Koyarwar Musulunci
  • Take: Koyarwar Musulunci
  • marubucin:
  • Source:
  • Ranar Saki: 21:22:7 10-10-1403

Da sunana Allah mai rahama mai jin kai

 

Ina muka kwana?.

Game da Musulumci da koyarwar sa dawwamammiya!!!

A yau ne na kammala muku addinin ku kuma na cika muku ni’ima ta.

 

 

   A wane karni muke rayuwa?  Ta yadda har yanzu wahala kawai muke sha ba mu fara amfana da abin da muke shukawa ba, wai shin meye sunan wadannan shekarun wadanda dan Adam yake shude su  yana mai fama da kunci da radadin jiki ?

  Wannan shi ne karni na ishirin da daya!

 Karnin miza’ail da satlait da kuma yin safara zuwa dunuyar wata, karnin da ilimi ya kai kololuwar sa wajen cigaban dan Adam da kuma kere- kere, karnin da tunanin dan Adam da wayewar sa suka kai kololuwa kuma koya ya fara jin cewa shi wani bangare ne na Al’ummar sa yana da hakki kamar yadda kowa yake da shi, kuma mutane suke bashi girman sa.

  Wai shin manenen wannan karnin na ishirin da dayan ne!!!?

  Hakika shi wani gutsure ne daga cikin zamanin da Dan Adam yake rayuwa a doron kasa wanda yake shudewa a kan rayuwar mutane, ba abin da ya shafe shi, shin mutane sun kasance a cikin ci gaba a cikin tunani ne ko kuma ci baya, shin sun hada kan su ne ko kuma sana ta fama da rarrabe-rarrabe da kuma fadace –fadace, babu ruwansa zai ci gaba ba tare da la’akari da abin da yake gudana a cikin rayuwar Dan Adam ba.

  Kuma da sannu karni na ashirin da biyu zai zo kuma rayuwa zata daukaka a cikin sa sama da yadda yake a yanzu, kuma da sannu ci gaban cikin sa zai karu da gaske, sanna zamu dawo muna kallon ci gaban da ya ke cikin karni na ashirin da daya ba wani abin a zo a agani ba. Alhali a farkon bayyanar su mun kasance muna ganin su wani babban lamari wanda ya girmama a cikin kwakwalen mu.

  Kuma da sannu zamu maimaita ainihin abin da muka fada a yayin da karni na ashirin da uku ya zo, kuma hakan zai ta faruwa mutukar motar rayuwar Dan Adam tana garawa a doron kasa.

  Saidai abu daya da baya canzawa duk da wannan ruguntsumin na wadannna canje- canjen masu sauri irin saurin mizayel da kuma yalwa da fadi irin ta satlayit shi ne; Dan Adam, shi ne wannan Dan adam dinnnan wanda yake kawo sauyi da canje-canje ya kuma ci gabantar da shi da irin wannan saurin, kama yana mai kwatanta rayuwar sa daidai da wadannan canje- canjen a cikin hanzari da sauki da kuma kaifin basira, amma shi kansa a daidai wannan lokacin ba zai yiyu ya canji ya shige shi ba (ba zai yiyu ya canza ba).

  Tabbataacce ne shi  ta bangaren dabi’arsa ta mutumtaka, ta bangaren garizar sa, haka ma ta bagaren dangogin adifofin sa, kuma tabbatacce ne shi ta bangaren ginin sa na jiki dana hankali.

  Hanyar da yake kosar da sha’awar sa bata canzawa har abada, kuma haka lamarin yake game da son mallaka da iko, hakama game da yunwa da ci da kuma kishirwa da sha, hakama game da jinsi da kuma jin dadi da wani jinsin, haka ma game da kosawa, da jin dadin kallon abubuwan kallo na dabi’a ko wadanda aka kera da kuma shakar daddadar iska da kuma kanshi.

  Kamar yadda ta bangaren adifar sa babu wata sabuwar adifa da ta haifu a cikin dabi’ar sa ta dan Adam watan wadanda aka saba da su, na daga fushi da yarda da bakinciki da farinciki da radadi da buri.

  Kamar yadda babu wani zamani da zai zo da tsarin jikin mutum zai cenza a cikin sa ko mu same shi da wani yanayi wanda ba lafiya ba kuma ba rashin lafiya ba ko kuma wanin dakikanci da kaifin basira ko kuma mutunm ya shude bisa kan matakan rayuwa wadanda ba yarinta da samarta da manyanta da tsufa a cikin su.

  Hakama ta bangaren hankali babu wani zamani da zai zo da mutum baya neman rabauta a cikin sa, ko kuma baya ganin fifici a matsayin alkhairin da ya cancanta a aikata shi, kuma kaskanci sharri ne wanda ya wajaba a nisance shi, kamar yadda daidai da rana bai taba barin yin sa’ayi a bisa nema kamala ba.

  Wadannan dukkanin lamura ne wadanda suke damfararru a cikin rayuwar mutum, wadanda basa bukatar wani bayani mai yawa, kuma a kafe suke a cikin dabi’ar Dan Adam tun asalin zamanin da aka halicci mutumtaka, kuma da sannu ba za su mutu ba sai da mutuwar sa. Kuma mutum ba shi da wata hanya ta ci gabantar da su ko wadatuwa daga gare su, kuma daga ainihin wadannan abubuwan ne ci gaba ya samo asali, kuma a kan su ne ya ginu kuma har yanzu yake ginuwa, kuma a kan su yake tsaye a iya gwargwadon mutukar sa, kuma bai isa ya wuce su ba har abada a fagen fadadar sa, da yalwatuwar sa da kuma ambaliyar sa. [zamu ci gaba]

 

Daga cikin hadisan hikima na sayyadina Ali (AS)

 

* An halicci duniya domin wanin ta kuma ba’a halicce ta ba domin kanta.

* Ku tuna da yankewar jin dadi da kuma wanzuwar sakamakon ayyuka.

* Mutane makiyan abin da suka jahilta ne.

* Babu wani gari da yafi cancantuwa da kai fiye da wani, mafi alhairi gari wanda yake dauke da kai.

* Wanda ya ke yin kasuwanci ba tare da masaniya (sanin hukuncin sa) ba hakika ya kutsa cikin cin riba.

 

Hajjin ban kwana

A yau ne na kammala muku addinin ku kuma na cika muku ni’ima ta.

 

  Menene amfanin yin bahaci ko Magana a kan halifanci bayan Manzo? kuma waye ma’abocin sa?

 Wannan tambaya ce da take ta maimaituwa a bakunan da yawa daga ciki malamai musamamn masu yin kira izuwa hadin kai!

  Kafin in kai ga bada wannan amsar zan Dan guzurce mu da wata babbar hadisa ta atrihi, wacce take mashhuriyar gaske!!!

A shekkara ta 23 bayan hijira Manzo (SAWW) ya yi hajjin bankwana wanda a cikin sa ya bayyana hukunce – hukuncen addini a dunkule kuma ya gayawa musulmi abubuwanda idan har suka yi riko da su har abada baza su bace ba, kuma dukkanin sihahus sitta sun rawaito wannan hadisin da lafuzza mabanbanta, a inda Manzo (SAWW) yake cewa: “Lalle ni mai bar muku abubuwa biyu ne a baya na nauyaya (masa girma) littafin Allah da kuma Tsatso na, `Yan gigana, lalle Allah madaukaki ya bani labari cewa baza su taba rabuwa ba har sai sun riske ni a tafki, don haka kuyi duba (nazari) bisa yadda zaku halifce ni a cikin su a baya na” a cikin wasu ruwayoyin a kwai karin “Ina tunasar daku Allah a cikin yan gidana! Ina tunasar daku Allah a cikin yan gidana!! Ina tunasar daku Allah a cikin yan gidana!!!”.

  Bayan da Manzo ya  baro maka kafin ya yi nisa, a ya yin da ya karaso wajen wani Dan tafki wanda yake a mararrabar hanyar garuruwa daban- daban, wamda ake kira khum wato GADIR KHUM sai wahayi ya sauka a gare shi daga Allah Ta'ala tare da aya, wacce malaman tarihi da malaman tafsiri suka bayyana cewa itace ayar{یا ایهاالرسول بلغ ما انزل الیك من ربک فانلم تفعل فما باغت رسالته والله یعصمک من الناس  .....} ma’idah aya ta 66. ma,ana: ( Ya kai Manzo ka isar da abinda aka saukar maka daga ubangijin ka idan kuma har baka aikataba to bakaisar da sakon sa ba, kuma Allah zai kare ka daga mutane)

  A wanna lokacin Manzo ya sa aka yi shela aka tsayar da dukkanin wadanda suka wuce gaba daga ayarin da wadanda suke tare da shi kuma aka jira wadanda suke baya sanna yasa aka yi masa minbari, ya tsaya yana mai bayyana abinnda Allah ya umarce shi da shi, Manzo yayi dogon bayani wanda wannan takardar baza ta iya kawo shi a yanzu ba daga ciki akwai cewa “wanda duk  nazama shugaban sa to Ali ma shugaban sa ne, ya ubangiji ka jibinci wanda ya jibing ce shi kuma ka ki wanda ya ki shi, ka karkata gaskiya a duk inda yake…….” Har karshe, wannan hadisa ce da dukkanin malaman tarihi suka rawaito kuma hakama sahihannan duga shida sun fitar da wannan hadisin da lafuzza mabanbanta bisa ma’ana daya.

  Bayan da Manzo ya isar da wannan sakon na wahayi sai aka kuma saukar masa da wannan ayar bayan da ya sakko daga kan minbari: {الیوم اکملت لکم دینکم واتممت علیکم نعمتی ورضیت لکم الاسلام دينا....}  suratul ma’idah/3.  (A yau ne na cika muku addinin ku kuma na cika ni’ima ta a gare ku kuma na yardar muku da muslumci addini….)

  Abin mamaki a nan shi ne zaka ga wasu suna ta kokarin su fassara wanna ma’anar da cewa: wai abinda ake nufi shi ne a so Imam Ali kawai! Wata tanbaya a nan shi ne ta ya ya hankali zai karbi wannan maganar! idan har son ne kawai don me zai bukaci sai an tara mutane, a tsakiyar rana da tsananin zafi kuma har Allah ya yiwa Manzo alkawarin zai kare shi gada sharrin mutanen da ba za su yarda da a binda zai fada ba? Idan har so ne kawai ai ya isa ya gayawa was daga sahabbai su kuma su gayawa sauran kamar yadda misalsalin wadannan hadisan su ke dayawa, kuma ba muji Manzo ya bukaci hawa minbari domin fadar su ba,! Haba!!! Ba muga abinda Allah yake fadi ba; (idan har baka aikata ba to baka ma isar da sakon da aka aiko ka a kan sa bas am- sam,) babu shakka sakon da girman sa yakai ga Allah Ta'ala yayi irin wannan babban hukunci ba Dan karami ne ba, lalle dole ya zama wani sako ne wanda zai amintar kuma ya kare sannan ya tabbatar da ci gaban ginin da Manzo ya fara na al’ummar sa wadanda ba su dade da barin kwanakinsu na jahiliyya da bunne `ya`ya mata da zalunci da kasha-kashen juna da sauran su ba.

  Wani irin hankali ne zai karbi cewa Manzo ya bar duniya bai yi wasicci ba alhali Allah ya wajabta yin wasici, a cikin alkur’ni kuma ya bayyana cewa Annabawan farko sun aikata, sannan a gefe gahadisan Manzo da dama sun zo suna yin umarni da hakan, shin muna so muce Manzo bai yi aiki da abin da Allah ya umarce shi ba, ko kuma shi kadai ne Manzon da baya so kuma baya tausayin al’ummarsa don haka sai ya tafi ya barta kamar garken dabbobi ba jagora su ci Karen sub a babbaka, a she yanzu hankali zai  yarda da wannan, ina yabon da Allah Ta'ala yayiwa Manzo a cikin Alkur'ani na kyawawan dadi’u da kuma cewa shi mai tausayi ne ga muminai?

  Ina mai kira gare ka ya Dan ‘uwa na mai girma da ka dawo hankalin ka ka riki hujja da gaskiya tun kafin ranar da dukiya da `ya`ya basa amfana komai sai wanda ya je wa Allah da kyakykywar juciya. Dolle ne idan kana so ka san hakika ka dauki gaskiya ka sa ta amatsayin ma’auni da zaka gwada kowa da ita. Ya zo a cikin hadisi daga Imam Ali (da wanna ma’anar) cewa “ka san mazaje da kaskiya kar ka nemi sanin gaskiya da mazaje” ma’ana kayi kokari kasan mecece gaskiya, sannan sai ka dauke ta a matsayin ma’aunin da zaka dora kowa akan ta domin ka tantance matsayin kowa, ba kariko wasu mutane su zame maka ma’aunin sanin gaskiya ba. A kwai abubuwa masu yawan gaske a tattare da wannan lamarin na gadir wanda babu lokacin da zan bayyana su, amma ga mai san karin bayani ya koma littafin gadir na allama amini da kuma sihahus sitta da saurn su.

  [Ka kasance tare damu a fitowa ta gaba don jin amsar tambayar nan ta sama].   

 

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.

KANO, NIGERIA      

Mail= munirsaid92@gmail.com

Whatsapp da telegram +2348038557822.