Tarihin Imam Hussain
  • Take: Tarihin Imam Hussain
  • marubucin:
  • Source:
  • Ranar Saki: 17:51:19 1-10-1403

Bayan mutuwar Mu'awiya da kuma fadawar mulki hannun lalataccen dansa Yazidu, sai ya hori gwamnoninsa da su karbi bai'a daga mutane, musamman daga Imam Husaini (a.s.); wannan kuwa saboda irin masaniyar da gidan Umayyawa ke da shi na cewa shi (Husaini) tsayayye ne da ba ya girgiza.

Cikin gaggawa Yazidu ya rubutawa gwamnansa na Madina, Walidu bin Utbata, yana horonsa da karba masa bai'ar mutanen Madina gaba daya, musamman Imam Husaini (a.s.). To sai dai Imam (a.s) ya ki amincewa da hakan. Yana mai bayyanawa wa gwamna Walidu cewa:

"Yazidu mutum ne fasiki, mashayin giya, mai kashe rai ba bisa hakki ba, mai bayyana fasikanci; iri na ba zai yi mubaya'a ga irinsa ba(1)

A gefe guda kuma, Imam Husaini (a.s.) ya bayyana siffofin jagoran da yi masa bai'a ta wajaba, a cikin wasikar da ya aikawa mutanen Kufa, yana mai cewa:

"Wallahi ba kowa ke shugaba ba face mai hukunci da Alkur'ani, mai tsayar da adalci, mai riko da addinin gaskiya mai iyakance kansa da Zatin Allah(2)".

Da wannan tafarkin hamayya da siyasar kisan mummuke da danniyar Umayyawa ta fara dasuwa. Sai Imam Husaini ya daura damarar sauke nauyin da aka tanaje shi don shi a Musulunci a matsayinsa na Imamin al'umma na halal kuma jagoranta da aka amincewa a kan sakon Musulunci mai tsarki.

Lokacin da al'amura suka ci gaba da yin tsamari, sai Imam Husaini (a.s.) ya ziyarci kabarin kakansa Manzo (s.a.w.a), ya yi wasu raka'o'in nafifoli a wajen sannan ya roki Ubangiji shi Allah Madaukaki yana mai cewa:

"Ya Allah wannan kabarin AnnabinKa Muhammadu (s.a.w.a) ne, kuma ni dan 'yan AnnabinKa ne. Hakika wani al'amari da ka san shi ya zo gare ni. Ya Allah lallai ni ina son abin kirki kuma ina kin abin ki. Ina rokon Ka, ya Ma'abucin buwaya da karimci, da darajar wannan kabarin da wanda ke cikinsa Ka zaba min abin da a cikinsa akwai yardarKa da yardar ManzonKa(3).

Sai Imam Husaini (a.s.) ya gaggauta tara mutan gidansa da Sahabbansa masu kyakkyawar niyya, ya sanar da su inda ya fuskanta da inda ya dosa zuwa Haramin Allah, wato Makka.

Sai Imam Husaini (a.s.) ya gaggauta tara mutan gidansa da Sahabbansa masu kyakkyawar niyya, ya sanar da su inda ya fuskanta da inda ya dosa zuwa Haramin Allah, wato Makka.

An samu mutane da yawa dai da suka nuna adawarsu da wannan mataki da kiransa da ya canza kudurinsa, don ya tsira da ransa, yayin da wasu kuwa suna kiransa da ya mika kai bori ya hau ne saboda wani rauni da suke fama da shi da rashin azama. Sai dai Imam Husaini (a.s.) ya riga ya yi azamar taimakon gaskiya, don haka barazana ko hamayya da wasunsu ba su kashe masa gwiwa ba.

Ayarin Imam Husaini (a.s.) ya hau hanyar Makka alhali harshensa na zikirin Allah Madaukaki, zuciyarsa na kawace da son Allah, sai ya shiga Makka alhali yana karanta Fadar Allah Madaukaki: Yayin da ya fuskanci (birnin) Madayana, sai ya ce: "Ina fatan Ubangijina ya shiryar da ni hanyar da ta fi dacewa". Sai ya sauka a gidan Abbas dan Abdul-Mudallibi, inda wani gungun Muminan mutanen Makka da wadanda suka shigo cikin garin suka hau dawaki suka bi ta bayansa, don su boye shigowarsa cikin Makka.

Labarin fitowarsa daga Makka da kin mubaya'arsa ga Yazidu ya yadu. Sai wasiku da wakilai suka shiga isowa gare shi daga lunguna daban daban. Sai shi kuma ya shiga aikawa da amsoshi yana kiransu zuwa ga yunkurawa don fito-na-fito da Yazidu da kifar da gwamnatinsa, da janye duk wata bai'a da aka karbar masa da karfin tsiya, ta'addanci, bayar da rashawa ko yaudara. Wannan ya tayar da ruhin neman juyi a cikin Iraki.

A lokacin da Imam Husaini (a.s.) ke fama da aikin kawo cikas ga hawan Yazidu mulki a yankunan Musulmi, sai labari ya zo gare shi cewa Kufa ta shiga cikin wani yanayi na yunkurin kawo sauyi da ya girgiza masu mulki.

Domin gamayyar 'yan hamayya, bayan kasancewa cikin kama-karya da danniya, mutanen Kufa sun yunkura, suka ga cewa ga lokaci ya yi da za su 'yantu daga siyasar dagawa; don haka sai suka shirya wani taro don nazarin yada al'amura suka fara sauwaya a Kufa, da abin da sabon yanayin hawa mulkin Yazidu ke bukata daga wajen su. Bayan dacewar kalma a kan yi wa Imam Husaini (a.s.) mubaya'a, sai shugabannin Kufa suka rubuto wasika da ta kunshi bayyana rashin amincewarsu da hukuncin Umayyawa ko ta wace fuska, da cewa su ba za su taba yarda da wanin Imam Husaini ba.

Daga nan sai wasiku suka yi ta bin juna daga Kufa, wadanda ke dauke da kiran Imam Husaini (a.s.) da ya hadu da su a Kufa a matsayin halifa kuma Imamin Musulmi. Abin ya kai ga har mutane suna aikawa Imam da sunayen kabilun da ke jiran isowarsa Kufa, inda adadin sunayen ya kai mayaka dubu dari(4).

Imam Husaini (a.s.) ya sakankance da wajibcin aikawa da wani wakilinsa don karbar bai'ar mutanen Iraki. Sai ya zabi dan baffansa Muslim bin Akil, mutum mai tsoron Allah da irinsa ya karanta.

Mutanen Kufa sun tarbi Muslim tarba irin ta biyayya da kauna, suka mika bai'arsu ga Imam Husaini ta hannunsa, ta yadda har sai da Muslim ya sakankance da cewa wannan wani sauyi ne da ke bayyana nasara ga Ahlulbaiti (a.s.) da sakon Allah Madaukaki.

A nan ne Muslim ya ga ya fi kyau ya rubutawa Imam Husaini (a.s.) wasika ya bayyana masa yadda al'amura ke gudana da halin da ake ciki; don haka sai ya rubuta masa cewa:

"Bayan haka, rana ba ta karya. Lallai dukkan mutanen Kufa na tare da kai. Hakika mutum dubu goma sha takwas daga cikin su sun yi mini mubaya'a, don haka ka gaggauta isowa daga lokacin da ka karanta wannan wasikar tawa. Amincin Allah da rahamarSa da albarkarSa su tabbata gare ka (5)".

Kara da cewa a daidai lokacin Imam Husaini (a.s.) ya ga cewa bari ya bayyana wa mutanen Basara kudurinsa na yakar zalunci da kaucewa hanya, don haka sai ya rubuta musu haka. Amsar Yazidu bin Mas'ud al-Nahshali ya kasance mafi kyawun amsa mai tattare da kyakkyawan kuduri, yayin da ya bayyana biyayyar iyalan Tamim da Bani Sa'ad ga Ahlulbaiti (a.s.). Sai dai wani abin takaici shi ne cewa amsar wasikarsa ta iso lokacin Imam Husaini na fagen daga a Karbala.

Da haka tawagar Nahshali ta yi jinkirin taimakawa gaskiya, ta yadda da ya sami labarin shahadar Imam Husaini (a.s.) hankalinsa ya yi matukar tashi a kan kufcewar daman taimakon jikan Manzo (s.a.w.a) da rashin samun daman bayar da gudunmawa a wajen.
 


____________
1- Ibn Dawus, Maktalul-Husain, shafi na 11.

2- Kitab al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 204.

3- Al-Mukarram, cikin Maktalul-Husaini, shafi na 147.

4- Asad Haidar, cikin Ma'al-Husaini Fi Nihdhatihi.

5- Al-Watha'ikul-Rasamiyyah Li-thauratil-Husaini alaihis-salam na AbdulKarim al-Kazwini.

 

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua