Iyaye da 'Ya'yansu
  • Take: Iyaye da 'Ya'yansu
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 19:26:50 1-10-1403

HAFIZ MUHAMMAD SA'ID hfazah@yahoo.com
Alakar Iyaye Da 'Ya'yansu
Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) Kuma Aminci ya kara tabbata ga bayinsa wadanda ya zaba
Ubangijinka ya hukunta cewa kada ku yi bauta sai gareshi, kuma ku kyautata wa iyaye…
Ya ku wadanda suka yi imani ku kare kawukanku da iyalenku daga wuta…
Gabatarwar Mai Yadawa
Kuma ka sassauta musu fikafikin rusunawa na rahama, kuma ka ce Ubangiji ka tausaya musu kamar yadda suka rene ni ina karami. Isra': 24.
Iyali su ne mafi muhimmancin abin da yake iya sanya mutum daukaka ko kaskanta, kuma alakar uba da uwa da 'ya'yansu, ko ta 'ya'ya da su iyaye, ita ce take samar da nauyi da ya hau kan kowanne daga cikinsu.
Kuma kai mutum! Shin ka taba jin cewa wani ya kai ga hadafinsa ba tare da neman sanin hanyar zuwa ga hadafin nasa ba? Ko kuwa kauna da samun arzuta ba su kasance fatan kowane iyali ba ne?. To wace hanya ce kuwa ta fi domin sanin koyarwar musulunci da ta kai hanyar sanya himmar neman sanin ilimin addini, da rusunawa da ladabi a bisa koyarwar manzon Allah (s.a.w) da Ahlul-baiti gidan tsarki.
Littafin da yake gabanku kokari ne na ganin an samar da soyayya da kauna tsakanin iyali da mai girma mawallafi Hafiz Muhammad Sa'id ya yi kokarin rubutawa ta hanyar amfani da littattafan musulunci. Bangaren tarjama da yada littattafai na Jami'ar Mustafa ne tare da girmamawa ga kokarin mawallafin ya dauki nauyin gabatar da shi ga masu magana da harshen Hausa.
Gabatarwar Mawallafi
"Ubangijinka ya hukunta cewa kada ku yi bauta sai gareshi, kuma ku kyautata wa iyaye… ". "Ya ku wadanda suka yi imani ku kare kawukanku da iyalenku daga wuta…" .
A cikin dukkan fadin duniya gaba daya akwai bukatar samuwar dokoki domin cigaban samuwar dan Adam wanda yake larura ne ga kamalar dan Adam. Wadannan dokoki suna iya tsara rayuwar mutum ga kansa da kuma a cikin alakokinsa da sauran 'yan Adam. Amma sanannan abu ne cewa mafi kusancin alakoki da tasiri su ne wadanda suke tsakanin gida daya suke tsara tsakanin iyali. Kuma mafi girma ita ce wacce take tsakanin uwaye da 'ya'yansu, don haka ne ma a cikin wannan rubutu takaitacce zamu kawo wasu bayanai game da hakan.
Kuma tabbas idan aka samu kiyaye wannan alaka mai girma to za a samu kamala da gina iyali na gari, kuma daga karshe duniya ke nan wacce daga daidaikun gidaje take haduwa zata kasance cikin kamala da rabauta.
Bayan cewa; kiyaye hakkokin da suke tsakanin iyaye da mahaifa wani umarni ne na Allah da ya saukar da shi a littafin Kur'ani mai girma, haka nan kuma wasu dokoki ne da zasu tsara wa duniya hanyar kai wa ga kamalarta, domin idan aka kiyaye wannan alaka mai girma, to za a sami al'umma mai ci gaba ta kowane janibi. Kuma tarihin wannan alaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu yana koma wa ne zuwa ga farkon samuwar dan Adam, kuma abu ne na nau'in halittar dan Adam na son kyautata wa mai ni'ima da kuma son na jikinsa.
Idan ba a samu kiyaye wannan alakoki ba, to maimakon samun al'umma saliha sai a samu al'umma asharariya da zata kama hanyar rushewa warwas.
A cikin al'adun musulunci an yi umarni da kiyaye wannan alaka umarni mai tsanani bayan kare hakkin Allah madaukaki, kuma ayoyi da yawa da ruwayoyi sun yi nuni da wajebcin kiyaye wannan alakoki. Idan an samu iyaye da suka tarbiyyatar da 'ya'yansu tarbiyya sahihiya to lallai wadannan 'ya'ya zasu kai ga daraja ta kamala mafi kololuwa, kuma zasu samu kaiwa ga kamalar da ake bukata ga dan Adam.
Kuma tabbas irin wadannan 'ya'ya su ne kawai suke iya kiyaye hakkokin iyayensu da na al'ummarsu da suka hau kansu, kuma su ne wadanda idan suka riki kasa zasu tsayar da kyawawan dabi'u da gyara da kawar da barna daga kasarsu. Idan kuwa iyaye ba su tarbiyyantar da 'ya'yansu ba to duk wani abu da ya haifu daga garesu na daga barna a bayan kasa ba zai taba zamantowa abin mamaki ba.
Iyaye su sani 'ya'ya amana ce a hannunsu da Allah ya damka musu ita, idan ba su kiyaye wannan amanar ba, to su sani sun kauce wa hanya madaidaiciya. A cikin wannan bahasi namu zamu fara da binciken hakkokin yara akan iyayensu, sannan sai mu shiga na iyaye kan 'ya'yansu, domin idan aka fara samun kamalar kiyaye hakkoki ta janibin iyaye, to yana da sauki a samu kiyaye na iyaye a gun 'ya'yansu.
Bahman 1386 - February 2008 - Safar 1429
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com

Alakar Iyaye Da 'Ya'yansu
Abisa dabi'ar mutum yana da son kamala wacce take kunshe a cikin ransa, kuma wannan kamalar tana bukatar samar da wasu dokoki da ka'idojin da zasu daidaita da tsara wa dan Adam motsinsa da ayyukansa na kashin kansa da na daidaiku da na jama'a da alakokin da yake tsakaninsu gaba daya cikin jimilla domin kaiwa gareta, kuma kamar yadda muka sani babu wata alaka da tafi kusa da ta mahaifa da 'ya'yansu, don haka ne ma muka ga ya dace mu kawo wannan al'amari da wani bayani takaitacce domin amfanar da al'umma, da tunatar da ita, da nuna mata hanyar da ya dace wajen yin alaka da manyan gobe, da kuma yadda ya kamata a girmama 'yan jiya.
Mun riga mun yi nuni da cewa alakar 'yan Adam musamman ta 'ya'ya da mahaifansu wata aba ce da ta faru tun farkon samuwar dan Adam, kuma wannan ba yana nuna komai ba ne sai abin da yake kunshe cikin nau'in halittar bil-adama.
A addinin musulmi madaukaki mai daraja an yi nuni da wannan al'amari muhimmi da aka gwama shi da biyayya ga Allah madaukaki, kuma aka yi gargadi mai tsanani da nuni da wajebcin kare kai daga wuta, da tsamar da iyalai daga fadawa cikin fushin azabar Allah, kuma sanannen abu ne cewa; babu wani da ya fi kusanci da hakki mai nauyi a cikin iyali fiye da 'ya'ya, kuma yin tarbiyya garesu yana iya kai duniyar dan Adam ga gaci da mafita daga dukkan bala'o'in da musibun da ta fada, musamman a wannan zamani da ake bukatar gyara dan Adam da tsamar da shi daga halaye na dabbanci da fifita kayan alatu da tarkacen duniya a kan mutumtaka da halaye kyawawa.
Kuma lallai mun sani a fili yake cewa; babu wani wanda zai iya yin wannan aiki koda kuwa hukuma ce mai karfin gaske in ban da iyaye da suke sane da sirrin 'ya'yansu, don haka ne abin kaddarawa shi ne; cewar iyayensu sun tarbiyyatar da su domin su shayar da na bayansu wannan tarbiyyar.
Kuma lallai wannan nauyi ne kuma aiki ne mai nauyi da Allah madaukaki ya dora shi a kan iyaye ba abu ne na ganin dama ba, kuma idan suka kiyaye wannan to lallai zasu fitar da sakamako mai kyau ga al'ummarsu da zata ci gaba har kiyama ta tashi tana tunawa da su tana yi musu addu'a. Tunda iyaye ne suke farawa, sannan 'ya'ya bayan sun girma su kiyaye nasu janibin nauyin da ya hau kansu, to ya kamata mu fara da batun hakkokin da suka hau kansu sannan sai mu gangara zuwa ga na 'ya'yansu.

Bayanin Wannan Mas'alar
Mas'alar bayani game da Alakar Iyaye Da 'Ya'yansu tana iya tasowa sakamakon wasu tambayoyi da zamu iya tambayar kawukanmu kamar haka; shin kamar yadda hakkokin 'ya'ya suke kan iyaye, su ma iyaye suna da irin wannan ko kuwa? Idan haka ne yaya suke? Kuma me shari'a ta ce game da wannan? Kuma suna daidaita ne a yanayinsu da adadinsu ko kuwa?
Wannan mas'ala ta Alakar Iyaye Da 'Ya'yansu al'amari ne mai girma fiye da yadda muke tsammani , kuma Kur'ani ya yi nuni da hakan da ya kawo ta bayan nuna tauhidin Allah madaukaki, don haka ne ma wannan yake karfafa muhimmancin wannan mas'alar.
Kuma muna iya da'awar cewa; gyara duniyar dan Adam yana kunshe cikin sanin ayyukanmu da kuma aikata su, kuma ba yadda za a samu wannan sai idan an samu al'umma mai tarbiyya mai sanin abin da ya hau kanta da ya kamata da girmama juna, kuma wannan aiki ne da ya hau kan iyaye a matakin farko tun kafin makaranta.

Muhimmancin Wannan Al'amari
Daga irin abin da muka nuna zata bayyana cewa kamalar cigaban dan Adam yana karkashin biyayya ga imani da aiki na gari ne, don haka sau da yawa a ayoyin Kur'ani mai girma zamu ga an zo da yabon masu imani da aiki nagari , kuma wannan ba komai ba ne sai nuni zuwa ga muhimmancin aiki . Kuma idan mun duba zamu ga wasu wurare da suka zo suna yabon ladan masu aiki. Kamar dai yadda zamu ga cewa shari'a ta gwama imani da aiki a wurare masu yawa.

Tarihin Wannan Mas'alar
Wannan mas'alar bayanin alakar mahaifa da 'ya'yansu tana daga cikin bahasi da ya dade a tarihin dan Adam, kuma marubuta sun yi rubutu da dama a kansa, kuma muna iya cewa lamari ne da tun farkon haihuwar dan farko na Annabi Adam (a.s) wannan lamari ya faru kai tsaye, kuma wannan mas'ala tarihin musulunci ya yi bayaninta yayin da Kabila ya fandare ya zamanto da na farko da ya saba wa ubansa saboda hassada ya kashe dan'uwansa Habila. Sai wannan ya kasance farkon sabon da dan Adam ya yi a duniya ya kauce wa biyayya ga iyayensa a matsayin umarni daga Allah da ya zo masa ta hanyar mahaifinsa .
Wato; a takaice dai; sai ya ki kiyaye hakkin iyaye, kuma tun wannan lokaci har zuwa yau din nan wannan mas'ala ba ta gushe ba tana gudana a kan dukkan bil-adama. Kuma har zuwa yau an rubuta littattafai masu yawa kan wannan al'amarin, kuma ya kasance maudu'i ne da ya jawo hankalin marubuta da malaman tarbiyya a dukkan fadin duniya gaba daya.

Makullan Asasin Bahasi
A wannan bangaren zamu kawo wasu ma'anoni na wasu kalmomi da suke asasin wannan bahasi namu; kamar: nauyi, juna, iyaye, 'ya'ya, a takaice.
Hakki ko Nauyi: Shi ne abin da ya hau kan mutum ya gudanar da shi . Jam'insa shi ne hakkoki, kuma shi ne hidimar da ta hau kan mutum ya gabatar da ita .
Juna: Abin da muke nufi da shi a nan shi ne abin da yake daurantar kowanne daga abubuwa biyu, wato alakar da take tsakanin juna a nan wato kamar yadda akwai hakki a kan iyaye, haka ma akwai shi a kan 'ya'ya .
Iyaye: Su ne uwa da uba, wadanda suka haifi mutum, suka zama sanadiyyar zuwansa wannan duniyar .
'Ya'ya: Wanda aka haifa namiji ne ko mace .
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012