shahara gun yahudawa cewa suna inkarin masu shafewa da ababan shafewa na daga ayoyin Kur'ani "Nasihu da Mansuh".
A daya bangaren kuma yana koma wa zuwa ga musun "Canja kaddarar Allah" da aka fi sani da "Bada" da larabci. Sai Allah ya yi musu da raddi cewa yana iya shafe hukuncin shari'a ya zo da wani, hannunsa ba shi da kukumi a kan hakan, kuma yana iya canja abin da ya kaddara kan mutane ko wani mutum ya sauya musu da wata kaddarar daban, don haka hannunsa ba shi da kukumi a bude yake.
Sannan a nan zamu so mu yi nuni da wasu abubuwa biyu da suka shafi "Dokar hannu", da kuma "Dokar ya hau kan hannu". Dokar hannu ita ce ka'idan nan mai cewa duk wani abu da aka samu a hannun wani mutum to yana nuna nasa ne, don haka idan zai sayar ko zai bayar kyauta za a iya karba a yi amfani da shi sai dai idan akwai wani dalili na musamman da ya tabbatar da cewa ba nasa ba ne. Wannan doka ta zo a cikin littattafai masu yawa kamar; Wasa'il, j 17, s 525, babi 8, h 4.
Amma "Dokar ya hau kan hannu" ita kuma doka ce wacce take wajbta girmama dukiyoyin mutane, tana mai cewa duk wanda ya lalata dukiyar wani to dole ne ya biya. Kamar wanda ya yi kwace, ko ya yi sata, ko ya yi sakaci da dukiyar wasu, da sauransu duk wadannan ya hau kansu ne su biya. Akwai ruwayoyi masu yawa da suke nuni da wannan kamar: mustadrak, j 3, babin kwace, s 145-6. da Sunan Ibn majah: j 2, s 802. Da yake ba muna maganar fikihu ne ba don haka muka takaita da wadannan takaitattun kalamai.
Hannu wani abu ne da ake yin amfani da shi wurin duka a kasashenmu, sau da yawa masu karfi ko iko kamar a hanya da titina, ko kuma 'yan sanda, ko kuma malamai da daliban manyan aji sukan yi amfani da hannunsu ko wani abu da suke dauke da shi domin dukan wasu. Yana da kyau mu sani babu wani wuri da addinin musulunci mai tsari ya yarda wani ya doke wani, idan kuwa ya doke shi a bisa ka'ida sai ya biya diyyar duka, kuma idan wurin ya tashi kamar ya yi ja, ko baki, duk akwai diyya.
Duka ba ya halatta sai ga mace mai kin mijinta a mataki na uku bayan matakai biyu na wa'azi da kauracewa a kwanciya. Sai kuma ga yara da iyayensa musamman uba zai ladabtar da shi domin gyaran halinsa ba don huce haushi ba, ko kuma bawa da ubangijinsa zai iya dukansa don gyaran halinsa. Amma dukan malami ga yara dalibansa don ladabtarwa yana bukatar izinin uba ko shugaban daular musulunci idan akwai shi.
Sannan duk inda aka yarda da duka don ladabtarwa ba a son ya wuce sau biyar, imma dai sau daya, ko biyu, ko uku, amma tsanantawa ga yaro shi ne sau shida, shi ma da wadancan dokoki da muka ambata. Haka nan ladabtar da bawa ba a son ya wuce sau biyar idan za a doke shi, da sauran hukunce-hukuncen duka.
Magana kan duka tana bukatar babban littafi ne, sai dai wanda yake son ya samu wasu karin bayanai yana iya duba littafin: Durrul Mandhud, na Gulpaigani: mas'ala ta hudu game da dukan yara, s 181, da sauran littattafai.
Haka nan hannu wani abu ne da ake amfani da shi domin nuna wani abu, ko sanya wata alama, ko nuna musiba, sai dai game da musiba an hana dukan fuska da kai da sauran jiki ko yakushinsa yayin musiba, kamar yadda aka hana fadin kalmomin da ba su dace ba.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Saturday, June 19, 2010