Hakkin 'Ya'ya
  • Take: Hakkin 'Ya'ya
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 6:59:1 2-10-1403

HAFIZ MUHAMMAD SA'ID hfazah@yahoo.com
Hakkokin 'Ya'ya
Nauyin Da Yake Kan Iyaye
Iyaye su ne wadanda suke da nauyi mai girma da muhimmanci a fagen tarbiyyar 'ya'yansu manyan gobe da ya hau kansu, suna iya cimma wannan buri da dan Adam yake bukatarsa matuka ta hanyar kiyaye dokokin da Ubangiji ya gindaya. Kuma kiyaye haka zai iya bayar da wata gudummuwa maras misali ga duniyar dan Adam, kuma su ma 'ya'ya da wannan ne zasu koma masu girmama iyaye da suke kawo ci gaba ga dan Adam.
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Kamar yadda iyaye zasu take hakkin 'ya'ya, haka ma 'ya'ya zasu take hakkin iyaye . Wannan al'amari ya sanya muka ga karancin biyayya ga iyaye sakamakon karancin kiyaye hakkokin 'ya'yansu da yake faruwa ne.

Zabar Jagoran Iyali (Mai Gida)
Dole ne uba a matsayinsa na shugaban iyali ya kasance mai karfi da amana, da kiyaye doka, da tausayi. Kuma mafi muhimmancin abin da zai taimaka masa wajen tarbiyyar yaransa shi ne; ya kiyaye hakkin matarsa wacce take uwar 'ya'yansa, kuma mataimakiyarsa a kan al'amuran gida. Kuma mafi muhimmanci kan wannan shi ne; ya zabar wa 'ya'yansa uwa ta gari tun farkon aurensa, domin samun gina salihin gida mai albarka. Wani mutum ya zo wajen Imam Hasan (a.s) domin ya ba shi shawara game da mijin da zai zaba wa 'yarsa. Sai Imam Hasan (a.s) ya ce: "Ka aura mata mutum mai tsoron Allah, domin shi idan ya so ta, sai ya girmama (karrama) ta, idan kuwa ya ki ta, to ba zai zalunce ta ba . Don haka ne yana da muhimmanci matuka a samarwa 'ya saurayi mai imani da takawa domin aure, domin idan yana son ta sai ya karrama ta, kuma idan ma ta bata masa to ba zai zalunce ta, kuma wannan yana daga sirri mai girma na gina gida mai tarbiyya.

Muhimmacin Matsayin Uwa
Uwa a bisa koyarwar addinin musulunci tana daga cikin mafi muhimmancin abubuwan da suke taka rawa ta musamman ga tarbiyyar yara, kuma sau da yawa 'ya'ya sukan kasance karkashin tasiri mai karfi na iyayensu, kuma wannan tasiri yana farawa ne tun daga lokacin da aka dauki ciki har zuwa balagar yaro. Don haka ne ma fiyayyen halitta ya ce: Ku kiyayi mace mai kyau da ta tashi ta girma a cikin mummunan gida kaskantacce . Kamar yadda Imam Sadik (a.s) yake cewa: Farin ciki ya tabbata ga wanda mahaifiyarsa ta kasance kamammiya .
Samun uwa ta gari yana daga cikin mafi muhimmancin abubuwan da suke da tasiri ga tarbiyyar yara, idan an samu uwa mai tausayi, da hankali, da ilimi, da sanin yakamata, wacce kuma mijinta yake ganin girmanta da darajarta, to wannan yana tasiri kwarai da gaske a cikin tarbiyar yara da halayensu.
Domin idan uwa ta kasance mai daraja da kima a wajen mijinta to wannan ne zai iya samar mata abin da muka fada a sama na kwanciyar hankali da nutsuwa da sakina wadanda suke da tasiri kwarai da gaske ga tarbiyyar yara. Domin uwar da ba ta samu wannan ba, to lallai zata kasance cikin fada kodayaushe da ganin laifin kowa, da kuma huce haushinta a kan 'ya'yanta.
Kuma wannan yana iya sanya ta la'ana ko zagin wadannan yara da kuma zaluntarsu, al'amarin da zai iya haifar musu da mummunar al'ada da lalacewa a rayuwarsu, kuma suna iya zama alakakai ga al'ummarsu su kasance tamkar guba a cikinta, kuma tabbas wannan rashin nutsuwar nata da rashin kwanciyar hankali zai yi tasiri a cikin rayuwar 'ya'yanta.

Samar Da Yanayin Tarbiyya
Dole ne a samar da wani yanayi da zai iya bayar da tarbiyya ga yaro, domin idan ba a samu wani yanayi mai kyau da yaro zai iya samun haka ba, to za a yi ta yin tubka da warwara ne, kuma al'amarin tarbiyya ba zai iya samun gindin zama ba ke nan. Tunda an damka al'amarin tarbiyyar 'ya'ya a hannun iyaye to ke nan ya zama dole ne iyaye su samar da wannan yanayi da zai iya samar da yara na gari masu tarbiyya.
Don haka ne masu tarbiyyar yara suka lurasshe da iyaye kan su kula da duk wadannan abubuwan da suka hada da zabar uwa da uba nagari, abincin da yaro yake ci ya kasance na halala, yanayin rayuwar uwa yayin da ta samu ciki, da irin abin da zata rika ci, sanya wa yaro suna nagari, da yi masa akika (yanka ranar suna), da samar masa da bukatunsa na jiki da na ruhi, da ya hada da kyautata kula da lafiyarsa, da ilmantarwa, da abokai na gari, da mutunta shi, da sanya masa jin daukar nauyi da ya hau kansa, da kuma tasowa cikin yanayin da yake ganin uwarsa kamammiya ce, da bayar da sadaka, da addu'ar iyaye ta gari garesu, da karfafarsa kan yin ayyuka na gari, kamar kyautata wa mutane, da girmama su, da ganin kimarsu, da kuma nuna masa munin rashin yin hakan, da nuna masa laifinsa, da nuna masa tsoron mahaliccinsa, da abubuwa masu yawa da suke da tasiri a rayuwarsa ta nan gaba.
Muna iya ganin tasirin irin wannan al'amarin da ya kai ga cewa shari'a ta yi nuni da dukkaninsu, tasirin siffofi da halaye da ayyukan iyaye hatta a lokacin kwanciya, yana nan a kan rayuwar yaro, da ayyukansa, da halayensa na halitta, da na dabi'a.
Abu ne muhimmi da ya zo a sharia da aka yi nuni da shi a wata ruwaya da cewa: "Idan lokacin kwanciya da kulluwar ciki suna da zuciya mai nutsuwa, da halin kwanciyar hankali, da annashuwa, kuma jijiyoyinsu suna kan halinsu na dabi'arsu, da kuma rashin raurawa a cikin jikinsu, to yaron zai yi kama da iyayensa ne .

Zabar Suna Mai Kyau
Kamar yadda muka kawo ne cewa akwai tasirin suna mai kyau a kan yaro, kuma masu hikima suna ganin cewa; sunan mutum yana nuna al'adun al'ummarsa ne, da addininta, da kuma iyalin gidansu, da akidarsu. Sau da yawa mukan ga mai kyakkyawan suna yana alfahari da shi, kuma yana jin duakaka a kan mai suna maras kyau, kuma wannan yana matukar tasiri sosai a kimar mutum a cikin al'ummar da mutum yake rayuwa.
Mun ga irin wannan tasiri sosai ga mai dauke da sunan makasa alayen gidan Annabi gun masoyansu ta yadda ba ya iya fadin sunansa da kyau domin jin kaskanci da kunya, kuma tabbas mutumin da ba shi da sunan da ya dace zai samu jin zogin ruhinsa, da jin wulakantuwa, da kaskantuwa, a cikin al'ummarsa.
Imam Bakir (a.s) yana fada game da al'amarin suna mai kyau: "Mafi soyuwar sunaye su ne wadanda suke nuna bauta ga Allah madaukaki, kuma mafi kyawu daga garesu su ne wadanda suke sunaye ne na annabawa . Sunayen da suke nuna bauta ga Allah (s.w.t) su ne kamar: Abdullah, Abdurrahman da sauransu.

Addu'a Domin Fata Nagari Ga Yara
Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka hau kan iya ye shi ne; kiyaye yalwa, da rabautar yaro a cikin rayuwa, wannan kuwa yana iya kansancewa ta hanyar yi musu kyakkyawan fata kodayaushe, da kuma yi musu addu'a mai kyau, kuma tana daya daga cikin hanyar arzutarsu ta duniya da lahira. Sannan kuma mu sani cewa; addu'ar iyaye ga 'ya'yansu tana daga cikin addu'ar da ba a mayar da ita.
Don haka ne ma gidan da uwaye suke tsinewa 'ya'yansu to tabbas wannan gida yana tare da lalacewa da tabewa, da kuma talaucewa da daidaicewa, kuma musifar hakan ba tana takaituwa, ko tsayuwa kan 'ya'ya ba ne kawai, tana shafar har su ma iyaye da suka yi, don haka ne ma yana daga cikin abu mafi muni iyaye su rika mummunan fata da muguwar addu'a kan 'ya'ya, idan suka yi fushi da su kada su ce komai idan dai ba zasu fadi alheri ba, idan kuwa zasu fada; to su ce: Allah ka shirya mana su.
Don haka ne iyaye ku zage damtse wajen yi wa 'ya'yanku addu'a ta gari dare da rana, kuma ku ba wa wannan al'amari muhimmanci na musamman.
Lalacewar mafi yawancin 'ya'ya sakamakon mugun baki da la'ana da mummunar addu'ar iyaye ne, kuma wannan yana shafar har su iyayen ne, kuma sannan sai ya dame su a rayuwarsu.
Muna iya ganin wani mutum da ya kai kukan 'ya'yansa masu tsananin saba masa wajen manzon rahama (s.a.w), sai Annabi (s.a.w) ya tambaye shi cewa; Shin ka kyamace su ne (da mugun baki)? sai ya ce: Haka ne. sai Annabi (s.a.w) ya ce: Kai ne ka jawo tabewarsu. A wata ruwayar manzon rahama (s.a.w) yana cewa: "Ku kiyayi mummunar addu'ar iyaye, domin tafi takobi kaifi" .
Don haka iyaye sai a kiyaye, kuma koda kuna da hakki kan 'ya'ya bisa abin da suka saba muku sai ku kiyaye, balle cewa ma wani lokaci 'ya'yan ne suke da hakki amma sai iyaye su runtse idanuwansu, su kawar da kai daga gaskiya, su yi musu mugun baki!

Karfafa Izzar Rai
Daya daga cikin matsalolin da samari da yara suke fama da su shi ne; rashin samun dogaro da kai, da jin daukaka a cikin ransu, wannan kuwa yana sanya su jin tsoron shiga cikin al'umma da bayyanar da baiwar da Allah ya huwace musu ta ilimi da fasaha, hada da rashin karbar wani nauyi da aka dora musu, kuma da yawa daga rashin dacewa, da rashin cin nasara, da rashin samun ci gaba, sun faru ne sakamakon hakan, musamman yayin da sukan ji cewa su wulakantantu ne kas-kantattu ba zasu iya tabuka komai ba.
Don haka ne ma jin daukaka a cikin rai daya daga cikin mafi muhimmancin abubuwa ne da ake iya amfani da su wajen tarbiyyantar da yara, da kuma samar da yanayi mai dacewa don cigabansu da na al'ummarsu. Wannan wata siffa ce, kuma hakki da ya hau kan iyaye su ga sun kafa a cikin zukatan 'ya'yansu, kuma wannan yana iya yiwuwa ta hanyoyi daban-daban.
Girmama 'ya'ya, da ba su kima, da mu'amala da su a matsayin cikakkun mutane, suna daga cikin hanyoyin da za a iya karfafa wanna siffa mai kima da muhimmanci garesu.

Bukatar Tausasawa Da Nuna Kauna
Daya daga cikin bala'o'in da wannan duniyar tamu ta yau take fuskanta shi ne; kasancewar duniyarmu ta ci gaban kere-kere ce, sai wannan lamarin ya kai ga daukar 'ya'ya da iyaye tamkar kayan kere-keren ci gaban zamani, wannan kuwa ya sanya mana fadawa cikin matsaloli da ba sa kirguwa, mafi girman matsalar yara da samari a yau shi ne karancin tausayawa, da nuna kauna da so da suka fuskanta daga wurin iyaye. Mu sani cewa; yara kamar yadda suke bukatar abinci da ruwan sha, da tufafin sawa, haka nan ma suna matukar bukatar nuna kauna da so daga iyaye fiye da wadancan abubuwan da muka lissafa.
Daya daga cikin mafi munin abin da ya fuskanci wannan duniyar shi ne; karancin soyayya daga bangaren iyaye da 'ya'ya, kuma wannan ya haifar da tazara tsakaninsu, ta yadda ba a iya samun dasa kyakkyawar tarbiyya da halaye na gari da jin daukar nauyin hidima ga al'umma ga samarin yau. Wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon dabi'ar fushi da kansa, da gidansu, da iyalansa, da yake cike a zuciyarsa sakamakon wancan tarbiyya ta karancin alakar soyayya da take tsakaninsu da iyayensu.
Rashin samun kauna yana kai wa ga yara da samari su ji wulakantuwa a cikin ransu, kuma su rasa jin girma a cikin zukatansu, kuma da wannan ne a hankali sai mutuncin su ya zube a idanuwansu, daga nan kuma sai su ji duk aikin da suka yi ba sa damuwa. Akwai nuni a wasu ruwayoyi da cewa; idan mutum ya rasa kunya ya kasane ba ya jin kunya to yana iya aikata duk wani aiki (na rashin kunya) da ya ga dama. Imam Ali al-Hadi (a.s) yana cewa: "Duk wanda ransa ta wulakanta (a gunsa), to kada ka aminta daga sharrinsa" .
Don haka ne nake cewa; ya kai uba mai daraja! ka fitar da danka daga fushin jin haushin kai saboda gudun jin wulakantuwa, ka fitar da shi daga wannan azaba ta ruhi idan ka jefa shi cikinta, sannan kuma tun farko kada ka kai shi ga wannan matsayi domin riga-kafi ya fi magani, ka sani yaran da suka taso suna masu jin izza a cikin ransu, suna masu ganin kima a zukatansu, wadanda suka fito a gidan da suka samu nuni na cikakkiyar soyayya ingantatta kuma sahihiya, to wadannan su ne suke zama masu daukar nauyin gidansu da al'ummarsu a nan gaba, kuma su ne wadanda suke abin dogaro a cikin jama'a.


Sakin Fuska Da Nuna Kauna
Sakin fuska da nuna kauna ga yara yana daga cikin abubuwan da manzon rahama (s.a.w) ya yi nuni da shi a matsayin wani al'amari mai lada da yawa, kuma ibada ce mai garabasa kamar yadda ya zo a cikin fadinsa mai tsira yana cewa: "Duk wanda ya sumbanci dansa to Allah zai rubuta masa kyakkyawa (lada)" .
Sai dai yana da kyau mu kula sosai da al'amarin girmama yaro, a game da kauna da girmama shi sai mu kiyaye kada mu wuce gona da iri, domin idan hakan ya faru ba zamu samu sakamako mai kyau ba, sai dai ma ya haifar da mummunan tasiri a tarbiyyar yaro, domin wannan yaron zai taso yana mai yarda da kansa a matsayin shi wankakke ne kuma ba wanda ya isa ya more shi, idan kuwa al'umma ba su ba shi wannan mahangar ba, to sai ya sanya shi ya ji yankewar kauna a al'ummarsa, kuma ya fuskanci matsalar kuncin rai da jin kaskantuwa.
Imam Bakir (a.s) yana cewa: "Mafi sharrin iyaye shi ne wanda kyautatawa (soyayya) ta kai shi ga shisshigi (wuce gona da iri)" . Wato: ya wuce gona da iri a nuna kauna da soyayya ga dansa, har ya sabbaba lalacewar yaronsa. Irin wannan wuce gona da iri, da ketare iyaka shi ne wanda yake kaiwa ga rufe ido, da danne gaskiya, da rashin ganin laifin 'ya'ya, da ba su gaskiya duk laifin da suka yi kuwa. Yakan kai ga idan suka yi mummuna sai wasu suka gaya mana domin suna kaunarmu, saboda mu gyara halayen 'ya'yanmu, amma maimakon iyaye su karbi wannan gyaran su yi godiya, sai su dauki wadannan masu nasiha din a matsayin gaba, da nuna cewa; ba sa kaunar 'ya'yansu ne!.

Daidaito Cikin Kauna Da Kyauta
Kiyaye daidaito da adalci tsakanin yara cikin mu'amala da su, yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci tsakanin yara, wannan mas'alar abu ce wacce take mai muhimmanci sosai matuka a gun yaro, don haka sai iyaye su kiyaye daidaito a nuna kaunarsu da sonsu ga 'ya'yansu, koda kuwa a badini akwai wanda suka fi so saboda wasu dalilai. Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Ku yi adalci tsakanin 'ya'yanku, kamar yadda kuma kuke son a kiyaye daidaito a tsakaninku, a cikin kyautatawa, da adalci .
Amma game da muhimmancin kyauta muna iya cewa; Kyauta wani abu ne da yake kawo kauna mai yawa a cikin zuciyar wanda aka ba wa kyauta ga mai yin kyauta, kuma kari kan hakan tana sanya karfafa alaka da dankon zumunci a zukata, sannan kuma alama ce ta girmamawa ga wanda aka ba wa kyauta din a matsayin cewa; ya kula da wanda ya ba wa kyauta kuma zuciyarsa tana kaunarsa, hada da cewa tana kawo jin dadin rai a zukata, da sanya jin nishadi ga wanda aka ba wa kyautar, kuma ana iya karfafa yaro da sanya shi jin farin ciki, da koya masa yin kyauta ga wasu, da karfafarsa.

Tanadin Arzikin Halal
Uba shi ne yake daukar nauyin uwa da 'ya'ya, don haka ya zama dole ne ya yi tanadin abincin halal garesu domin gina musu jiki mai lafiya ta hanyar halal, kuma wannan shi ne zai sanya albarka a cikin rayuwarsu. Mu sani cewa; abinci yana da tasiri mai yawa a cikin jiki da ruhin mutum, kuma yana da babbar rawa da yake takawa a kan tarbiyyar yara na gari.
Sannan tasirin abinci kan yaro yana farawa ne tun yana cikin mahaifiyarsa, wannan al'amari ne da addini, da ilimin zamani ya tabbatar da shi.
Sannan kuma shari'a ta yi umarni da yalwata wa yara da dukkan iyali wajen ciyarwa da tufatarwa, babu kwauro, babu barna, kuma daidai gwargwadon hali, kada a tsananta kan yara, kuma dukkan wadannan abubuwan suna da tasiri mai yawa wajen tarbiyyar yara na gari.



Samar Da Wani Yanayi Mai Sanya Nishadi
Daya daga cikin mafi muhimmancin bukatun yara shi ne samar da hanyar reno da tarbiyya mai kyau, yanayin da yake na farin ciki da nishadi ga yaro da nuna kauna da soyayya shi ne na farko a muhimmanci. Kuma ya hau kan iyaye su tabbatar da cewa ba su hana yara wannan yanayin ba, abubuwan da sukan iya samar da wannan yanayi mai tasiri a tarbiyya suna iya hadawa da kyakkyawan hali, da nuna kauna ga yaro, yin wasa da yara da raha, da kuma sanya su farin ciki da annashuwa.
Iyayen da suke damuwa da tarbiyyar yaransu ba zasu taba dora haushin fushinsu ko bakin cikinsu ko daukar fansar haka a kan yara ba, domin wani babban abin takaici wani lokaci iyaye sukan samu bakin ciki sai su huce haushinsa kan yaransu da ba su ji ba su gani ba.
Iyaye masu kishin tarbiyya ta gari ba sa lalata wa 'ya'yansu yanayi mai kyau na farin ciki kuma ba sa gurbata musu shi.
Sannan kuma suna kokarin ganin sun boye wannan bakin cikin ne a cikin zukatansu, sai kuma su bayyanar da farin ciki da annashuwa a fusakunsu. Ya zo a wata ruwaya cewa; "Mumini shi ne wanda yake farin cikinsa yana fuskarsa, bakin cikinsa yana zuciyarsa .
?
Muhimmancin Wasan Yara
Ya zo a cikin surar yusuf aya ta 12, cewa; Ka aika mu tare da shi gobe ya yi annashuwa ya yi wasa…". Wasa yana daga cikin abubuwan bukata na yarinta, kuma wasa yana sanya wa yara kaifin kwakwalwa da karfin jiki, da koya musu dubaru da hikimomi.
Ana iya karfafar ruhin yara ta hanyar sanya masu wasanni da tsararrakinsu, da koya musu abubuwa ba kai tsaye ba, da kuma koya masa shiga cikin al'umma da hulda da mutane tun yana karami, da mayar da shi na al'umma.
Wasa hanya ce da yara suke bayyanar da ra'ayoyinsu da tunaninsu da abubuwan da suke damunsu sannan kuma yana sanya wa yara yin farin ciki, don haka ne a bisa koyarwar mazhabin Ahlul Baiti (a.s) masana suka bayar da muhimmanci sosai ga wasan yara.
Wata rana a kan hanya manzon rahama (s.a.w) ya ga wasu yara suna wasa da kasa, sai wasu daga sahabbansa suka so su hana su yin wannan wasan, sai manzon Allah (s.a.w) ya ce da su: "Ku kyale su, hakika kasa kakar (farin cikin) yara ce" .



Tsammani Da Buri Marasa Amfani
Wasu iyayen suka so su sanya yara a matsayinsu ba tare da sun san suna hakan ba, sai su dauki yaro kamar babba irinsu, sai su takura shi duk abin da ya yi saboda suna ganin bai cika ba ko bai yi daidai ba, sai su rika tsammani da burin abin da ba zai yiwu a same shi ga yaro ba.
Suna ganin laifin yaro duk abin da ya yi, wani lokaci sukan doke shi saboda ba daidai ya yi ba. Sun manta cewa ya kamata ne su kalli yaro ta mahangar yara ba ta manya ba, sun manta cewa yaro yana da halaye da tunani da tajriba da hankali da sani da karfi da ya saba da nasu da sauran manya.
Mu sani yaro ba kamar babba ba ne, yaro ba ya fahimtar muhimmancin aiwatar da alkawura da yin ayyukan da suka hau kansa kamar babba, dole ne mu shiga duniyar yaro domin mu'amala da shi, mu nisanci ba shi ayyukan wahala da suka wuce haddinsa, sannan mu yi mu'amala da shi da tausasawa.

Kula Da Lafiyar Yaro
Kamar yadda aka yi umarni da kiyaye tarbiyyar yara wacce take abu ce da ta shafi ruhinsa da gyaran kansa, haka nan aka yi umarni da kula da lafiyar yara, da muhimmantar da mas'alar lafiyar jikinsu, da tanadar musu da duk wani yanayi mai kyau da zai hana su daukar cututtuka.
Daya daga mafi muhimmancin al'amura da suka zama dole mu ambata a nan shi ne: al'amarin nan da musulunci ya karfafa na shayarwa ga yaro har zuwa shekaru biyu, wannan wani abu ne da aka karfafa shi a Kur'ani mai girma da sunnar ma'aiki mai daraja, sannan kuma a wannan zamanin bayan kusan karni goma sha hudu da wannan umarni mai kima na musulunci sai ga ilimin lafiya da tarbiyya ya karfafa shi matuka.

Wajebcin Tarbiyya
A koyarwar nan ta musulunci da Ahlul bait (a.s) sun karfafa kan tarbiyyar yaro ta zamantakewa da kyawawan halaye, don haka a wannan al'umma ya hau kan iyaye su kiyaye hadarin fadawa cikin miyagun halaye da sukan iya jefa yara cikin munanan halaye masu hadari, kuma wannan al'amari na tarbiyya yana farawa ne daga ranar da aka haifi yaro.
Na farko dai dole ne su sanar da yaransu akida sahihiya da take kunshe da koyarwar kadaita Allah madaukaki wacce take ba ta da wata kaucewa daga tafarki madaidaici na tsira, da dora shi bisa tafarkin shiriya, da kuma kare shi daga fadawa hannun masu tunanin shaidanci da batarwa, wannan tauhidi shi ne zai kasance mataki na farko, kuma dandano mai dadi da yaro zai fara dandana, kuma shuka tafarko da ya hau kan iya ye su dasa kuma su ba ta ruwa don ta tofu ta yi karfi da kwari.
Wannan ne ma ya sanya aka yi umarnin yin kiran salla da ikama a kunnuwan yaro yayin da ya zo duniya, sai a yi kiran salla a na dama, a yi ikama a na hagu, domin yaro ya fara da jin mafi dadin kalmomi, kuma mafi tsarkinsu, wadanda su ne tushen addini kuma asasinsa da suke dauke da kadaita Allah madaukaki, kuma su ne mafi tasiri a ruhin yara wajen tarbiyya da dasa imani a zukatansu, kuma wannan shi ne mataki na farko da jagoran wannan duniya da lahira ya koyar da mabiyansa (s.a.w) .
Imam Sadik (a.s) ya yi nuni da cewa; shekara ta bakwai ita ce shekarar da za a fara koyawa yaro sanin tarbiyyar addini, da koyar da shi hukunce-hukuncensa, yana mai cewa: Ya zama wajibi ne a kan iyaye a shekara ta bakwai su sanar da 'ya'yansu haram.

Kula Da Mutuncin Yaro
Kula da mutuncin yaro da kimarsa ta hanyoyi daban-daban kamar yin shawara da shi yana daga cikin mafi muhimmancin abu da yake karfafarsa a lokacin yarinta da samartaka. Duk sadda wani mutum ya kasance abin shawarta to wannan yana sanya masa jin cewa; yana da wata kamala ta tunani da gudummuwa wajen gina al'ummarsa ta hanyar tunani da hankali da baiwar da Allah ya yi masa, kuma ya samu jin farin cikin cewa shi mai amfanar da al'ummarsa ne ta hanyar shawararsa.
A musulunci an dauki samari da suka kai matakin balaga wato; shekaru 14 ga yaro ko 9 ga yarinya a matsayin mataimaka kuma wazirai masu bayar da shawara ga uwa da uba.
Wannan al'amarin yana nuni da cewa ya kamata mu amfana daga tunani da ra'ayoyin yara ne, kuma muna iya ganin wannan a fili a hadisin Annabi (s.a.w) mai daraja a fadinsa: "Yaro shugaba ne a shekaru bakwai, kuma bawa ne a shekaru bakwai, kuma waziri ne a shekaru bakwai" .

Karfafa Alakar Tattaunawa
Mutane gaba daya musamman yara da samari suna bukatar alakar tattaunawa da zantawa matukar gaske, kuma akwai bukatar iyaye da malamai da masu tarbiyyarsu su yi magana da su da tausayawa, hakika yara suna bukatar magana mai tausasa zukata da lausasawa da tausayawa mai cike da nuna kauna da soyayya, kuma wannan yana taimakawa wajen maganin matsalolinsu na rayinsu, kuma yana ba su sauki da nishadi matukar gaske.
Sau da yawa magana mai zafi da kaushi mai uzzurawa, da nuna karfi, da sanya tsanani, suka sanya katsewa da yankewar alaka tsakanin masu tarbiyya da yara, kuma samun wannan tazara yakan kai ga nisantar juna tsakanin masu tarbiyya kamar iyaye da yara, wannan lamarin yakan kai ga shedanun mutane su samu dammar ba su wata mummunar tarbiyya.
Musulunci ya ba mu kyakkyawan misali wajen tarbiyya a game da wannan al'amari yayin da ya yi umarni da yin sallama ga yara, don haka yin sallama yana daga cikin mafi kyawun koyarwar addinin musulunci. Sallama tana daya daga cikin nau'in alakar al'umma, kuma aiki da wannan koyarwar ta Kur'ani tana sanya jin dadin rai da samun daukaka.

Habbaka Yanayin Yara
Karbar habbaka da karuwa da ci gaban kamala a dabi'u da halaye yana daga cikin muhimman siffofin da mutum yake da su bisa sauran halittu, kuma wannan ne yake iya ba mu hakikanin mutum, kuma da wannan ne yake samun kammaluwa da daukaka. Bisa hakika, kimar dan'Adam tana karkashin wannan ne, tana karkashin samun canji zuwa ga kamala da samun cika ta yadda za a canja jahilci da ilimi, rauni da karfi, kaskanci da daukaka, yin sabo kuwa da biyayya.
Don haka ne ma mahaliccin mutum wato Ubangiji madaukaki ya sanya dukkan halittu domin kamalar mutum, ya hore duk abin da yake wannan duniya domin amfaninsa, ya sanya masa shiriya ta badini da zahiri, sannan sai ya sanya masa shiriya da daidaito ta hanyar sakon annabawa (a.s).
Kafin aiko annabawa (a.s) Allah madaukaki ya riga ya ba wa mutum shiriya ta badini ta hankali domin ya janye shi zuwa gareshi, shi kuma ya amsa kiran nan na fidirar halittarsa. A takaice dai hadafin yin haka duk yana komawa zuwa ga rabauta da tarbiyyar mutum ne da kuma gaskiya da neman kusanci zuwa ga Allah madaukaki.
Saboda haka ya hau kan iyaye su yi kokarin habaka wannan ajiya da Allah ya sanya cikin yara, su shayar da mahalli kwanciyar yaro a ciki ruwa mai kyau mai tsafta, su nemi habaka halayensu da siffofinsu bayan zuwansu duniya domin kaiwa ga wannan baiwa ta Allah da ajiyarsa cikin manyan gobe, domin kuwa mu ababan tambaya ne game da wadannan yara. Ma'aiki (s.a.w) yana cewa: "Ku tarbiyyantar da 'ya'yanku, domin ku ababan tambaya ne game da su".
Daya daga cikin hanyoyin da zasu kasance masu amfani matuka a kan wannan al'amari ita ce hanyar karfafa gwiwa, da sanya musu burin cimma nasara kan abin da suke yi na alheri. Karfafa gwiwa yana daga mafi muhimmnacin hanyoyin da zasu sanya yaro jin karfi wajen abin da ya sanya gaba, kuma ita hanya ce da take mai dacewa da cin nasara bisa tajriba, kuma idan ta samu sharudda na gari to zata kasance wata hanya ce mai samar da halaye karbabbu nagari ga yara.
Ana iya karfafar gwiwar yara ta hanyoyi masu yawa da wasu daga cikinsu sun hada da: yi masa tafi, ko salati, godiya, girmamawa, ba shi kyauta, kara masa kauna, kusantar da shi, da saya masa wani abu muhimmi a wajensa.

Amsa Wa Yara Tambayoyi
Sau da yawa tambayoyi sukan yi kai-kawo a cikin zukatan samari a lokacin da suke fara girma, don haka yana da kyau iyaye su fuskanci wannan tambayoyi da idanun basira suk yi kokrain amsa musu bisa hankali, domin su kama hannayensu zuwa ga shiriya. Yana da muhimmanci ga iyaye su yi kokarin ganin sun amsa wa 'ya'yansu abubuwan da zasu kai su ga kamalar 'yan'adamtaka kamar ilimi da kyawawan halaye ta hanyar da zata yi tasiri, domin su nuna musu cewa; su ne masu daukar nauyin al'umma a nan gaba, don haka ne dole ne su kasance sun shirya wa daukar wannan nauyin. Da irin wadannan amsoshin za a iya samun digon dan ba na ci gaba mai dorewa da kai wa zuwa ga tarbiyya karbabbiya da zata kai ga gyaran al'umma.

Yada Jin Kunya
Hakki ne mai nauyi a kan iyaye su koyar da 'ya'yansu jin kunya da kamewa, muna iya ganin yadda Ubangiji madaukaki yake cewa da muminai su rintse ganin su … surar nur: 30 - 31. wannan ayar tana koyar da muminai su kawar da kai daga ganin haramun, kuma su kame kai daga sha'awar haramun kuma wannan shi ne ya fiye masu tsarki; Ubangiji yana gaya wa muminai mata a cikin wannan ayar cewa; su kiyaye lullubinsu da adonsu idan dai ban da abin da yake zahirinsu ne kamar fuska da tafukan hannaye, su dora abin lullubin akan wuyan su domin kada a ga kirjinsu da wuyansu, sannan kuma kada su bayyanar da adonsu sai ga mazajensu, ko kuma iyayensu, ko baban mazajensu, ko 'ya'yansu ko 'ya'yan mazajensu, ko 'yan'uwansu, ko 'ya'yan 'yan'uwansu ko 'ya'yan 'yan'uwansu mata, ko kuma mata irinsu, ko bayinsu, ko kuma wawayen da ba su da bukatuwa zuwa ga mata, ko yaran da ba su san wani abu na sha'awa ba.
Kuma kada su rika buga wani abu da kafafunsu wanda zai iya bayyanar da adon kafafunsu ko jawo hankulan maza zuwa garesu. Idan muka duba abin da wannan aya ta kunsa kamar yadda muka kawo wasu daga cikinsu zamu ga yadda Ubangiji madaukaki ya dauki nauyin yin tarbiyya ga muminai domin su kame kai, kunya ta yadu cikin al'umma.
Don haka ya dace ga iyaye su bi koyarwar Ubangiji madaukaki da jagororin addini domin kafuwar tarbiyya ta gari a cikin al'umma, musamman ma darussan da suke kunshe cikin wannan aya mai girma wadanda suke yada kamewa da kunya a cikin al'ummar musulmi.

Koyon Ilimi Da Ladabi
Koyar da ilimi da ladabi da kyawawan halaye ga 'ya'ya yana daga cikin abin da ya hau kan iyaye kuma wannan yana daga cikin mafi muhimmancin ayyukan da suka hau kan su a bisa koyarwar manzon Allah (s.a.w). Imam Ali (a.s) yana cewa: "Hakki ne na da a kan uba ya kyautata sunansa, ya kyautata tarbiyyarsa, ya sanar da shi Kur'ani" .
Haka nan yana fada a cikin wasiyyarsa ga dan sa Imam Hasan (a.s) cewa: "Hakika zuciyar yaro danye kamar kasa ce maras komai, duk abin da aka jefa mata sai ta karba, don haka sai na gaggauta tarbiyyarka kafin zuciyarka ta kekashe, hankalinka kuma ya shagaltu" .


Gaskiya Da Rikon Amana
Koya wa yara gaskiya da rikon amana yana daga cikin ayyukan da suka hau kan iyaye, domin wannan yana daga mafi muhimmancin ayyukan da suka doru a kansu na tarbiyyantarwa tun suna kanana. Don haka ne ya hau kan iyaye su kiyaye wannan al'amari mai muhimmanci domin samar da zuriya da al'umma mai addini mai tsarki, mai tausayi da tunani, mai hangen nesa.
Dukkan al'ummar da ba ta samu irin wannan tarbiyya ba to ma'aikatanta da jagororinta zasu kasance maha'inta, kuma wannan zai sanya ba zasu taba cin nasarar rayuwar duniya ba, domin ci gaba da yalwata da 'yancin al'umma ya doru ne bisa samar da al'umma mai rikon amana da gaskiya.

Koyar Da Kur'ani
Kur'ani zancen Allah ne kuma mabubbugar hikimarsa da iliminsa, kuma ayoyinsa masu girma suna nuna mana girman Ubangiji madaukaki. Kur'ani wata taska ce mai girma da kima maras iyaka ga dukkan musulmi da ma al'ummar duniya baki daya.
Wani abu muhimmi a nan shi ne; Kur'ani wani alkawari ne tsakanin Ubangiji da mutane, don haka ne ya hau kan iyaye su koyar da 'ya'yansu ilimomi masu kima da suke cikin wannan littafi mai girma wadanda suke raya al'umma, ta yadda dukkan ma'anoninsa da abubuwan da ya kunsa a dunkule zasu kasance a cikin kwakwalensu a matsayin wani tunani da sani da ilimi mai daraja .

Soyayyar Alayen Annabi (s.a.w)
Tarbiyyantar da soyayyar Ahlul Baiti (a.s) ga yara yana daga cikin mafi muhimmancin nauyin da ya hau kan iyaye, da akwai hanyoyi masu yawa da na koyar da soyayya ga Ahlul Baiti (a.s) a cikin tarihinsu da koyarwarsu da zantuttukansu da ayyukansu wadanda suke masu yawa a cikin littattafai. Sannan a rika sanya wa 'ya'ya sunayen Ahlul Baiti (a.s) da kai su wajen ziyararsu da majalisosin da ake yin a ranakun haihuwarsu ko shahadarsu, hada da kula da abincin halal ga yaro, da ambaton falalolin Ahlul Baiti da sanar da su matsayinsu (a.s).
Sannan da yin salati yayin samun wani abu na farin ciki ta yadda zamu rika tunasu, da yi musu salati yayin faruwar wani abu domin tunawa da su ya dawwama a kwakwalensu, kuma harsunansu su nuna da ambatonsu, rayuwarsu ta cakuda da tunaninsu.
A wata ruwaya ya zo cewa: "Ku ladabtar da 'ya'yanku a kan abubuwa uku; son annabinku, da son ahlin gidansa, da karanta Kur'ani .
Soyayya da kauna ga Ahlul Baiti (a.s) soyayya ce da kauna ga Allah madaukaki da manzonsa (s.a.w) , kuma damfaruwa ne da abubuwa masu kima na Ubangiji da koyarwar addini mai girma, kuma kaiwa ga mafi daukakar matsayi ne na kamala da cikar mutumtakar dan Adam, kuma idan babu wannan soyayyar to kaiwa ga wannan kamala ba zai yiwu ba har abada, kuma idan babu ita ayyukan da mutum musulmi yake yi na alheri ba zasu karbu ba a wajen mai girma Ubangijin talikai kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyin . Don haka ne ma kusanci zuwa ga Allah madaukaki da isa zuwa ga sa'adar duniya da lahira ba zai yiwu ba sai da soyayya ga Annabi Muhammad da alayen Muhammad (s.a.w) domin soyayyarsu an hada ta tare ne.

Motsa Jiki Da Yawon Shakatawa
Samar da yanayin farin ciki da annashuwa da motsa jiki ga yara da wajen wasanni yana daga abubuwa masu muhimmanci matukar gaske, kuma daya ne daga bukatun yara masu matukar amfani. Don haka ya hau kan iyaye su karfafi ruhi da jikin yara da bayar da muhimmanci kan wannan mas'ala ta motsa jiki, annabin rahama (s.a.w) a cikin maganarsa madaukakiya ya bayar da muhimmanci kan wannan mas'ala ta yara a a cikin abubuwan da ya lissafa da suka hada da; koyar da littafin Allah, da koyar da harbi da iyo a ruwa, da kuma barin gadon dukiya ta halal .
Al'ummar da take mai lafiya mai annashuwa ita ce wacce take da daidaikun mutane da suke da nishadi da karfin himma, kuma ya zo a cikin dabi'un imamai (a.s) game da wasanni da motsa jiki cewa suna daga hanyoyin watayawa da karfafa ruhi da jiki wadanda suke kawo habaka da ci gaba, don haka ne a fili yake cewa; muna iya gani shari'a ba ta gafala daga wannan al'amari mai muhimmanci ba.


Zabar Aiki Mai Dacewa
Rashin aikin yi bayan lalata karfin da Allah ya ba wa samari da yake yi, haka nan yana sanya su jin kaskanci da lalaci, sannan ya mayar da shi cima-zaune dan kashe wando, wannan al'amari ne mai taba tunani da rayuwar samari matuka, sannan kuma wani bala'i ne na al'umma. Muna iya gani sau da yawa wannan yakan kai ga nau'o'in fasadi iri-iri na kyawawan halaye ne ko na zamantakewa.
Saurayi matashi dole ne ya kasance mai sadaukarwa da karfinsa ga al'umma, don haka ne saurayi mai kishin al'umma sai ya yi kokarin zabar aikin da zai yi domin ya bayar da gudummuwa cikin al'ummarsa, kuma ya taimaka wa kansa da danginsa, da al'ummarsa da kasarsa. Kuma iyaye suna da rawar da zasu taka mai girma wajen ganin sun taimaka masa samun aikin da yake na halal a shari'ance.

Taimakawa Don Yin Aure
Aure wani abu ne mai daraja a cikin al'umma wanda musulunci ya shar'anta shi, ya dauke shi a matsayin ibada mai girma, da yin aure ne saurayi zai taka matakin farko na rabuwa da son kansa da komawa zuwa ga son waninsa, domin idan ya yi aure a lokacin ne zai yaye kansa daga son kansa da kebantar komai nasa da kansa domin ya sanya shi a hannun waninsa wanda yake ita ce matarsa. Kuma ta hanyar shiga wannan sabuwar marhalar ne zai cike tawayar da take tattare da shi yayin zaman gwauranci.
Sannan kuma ta hanyar aure ne za a kiyaye samuwar manyan gobe masu albarka, da samun nutsuwar ruhi da zama waje daya, da kammaluwa da kuma biyan bukatun sha'awa ta hanyar halal, da samun lafiya cikakkiya, da amincin al'umma, da kuma biyan bukatun nan da suke damun tunanin rayinsa.
Manzon rahama mai tsira da aminci yana cewa: "Duk wanda ya yi wa 'ya aure, kuma ya aika ta gidan mijinta, to Allah zai sanya masa hular sarauta a kansa ranar kiyama .

Yin Wa'azi D a Shiryarwa
Yin wa'azi da nasiha da shiryarwa suna daga mafi muhimmnacin al'amuran tarbiyya ga yara, kuma iyaye suna da babbar rawar da zasu taka a nan domin shiryar da saurayi ga zabi nagari. Muna iya gani da farko rayuwar samari da 'yan mata cike take da matsalolin rayuwa, kuma akwai masu rashin halaye nagari domin bata su. Don haka ne ya zama wajibi kan iyaye su shiryar da su ga tafarkin kwarai da hanyar shiriya, kuma su yi amfani da tajribar rayuwa da suke da ita domin ganin sun koyar da 'ya'yansu ita.
Su sani da yin nasiha da shiryarwa da gargadi da tsoratarwa ga Allah suna iya sanya 'ya'yansu tashi cikin shiriyar da ake bukata garesu da al'ummarsu.
kuma ta hakan suna iya kautar da 'ya'yansu daga fadawa tafarkin kauce hanya da barna, don haka ne ma Allah ya kawo mana misalin nasiha ta uban nan mai tausayi ga dansa a cikin Kur'ani mai girma a surar nan ta Lukman, kuma ya sanya mana wannan a matsayin kyakkyawan abin koyi ga iyaye da 'ya'yansu .
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012