Akwai Shedan (Iblis)
Da fatan malam Sa'adu Lawal yana lafiya, na ga tambayarka, amma na sha'afa, domin tun da na dawo daga hutu sai ayyuka suka rincabe mini, ta yadda kullum dole in yi rubuce-rubuce na Konfarans (conference) da nake bayarwa duk sati, don haka sai na samu raunin rubutun makalolin hausa! Amma yau na samu zama na rubuta maka wannan a takaice cikin awa daya, tun da na rubuta shi a karamin lokaci ne don haka ko lambar ayoyin da na kawo d.s.s ban samu koma wa don rubuto su ba. Da fatan zai amfanar;
Akwai Shedan (Iblis)?!
Matsayin Shedan
Idan bahaushe ya ce Shedan to yana magana kan wani abin halitta ne da labarinsa ya zo a shari'a da ya ki yi wa annabi Adam (a.s) sujada, wanda yake da sunaye kamar haka: Azazil, Harith, Kitra, Algirban, Hakam, Abumurra, AbulKarrubiyyin, Abukardus, da sauran sunaye da ba mu kawo su ba, kuma ana ce masa Iblis.
Sai dai kalmar shedan ba ta kebance shi ba shi kadai, ita kalma ce da ake gaya wa dukkan wanda yake da halaye irin nasa na girman kai, ko batar da mutane, ko munanan halaye da sauransu. Kuma duk abin da yake hana mutum biyayya ga Allah shi ne shedan dinsa, don haka shedan yana iya zama aljani, ko mutum, ko wata gaba ta mutum kamar zuciyarsa, ko abokinsa, ko matarsa, ko 'ya'yansa, ko dukiya, da sauransu, matukar sun yi sanadiyyar lalacewarsa da kauce hanya da barin abin da ya dace.
Dalilai masu yawa ne a dukkan littattafai saukakku tun daga Suhufi Ibrahim, da Attaurar Musa, da Injilar Isa (a.s) suke nuni da samuwar Shedan, kamar yadda zamu ga Kur'nai mai daraja ya zo da bayanai dalla-dalla game da shi. Wannan Mas'ala ce ta akida da imani da abin da ya zo a wahayi, don haka mu masana Falsafa muna yin bincikenta ne a matsayin wani maudu'i da addini ya zo mana da shi!.
Ko wane mahaluki yana da sunan da ya ta'allaka da shi, wanda yake ayyana matsayinsa na martabarsa a tsarin samammu ta yadda ba yadda zai iya kamo matsayin waninsa da yake sama da shi, kuma ba yadda wanda yake kasa da shi zai iya kamo shi. (sai dai wannan mas'ala ce ta Irfani). Shi Iblis ya samu damfaruwa da sunan Allah "Addhallu" ne, don haka babu wani abu da zai aiwatar sai batarwa, wannan kuwa da zabinsa da kansa ne.
Iblis ya hada dukkan siffofin tawaya da sharri, yana dauke da dukkan abin da zai kai ga yin kasa da faduwa warwas da tabewa ne. Siffofin da suka fara bayyana tare shi su ne Girman kai, Hassada, da Jahilci:
Girman kansa; ya sanya shi saba wa Ubangijinsa ya ki yin sujada umarnin Allah (s.w.t), don haka ne ma ya fi kusa da mutum yayin da mutum zai yi salla, sai ya yi masa waswasin kasala, babban abin da yake so shi ne kada mutum ya yi sujada kamar yadda shi ma bai yi ba.
Hassadarsa; ta sanya shi jin haushin annabi Adam (a.s) da kin yi masa sujada, don haka ne sai ya hura wutar gaba ta har abada da Adam (a.s) da zuriyarsa, kuma ya yi alkawarin sai ya kai wannan zuriyar dukkanta gidan wuta. Don haka ne zai bi dukkan hanyoyi ta dama da hagu, ta gaba da baya, ta sama da kasa, don ya cimma wannan burin.
Jahilcinsa; ya sanya shi ganin wuta ta fi kasa ba tare da wani dalili ba, ko da yake wasu sun ba shi kariya da cewa abin da ake nufi da wuta a nan yana nufin haske. Suna cewa wani lokaci wuta tana da ma'anar haske ne, sun kafa sheda da cewar Musa (a.s) ya ga haske, sai ya ambace shi da wuta!.
Ko ma dai meye, shedan ya yi kiyasin da a mantik muke kiransa Tamsil, wanda ba ya kaiwa ga yakini sai zato. Shi kuwa zato wani kaso ne na jahilci, kuma mafi yawancinsa ba ya kai wa ga dacewa, don haka ne ma shari'ar Allah ta haramta yin sa.
Imam Sadik yana cewa: Addini idan aka yi masa kiyasi za a shafe shi ne. (wato duk wanda yake yin kiyasi a addini to zai ta haramta halal, ya halatta haram, domin da kiyasa ba a iya kai wa ga shari'a).
Waye Shedan (Iblis)
Wasu sun tafi a kan cewa shedan aljani ne yayin da wasu suke da ra'ayin cewa shi mal'ika ne, kuma kowa ya kawo dalilansa kan haka. Sai dai muhimmin abu da ya kamata mu sani a nan shi ne cewar sunan mai batarwa shi ne ya lizimci shedan, kuma abin da ya bayyana gareshi ke nan, don haka ko ya kasance mala'ika ko aljani ba shi ne muhimmi ba.
Masu cewa shedan aljani ne sun tafi kan cewa: Fadin Allah madaukaki: "Ya kasance daga aljanu", yana nuni da cewa shi aljani ne. Sai dai masu ba su amsa sun yi musu raddi da cewa, a nan ma'anar aljani tana nufin mai boyewa, wanda ya hada duk wani abu da ya boyu ga mutane kamar mala'iku da aljanu. Don haka a nan ma'anar "Ya kasance daga aljanu", ma'anar luga ce ta aljani wato mai boyewa, ba aljani da aka sani ba na isdilahi.
Kamar yadda zamu ga yadda masu ra'ayin cewa shi mala'ika ne suka kara da cewa: Allah madaukaki yana cewa: "Sun sanya nasaba tsakaninsa da aljanu", wanda yake a fili a nan cewa Kafirai sun sanya nasaba tsakanin Allah madaukaki da mala'iku ne yayin da suke cewa: Mala'iku 'ya'yan Allah ne. Sai Allah ya ambaci mala'iku a nan da kalmar "Jinnati", al'amarin da yake nuni da cewa kalmar aljanu kalma ce da Kur'ani ya yi amfani da ita yayin da yake Magana kan aljani da mala'ika.
Wannan wani ra'ayi ne da masu tarihin addinai suka yi da'awar cewa kafiran yankin larabawa sun samu wannan akida da sa'i'bawa ne. Kur'ani mai girma ya zo da bayin wannan akida kuma ya yi masu raddi a kanta.
Wasu sun kallafa wa kansu tafsirin wannan aya da abin da ba shi da wata ma'ana kuma bai zo a tarihin wata al'umma ba don kawai su fassara kalmar aljanu da ma'anar aljanu da aka sani na isdilahi, da cewa:
Wai kafirai suna cewa: Mala'iku 'ya'yan Allah ne, kuma uwayensu su ne aljanu.
Sai suka yi kokarin kawo wannan don su nuna cewa; Aljanu ma suna da alaka da Allah gun kafirai alhalin wannan kallafa wa kai ne, kuma magana ce wacce ba ta da tushe, kuma sun kallafa wa kansu hakan ne domin kawai su gamsar da cewa ma'anar "jinnati" a ayar tana nufin aljanu, alhalin ayar tana magana kan masu boye wa ne a lugga da suke nufin mala'iku.
Masu ra'ayin cewa shi mala'ika ne suka kara da amsar cewa, kafin korar sa daga rahama ya kasance daga cikin masu bauta na mala'iku.
Shi ya sanya zamu ga wata ruwaya ta zo da cewa: Aljanin da yake baban aljannu sunansa "Showman", kuma ba shi ba ne Iblis da ya ki yin sujada. Kuma Allah ya aika musu da wani annabi aljani (a.s) mai suna "Yusuf" (a.s) sai suka kashe shi. Kuma ba mamaki wasu masu bautar shedan da gangan ne suke Lika Kalmar (Showman).
Wasu da suka ga ba zasu iya tabbatar da cewa shi aljani ba ne, sai suka ce shi ba mala'ika ba ne, kuma ba aljani ba ne, don sun dauka cewa mala'ika ba ya iya sabo, alhalin akwai mala'iku da suka saba umarnin Allah, kuma mala'iku suna da zabi kamar mutane kamar yadda kissar Harut da Marut take a fili!.
Neman Tsari daga Shedan
Shedan sharri ne gare mu domin shi karen farauta ne don ya ja mu zuwa ga wuta da ya san can zai koma saboda taurin kansa da rashin biyayyarsa da rashin kunya da tsaurin idonsa ga Ubangijinsa. Ya gwammace ya tafi wuta da ya rusuna wa annabawan Allah (a.s), kuma yana da yara daga aljanu da mutane masu taya shi farautar mu don mu je gidansu na wuta!!
Shedan yana da tasiri a kanmu, sai dai tasirin nasa na waswasi ne da ba ya hana mu fahimtar mai kyau da mai muni, kuma tasirinsa a kanmu ba ya cire mana nauyin da ya hau kanmu na yin tunani da zabin abin da yake mai kyau, da nisantar abin da yake mummuna. Don haka tasirin shedan a kan mutum ba ya cire wa mutum zabin da yake da shi, kamar yadda ba ya iya kawar masa da hankalinsa da tunaninsa ko iliminsa.
Don haka duk sabon da bawa ya yi ba ya hana zarginsa da sukansa da ma yi masa ukuba da azaba a kai saboda shi ne yake daukar nauyin laifinsa. Kamar dai yadda tasirin Allah da mala'iku a kanmu, da ma sauran bayin Allah salihai na gari kamar annabawa da wasiyyansu (a.s) shi ma ba ya cire mana yabo kan abubuwan da muka yi na alheri.
Kamar yadda Kaddara ba ta cire wa mutum zabi, haka ma tasirin shedan ba ya cire masa zabi; don haka ne zamu ga sau da yawa aka samu wadanda suka ga dama suka ce wa shedan karya yake a duk lokacin da ya yi musu waswasi da jan su zuwa ga aikata sharri.
Shi shedan yana kama da mugun aboki ne da yake bayar da shawara mummuna da idan aka yi aiki da ita sai a samu hasara, idan kuma aka sanya hankali aka watsar da ita sai a samu rabauta.
Wasu jama'a masu son shedan masu tausaya masa suna ganin cewa: Don me Allah zai tsane shi! Idan rahamar Allah tana da fadi to don me wasu suka fita daga ciki kamar shedan!! Sai mu ce:
1- Shedan ya saba umarnin Allah ne kuma ya ki furuci da fifikon annabawan Allah a kansa, don haka ne Allah ya saka masa da sakamakon laifinsa, kuma idan ya tuba ya dawo ya yi imani ko da yaushe ne, to kofa a bude take gareshi. Lamarinsa ya yi kama da ma'abota wasu addini ne daga Ahlul-kitabi wadanda duk da sun yarda Allah daya ne, amma sun ki imani da annabawansa, kamar annabi Isa (a.s), ko annabi Muhammad (s.a.w) da wasu ba su yi imani da shi ba, to Allah ba zai gafarta musu ba, kuma zai sanya su wuta matukar ba su imani da annabawansa ba.
2- Hikimar Allah ta hukunta cewa zai saka wa kowa da aikinsa bisa hikima, domin babu hikima ya daidaita mai kyautatawa da mai sabawa a hukunci daya, kamar soja ne da ya yi yaki ya kare kasa daga sharrin makiyanta, ba yadda za a daidaita sakamakonsa da wanda yake barawo dan fashi da ya addabi al'umma ya hana ta zaman lafiya.
2- Adalcin Allah: Ba zai yiwu a daidaita masu kyautatawa da munanawa kawai ba a matsayin madaidaita. A cikin wannan akwai karfafar mai munanawa ya ci gaba, da kashe gwiwar mai kyautatawa ya bar yin alheri. Don haka adalcin Allah shi ne ya ba wa kowa sakamakon abin da ya yi na alheri ko na sharri!.
3- Rahamar Allah ta sanya azabtar da masu yin sharri, domin a cikin azabatar da su akwai rahama. Kamar 'yan fashi da barayi masu takura al'umma da masu fyade da 'yan zambo ne, sai kawai don kasancewar ana son su samu rahama sai a kyale su suna kashe mutane suna kwace musu dukiya, wannan kuwa shi ne azaba ainihinta. Don haka rahama shi ne daukar mataki kan wadancan kashi 1% don kashi 90% su samu rayuwa cikin yalwa da aminci. Wannan ne ma ya sanya fadin nan na Allah mai hikima cewa "Kuna da rayuwa cikin kisasi".
Domin wanda ya san idan ya kashe shi ma za a kashe shi, sai ya kame hannunsa, mutane su amintu daga sharrinsa, sai ya kasance sun samu rayuwa!.
Hafiz Muhammad Sa'id
Cibiyar Haidar don Yada Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Wednesday, November 09, 2011