Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
UMMUL BANIN Ummul Banin kuma ana ce mata Fadima Kilabiyya wacce ta rasu a shekara ta 70 bayan hijira, ita ce matar imam Ali (a.s) wacce take Uwa ga sayyidi Abbas gwarzon mayakan nan na kare addinin Allah kuma kwamandan rundunar Imam Husain (a.s) a Karbala mai rike tutarsa.
Babanta shi ne Huzam, tana daga cikin mata masu imani da sadaukar da kai, da jarumtaka, an ruwaito cewa bayan wafatin sayyida Zahara (a.s) sai Imam Ali (a.s) ya gaya wa dan'uwansa Akil cewa ya duba nasabar kabilun larabawa ya samo masa mace mai nasaba madaukakiya, wacce take da dangi masu daraja, da sadaukantaka, domin ta kawo masa 'ya'ya gwaraza masu jarumtaka, sai Akil ya yi masa bayanin Fadima da aka fi sani da Ummul Banin. Ya gaya wa Imam Ali (a.s) cewa: A tsakanin kabilun larabawa ba mu da wani gida da ya kai gidansu jarumtaka.
Wannan mata ta haifa wa Imam Ali (a.s) 'ya'ya masu jarumtaka da sadaukarwa, kuma ta tarbiyyantar da su suka kasance masu biyayya ga Imam Husain (a.s) har sai da suka yi shahada tare da shi a karbala, wadannan 'ya'ya su ne; Abbas, Ja'afar, Abdullah, da kuma Usman.
Da yake ba ta samu halartar Karbala ba, yayin da mai bayar da labarin abin da ya faru ya zo Madina ya samu ganin ta, yana son ba ta labarin kashe dukkan 'ya'yanta sai take ce masa: Ka katse mini jijiyar zuciyata, duk abin da yake karkashin kasa fansa ne ga ran Abu Abdullah (Imam Husain) ba ni labarin Imam Husain (a.s)?
Idan mun duba sosai zamu ga ba ta bayar da wani muhimmanci ba kan 'ya'yanta, ita dai burinta ta ji cewa Imam Husain (a.s) ya kubuta, don haka ne ma ba ta muhimmantar ba sai jin halin da Imam Husain (a.s) yake ciki. Bayan wannan lamarin mai tsananin bakin ciki ne sai ta kasance tana zuwa Bakiyya tana kuka kowace rana da ita da jikanta Ubaidullah dan Abbas tana yi wa Abbas kirari da cewa ba don an yanke hannyensa ba, da babu wani mayaki da ya isa ya kusanto wurinsa .
Ummul Banin ta kasance mai tsananin girmamawa ga Imam Ali (a.s) da kuma sayyida Zahara (a.s) da 'ya'yansu musamman Imam Hasan da Imam Husain (a.s), girmamawar ta kai ga cewa yayin da ta zo gidan sai da ta nemi izininsu domin tana ganin gidan su ne, kuma tana ganin kanta a matsayin mai hidima ce garesu. Da yake ita ma sunanta Fadima, sai ta gaya wa Imam Ali (a.s) da cewa kada ya kira ta da wannan sunan, domin ba zata iya jurewa bakin cikin da wadannan yara wato Imam Hasan da Imam Husain da Zainab (a.s) zasu ji idan ana tuna musu da wannan sunan na babarsu mai tsarki da daraja da ta yi wafati. Ta ce masa: Idan Zainab ta ji wannan sunan, zuciyarta tana kadawa ta dauki zafi saboda bakin cikin tunawa da babarta, a lokacin ne ya sanya mata suna Ummul banin, wato Uwar gwarazan 'ya'ya masu 'yanci.
A yayin da ta ji labarin shahadar 'ya'yata gaba daya, sai ta samu yankewa ta ce: Dana fansa ne ga Husain dan Fadima (a.s), aminci ya tabbata gareka. Wannan uwa mai cika alkawari, da ladabi, da soyayya da kauna, Ummul banin aminci ya tabbata gareka, sai ta hana a kira ta Ummul banin, wato tana hana kiranta da Uwar 'ya'ya, domin duk an kashe 'ya'yan a Karbala, don haka ne sai aka takaita kiranta da Uwa kawai.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Tuesday, May 25, 2010