Abdullah dan Saba
  • Take: Abdullah dan Saba
  • marubucin: Sheikh Waili
  • Source:
  • Ranar Saki: 14:57:19 1-9-1403

Abdullah dan Saba

SHEIKH WA'ILI
Fasali Na Biyu
Abdullahi Bin Saba'
Duk dayawan masdari da su ke magana a kan Shi'a da kuma hadarin yin rubutu a kan lamarin akida, da kuma dukkanin yadda hakikanin Shi'a ya ke a sarari ta hanyar muassasoshi da kuma ayyukan na akida, da masallatai da suke ta maimaita kalmar kira zuwa hadin kai dare da rana, tare da dukkanin wadannan, mu ba mu gushe ba muna ganin mai yin rabutu a kan Shi'a yana barin wannan gaskiyar a bayansa kuma ya na juya fuskarsa zuwa rubuce-rubucen mutanen da su da wadanda suka gabace su, sun ta rubuta abubuwan da ba ingantattuba sabo da dalilai daban-daban maimako su koma zuwa litattafan Shi'a kansu, sai mu ga suna koma wa zuwa maganganu da rudani ya kirkira, sannan keta ta haifo su, sannan kuma kiyayya ta halitto su, kuma ta yiwu ma jahilci ya zama daya daga cikin dalilan samun su, daga cikin abin da wadannan marubutan suka raya shi ne cewa, akidojin Shi'a wani mutum ne bayahude mugu mai dasisa ya kirkiro su a cikin farfajiyar malamai wanda ake kiran sa Abdullahi dan Saba'.
Wannan bawan da aka kaddaro shi (a ka yi mutum- mutumin sa) lamarin sa mai ban mamaki ne, wasu matane sun sana'anta shi kuma suka kirkire shi kirkira, kuma suka ba shi siffofin da suka gajiyar da dan Adam a tunani, kama suka kirkiro masa damar yin abu irin wanda ba zai yiwu a jingina shi ba sai ga ifritan da muridan aljanun nan na cikin tatsuniya, kai harma da abin da al'umma mai karfi ba zata iya cimma sa ba sun jingina masa, ballana tana kuma mutum daya, lalle irin wannan maganar kan dakin tunanin mukafin ta ta zama tatsuniya a cikin tarihin mu, kuma da sannu zamu gani! Shin wane ne ya kirkiri Abdullah dan Saba'? kuma waye shi? Kuma me ya aikata? kuma saboda me yake da alaka da Shi'a.

Wa ya Kirkiri Abdullah Bini Saba'
Lalle wnada ya ke so ya san asalin inda aka haifo Abdullah dan Saba', zai samu cewa a ruwayoyin Dabari ne, kuma ruwayoyin Dabari a wannan mahalli sun jingina da majingina biyu ne, wadanda sune:
A- Majingina ta farko:
Saifu dan Umar, kuma ga abin da masu ruwaya suka fadi a kan sa, da kalma guda kuma iri daya.
Ibn Hibban yana cewa: Saifu dan Umar ya kasance yana ruwaito kirkirarrun hadisai daga amintattu, kuma sun ce ya kasance yana kirkirar hadisai, kuma an tuhumce shi da zindikanci, kamar yadda Hakimun Nisaburi ya ruwaito a a kan sa cewa an tuhumce shi da zingikanci kuma shi fadadden mai ruwaya ne, kuma Udayyu yana fadi game da shi, cewa sashin hadisan sa mashhurai ne kuma dukkaninsu munkarai ne ba a la'akari da su, kuma ibn Mu'in yana fadi game da shi mai raunanannun hadisai ne babau alheri a tare da shi, kuma Ibn Khatam ya ce: Abin barin hadisan san sa ne, kuma maganar sa tana yin kama da ta Wakidi. Kuma abin Dawud ma'abocin Sunan ya ce shi ba komai ba ne, kuma Nisa'i ma'abocin Sunan ma ya ce shi mai rauni ne, Saifu dan Umar abin bari ne, kuma an tuhumce shi da kirkirar hadisi da zindikanci kuma ya kasance mai yawaita kire.
B- Sariyyi dan Yahya kamar yadda Dabari ya kira shi kuma ba shi ne Sariyyi dan Yahya Sikka (amintacce) ba, domin Sariyyi dan Yahya amintacce zamanin sa ya rigayi zamanin, Dabari ya rasu a a shekara ta 167 BH. A yayin da shi kuma Dabari an haife shi a shekara ta 224, bambancin da ke tsakaninsu shekara hamsin da bakwai ne (57), kuma masu ruwaya ba su da Sariyyi dan Yahaya banda shi, don haka ne ma masu raunatawa da adaltarwa suka hasashi cewa lalle Sariyyi din da Dabari yake rawaitowa daga gare shi dole ne ya zama daya daga cikin wadannan guda biyun: Kuma kowanne daga cikin su makaryaci ne, sune Sariyyu dan Isma'il bahamdane bakufe wannan ne na farkon su, na biyun su shi ne, Sariyyi dan Asim bahamdane wanda ya sauka a Bagdad, wanda ya rasu a shekara ta 258, wanda shi ne wanda Ibn Jarir Dabri ya riska, kuma ya zauna da shi sama da shekara talatin. Kuma dukkanin wadannan lalle ma'abota hadisi sun karyata su, kuma sun tuhumce shi da kire.
Ma'abocin Tahzibul tahzib ya ce su (su biyun) makaryata ne, haka ma mai Mizanul i'itidal, da mai Tazkiratul maudu'at, da mai Lisanul mizan, da wasunsu kuma sun tuhumci daukkanin su da kirkirar hadisi kuma mai karrtu zai iya komawa zuwa masdarorin da muka ambata a karkashin tarjamar wadanda muka ambata. Masu nakadi sun ce: Dabari yana da hadisai dari bakwai da daya wadanda suka shafi lokacin halifancin halifofi uku kuma sanadan wadannan hadisan dukkanin su daga Sariyyu makaryaci suke, shi da kuma Shu'aibun da ba a san da samuwar sa ba da kuma Saifui makirkrin hadisi wanda aka tuhuma da zindikanci.
Daga cikin wadannan ruwayoyinn akwai ruwayar dake dauke da halayen Abdullahi dan Saba' kuma sanadinsa daga shu'aibu, sai Saifu dan Umar, kuma dukkanin wadanda suka yi rubutu a kan Abdullah dan Saba' zaka samu ya jingina ne da dabari kuma daga gare shi yake dauka kuma gare shi ya jingina daga nan ne zaka san gwaurgwadon abin da ke tattare da lamarin Abdullahi dan Saba' na daga tabbaci da gaskiya, a ra'ayi na yana daga cikin wargi mu tsaya muna waiwayar da fusakun wadannan da suka dage a kan samuwar sa da kuma abin da ya tsaya da shi na daga ayyuka, domin naga suna ta kokarin samar da shi, duk da cewa a gaske bai zama samammen ba, ba don komai ba sai don wasu abubuwa da suke cikin zukatan sa.

1- Waye Abdullah dan Saba'
Domin sanin hakikanin Abdullah Dan Saba' da sannu zamu fara da mububbuga ta asasi wato tarihin Dabari sannan in biyo bayan sa da sauran masdarori kuma da sannu zan cirato fadin Dabair ta hanyar abin Abu Zuhrah ya cirato, ya ce: Abdullah dan Saba' ya Kasance Bayahude ne daga cikin mutanen San'a' Babarsa bakace, sai ya musulunta a lokacin Usman sannan ya yawaita garuruwan musulmai yana kokarin ya batar da su, sai ya fara da garuruwan Hijaz sannan Basra sannan Shama, bai sami ikon cimma abin da yake so ba awajen wani daga cikin mutane Sham, sai suka fiatr da shi, har ya zo Misra sai ya ce da su, a irin maganganun da yake yi mamaki ya tabbata ga wanda yake raya cewa Isa zai dawo kuma yake karyata cewa Muhammad zai dawo, kuma lalle Allah Madaukaki yana cewa "Lalle wannan da ya farlanta maka Kur'ani zai komar dakai zuwa tashi bayan mutuwa" Alkasas/85.
Sannan lalle Muhammad ya fi cacantar dawowa fiye da Isa, sannan ya ce bayan haka lalle anyi Annabawa dubu kuma kowane Annabi yana da wasiyyi kuma Ali shi ne wasiiyin Muhammad kuma Muhammad ne cikamakin annabawa, Ali kuma cikanmakin wasiyyai.
Ana akwai wasu nukdodi da ya fadi, in so in karfafe su domin in gwama su tare da wasun su, shi ne cewa: Na farko dai shi dan bakar mace ne, na biyu kuma shi dan mutanen San'a' ne, na uku kuma shi ne yana karfafa dawowar Manzo (s.a.w) wannan duniyar, na hudu kuma yana cewa Ali wasiyyin Annabi ne, na biyar shi ne cewa ya musulunta a lokacin Usman, bayan wannan kuma, bari mu kuma komawa wajen abu zuhra a dai wannan littafin nasa abin ambato, Tarihu mazahibul islamiyya a wani wajen yana cewa, Abdullah dan Saba' ya kasance bayahude, daga cikin mutane Haira ya bayyana musulumtar sa sai yafara yada cewa lalle ya samu a cikin attaura cewa: Lalle kowane Annabi yana da wasiyyi kuma lalle Ali shi me wasiyyin Muhammad, kuma lalle Ali yaso ya kashe shi sai Abdullah dan Abbas ya hana shi. Sai ya kora shi mada'in a maimakon kashe shi.
Tsakanin wadannan yan tsokaci kan guda biyu akwai banbance banbance masu zuwa wadanda na kallae so kallo na nazari su ne:
Cewa shi dan San'a' ne, a magana ta biyu kuma shi dan Haira ne, da kuma cewa ya musulunta a lokacin Usman a magana ta biyu kuma ya bayyana musuluncinsa kuma bai tantance lokacin musulumtar sa ba, da kuma cewa Imam Ali ya yi niyyar kashe shi kamar yadda ya fadi a magana ta biyu a yayin da bai ambaci hakan ba a ta farko, kuma lalle yana daga cikin abin yin tsakaci a kan sa sanya lamarin wasiyya na cikin attaura, a yayin da a magana ta farko bai ambaci, matsamar wannan tunanin ba, mu lura da wadannan abubuwan domin muga abin da ke tsakanin wadannan maganganun na daga banbamce- banbamce, da kebance- kebancen da suke cin karo da juna.
2- Muhammad Farid Wajdi a Cikin Da'iratul Ma'arif
Saba'iyyawa mabiyan Abdullahi dan Saba' wanda ya kai mutuka wajen temaka wa Ali kuma ya raya cewa Ali Annabi ne sannan ya wuce mutuka ya raya cewa shi Allah ne, kuma ya kira wasu daga cikin mutanen Kufa zuwa hakan sai labarin su ya isa ga Ali sannan ya yi umarni da a kona wasu daga cikin su, sannan sai ya ji tsoron kada wasu su yi masa tawaye idan ya kona sauran, don haka sai ya kora Abdullah dan Saba' zuwa Mada'in, yayin da aka kashe Ali sai ya raya cewa ba Ali aka kashe ba, kadai shedan ne ya bayyana a irin kamar sa kuma wadannan jama'un suna ganin cewa Mahdin da ake sauraro Ali ne ba wani ba, kuma dan bakar mace a da cen ya kasance bayahude ne daga cikin mutane Haira, sai ya bayyana musulunci kuma ya so ya zama yana da matsayi da shugabanci a wajen mutanen kufa, sai ya ce musu, lalle ya samu a cikin attaura cewa lalle kowane Annabi yana da wasiyyi kuma lalle Ali ne wasiyin Muhammad (s.a.w) yayin da suka ji hakan sai suka ce da Ali lalle yana daga cikin masoyanka sai Ali ya daga martabar sa, sannan ya zaunar da shi a karkashin darajar mimbari yayin da labrin gullanci sa ya isa zuwa gare shi sai ya yi kokarin kashe shi, sai Abdullah dan Abbas ya hana shi, sai ya kora shi zuwa Mada'in.
A wannan maganar kuma shi dan Hairan ne ba Sana'a ba kuma shi dan Bakar mace ne kuma lalle Imam Ali ya yaudaru da shi, kuma lalle ya yi da'awar Annabta ga Ali sannan kuma ya yi da'awar allantaka a gare shi!.
Daga nan za a iya tattara wannnan cakude mai ban mamaki, sai dai ta yaya ta za a iya hada tsakanin wannan tafarki mai ban mamaki, kuma ta yaya zai yiwu a lokaci guda mu hada cewa yana jingina masa allantaka kuma yana cewa shi wasiyyi ne, zan bar wadannan kaddare- kaddaren ga hankula da kwakwalen da suka gagara kamar su Muhammad Farid Wajdi da makamantan sa na daga cikin wadanda suke jagorantar takunkumin al'umma a cikin mabambantan al'adu, kuma godiya ta tabbata ga Allah wanda ba wanda ake godewa akan wani abin ki in ba shi ba, kuma kada ka yi gaggawa ya kai mai karatu, da sannu zaka ji wasu abubuwan daga cikin maganganu masu zuwa wadanda suka ci karo da abin da ya gabata.

3- Ahmad Adiyya
Ibn saba' shi ne shugaban gungun saba`iyyawa daga cikin Shi'a kuma shi ne Abdullah dan Saba' ya kasance daga cikin yahudawan San'a' kuma ya bayyana musuluncinsa a lalokacin halifancin Usman, kuma ana kiran sa dan bakar mace ya ciratu zuwa madina kuma ya yada wasu maganganu da ra'ayoyi wadanda suka saba da hakikanin musulunci kuma wadanda suka samo asali daga yahudanci da akidar farisawa, wacce ta yadu a yamen, ya bayyana a matsayin wanda yake temakawa Ali kuma ya yi da'awar cewa lalle kowane Annabi yan da wasiyyi kuma lalle Ali ne wasiyin Muhammad kumar yadda ya yi da,awar cewa a cikin Ali akwai wani bangare na Allantaka ya kewaya sasannin Irak yana mai yada manufar sa sai Abdullah dan Amir ya kore shi daga basra sai ya sauka a kufa sannan ya cusawa mutane kin Usman, sannan ya ciratu zuwa Damashaka a lokaci Ma'awuya a cen ne ya hadu da Abi Zarrul Giffafi ya kwadaitar da shi a kan yin tawaye yana mai da'awar cewa mawadata ba su da hakkin tara dukiya, sai aka fitar da shi daga Sham sai ya sauka a Misra sai masu kin Usman suka taru a gefen sa, daga cikin su akwai Muhammad dan Abubakar da Abu Huzaifa, kuma ya kirkiri maganganu da sunan Ali wadanda shi bai fadi ba, kamar da'awar sanin gaibu, bayan shahadar Ali sai ya ce sam ba a kashe shi ba kuma da sannu zai dawo, ta haka ne ya kirkiri tunanin raja'a a cikin Shi'a.
A cikin wannan maganar da Adiyyatullah ya ruwaito akwai abubuwa masu zuwa,
Daga ciki akwai cewa dan Saba' ya hada wasu akidu daga akidun Yahudawa sai ya cirato su zuwa shi'anci, sannan daga cikin su akwai raja'a (dawowa), sai dai raja'ar a nan ga Ali take, ba ga muhammad ba, kamar yadda yake a wajen abu Zuhra. Daga ciki akwai cewa ya jinginawa Ali wani bangare na alantaka, ba dukkanin ta ba, ta yadda zai iya yiyuwa a hada tsakanin kasancewar sa Allah ta wani bangare da kuma kasancewar sa wasiyin Manzo (s.a.w) ta wani bangaren daban ke nan, daga ciki akwai gano kwazo da iko na banmamaki irin na Abdullahi bin Saba' ta yadda ya zama dukkanin twayen da a ka yi wa Usman da Ma'awiyah sakamakon aikinsa ne.
4- Da irin wannan salon mai cin karo da juna, kowanne daga cikin Ahmad Amin a cikin Fajril islam da kuma Muhammad Bin Yahya a cikin Attamhid wal bayan fi maktali Usman da kuma Zirkali a cikin A'alam, suka yi bayani.
Ba ina so in tsawaita maka ba ne, domin kowane na baya yana dauka daga wanda ya gabace shi, ba tare da tantancewa ba, al'amarin da ya kai ga samun tsakudedeniya da cin karo a cikin ruwayoyi, zaka same shi a cikin wadannan labaran wani lokaci daga cikin mutanen Haira wani lokacin kuma daga matanen San'a'. A wajen sa Ibn Hazam da Shaharustani da makamancin su kuma, shi dan baker mace ne, a yayin da Ibn Dahir Babagdade a cikin Alfarku bainal furuk da Attabsiratu fiddini yana ganin cewa, dan baka wani mutum ne daban, ba Abdullahi dan Saba' ba ne.
Kuma a wasu ruwayoyin yana yin da'awar raja'a ga Manzo a yayin da kuma a wasu ruwayoyin yana yin da'awar ne ga Imam Ali kuma awani lokaci yana yin da'awar cewa Ali yana dauke da wani bangare na allantaka, a wata ruwayar kuma shi cikakken ubangiji ne, a wadannan ruwayoyin zamu samu cewa Ali ya kona gullat ba tare da yana jin tsoro ba, a wata ruwayar kuma yana jin tsoron ya kona dan baka, tare da cewa shi Bayahude ne mutumin gari ba wanda lura da ghi, haka muke samun kanmu a cikin wannan tsakudedeniya mai rudani, mafi mihimmanci wannan lamarin a mahangar mu shi ne cewa wani lokaci zaka ga an bayyana shi a matsayin mai yin kira domin bayyana falalar Ali kawai, wani lokaci kuma sai kaga an bayyana shi a mastayin mai harzuka mutane a kan Usman, kuma wanda ya kirkiri mihimman akidojin Shi'a na daga abin da ya shafi wasiyya da sanin gaibun Imamai da kuma ra'ayin raja'a, kuma wadannan al'amuran guda biyu su ne kwaunduwar madui'n. lalle wanda ya kagi abin kunyar Abdullah dan Sa'ba a ya jefi tsuntsu biu da hage daya, kuma wadannan abubwan duga biyu ya nufata:

Na daya: Usman an kashe shi ne sakamakon harzukawar saba'iyyawa ba wai ya yi wasu abubuwan da ya sa mutane suka kyamace shi kuma suka hadu a kan kashe shi ba, alhali a cikin su akwai sahabban Annabi, kamar yadda tarihi ya ambata dalla-dalla. Abin da ake so a ce shi ne wani bayahude ne da ya ke tsananin kin musulunci ya motsa musulmai sai suka bi shi saboda wauta ba tare da wani tunani ba, har sai da suka yi wannan aika-aikar har suka kashe halifa ba tare da ya yi wani laifi ba.
Na biyu: Fadin cewa Akidar Shi'a ba ta da alaka da musulunci ta samo asali ne kawai daga wannan gagararran bayahuden Abdullah dan Saba', ka ga ke nan Shi'a Yahudawa ne da ba su da sila da musulmai. A bisa kowane hali, wannan rudanin ta hanyar wannan tsararran yanayin na Abdullah dan Saba' ya sa masu bincike sun fadaka kuma ya kai su ga su idanuwansu a kan wannan tatsuniyyen mutumin, sai suka fitar da ra'ayoyinsu kuma suka karairaya wannan alkadarin sannan suka shelanta wa mutane karyar wannan labarin na kire wanda babu wata hanya da za a iya hada tsakanin abin da sasannin labarin ya kunsa, sai ga hakika ta fara bayyana a hankali a hankali kuma hadafofin aka boye a bayan wannan tatsuniyar suka bayyana a sarari, kuma da sannu zan fada maka ra'ayoyin da yawa daga cikin masu warwara, bayan na gaya maka nawa ra'ayin a kan wannan masa'alar domin mu isa zuwa zuwa bayyanar sura a kan wannan lamarin ko maudu'in.
?
Ra'ayinmu Kan Abdullahi dan Saba'
Mu dai muna ganin mutum ne na rudu kirkirarre kuma muna kafa hujja a kan cewa shi tatsuniya ce kawai saboda abubuwa masu zuwa:
1- Yin sabani a kan cewa shi ne dan bakar mace, ko kuwa, tare da cewa wanda ya aikata dukkanin wadannan musibu shi ne dan bakar mace, kuma Ibn Dahir da Isfarayini suna cewa lalle dan bakar mace wani mutun ne daban da ya yi tarayya da Abdullah dan Saba' a cikin abin da ya ke da'awa.
2- Yin sabani a kan lokacin bayyanar sa, Dabari ya tare da wasu jama'a sun tafi a kan cewa ya bayyana ne a lokacin Usman a yayin da wasu kuma suka tafi a kan cewa ya bayyanan ne a lokcin Ali (a.s) ko kuma bayan mutuwarr sa, daga cikin su akwai Sa'id dan Abdullah ba'ash'are, a cikin littafinsa Makalat, haka ma Ibn Dahir a cikin Alfarak bainal frak, da wasun su masu yawa.
3- Yin maganganu masu karo da juna a cikn ruwayoyin dangane da aslin kiran sa, a yayin da Dabari da wasu jama'a suke ganin cewa lalle da'awar sa ta takaitu da gullatanci, da kuma kira zuwa taimaka wa Ali da ma dai dukkanin abin da ya shafi Ali, a yayin da kuma muka sami wasu daga cikin `yan baya suke ganin cewa daidai da yadda masdarin su su ke cewa lalle ya na da'awar da yake yi a kowane gari. Muhibbud dinul Khadib yana cewa bisa isnadin da ya ambata.
Dago cikin kaifin basirar Ibn Saba' da makircin sa, ya kasance yana yada kira zuwa Ali a cikin mutanen Fusdad, a cikin mutanen Kufa kuma yana yada kira zuwa Dalhatu, a cikin mutanen Basara kuma ga Zubair.
4- Lalle sashin ruwayoyi sun ambaci cewa ya takaitu a kan yada falalar Ali a yayin da wasu kuma suka tafi a kan cewa ya kasance yana harzuka jama'a a kan Usman yana ta kafa dasisa, kuma shi ne ma ya ingiza Abuzar zuwa yin tawaye, ko dai ga Mu'awuya ko kuma Usman a wasu ruwayoyin.
5- Wadanda suka kirkiri kissar dan Saba' ba su fada mana dalilin da ya sa Usman ya kyale shi ba shi da mabiyan sa tare da cewa sun daddaki wadanda suka yi fito na fito tare da mafi munin tsanantawa da rashin tausayi, alhali suna daga cikin mafi zababbubu daga cikin Sahabbai. Kamar Ammar da Ibn Mas'ud, da makamancin su.
6- Saboda me ingantattun masadarori suka wofinta da ga ambaton wannan kissar ta Dan Saba' kamar Balazuri da Ibn Sa'ad da makamancin su daga cikin wadanda ake dogaro da maganganunsu.
7- Lalle ruwayar Abdullah Dan Saba' makirkira kuma makaryata ne suka ruwaito ta kamar yadda muka ambata a baya.
8- Daga cikin abin da zai dada fito da kiren a fili kasantuwar cewa ba wannan ce kadai kissar ta karya da a ka jinginawa Shi'a ba, lalle wannan ba komai ba ce face sai wani dan bangare daga cikin karerakin da a ke yi wa Shi'a, wanda da sannu zamau bayyana maka su a nan gaba, kuma mukafa maka dalili a kan kasantuwar su gabaki daya karya ce. Har kasan cewa kissar Abdullah dan Saba' ta fito ne daga macira daya da kuma ainihin manufa guda. Amma yanzo bari mu dan bijiro da ra'ayoyin mawarwara (masu nakadi) da masu bincike wannan kissar domin mu isa zuwa gaskiya.

Ra'ayin Daha Husain
Dakta Daha Husain ya bijiro da surar da aka kera wa Abdullah dan Saba' sannan ya yi kaca-kaca da ita bayan warwara mai zurfi, kuma ya tuke a kan cewa lalle Ibn Saba' mutum ne nawahami da makiyan Shi,a suka kirkira kuma ya karfafi ra'ayin sa da abubuwa masu zuwa:
Na daya: Lalle dukkanin masana tarihi amintattu ba su ruwaito kissar Abdullah dan Saba' ba kuma ba su fadi komai a kan sa ba.
Na biyu: Madogarar labarinsa mutum daya ne kawai, shi ne Saifu dan Umar kuma shi mutum ne da aka san shi da karya, kai an tabbatar kuma an yanke a kan cewa shi makirin hadisai ne.
Na uku: Abubuwan da aka jingina wa Abdullahi dan Saba' suna bukatar mu'ujizojin da suka wuce hankali, kamar yadda ya zama dole musulman da Abdullah dan Saba' ya yaudara kuma ya sihirce su zama wadanda suke zartar da hadafofinsa ba tare da ja-inja ba, da kai mutuka da rashin ko in kula.
Na hudu: Rashin samun wani gamsashshen bayani a kan yin shirun Usman shi da wakilan sa, tare da cewa sun doki wanin sa daga cikin masu yin ja-in-ja, kamar su Muhammad dan Abi Huzaifa da Muhammad dan Abubakar da Ammar da makamancin su.
Na biyar: Labarin konawa da kuma ayyana irin sunnar da dan Saba' ya tsira da ga konawa a sakamakon ta, ta wufinta daga cikin litattafan tarihi ingantattu, kuma babu iri-irin alamar ta a cikin su.
Na shida: Rashin samun wata alama ta Abdullah dan Saba' da jama'ar sa a yakin Siffin da yakin Nahrawan, kuma lalle Daha Husain ya tuke a kan cewa: Hkika dan Saba' mutum ne da makiya Shi'a suka tanade shi domin yakar Shi'a, kuma ba samamme ba ne a sarari, kuma da yawa daga cikin marubutan yamma sun dace da Daha Husai a kan wahamcin samuwar Abdullahi dan Saba', daga cikin su akwai:
Ra'ayoyin Marubutan Yamma
1- Dakta Barnad Luwuis: Yana cewa: Sai dai bincike ya tabbatar da cewa lalle rigyangyantu ne da `yar tsere, da aka shirya a kan abubuwan da suka faru, kuma lalle wannan mutumin - wato Abdullahi dan Saba'- wani mutum-mutumi ne da aka misalta shi bisa abin da ya gabata, kuma ma'abota hadisan karni na biyu bayan hijira suka sauwara shi bisa yanayin su, da kuma irin nasu tunanin da yake yawo a wannan zamanin.
2- Falhozan: Ya tafi akan cewa, mutum-mutumin da kiraye-kiraye da kuma abubuwan da ake jinginawa ga dan Saba' yana daga cikin kiren karyar mutanen da suka zo daga baya, kuma lalle ya tantance nassosin kuma ya karanto yanayin daga karshe ya zo da warwara mai zurfi.
3- Kayitani: Ya yi shakka a cikin samuwar Abdullahi dan Saba' kuma ya yi magana a kan abubuwan da ake jingaina masa na daga manya- manyan ayyuka, da kuma irin wannan tashifadin bisa irin wannan tunanin da kuma tsarin, ba zai taba yiyuwa duniyar larabawa wadda aka sani ta shekara talatin da biyar, wacce take tafiyar da mulkin ta bisa tsarin `yan'ubanci, lalle kacokaf lokacin sa ya saba da lokacin abbasawa na farko.
Ra'a'yoyin Wasu Daga Cikin Malaman Musulumci Akan Dan Saba':
Akwai wasu ra'ayoyin akan Abdullahi dan Saba' wadanda suke kaikawo a tsakanin samuwar sa da rashin ta da kuma rashin alakar sa da Shi'a, da kuma tsakanin rashin gasgata abin da ake jinginawa a gare shi domin yana daga cikin abin da ba mai yiwuwar faruwa ba ne daga dan Adam na dabi'a ba, kuma da tsakanin jingina wadannan ayyukan ga wani mutum na daban wanda aka kira da dan bakar mace, don haka bari mu ji wadannan ra'ayyoyin.
A- Muhammad kard Ali ya fadi a cikin Hudadush Sham:
Amma abin da wasu daga cikin marubuta suka tafi a kan cewa mazhabar Shi'a tana daga cikin bidi'ar Abdullah dan Saba' wanda aka sani da dan Baka, wannan rudu ne da karancin ilimin sanin hakikanin mazhabarsu, kuma wanda ya san matsayin wannan mutumin a wajen Shi'a da kuma barrantar su daga gare shi da maganganun su da ayyukan su, da kuma maganganun malaman su a wajen sukar sa ba tare da sabani ba a tsakanin su a cikin wannan, zai san mutukar gaskiyar wannan maganar.
3- Dakta Ahmad Mahmud Subhi A Cikin Nazariyyatul Imamah:
Ba abin da zai hana Yahudawa su yi amfani da fare- faren da suka gudana a lokacin Usman ba, su kara mata huruwa kuma su dada zuga mutane akan Usman, kai har ma su yi kira a kan tunanunnukan da ba a san su ba, sai dai abin da ya rigayi lokacin sa, shi ne cewa, shin dan Saba' yana da irin wannan tasirin mai tsananin da har zai iya haifar da wannan rarrabar ta akida tsakanin wani bangare mai girma daga musulmai?.
4- Daktoci guda biyu, Aliyul Wardi Da Kamilush Shaibi sun hadu a kan abin da zai zo.
Lalle wanda ake nufi da dan Baka Ammar Bin Yasir ne, domin yana da girma da matsayi a cikin Sahabbai kuma ya kasance a gaba- gaban yan tawaye ga Usman, kuraishawa ba sa so su ajiye shi daura da Uaman kuma a gefen Ali, domin yana rinjayar da dangaren Ali ya kuma rusa na Usman, don haka sai suka yi masa ramzi (suka bashi take) suka ambace shi da dan Baka domin Babarsa Baiwa ce Baka kuma babu wani dan Baka ba shi ba.
Ra'ayin daktocin nan guda biyu ya yi daidai da ra'ayin Asfarani da Ibn Dahir Babaadade wanda mukayi nuni a kan sa a cikin abin da ya gabata a yayin da muke yin bayani a kan ayyana hakikanin dan Saba'
Bayan wannan `yar jaular (kewayen) a kan ra'ayoyin, ya bayyana a sarari cewa babu samuwar dan Saba' domin sallamawar mu akan samuwar sa ya na bukatar mu wurgar da hankulan mu, kuma tafarkin bincike na ilimi ya ki yarda da samuwar sa domin masdarorin sa sun saba, kuma saboda wadanda suka halitto Abdullahi dan Saba' sun halitto masa yan'uwa na daga da'awoyin da dasannu zamu dora hannun ka a kan sun a nan kusa- kusa, duk da cewa da sannu zasu girgiza tunanin ka su kuma rusa sikkar ka (amincin ka) da wadanda kake ganin su daga cikin kololuwa a Musulumci, domin abubuwan kece al'adan da ake jinginawa dan Saba' ba zai taba yiyuwa a gasgata su ba, kuma saboda yin shurun Usman a kan sa yana da ban mamaki tare da cewa ya nisanta (kora) Abuzar zuwa Rabza tare da cewa Abuzar yana daga cikin mamaya-manyan Sahabbai, ba don komai ba sai don Abuzar ya kasance yana da ra'ayin a kyautata rayuwar Musulmai a lokacin Usman, don me ake yin irin wannan mafarkin a kan dan Saba', kuma saboda kasantuwar Ali mai tsauri ne a kan lamarin Ubangiji ta yaya zai yi shiru a kan dan Saba' kuma ya ki kona shi kamar yadda ya yi wa wanin sa, kuma saboda ma'awiya shi ne wanda ya ke kashewa a sakamakon tuhuma da zato, ta yaya a ka yi ya yi shiru game da lamarin dan Saba' alhai shi ne wanda ya aika Busir ya kaiwa makiyan sa hari kuma harin ya kai ga kashe mutun dubu talatin, dukkanin irin wadannan abubuwan na labarin Dan Saba' suna daga cikin dalilan da suka sa ya zama labari abin kirkira, kadai an kikire shi ne domin manufar da muka ambata a baya domin a sa shi a matsayin masdarin ko tushen na akidun Shi'a baki dayan ta, kamar yadda kowanne daga cikin Muhyuddin Abdulhamid a cikin ta'alikin da yayiwa littafin Makalatul Islamiyyin da kuma Ali Samin Nashshar a cikin littafinsa Nasha'atul Fikiril Falsafi, kuma kowanne daga cikin Aliyun Nashshar da Muhyid Din ba sa daga cikin wadanda suka jahilci akidun Shi'a, ko kuma wadanda ba su da hanyar da zasu sami masdaran su ba, alhali a inda suke akwai masdaran da suke dauke da dukkanin abin da ake bukata, kuma ga ayyakan nan na akida a gaban idanun su kuma a sarari ana gabatarwa wanda yake nuna yadda akidar Shi'a take, kuma tare dadukkanin hakan suka rubuta abin da bai yi daidai da amanar tarihi da kuma tarbiyyar Musulumci ba, a kan Shi'a, bai kamata misalin irin wadannan su rika sa rigar masu kawo gyara a cikin mihimman al'amuran musulmi ba wadanda su wadannan bisa hakika, yan saddu ne (masu tare hanya ne) masu wautar da wadansun su, in ba haka ba, ai alamomin tambaya na nan birjik a cikin abin da suka rubuta, a yayin da marubutan da suka san abin da suke yi, su na karfafa cewa lalle labarin dan Saba' kire ne. Ahmad Abbas Salih yana cewa: Abdullah dan Saba' mutum ne na kire ba tare da wani shakku ba, ina shi ina dukkinin wadannan fare- fare, kuma lalle babu wani kokwauto sakarai ne zai yi kokarin halittar wani mutum kamar wannan domin ya ba shi wani irin tasiri a cikin fare- faren da suka kasance, lalle dukkanin abin da aka hakaito na daga labari a kan Abdallahi dan Saba' yana daga cikin kiren mutanen baya domin babu wata hujja ta samuwar sa a cikin litattafai.
Haidar Center for Islamic Propagation
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012