Sayyida Zahara
  • Take: Sayyida Zahara
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:50:18 10-10-1403

FADIMA AZZAHARA (a.s] FADIMA AZZAHARA (a.s] Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Fadima Azzahra 'Yar Muhammad (a.s) Sunanata da Nasabarta: Ita ce Fadima Azzahara 'yar Muhammad (a.s). Babarta: KHadijatul Kubra (a.s).
Al-kunyarta: Uwar babanta, Uwar Raihantaini, Uwar Imamai. Lakabinta: Zahra, Al-batul, Assidika, Al-mubaraka, Addahira, Azzakiyya, Al-mardiyya, Al-muhaddasa. Tarihin haihuwarta: 20 Jimada Akhir a shekara ta biyar da aike gun Ahlul Baiti (a.s). Inda aka haife ta: Makka Mai girma.
Mijinta: Imam Ali (a.s). 'Ya'yanta: Imam Hasan (a.s) da Imam Husain (a.s), Zainab uwar musibu (Saboda musibar da ta gani a Karbala), Muhsin (wanda aka yi barinsa a jikin bango), Zainb karama (Zainab As-Sugura).
Tambarin zobinta: Aminal mutawakkilun. Mai hidimarta: Fidda. Tsawon shekarunta: 18 a mashhuriyar magana. Tarihin sahahadarta: 3 Jimada Akhir shekara 11 hijira, a wata ruwaya Jimada Auwal, tana mai ciwon sukan nan… da barin jariri da karayar kirji da hudar nan ta kusa.
Inda aka binne ta: Madina. Amma ba wanda ya san inda kabarinta yake har yanzu.
Ita ce Fadima Zahara (A.S) kuma babanta shi ne Muhammad dan Abdullahi, kuma babarta ita ce sayyida Hadiza uwar muminai, mijinta shi ne Imam Ali shugaban wasiyyai, kuma daga 'ya'yanta da jikokinta akwai imamai masu tsarki.
An haifi Fadima ishirin ga jimada sani a shekara ta arba'in daga rayuwar Annabi (S.A.W) kuma ta yi shahada tana abar zalunta a ranar talata uku ga jimada sani shekara ta sha daya hijira, shekarunta goma sha takwas ne .
Imam Ali (A.S) shi ne ya binne ta a Madina ya boye kabarinta da wasiyyarta domin ta kafa hujja kan al'umma da zaluntar ta da aka yi da kuma kwace mata hakkinta. Kuma ta kasance kamar babanta a ibada da zuhudu da fifiko da takawa, kuma Allah madaukaki ya saukar da ayoyin Kur'ani game da ita .
Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yi mata lakabi da "shugabar matan talikai" kuma ya yi mata alkunya da "babar babanta" yana son ta so mai tsanani, kuma yana girmama ta girmamawa mai girma, har ya kasance idan ta shiga wajansa sai ya yi maraba da ita ya mike tsaye domin girmama wa gareta, sannan kuma ya zaunar da ita wurinsa, wani lokaci har ya sumbanci hannunta, kuma ya kasance yana cewa: Allah yana yarda da yardar Fadima yana kuma fushi da fushinta .
Ta haifa wa Imam Ali (A.S) Imam Hasan da Imam Husain da Muhsin (A.S) wanda aka yi barinsa saboda cutarwa da babarsa ta fuskanta, da kuma sayyida Zainab, da Ummu kulsum (A.S).