Sirrin Azumi
  • Take: Sirrin Azumi
  • marubucin: Muhammad Sulaiman
  • Source: jaridar al-mizan
  • Ranar Saki: 7:18:15 2-10-1403

Asrar da ibadodi na watannin Rajab, Sha'aban da Ramadan
Daga Muhammad Sulaiman

Watannin Rajab, Sha'aban da kuma Ramadan, watanni ne masu gayar falaloli da kuma Asrar. Domin a dukkan watanni 12 na Musulunci, babu watannin da suke da ayyuka na ibadodi kamar su. Shi ya sa bayin Allah (T) suke farin ciki da shaukin zuwansu. Haka nan kuma suke bakin ciki, da ma kuka idan sun zo karshe. Wato saboda yankewar da za su samu na falaloli da darajoji da zaukiyyat da halawat da kuma ma'anawiyyat na ibadodin da ake samu a cikin watannin, wanda babu irin haka a sauran watannin.

Saboda ma muhimmancin wadannan watannin, za mu ga wasu daga cikin Malaman Madrasah din Ahlul Bayt, sun yi littafai khususan a kan su. Misali littafin Fadha'ilul Ash-huris-salasa na Shaikh Saduk. Saboda haka a nan insha Allah, rubutun zai gudana ne a kan wadannan ababe. Sune:

1- Asrar na wadannan watanni.

2- Falalolin wadannan watanni.

3- Ibadodin wadannan watanni.

4- Munasabobin wadannan watanni.

5- Tsokaci kan kiyaye muhimman lokuta.

1- ASRAR NA WADANNAN WATANNI: Idan mutum ya yi binciken ruwayoyi na hadisai daban-daban da suka zo dangane da falaloli da darajoji na watannin Rajab, Sha'aban da kuma Ramadan, da kuma shaidar da za su yi wa mutumin da ya girmama su a wannan gida na duniya; wannan kawai ya isa ya nuna ma mutum cewa lalle wadannan watannin suna da wani Asrar gaibiyya a wajen Allah Ta'ala. Misali wannan Hadisi wanda aka samo daga Manzon Allah (S) ya ce, "Duk wanda ya san daraja da matsayin watannin Rajab, Sha'aban da kuma watan Ramadan, to wadannan watanni za su yi masa shaida ranar kiyama cewa ya darajta su da kuma girmama su. Sai mai kira ya yi kira, ya Rajab,ya Sha'aban, ya watan Ramadan! Yaya wannan bawa ya yi aiki a cikin ku, ya kuma da'arsa take ga Ubangiji? Sai Rajab, Sha'aban da kuma watan Ramadan, su ce ya Ubangijinmu a cikin mu bai yi wani abu ba face neman yi maka da'a da kuma neman falalarka. Kuma ya yi iya kokarinsa wajen neman yardarka da kuma neman son ka.

Sai Allah Ta'ala ya ce ma Mala'ikun da ya wakilta ga wadannan watanni: Me za ku ce dangane da wannan shaida da suka yi ga wannan bawa? Sai su ce ya Ubangijinmu! Rajab da Sha'aban da watan Ramadan sun yi gaskiya! Wannan bawa ya kasance a wadannan watanni yana mai yin kokari wajen neman yardarka da kuma yi maka da'a. Kuma ya kasance yana mai farin ciki da murna ga wadannan watannin, yana fatan rahamarka da kuma kaunar afuwarka da gafararka…" Hadisin na da tsawo. Ga mai bukatar ganin Hadisin yana iya duba Biharul Anwar juz'i na 94 ko littafin Zadul Ma'ad. Dukkan littafan biyu da aka ambata na Allama Majlisi ne.

Dawowa ga cikon wancan hadisin, daga karshe Mala'ikun za su ce, madalla da wannan bawa. A lokacin sai Allah Ta'ala ya ba da umurnin a kai wannan bawa Aljanna. Wato saboda girmamawarsa ga wadannan watanni da kuma tsayuwa da ibadodi da kuma ayyukan da'a da ya yi a cikin su. Saboda haka wannan shaida da wadannan watanni za su yi wa bawa, koma bayan sauran watanni, ya nuna lalle suna da wani Asrar na musamman a wajen Allah (T).

Haka kuma daga cikin abubuwan da suke nuna Asrar na wadannan watanni, misali ruwayoyin addu'oi na bankwana da watan Ramadan. Domin idan mutum ya bincika, zai ga cewa a duk watanni 12 na Musulunci, babu wani wata da aka samu ruwayoyi daga Manzon Allah (S) da kuma A'imma (AS) na bankwana da shi da kuma umurnin yin haka face watan Ramadan. Idan mutum ya biya addu'o'i na bankwanan, misali wadda aka ruwaito daga Imam Zainul Abidin (AS), kuma lokacin da yake biyawa a ce zuciyarsa na halarce, tabbas zai samu tasirin haka a ruhinsa. Domin zai ga yadda Imam Zainul Abidin (AS) yake magana da sallama da bankwana da watan Ramadan da kuma jin zafin rabuwa da shi, kamar ka ce mutum ne yake gabansa yake bankwana da shi, da kuma nuna damuwa na rabuwa da shi.

2- FALALOLIN WADANNAN WATANNIN: Idan mutum ya dauki wadannan watanni daya bayan daya zai ga kowane daya daga ciki, akwai falalolin da suka zo dangane da shi.

A- Watan Rajab yana daya daga cikin watanni guda hudu masu alfarma. Kuma Allah Ta'ala ya hana zaluntar kai a cikinsu. Ya zo a kan cewa hatta lokacin jahiliyya sun kasance suna girmama watan, kuma wata ne na Allah Ta'ala. Sha'ban kuma watan Manzon Allah (S), watan Ramadan kuma watan Al'ummarsa.

Ga wasu Hadisai daga cikin falalar watan Rajab. An samo daga Imam Kazim (AS) ya ce, "Rajab wani kogi ne a cikin Aljanna. Farinsa ya fi nono, zakinsa kuma ya fi zuma. Duk wanda ya azumci rana guda daga cikin sa, to Allah Ta'ala zai shayar da shi daga wannan kogi."

Haka nan a wani Hadisi da aka samo daga Manzon Allah (S) ya ce, "Duk wanda ya azumci rana guda a cikin watan Rajab, to zai samu yardar Allah (T) da kuma nisanta daga fushinsa, kuma za a rufe masa kofa daga cikin kofofin wuta".

Wani hadisi har wala yau daga Imam Kazim (AS) ya ce, "Wanda ya azumci rana guda a cikin watan Rajab, to za a nisanta shi daga wuta kimanin tafiyar shekara guda. Wanda ko ya azumce shi kwana 3, to za a sanya shi a Aljanna". Wata rana wani tsoho ya zo wajen Manzon Allah (S) ya ce masa: Ya Manzon Allah, lalle ba ni da karfin azumtar dukkannin kwanukan Rajab. Sai Manzon Allah ya ce masa; ka azumci farkon watan, tsakiyarsa da kuma karshensa; to za a ba ka lada kamar wanda ya azumci dukkan watan.

Haka nan a wani Hadisi da aka samo daga Imam Sadik (AS) ya ce: Ranar Alkiyama mai kira zai yi kira a karkashin Al-arshi, ina Rajabawa? Sai wadansu mutane su tashi, fuskokinsu suna haske da kuma haskakawa. A kawukansu akwai kambi na mulki, wanda aka yi masa ado da lu'ulu'u da yakuti, kuma kowanne daga cikin wadannan Rajabawa akwai Mala'ika dubu a gefensa na dama da kuma dubu a gefensa na hagu. Mala'ikun suna ce masa, farin ciki ya tabbata gare ka, ya kai wannan bawan Allah. Sai kira ya zo daga wajen Allah ya ce: "Bayina na rantse da buwayata zan girmama makomarku, kuma zan nunnunka sakamakonku. Kun yi azumi saboda ni a cikin watan da na girmama darajarsa." Sai Allah ya ce, "Mala'ikuna ku shigar da bayina Aljanna." Da dai sauran hadisai masu yawa da suka zo dangane da falalar watan Rajab.

B- Falalar watan Sha'aban: Manzon Allah (S) ya kasance yana cewa Sha'aban wata na ne,duk wanda ya azumci yini daga cikin watan to Aljanna ta wajaba gareshi.An ruwaito daga Imam Sadik (AS) ya ce Imam Sajjad (AS) ya kasance idan watan sha'aban ya kama yakan tara sahabbansa ya ce: "Ya sahabbai na ko kun san wannan watan Sha'aban ne?" Manzon Allah ya kasance yana cewa, "Sha'aban watana ne, saboda haka ku azumci wannan watan, saboda so ga Annabinku da kuma kusanci ga Ubangijinku."

A wani hadisin kuma, "Ina rantsuwa da wanda raina yake hannunsa, hakika na ji Babana Husain yana cewa, ya ji daga BabansaAmirul Muminin yana cewa, duk wanda ya azumci Sha'aban, saboda so ga Manzon Allah da kuma neman kusanci zuwa ga Allah Madaukaki, to Allah zai so shi, kuma zai kusantar da shi zuwa ga darajojinsa. Ranar alkiyama kuma zai wajabtar da Aljanna gare shi."

Haka nan an ruwaito daga Safwan Jammal ya ce, Imam Sadik ya ce mana: "Ku kwadaitar da wadanda suke kusa da ku dangane da azumin Sha'aban." Sai na ce masa, in zamo fansa gare ka, akwai wani abu ne a kan haka? Sai Imam Sadik (AS) ya ce: Lalle Manzon Allah ya kasance idan ya ga watan Sha'aban, yakan sa mai kira ya yi kira a cikin Madina ya ce: Ya ku mutanen Madina! Ni dan sakon Manzon Allah ne zuwa gare ku. Ya ce, Sha'aban watana ne, Allah ya yi rahama ga wanda ya taimake ni a watana. Sai Imam Sadik ya ci gaba da ce masa; Lalle Amirul Muminin ya kasance yana cewa: Azumin Sha'aban bai taba kubuce min ba tun lokacin da na ji mai kiran Manzon Allah yana kira a watan Sha'aban. Kuma in Allah ya yarda azumin Sha'aban ba zai taba kubuce min ba matukar ina da rai." Wannan kenan a takaice dangane da falalar watan Sha'aban.

C - Watan Ramadan: Wata ne wanda yake da falaloli da darajoji fiye da sauran watanni, kamar yadda ya zo a ruwayoyi na Hadisai. Wata ne wanda a cikinsa Allah Ta'ala yake 'yanta bayinsa daga wuta, fiye da yadda yake 'yantawa a sauran watanni. Wata ne wanda Allah Ta'ala kan nunnuka ayyukan bayinsa a ciki. Wata ne, wanda a cikin sa ake bude kofofin rahama, kofofin Aljanna, ake kuma kulle kofofin wuta. Wata ne, wanda a cikinsa ake daure Shaidanu. Wata ne wanda a cikinsa Allah Ta'ala ke gafarta ma bayinsa zunubbansu baki daya. Wata ne wanda a cikinsa yake daukaka darajojin bayinsa. Wata ne wanda a cikinsa akwai wani dare wanda ibada a cikinsa, ta fi ibadar wata dubu, wato daren Lailatul kadri. Wata ne wanda a cikinsa Allah Ta'ala yake tsarkake bayinsa, ya kusanta su gare shi. Wata ne na samun Takawa fiye da sauran watanni. A takaice dai wata ne wanda yake cike da tarin alkhairai da kuma albarkoki wadanda ba za a iya lissafa su ba. Kuma watan Ramadan shi ne Shugaban watanni.

3- IBADODIN WADANNAN WATANNI: Kamar yadda aka ambata a baya, wadannan watanni uku, suna da ayyuka na ibadodi masu yawa fiye da sauran watanni. Ayyukan ibadodi da ake aikatawa cikin watannin sun kasu kashi biyu. Akwai ayyukan ibadodi na 'Amma' da kuma 'khassa.' Ibododi na 'Amma' cikin watannin sune wadanda mutum zai kwashe watanni uku yana aikatawa. Misali sallolin nafila na kowane dare. Idan mutum ya duba littafin Dhiya'us Salihin ko Baladul Amin ko littafin Ikbal, sun kawo wadannan salloli, wanda mutum zai soma tun daga daren farko na watan Rajab har ya zuwa daren karshe na watan Ramadan. Yana da muhimmanci mutum ya yi iyaka iyawarsa ya ga cewa wadannan salloli na watannin uku bai rasa ko daya daga ciki ba.

Daga cikin Ayyukan da ake aikatawa a wadannan watannin baki daya, akwai wasu surori na Alkur'ani da Azkar da ake son biyawa kowace rana. Mai son ganin wadannan surori da Azkar yana iya duba littafin Mafatihul Jinan, Babi na biyu, a ayyuka na 20 na kismil Awwal na ayyukan wata Rajab.

Haka nan akwai wasu salloli da ake son yi a dararen 13,14,15 na wadannan watanni guda uku, mutum na iya duba kismus sani na ayyukan watan Rajab, a ayyukan daren 13. Za a ga yadda sallar take da kuma abin da ake biyawa.

Sai kuma ayyukan ibadodi na 'khassa', sune ibadodin da ake son yi a muhimman kwanuka a cikin wadannan watanni uku. Misali daren farko da ranar farko na watan Rajab, ko 13,14,15,27 dinsa. Ko kuma misali a watan Sha'aban shi ma daren farko da ranar farko, ko daren 15 dinsa. Misali kuma na watan Ramadan daren farkonsa da kuma ranar farkon sa, ko 13,14,15, ko kuma daren 19, 21 da 23.Wadannan sune misalan wasu daga cikin ayyukan ibadodi 'khassa' na watanni ukun. Kuma ana son mutum ya tsayu da wadannan ibadodi na 'Amma' da kuma 'khassa', wato wadanda ake yi kullum a cikin watannin da kuma wadanda ake yi a muhimman kwanuka na watannin.

4- MUNASABOBIN WADANNAN WATANNIN: Wato muhimman ababen da suka auku na tarihi a cikin watannin, ko kuma haihuwa ko rasuwa na daya daga cikin A'imma na Ahlul Bayt (AS) da dai sauransu.

1-Munasabobin watan Rajab:1 ga watan Rajab, haihuwar Imam Bakir (AS). 3 ga watan Rajab, shahadar Imam Ali al-Hadi (AS). 10 ga watan Rajab, haihuwar Imam Jawad (AS). 13 ga watan Rajab, haihuwar Imam Ali (AS). 15 ga watan Rajab, wafatin Sayyida Zainab (AS). 25 ga watan Rajab shahadar Imam Musa al-Kazim (AS). 26 ga watan Rajab, wafatin Sayyidina Abu Talib (AS). 27 ga watan Rajab Ranar Mab'as, wato ranar da aka aiko ma Manzon Allah (S) da sako. 29 ga watan Rajab, wafatin Ummul Muminin Khadija.

Sai kuma munasabobin watan Sha'aban: 3 ga watan Sha'aban, haihuwar Imam Husain (AS). 4 ga watan Sha'aban, haihuwar Sayyid Abul-Fadhal Abbas (AS). 5 ga watan Sha'aban, haihuwar Imam Zainul Abidin (AS). 15 ga watan Sha'aban, haihuwar Imam Mahdi (AF).

Sai kuma munasabobin watan Ramadan: 15 ga watan Ramadan, haihuwar Imam Hasan (AS). 17 ga watan Ramadan, yakin Badar ya kasance. 21 ga watan Ramadan, shahadar Imam Ali (AS) . Wadannan sune wasu daga cikin muhimmman munasabobin wadannan watanni. Sai dai wani tambihi a nan shi ne, ana iya samun sabani na ruwayoyi a irin wadannan kwanuka na wilada ko wafatin daya daga cikin Ma'asumin (AS). Wadanda aka kawo a nan, wadanda suka fi shahara ne a tsakanin Malaman Tarihi.

5- TSOKACI KAN KIYAYE MUHIMMAN LOKUTA: Yana da gayar muhimmanci mutum ya kasance yana kiyaye muhimman lokuttan wadannan watanni 12 na Musulunci. Saboda wadansu lokuta akwai ayyuka na ibadodi da ake son aikatawa a cikin su, idan mutum ba yana kiyayewa ba, sai irin wadannan ayyuka su dinga kubuce ma mutum, ko kuma ya dinga abin da ake ce ma fargad daji. Wato bayan ranar ko daren da ake son aikata wani aiki na ibada, sai mutum ya ji, alhali kuma ga lokacin ya wuce. Sai mutum ya kasance ya yi hasarar ladar aikata ayyukan. Ko kuma wata munasaba ta gitto na wilada ko wafatin daya daga cikin A'imma na Ahlul Bayt (AS), in mutum bai kiyayewa, sai ta gitto, ta wuce, mutum bai sani ba, ga shi ko ya zo daga Imam Sadik (AS) ya ce, "Masoyanmu sune wadanda suke murna da murnarmu, suke kuma bakin ciki da bakin cikinmu." Kuma kiyaye wadannan munasabobi yana daga cikin hanyoyin kyautata alakar mutum da Manzon Allah (S) da kuma Ahlul Bayt (AS).

 

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua