Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Muhammad Mahadi (a.s) Imami Na Sha Biyu: Muhammad Al-Mahadi Dan Hasan (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Hasan dan Ali dan Muhammad (a.s). Babarsa: Kuyanga ce Mai suna Narjis. Kinayara: Abul Kasim. Lakabinsa: Al-Mahadi, Al-muntazar, Sahibuz Zamani, Al-hujja, Al-ka'im, Waliyyul Asri, Assahib. Tarihin haihwarsa: 15 Sha'aban 255 a lokacin Al-mu'utamad. Inda aka haife shi: Samra'u. Tsawon rayuwarsa: Rayayye ne boyayye daga ganin mutane, zai fito karshen zamani da umarnin Allah (s.w.t) domin ya cika Duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci, muna rokon Allah ya gaggauta bayyanarsa. Tsawon Imamancinsa: Yana da tsawo, har yanzu yana raye. Buyansa: Yana da buya biyu:
1-Karami: Yana da tsawon shekara 74, ya fara daga shekarar 260 H har zuwa shekarar 329 H.
2-Babba: Ya fara daga shekarar 329H bayan mutuwar jakadansa na karshe har zuwa wannan zamanin.
Jakadunsa: Su hudu ne, su ne mutane suke karbar hukunce-hukuncensa daga gare su a lokacin buyansa karami. Wadannan jakadon su ne; 1-Usman dan Sa'id 2-Muhammad dan Usman 3-Husaini dan Ruhu 4-Ali dan Muhammad Assimiri. Alamomin bayyanarsa: Ba zasu kirgu ba sai dai zamu kawo guda hudu a nan: 1-Fitowar Sufyani 2-Kashe Al-Hasani 3-Zuwan Tutoci Bakake daga Khurasan 4-Fitowar Al-yamani.
Shi ne Muhammad Mahadi dan Hasan Askari (A.S) babarsa ita ce sayyida Narjis (A.S) an haife shi a Samarra a daren rabin Sha'aban a sekara ta dari biyu da hamsin da biyar hijira.
Ya kasance karshen hujjar Allah a bayan kasa kuma cikon halifofin Manzon Allah kuma karshen imaman musulmi, kuma Allah (S.W.T) ya tsawaita rayuwarsa madaukakiya a wannan duniya domin kada ta zauna ba hujja, domin ba don hujja ba da kasa ta kisfe da na kanta, kuma shi ya boyu daga ganin mutane kuma Allah zai bayyanar da shi a karshen zamani bayan an cika ta da zalunci domin ya cika ta da adalci.
Annabi (S.A.W) da imamai (A.S) sun bayar da labarin cewa zai boyu kuma boyuwar ta yi tsayi da ba mai tabbata a kan biyayyarsa sai wanda Allah ya cika shi da imani, kuma kwanakin boyuwarsa suna da amfani ga mutanen duniya kamar rana da take da amfani koda tana bayan gajimare. Kuma Allah zai wanzar da shi rayayye, yana mai boyuwa har sai lokacin bayyanarsa ya yi sai Allah ya bayyanar da shi da izininsa, ya mallaki duniya gaba daya ya shimfida adalci, kuma ya yada musulunci a duk fadinta kuma ya aiwatar da Kur'ani a kan kowa a dukkan rayuwa, sai alheri ya cika su, kuma dukkan duniya ta arzuta da dukkan bayi, sai fadin Allah madaukaki ya tabbata "Domin ya sanya shi mai galaba a kan addini dukkaninsa koda kuwa mushrikai sun ki" .
Allah ka gaggauta bayyanarsa kuma ka saukaka fitowarsa, kuma ka sanya mu daga mataimakansa.
Wannan kuwa bai buya ba ga mutane cewa yayin da Imam Mahadi (A.S) ya zo domin janazar babansa Imam Askari, azzaluman mahukunta sun gan shi, saboda haka ne ma suka ji tsoron mulkinsu suka yi tunanin kama shi da tsare shi da gamawa da shi kamar yadda suka yi wa kakanninsa domin su kubuta daga abin da suke ji daga Manzon Allah (S.A.W) na labarinsa cewa shi ne zai kawo karshen mulkin zalunci.
An umarci Imam Mahadi (A.S) da buya daga wajan Allah don haka ne ma ya bace daga ganin mutane, yayin da 'yan leken asirin halifa suka zo gidansa sai ya bace daga ganinsu ya buya daga gani kuma ya fita ta kofar da take bude ta gidan kasa zuwa wajen gida ba tare da wani daga cikinsu ya gani shi ba, wannan ne ma ya sanya musulmi suka riki wajen wurin yin salla wanda yake a garin Samarra da ya shahara.