WAHABIYYANCI
  • Take: WAHABIYYANCI
  • marubucin:
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:52:40 1-10-1403

DA SUNAN Allah  MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Da yawa daga wahabiyawa masu kyakykyawar niyya ne a wahabiyancin su, ba kamar yadda wasu mutane da yawa su ka dauka cewa da gangan su ke yi don rusa addini ba kuma ana basu kudi, e ana basu kudi amma kudin ba yana nufin sakamakon wannan kudin ne kawai ya mayar da su wahabiyawa ba saidai kuma kudin na karfafar su, yawanci da dalili su ke son yin wahabiyancin su kamar yadda idan mu ka duba wasun su ai talakawa ne duk da haka akwai wadanda ke da riba idan aka yi wahabiyanci ta fannin aljihun su musamman jagorori da shgabanni wannan ta sa dole au kare wahabiyai/salafanci koda sun gane cewa kuskure ne baki dayan sa ko kuma akwai kuskure a ciki, sabida haka sanin wahabiyanci na da matukar muhimmanci sosai.
Wahabiyawa sun shahara da matsaloli daban daban na cakudewa tsakanin abubuwa biyu, akwai shubahar da su ka fada kan Lazeem da Malzoom wanda ilimin Mandik{logic] ke Magana kan sa sannan ilimin Usul na karfafar sa, duk sanda su ka yi Magana kawai sun a nufin lazeem da malzoom na zuwa cikin sauki, wannan matsala ta same su ne sabida rashin kar6ar addinin su daga gidan Manzo (SAW) wajan Ahlulbait (AS) sai ya zama da yawan abubuwa sun samu 6ata, cakudewa wajan rashin sanin zamanin su, da dora zamanin da ya zama na yanzu, cakudewa wajan ma'anar kafirci, cakudewa wajan menene tawili, cakudewa game da wilaya da tawiloli daban – daban, da amfani da mushtarakatil lafziyya (daukar dukkan lafuzza da ma'ana daya), cakudewa wajan ma'anar gullat, meye guluwwi cikin fatawa, usulul akeeda, masa'ilul akeeda, sun cakuda wadannan abubuwa uku a daya, sabida haka ana cewa guluwwi sais u bada mummunan tunani kan lamarin, wannan kuma na daga cikin babban raunin wahabiyanci.
Misalin lazeem da malzoom da ke cakudewa wahabiyawa shine: ana cewa wannan kafiri ne sai bawahabiye ya dakko dukkanin ma'anar yadda ya ke siffanta kafirci ya dora masa, ba ruwan sa da cewa shin kafiri harbi ne, kafiri ahadi, kafiri fikihi, kafiri wilayi, kafiri siyasi, kafiri ulubi duk sai ya sanya hukuncin su daya cikin ma'ana daya, a wajan sa rashin dama ce ke sanya shi zama da kowane irin kafiri,  sabida haka rashin dama ce ta sanya shi zama da kafiri, ya kasa ganewa cewa kafiri idan da nufin wanda ba muslmi ba da yawa hukuncin su ya canja sabida zamantakewar kasashe a yau bisa sharudda ne, maimakon wajen mafiya malaman musulunci sun ayyana kafirci da ma'aunai daban – daban a duniya, kuma a duniyar yau kakaf babu kafiri harbi kamar yadda ya ke a zamanin da sabida canjawar yanayi sabida dukkan kasashen duniya yanzu na zaune ne karkashin dokoki da al'kawurra daban, in dai ba bisa kariya ba (daga wanda ya kai hari kan musulmi) shi kuma wannan wani abu ne daban, zamu iya ganin yadda Manzo (SAW) ya zauna da banu kainika'a da banu Nadheer bisa sharudda, amman har gobe wajan Wahabiyawa ana cewa kafiri sai su dauki dukkan wadannan ma'anoni hatta wanda za'a yaka ma su kan sanya shi cikin waccenn ma'ana, ba ruwan su kuma da cewa kafirin kasir ne, mukassar ne, ya ga shiriya ko bai gani ba, bayan wannan wani abu ne da ke hannun Ubangiji, duk bai shafe su ba, wannan kuma babban kuskure ne mai hadarin gaske, domin ya kan sa cikin sauki kan kankanin laifi a kashe rayuka, kuma a wajan su mutum na zama kowane irin kafir to zai shiga wuta, ba ruwan su da bisa wacce ma'ana ya zama kafiri, har ma idan su ka zo wajan haddi a yankunan da wahabiyawa su ka kama zaka ga su na cewa mutum ya yi kalmar shahada kafin a kashe shi ba don ya dawo musulmi ba kawai don ko zai dace a lahira ba afuwa ko tuba, wannan abun takaici da yawa yake, duk irin wadannan lazeem da malzoom na cakude musu kuma bisa wannan cakudedeniya su ke hukunci bisa kuskure, haka nan sun samu cakudewa kan ma'anar haramcin tawili duk da cewa sun samu raddi mai karfi daga malamai Daban – Daban, da yawa su na fama da rashin sanin zamanin su har ma wasun su kan haramta aikin bankiko ajiya a bankin da suran abubuwa masu yawa.
Wannan shubuha da su ka fada sun manta cewa idan ka kalli ruwayoyi da ayoyin kurani baki daya zaka ga cewa tawili kan su ya zama dole domin ba yadda za a yi ka sanya ma'auni daya kan su baki daya, Misal : ya za su fassara hadisi da ayar da su ka zo kan cewa jin Mumini, ganin sa, kamun sa da hannu da kafar da ya ke tafiya da ita su na zama na Allah idan ya kusanci Allah sosai? Allah na cewa zan zama jin da yake ji dashi, ganin da yake gani da shi, kafar da yake taku da ita da hannun da yake kamu da shi, wannan hadisi ne ingantacce kan sunna da shia bakidaya, Da ayar da ke cewa: hannun Allah na kan hannun wadanda su ka yi wa Manzo (SAW) mubayi'a? Ya zasu yi da ayar da ke cewa; "duk wanda ya zama makaho a nan a lahira ma makaho ne kuma ya bata daga kan tafarki madaidaici? Manyan malaman da mu sa sani a Saudiyya wadanda su ke makafi ya kenan? Shin ya na nufin a lahira ma za su tashi makafi kena? Cakuda kalmar "wilaya' duk da dai wu na son 6ata ma'nar gadir ne, (duk da cewa wannan kalmar hatta wajan wasu daga shia ta dan samu tazgaro amman ba kamar yadda wahabiyawa ke akkasa ta ba), da misalai da yawa wadanda basu da amsar su.
Kashi na uku na nan tafe in Allah ya so