Falalar Karanta Tasbihuz- Zahara (AS)
An ruwaito daga Imam Sadik (AS) yana cewa, “Mun kasance muna umurtar ’ya’yanmu da yin Tasbihu Fadima Az-Zahara (AS), kamar yadda muke umurtar su da yin Salla, to ku lizimci yin sa.” Ya zo a wani Isnadi mai girma daga Imam Bakir (AS) ya ce, “Wanda ya karanta Tasbihin Fadima, sannan ya yi Istigifari, to za a gafarta masa. Ya fada sau 100 da harshensa, za a cika ma’auninsa da lada 1000, a kore Shaidan daga gare shi. Allah zai yarda da shi.” Imam Sadik (AS) yana cewa, “Wanda ya yi Tasbihin Fatima, kafin ya bar wajen da ya yi Sallar farilla an gafarta masa, Aljanna ta wajaba a gare shi. Daga Sadik (AS) yana cewa; “Tasbihin Zahara’(AS) a karshen kowace Sallar Farilla ya fi falala a gun Allah (T) fiye da sallah raka’a dubu a kowaca rana.” A wata ruwayar mai girma daga Imam Bakir (AS) ya ce; ba a bauta wa Allah da wani abu na Tasbihi ba, ko Tamjidi, wanda ya fi Tasbihin Fadima (AS). Da a ce akwai wanda ya fi falala, da Manzon Allah ya koya wa Fadima (AS). Hadisan da suka zo a kan falalar suna da yawa a kan haka. Ga Tasbihin kamar haka: ‘Allahu Akbar 34, Alhamdulillah 33, Subhanallah 33. Karin bayani a dubaMafatihul Jinan Fasali na 1 shafi na 637.
wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua