Imam Kazim
  • Take: Imam Kazim
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:38:8 10-10-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Musa Al-Kazim (a.s) Imami Na Bakwai: Musa Al-Kazim Xan Ja'afar (a.s)

Sunansa da Nasabarsa: Musa xan Ja'afar (a.s), Babarsa: kuyanga ce sunanta (Hamida). Alkunyarsa: Abul-Hasan, Abu Ibrahim, Abu Ali, Abu Isma'il. Laqabinsa: Al-Abdussalih, Assabir, Al-amin, Al-Kazim shi ne ya fi shahara. Tarihin haihuwarsa: 7 Safar shekara 128H. Inda aka haife shi: Al-abwa'i a Madina. Matansa: Dukkaninsu kuyangi ne. 'Ya'yansa: Yana da 'ya'ya 37 : 1-Ali Rida 2-Ibrahim 3- Abbas 4-Isma'il 5- Ja'afar 6-Harun 7-Husaini 8-Al-Qasim 9-Ahmad 10-Muhammad 11-Hamza 12-Abdullah 13-ishak 14-Ubaidul- Lahi 15-Zaid 16-Hasan 17-Al-fadl 18-Sulaiman 19-Faximatul-kubra 20- Fadimatus-sugra 21-Ruqayya 22- Hakima 23-Ummu Abiha 24-Ruqayya 25-Kulsum 26-Ummu Ja'afar 27-Lubabatu 28-Zainab 29-Khadiza 30-Aliya (Ulayya) 31-Amina 32-Hasana 33-Bariha 34- A'isha 35-Ummusalama 36-Maimuna 37-Ummu Kulsum.
Tambarin zobensa: Hasbiyallah. Tsawon rayuwarsa: shekara 55. Tsawon Imamancinsa: shekara 35. Sarakunan zamaninsa Lokacin Umayyawa: Marwanal himar. Lokacin Abbasawa su ne: Abul Abbas Assaffah da Abu Ja'afar Al-mansur da Muhammad Mahadi da Musa Alhadi da Harunar -Rashid. Tarihin shahadarsa: 25 Rajab 183H. Inda ya yi shahada: Bagdad.
Dalilin shahadarsa: An kashe shi da guba a lokacin Harunar-Rashid. Inda aka binne shi: A Maqabartar Quraishawa a Kazimiyya a Arewacin Bagdad.
Shi ne Musa Kazim xan Ja'afar (A.S) babarsa sunanta Hamida mai tsarki, an haife shi a abwa'i a wani gida tsakanin Makka da Madina, ranar lahadi bakwai ga watan safar shekara ta xari da ishirin da takwas kuma ya yi shekara kusan hamsin da biyar, an kashe shi da guba yana mai shahada a kurkukun Harun Rashid, bayan ya tsare shi kusan shekaru goma sha huxu a cikinsa bisa zalunci da shisshigi, wannan kuwa ranar juma'a ishirin da biyar ga watan Rajab shekara ta xari da tamanin da uku, kuma xansa Imam Ali Ridha (A.S) shi ne ya yi mas ajanaza ya binne shi a kabarinsa na yau a kazimiyya.
Ya kasance mafi ilimin mutanen zamaninsa kuma mafificinsu kuma mafi baiwarsau kuma mafi jarumtakarsu mai kyawawan halaye mai taushin xabi'u, mai falala da ilimi, mai girman daraja, mai giman sha'ani, mai yawan ibada, mai tsawaita sujada mai yawan haxiye baqin ciki, saboda haka ne aka ambace shi da Kazim, kuma saboda gyaransa aka kira shi da "abdus salih".
Kuma iliminsa a dukkan fagagen ilimi ya ximautar da masana daga cikinsku akwai baban kiristoci mai suna "Burahatu " wanda Imam ya qure shi ya musulunta.
Daga kyautarsa ya kasance wani talaka ya tambaye shi sai ya ba shi dirhami xari, sai Imam ya tambaye shi wata mas'ala domin ya jarraba shi ya san gwargwadon iliminsa, sai ya amsa sai ya qara masa dirhami dubu biyu.
Ya kasance mafi kyawun mutane sauti da Kur'ani, kuma mafi yawansu ibada da tilawa, mafi tsayinsu sujada da ruku'u, mafi zubarsu hawaye da kuka, kuma ya yi shahada yana cikin sujada.