Hakkin Matar Aure
  • Take: Hakkin Matar Aure
  • marubucin: Imam Aliyyu Assajjad a.s
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:41:47 10-10-1403


Hakkin Matar Aure
Imam Aliyyu Zainul-abidin dan imam Husain (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin mata shi ne ka san cewa Allah madaukaki ya sanya ta mazauni da wurin nutsuwa gareka, kuma ka san cewa wannan ni'ima ce daga Allah madaukaki gareka, sai ka girmama ta, ka tausaya mata, duk da kuwa hakkinka a kanta ya fi karfi, amma tana da hakki a kanka na ka tausaya mata domin ita ribacewarka ce, kuma ka ciyar da ita, ka tufatar da ita, sannan idan ta yi rashin sani da wauta sai ka yafe mata" .
Mace wata ni'ima ce mafi girma a cikin halittun Allah masu daukaka da babu kamarta, don haka sai Imam Ali (a.s) ya yi mana wasiyya da kiyaye ta, da yafe wa kuskurenta, da fita domin nemo mata abin da zata ci, tamkar dai ita wata sarauniya ce, shi kuma namiji mai yi mata hidima ne.
Don haka idan za a yi aure, to tun farko sai a duba wane mutum ne za a ba wa 'ya, a daya bangaren kuma shi ma namiji a sanar da shi wace yarinya ce za a ba shi. Sau da yawa na ga wanda ya yi aure amma yana kukan cewa ba a gaya masa wani ciwo da ita yarinyar take da shi ba.
Don haka idan ana son gina gida ba na toka ba, gida mai kwari wanda za a samu yarda da juna, da kaunar juna, da taimakon juna, tun farkon haduwa har zuwa kulla aure kada a boye wa juna matsalolin juna, da tunanin juna, da ma akidar juna, domin boye-boye ba ya kaiwa ga komai sai rusa zaman tare.
Mace taushi da kanshi ce kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi, kuma mata suna daga cikin abubuwa uku da aka sanya sonsu a zuciyar ma'aikin Allah (s.a.w), don haka son mata ba aibi ba ne, sai dai son da Manzon Allah (s.a.w) yake masu so ne na tajallin jamalul-Lah ne garesu, ba so na sha'awa ba.
Don haka so da sha'awa ga mata ta hanyar kallon janibi daya na halittarsu shi ne aibi, domin wannan yana komawa zuwa ga bukatun jiki ne tsantsa da dulmuya cikin kogin sh'awar rai, amma son su don kasancewarsu halarar adon Allah (jamalulla-Lah), kamar yadda namiji yake tajallin jalalulla-Lah ne wannan duk ba aibi ba ne.
Imam Ali (a.s) yana cewa: Babu wani abu da zan gani sai na ga Allah a cikinsa da wajensa, da samansa da kasansa . Ganin wasiyyin Manzon Allah (s.a.w) gani ne da ya hada da ganin zuci wanda ya kunshi so, da kaunar abu, ko saninsa, ko tunani game da shi, bai takaita da gani na zahiri ba!.
Don haka idan mace ta yi laifi sai a yafe mata, sai a tausasa mata, a tausaya mata, sai wannan ya sanya ta koma wa zuwa ga ma'arufi, amma tankwara ta da karfi, da takurawa, ba ya kai komai sai ga fandarewa, sai dai wasu lokuta ayyanannu da yanayi yake kawowa.
Sau da yawa wani lokaci laifin da mace take yi yana bukatar magani ne, kamar misalin wanda matarsa take kin sa a shimfida, sau da yawa wani lokacin yana bukatar koma wa likita ne ba duka da takurawa da musgunawa ba.
Yawan takura mata a duniya ya jawo bahasin 'yancin mace, sai dai daga bangaren biyu duka suna kuskure, da masu kare hakkin mace, da masu kushe da kin yarda da bahasin hakkin mace duka suna kuskure ne. Domin musulunci ya zo da Fomular "Kallon mutuntaka ga jinsi ba kallon jinsi ga mutum ba".
Wannan nazari na musulunci shi ne kawai mafita, don haka yabo da sukan "feminism" duka kuskure ne, domin asalin maudu'in ya taso ne daga masu kallon cewa akwai bambanci tsakanin mace da namiji.
Kamar dai yadda wasu suke rikici kan liberal ne daidai ko communism a tsarin siyasa ko tattalin arziki alhalin duk biyu suna nuni zuwa ga kallon mutum ta fuskacin tattalin arziki, ba kamar yadda Allah ko musulunci yake ganin sa ta fuskacin dan'adamtaka ba.
Musulunci yana kallon mace a matsayin mutum ne, kamar yadda yake kallon namiji a matsayin mutum, bai ce mace daban namiji daban ba a matsayin halittu biyu; ya zo ne da hukunce-hukunce garesu iri daya, sai dai ya bambanta su a hukunce-hukunce a wurin da suka saba, domin kowannensu ya kasance ya samu nasa hakkin daidai yadda ya dace da rauninsa ko karfinsa. Sai mace ta zama sarauniya mai aiki da halitta da dabi'un zuciyarta domin gyara al'umma, sai namiji ya zama bawa amma shugaba domin jagoran mutane shi ne hadiminsu kamar yadda ya zo a hadisi, don haka sai ya sanya ci gaban gida da al'umma da hankalinsa, kamar yadda mace zata sanya ci gaban gida da al'umma da dabi'un zuciyarta.
Kawai da kai ga barin duk maganar wani mai magana ta jahilci ko da kuwa ya sanya rawani yana magana da sunan musulunci. Musulunci bai bar wani abu ba sai da ya yi bayaninsa dalla-dalla, don haka mai magana game da sukan mace ba kowa ba ne sai jahili bayyananne. Akwai hadisai da yawa masu tawili da sai an hada wasu ake gane su, a zahirinsu kamar suka ne amma badininsu yabo ne.
Kamar hadisin nan da yake cewa: Imam Ali (a.s) ya ce: "Mace sharri ce dukkanta, sharrin da yake cikinta shi ne babu makawa daga gareta!" .
Mai daraja Allah ya kara jan zamaninsa Ayatul-Lahi Jawadi Amuli, (Allah ya ba mu ikon yi masa hidima) yana fassara hadisin nan da ya yi magana kan cewa: "Hankulan mata suna cikin kyawunsu, amma kyawun maza suna cikin hankulansu", da wasu suka dauka aibi ne ko tawaya ga mace, amma sai ga shi ya kawo bayanai kusan shafi 300 kan wannan hadisi da idan Allah ya tsawaita rayuwarmu zamu so kawo wa mai karatu shi cikin harshen Hausa.
Hadisin ba ya yabon namiji ko sukan mace, kamar yadda ba zai yiwu a juya shi ba a ce yana yabon mace yana sukan namiji. Sai dai yana nuna nau'in ayyuka da fagen da kowanne ya kware ne.
Tajallin Allah a cikin halittunsa wani lokaci yana kasancewa ta fuskacin hankula, wani lokaci kuma ta fuskacin kyawu, don haka babu wani martaba sai ta kasance mai komawa zuwa ga ubangijin bayi. Babu ma'ana wancan tajallin ya kasance an kaskantar da shi domin yana da wani kyawu da siffofi da sukan kai ga wani hadafin da Allah yake son tabbatarsa a duniya halittu!.
Wannan hadisin ba yana kasa mutane gida biyu ba ne, sai dai yana nuni da siffar nau'in ayyukan da kowanne ya kware kansa ne, don haka yabo ne ba suka ba!. Domin namiji yana iya tsayar da ayyukansa bisa gini da hankali ba don ya rasa janibin kyawu da kayatarwa ba, kamar yadda mace take iya kyautata ayyukanta da kyawu da kayatarwa ba don ta rasa janibin hankali ba, domin da mai yin amfani da kayatarwa da mai amfani da hankali duk suna amfani da biyun ne yayin ayyukansu.
Kamar dai fadin Allah ne cewa: "Maza su ne masu tsayuwa da al'amuran mata…", ba don mace ita ma ba ta tsayuwa da al'amuran namiji ba!, don haka nassin shari'a yana bukatar zurfafawa domin saninsa.
Musulunci ya fadi hakan, amma sai ya sanya nauyin kofar gida zuwa waje a hannun namiji, ya sanya nauyin kofar gida zuwa cikin a hannun mace, sai ya kasance idan gida ya gyaru, to mace ce ta gyara shi, idan ya bace to ita ta bata shi, wane karfi ne ya fi wannan ku gaya mini!.
Wannan kuwa ba don komai ba sai domin cikin gida yana bukatar kayatarwa da sanya tausasawar zuciya da tausayawa domin ya daidaitu, kamar yadda waje take bukatar kutsawa fagen dagar neman abin rayuwa domin cikin gida ya daidaitu.
Bai kamata ba dan kayi-nayi ya shiga hawa kan doron Kur'ani don kawai ya san kalmomin larabci, domin Kur'ani yana da zurfafan ma'anoni da yake bukatar makoma don yaye su.
Mu sani maganar Annabi Ibrahim (a.s) da mala'iku ba ta sanya ba shi dansa Ishaka (a.s) ba, amma dariyar matarsa kawai ta sanya mala'iku sun yi mata albishir da dansa Ishaka, domin Jamalul-Lah da yake tattare da wannan dariya ta Sara (s), sai wannan ya nuna mana kowane halitta mace da namiji yana da nasa fagen kwarewa.
A cikin wannan hadisi akwai bayani da yake nuna mana muhimmancin mace a matsayinta na cibiyar da nan ne madogara kuma matattarar samar da iyali da hada alakoki tsakanin iyalai da gidaje da garuwa da kasashe mabambanta. Da bayanai masu yawa da wannan mahallin ba zai iya dauke su ba!.
A cikin littafin Saduk ya zo cewa: Zurara ya tambayi Imam Sadik (a.s) cewa: Wasu mutane suna cewa an halicci Hawwa daga kashin kirjin Annabi adam (a.s) na hagu. Sai ya ce: Tsarkin Allah ya tabbata kuma ya barranta daga hakan, shin wanda yake fadin hakan yana ganin cewa Allah ba shi da ikon ya halicci mata ga adam ba ta kirjinsa ba?... har dai inda yake cewa: Sannan sai Allah ya halicci Hawwa, sai Adam (a.s) ya ce: Ya Ubangjiji wane abin halitta ne wannan kyakkyawa wanda na samu debe kewa da kasancewarsa kusa da ni da kallonsa? Sai Allah madaukaki ya ce: Ya Adam (a.s) wannan baiwata Hawwa ce, shin kana son ta kasance tare da kai? Sai ya ce: Na'am, kuma ni mai gode maka ne kan hakan matukar ina raye, sai Allah madaukaki ya ce masa: Ka nemi aurenta domin ita baiwata ce, kuma ta dace da kai a matsayin macen sha'awa, sannan sai Allah ya halitta masa sha'awa…" .
Akwai wasu abubuwa masu muhimmanci a nan da zamu lura da su cewa:
Batun halittar hawwa daga adam (a.s) daga kirjinsa na hagu bai inganta ba.
Halittar hawwa ta kasance ne daban mai zaman kanta, ba ta tsuro daga halittar adam ba.
Kallon da annabi adam (a.s) ya yi wa hawwa shi ne ya sanya shi samun nutsuwa da kuma alaka daga baya. Sai dai ba kallo na sha'awa ba ne, domin an sanya mishi sha'awa ne ma bayan ya samu nutsuwa da ita.
Allah ya sanya wa adam (a.s) sha'awarta ne bayan ya samu nutsuwa da soyayya da ita.
Sadaki mafi daraja shi ne koyar da matar da aka aura, a sanar da ita ubangiji da siffofinsa da ayyukansa, da kuma nauyin da ya hau kanta da Allah ya dora mata.
Bayan aure sai adam (a.s) ya ce da hawwa ta zo wurinsa yana kiranta, sai Allah ya umarce shi da ya tashi ya je wurinta. Wannan yana nuna cewa namiji ne yake zuwa ya nemi auren mace, kuma shi ne zai rika zuwa gidansu ko wurinta, kai shi ne ma zai rika bin ta ko nemanta ko da a daki ne.
Da wannan ne zamu gane cewa mace da namiji daga asali daya suke, ba wai namiji ne asali ba, mace kuma reshe, kuma dukkansu suna mikuwa zuwa ga mahallici ubangiji daya wanda ya yi su duka kai tsaye.
Sai dai yin magana da adam (a.s) yana nuna cewa; Namiji yana da wata baiwa ta samun wahayi daga Allah a matsayin dan sakonsa, duk da kuwa wilayar Allah da soyayyarsa da kusancinsa ba su kebanta da shi ba.
Kamar yadda aka dora alhakin kare iyali, da ciyar da su a kan namiji da sauran hidimom da aka dora masa wanda ayar Kur'ani ta yi nuni da hakan da cewa: Maza su ne masu tsayuwa da al'amuran mata.
Wannan lamarin duk yana nuna mana muhimmancin gina iyali cikin tausaya wa juna da tausasawa, ba cikin kausasawa da takurawa ba.
Kuma halitta ce ta Allah (s.w.t) mace ta kasance wani abu ne kamar maganadisu da namiji yake fizguwa zuwa gareshi. Kuma wannan daraja ce ga mace, kima ce ga namiji ba kaskanci ba ne garesu. Don haka zuwa gurin mace alama ce ta daukaka ga namiji, kuma daraja ce ga mace a lokaci guda.
Haduwa wadannan halittu biyu namiji a matsayinsa na nagatib da mace a matsayinta na positib yana hada mana cakudewa tsakanin jalalul-Lah (nagatib) da jamalul-Lah (positib) domin gina natija mai kyau da al'umma ta gari wacce take dauke da sunayen Allah da sakonsa domin cika duniya da hasken ubangiji, sai wannan kasa da dukkan halittu su haskaka da hasken Allah madaukaki.
Sannan wannan yana nuna mana hakikanin sirrin mutum ba namiji ba ne, ba kuma mace ba ne, shi ne ruhin da yake halittar Allah wanda idan aka sanya masa tufafin jiki to a lokacin ne zai tashi da suran namiji ko mace daidai gwargwadon jikin da aka sanya masa.
Sai dai ina da mahangar cewa wannan ra'ayi da na kai gareshi har yanzu bai nutsu a raina ba, domin ina ganin cewa shin jiki zai kasance shi ne kawai abin da ya sanya tasiri a bambancin dabi'ar halitta da halaye ko kuwa? Sai dai daga karshe idan mun duba sosai zamu iya ganin hakan, domin shi jiki ba kawai kamar fatanya ba ce a hannun mai noma da idan ya ga dama ya yi amdani da ita, idan kuma ba ya so ya wurgar da ita. Domin jiki halitta ce wacce sharadi ne ga rai idan zai yi aiki sai da shi, don haka jiki yana da rawar da yake takawa.
Da wanann ne zamu ga muhimmancin wannan bahasi a bayanin halittu da sakamakon da zasu samau a ranar kiyama. Sannan da wannan ne zamu gane cewa binciken da ya shagaltar da marubuta cewa; shin da namiji da mace suna da daidaito ne ko suna da sabani ba shi da ma'ana. Domin sabanin yana koma wa zuwa ga mallakar siffa da rashin mallakar siffa kamar yadda yake a ilimin Mantik.
Haka nan da wannan bayanin muna iya gane cewa ruhin mutum shi ne asali, jiki reshen samuwarsa ne, sai dai tun da jiki yana bambanta tsakanin namiji da mace, saboda bambancin da ke tsakanin kyawu da kwarjini, don haka sai aka samu bambanci a hukuncin shari'a a wasu janibobin sakamakon hakan, kuma da la'akari da ruhi (rai) ne aka samu wannan duniyar, da duniyar Barzahu, da lahira.
Da wannan ne aka samu bambanci tsakanin masu imani da gaibi (Allah), da kuma wadanda ba su yi imani da shi ba. Sai mulhidai (wadanda ba su yi imani da Allah ba) suka tafi a kan cewa mutum yana zama mutum ne da jiki, kuma tun da jiki iri daya ne, babu wata ma'ana hukuncinsu ya bambanta. Amma masu imani (masu dukkan wani addini da yarda da samuwar Allah), suna ganin cewa mutum yana zama mutum ne da ruhinsa ba da jikinsa ba, duk da kuwa jiki abu ne wanda yake dole ga ruhi kamar yadda muka kawo.
Don haka idan Allah madaukaki yana magana da mutum to yana magana da shi da la'akari da ruhinsa ne ba jikinsa ba. Sai dai a wasu hukunce-hukuncen suna da bambanci bisa la'akari da jikinsu. Don haka lokacin da Kur'ani mai daraja yake magana da yana yi ne da rayuka. Amam masu magana kan daidaiton namiji da mace ba mu sani ba ko maza da mata sun koka ne kan wannan lamarin, ko kuma sun yi tawaye kan wannan lamarin, ko sun nuna rashin yarda ne!?
Wannan kimar ta halittar mutum namiji da mace ta sanya su zama halifofin Allah a wannan duniya, sai suka kasance su ne masu gaje wannan duniya da izinin Allah, don haka ne maganar da Allah ya yi da adam (a.s) ba ta shafe shi kawai ba, sai muka ga ta shafi adam da hawwa (a.s), yayin da yake yi musu gargadin shedan da yaudararsa, ya gaya musu cewa shedan makiyinsu ne su biyun. Kuma shi ma shedan da ya tashi yi musu rantsuwa ya yi musu su duka biyun ne, bai takaita da adam (a.s) ba! Fadinsa madaukaki: "Shedan makiyi ne gareku" , da fadinsa: "Sai ya rantse musu da Allah cewa ni mai ina daga cikin masu yi muku nasiha" .
Akwai maganganu masu yawa kan wasu hukunce-hukunce masu hikima, kamar hawan takalifi kan mace tana shekaru 9, shi kuwa namiji sai ya kai shekaru 14, da batun gado, da ikon fita, da diyya, da kuma wasu bayanai da suka shafi Rayuwar Bulkis da sayyid Zahara (a.s), sai dai mun takaita hakan don gudun tsawaitawa.
Girmama juna yana daga hakkokin ma'aurata a kan junansu, ya hau kan miji ya tausaya wa matarsa da tausasa mata, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata, kada ya la'ance ta, ko ya zage ta, ko ya doke ta. Kada ya muzanta ta, ko ya kunyata ta ko ya daidaita mata asiri. Haka nan akwai hadisan da suka zo game da falalar mutumen da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al'ada ta rinjayi Addini.
Wajibi ne miji ya yi adalci ga matarsa da tsakanin 'ya'yansa da matansa, kamar yadda ya hau kansa ya nuna mata soyayyarsa, ya nuna mata wannan a fili ta yadda zata zama abokiyarsa a komai. Kuma ya rika yi mata maganganu irin na soyayya da nuna kauna ga juna, bai isa ba ya ba ta kudi kawai don yana da shi, wannan ba ya isa ga bukatun mace. Allah (s.w.t) ya fada a cikin littafinsa cewa: "Ya sanya soyayya da tausayi a tsakaninku" .
Haka nan ba shi da kyau ga miji ya munana zato ga matarsa, ko ba komai munana zato ga musulmi haramun ne, idan mace ta san mijinta yana munana mata zato alhalin tana mai kame kanta wannan yana iya rusa alakar soyayya da girmama juna da ke tsakaninsu har ya kai su ga rabuwa.
Sai dai kamar yadda mace take da hakki shi ma namiji yana da hakki, don haka hakkokinsa sun hada da kada mace ta ki shimfidar miji in ya neme ta, kada ta bayar da izinin shiga gidansa ga wanda ba ya son shigarsu, kada ta yada sirrinsa ko ta yi masa barnar dukiya, ta kula da yaransa da ayyukansa na gida da suka shafeta, kada ta kausasa masa harshe, ta yi kokarin faranta masa rai. Sannan ta rika ba shi uzuri a kan wasu al'amuran, kada ta yi abin da zai sa shi ya ji baya son zama da ita a gida ko abin da zai sanya shi nisantar hira da ita ko kaurace mata.
Wasu ruwayoyi sun kawo hakkin miji kan matarsa kamar haka: Yayin da wani sahabi ya ba wa Manzon Allah (s.a.w) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki sai ta yaye masa shi, idan kuwa ba ya nan tana kare shimfidarsa ba ta ha'intarsa, kuma ta kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. Sai Manzon Rahama (s.a.w) ya ba shi amsa da cewa: "Allah yana da ma'aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidi" . Haka nan wata ruwaya ta nuna cewa: "Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah" .
Mace ta yi biyayya ga mijinta domin shi shugaba ne a gida babu kuma yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ta sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, sai ya fara tunanin daukar fansa sai gaba ta faru, kuma zamansu ya gurbace, ko wannan fushin ya tura shi ga miyagun halaye da yawan fusata da fada.
Kada wata mata ta rika gasa da wasu mata ta ce: An saya wa kawata kaza kai ma sai ka yi min kaza wannan ko kadan ba shi da kyau.
Yana da kyau mata su dauki samfurin rayuwar zamantakewa daga Imam Ali (a.s) da sayyida Zahara (a.s), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (a.s) ya shiga wajan Fadima (a.s) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu. Sai ta ce: "Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai". Sai ya ce: "Me ya sa ba ki gaya min ba" Sai ta ce: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi" .
Daga Saifu, daga Najmu, daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: "Hakika Fadima (a.s) ta lamunce wa imam Ali (a.s) aikin gida da kwaba gari da yin gurasa da share gida, shi kuwa ya lamunce mata abin da yake bayan kofa: yin itace, kawo abinci… sai wata rana ya ce da ita: Ya Fadima shin kina da wani abu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama hakkinka ba mu da komai tun tsawon kwana uku ke nan sai dai abin da muka tanadar maka kai kadai, sai ya ce: Me yasa ba ki ba ni labari ba? Sai ta ce: Manzon Allah (s.a.w) ya hana ni in tambaye ka wani abu, ya ce da ni: Kada ki tambayi dan amminki wani abu, in ya zo da shi, shi ke nan, in ba haka ba to kada ki tambaye shi".
Yahaya da sanadinsa daga Abi Sa'idul khuduri, ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari sai ya ce da Fadima (a.s): Ya Fadima shin kina da wani abu da zamu ci. Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta babu wani abu da ya kwana gunmu da zamu ciyar da kai shi yau, ba ni da komai kwana biyu ke nan sai abin da na zabe ka a kaina da shi da kuma abin da zabi wadannan biyu -tana nufi Hasan da Husain- a kaina da shi. Sai ya ce: Don me ba ki gaya mini ba sai in samo miki wani abu? Sai ta ce: Ni ina jin kunyar Allah in kallafa maka abin da ba zaka iya ba, kuma ka kasa samu .
Daga Abil mufaddal, ya ce : Muhammad dan Ja'afar dan Kais dan Maskana ...da dogon sanadinsa sai a koma wa littafin… daga Abi Sa'idul khuduri ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari mai yunwa, sai ya ce: Ya Fadima, shin kina da wani abu da zaki ciyar da mu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta, ya girmama ka da wasiyya, babu wani abu da ya wayi gari a wajenmu da zamu ciyar da wani mutum shi tun kwana biyu ke nan sai abin da na fifita ka da kai da Hasan da Husain da shi a kaina. Ya ce: Har da ma yara biyu! Me yasa ba ki sanar da ni ba sai in zo muku da shi? Sai ta ce: Ya Abal Hasan, ina jin kunya daga ubangijina in kallafa maka abin da ba zaka iya ba" .
Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (a.s) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado.
Idan mun koma maganar imam Sajjad as da muka kawo farkon wannan bayanin zamu ga ta kunshi darussa masu yawa da kima matuka yayin da yake nuni da girmamawa tana daga hakkokin ma'aurata a kan junansu, kuma ya hau kan miji ya tausaya wa matarsa da tausasa mata, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata. A nan ne zamu ga matukar jahilci da nesantar al'adun musulunci ga irin mutanen nan da suke la'antar matansu ko su zage su ko su doke su. A wasu hadisai an yi nuni da falalar mutumin da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al'ada ta rinjayi Addini.
Wajibi ne miji ya nuna kauna da adalci tsakanin matansa, kamar yadda ya hau kansa ya nuna mata soyayyarsa, da kyakkyawan zato gareta. Wannan alakar da Allah (s.w.t) ya sanya tsakanin maza da mata ba don wasa da rashin hadafi ba ne. ubangiji madaukaki yana nuni da muhimmancin wannan lamarin yana mai cewa: "Ya sanya soyayya da tausayi a tsakaninku" .
A wasu hadisai an kawo jeren wasu hakkoki da miji yake da su kan matarsa kamar haka: Kada mace ta ki shimfidar miji in ya neme ta, kada ta bayar da izinin shiga gidansa ga wanda ba ya son shigarsu, kada ta yada sirrinsa ko ta yi masa barnar dukiya, ta kula da yaransa da ayyukansa na gida da suka shafeta, kada ta kausasa masa harshe, ta yi kokarin faranta masa rai. Sannan ta rika ba shi uzuri a kan wasu al'amuran, kada ta yi abin da zai sa shi ya ji baya son zama da ita a gida ko abin da zai sanya shi nisantar hira da ita ko kaurace mata.
Wasu ruwayoyi sun kawo hakkin miji kan matarsa kamar haka: Yayin da wani sahabi ya ba wa Manzon Allah (s.a.w) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki sai ta yaye masa shi, idan kuwa ba ya nan tana kare shimfidarsa ba ta ha'intarsa, kuma ta kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. Sai Manzon Rahama (s.a.w) ya ba shi amsa da cewa: "Allah yana da ma'aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidi" . Haka nan wata ruwaya ta nuna cewa: "Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah" .
Mace ta yi biyayya ga mijinta domin shi shugaba ne a gida babu kuma yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ta sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, sai ya fara tunanin daukar fansa sai gaba ta faru, kuma zamansu ya gurbace, ko kuma wannan fushin ya tura shi ga miyagun halaye da yawan fusata da fada.
Matan da suke son zama kammalallun mata masu daraja a duniya to sai su yi koyi da mata masu daukaka kuma su dauki samfurin rayuwar zaman tare daga Imam Ali (a.s) da sayyida Zahara (a.s), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (a.s) ya shiga wajan Fadima (a.s) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu. Sai ta ce: "Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai". Sai ya ce: "Me ya sa ba ki gaya min ba" Sai ta ce: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi" .
Daga Saifu, daga Najmu, daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: "Hakika Fadima (a.s) ta lamunce wa Imam Ali (a.s) aikin gida da kwaba gari da yin gurasa da share gida, shi kuwa ya lamunce mata abin da yake bayan kofa: yin itace, kawo abinci… sai wata rana ya ce da ita: Ya Fadima shin kina da wani abu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama hakkinka ba mu da komai tun tsawon kwana uku ke nan sai dai abin da muka tanadar maka kai kadai, sai ya ce: Me yasa ba ki ba ni labari ba? Sai ta ce: Manzon Allah (s.a.w) ya hana ni in tambaye ka wani abu, ya ce da ni: Kada ki tambayi dan amminki wani abu, in ya zo da shi, shi ke nan, in ba haka ba to kada ki tambaye shi".
Yahaya da sanadinsa daga Abi Sa'idul khuduri, ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari sai ya ce da Fadima (a.s): Ya Fadima shin kina da wani abu da zamu ci. Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta babu wani abu da ya kwana gunmu da zamu ciyar da kai shi yau, ba ni da komai kwana biyu ke nan sai abin da na zabe ka a kaina da shi da kuma abin da zabi wadannan biyu -tana nufi Hasan da Husain- a kaina da shi. Sai ya ce: Don me ba ki gaya mini ba sai in samo miki wani abu? Sai ta ce: Ni ina jin kunyar Allah in kallafa maka abin da ba zaka iya ba, kuma ka kasa samu .
Daga Abil mufaddal, ya ce : Muhammad dan Ja'afar dan Kais dan Maskana ...da dogon sanadinsa sai a koma wa littafin… daga Abi Sa'idul khuduri ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari mai yunwa, sai ya ce: Ya Fadima, shin kina da wani abu da zaki ciyar da mu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta, ya girmama ka da wasiyya, babu wani abu da ya wayi gari a wajenmu da zamu ciyar da wani mutum shi tun kwana biyu ke nan sai abin da na fifita ka da kai da Hasan da Husain da shi a kaina. Ya ce: Har da ma yara biyu! Me yasa ba ki sanar da ni ba sai in zo muku da shi? Sai ta ce: Ya Abal Hasan, ina jin kunya daga ubangijina in kallafa maka abin da ba zaka iya ba" .
Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (a.s) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado.
Sannan mace tana da hakkin yin aiki bisa yarjejeniya da mijinta domin kyautata rayuwarta da ta danginta ko 'ya'yanta, tana da hakkin yin al'amuran siyasa, da na zaman tare a al'umma, da na kasuwanci, da na ilimi kamar koyarwa, da sauransu matukar a cikin akwai kiyaye hakkin allah da na mijinta, kamar dai yadda namiji shi ma ya halatta ya yi su tare da kiyaye hakkokin allah da na iyalinsa babu wani bambanci.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Saturday, April 30, 2011