Imam Hadi
  • Take: Imam Hadi
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:8:46 1-10-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Ali Hadi (a.s) Imami Na Goma: Imam Ali Hadi Dan Muhammad (a.s) Sunansa da Nasabarsa: Ali Dan Muhammad Dan Ali Dan Musa (a.s). Mahaifiyarsa: kuyanga ce mai suna Sumana. Alkunyarsa: Abul Hasan ko Abul Hasan Assalis. LaKabinsa: Al-Hadi, Al-mutawakkil, Annakiyyi, Al-fattah, Al-murtada, Annajib da Al-alim. Tarihin haihuwarsa: 15 julhajji 212H. Inda aka haife shi: Alkaryar Sarya (صريا) nisanta da Madina mil uku ne. Matansa: Kuyanga ce ana ce mata Susan. 'Ya'yansa: 1-Imam Hasan 2-Husaini 3-Muhammad 4-Ja'afar 5-A'isha. Tambarin zobensa: Hifzul uhud min akhlakil ma'abud. Tsawon rayuwarsa: Shekara 42. Tsawon Imamancinsa: 33. Sarakunan zamaninsa: Karshen mulki Ma'amun da Al-mu'uta- sim da Al-wasiK da Al-mutawakkil. Tarihin shahadarsa: 3 Rajab shekara 254H. Inda ya yi shahada: Samarra'u. Dalilin shahadarsa: An kashe shi da guba a lokcin mutawakkil. Inda aka binne shi: Samarra (IraKi). Imam Ali Hadi Dan Muhammad (A.S) babarsa ita ce sayyida Sumana kuma an haife shi a Madina ranar juma'a biyu ga watan Rajab shekara ta Dari biyu da sha biyu, sannan ya yi shahada da guba a samarra a ranar litinin uku ga watan rajab shekara ta Dari biyu da hamsin da huDu, kuma Dansa imam Hasan Askari (A.S) ya shirya shi ya binne shi a samarra inda yake yanzu. Ya kasance mafificin mutanen zamaninsa kuma mafi ilminisu kuma mafi kyautarsu kuma mafi taushinsu harshe, kuma mafi bautarsu ga Allah, kuma mafificinsu kyawun zuciya da kyawun halaye. Daga cikin baiwarsa abin da 'arbili' ya ruwaito a Kissarsa cewa halifa ya aika masa da dirhami dubu talatin sai ya bayar da ita ga wani mutumin Kufa, ya ce da shi: ka biya bashinka kuma ka ciyar da iyalanka kuma ka yi mana uzuri. Sai mutumin ya ce masa: Ya Dan Manzon Allah (S.A.W) ai abin da yake kaina bai kai sulusin hakan ba, sai dai "Allah ne ya san inda yake sanya sakonsa" sai ya karBi dukiya ya juya .