Hukunci da Kaddara
  • Take: Hukunci da Kaddara
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:44:13 13-9-1403

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
KADDARAWAR UBANGIJI Haka Allah Ya So! Allah Ya Yarda! Allah Ya Kaddara! Hukuncin Allah! Allah Ya Zartar! Haka Allah Ya So! Haka Allah Ya Yi!

Saudayawa mutane sukan yi magana su ce: Allah ya kaddara ko ya hukunta, ko kuma Allah ya so ko Allah ya yarda, ko kuma al'amarin Allah ne da sauran kalmomi da suke amfani da su wajen bayanin wani abu da ya wakana, wannan al'amarin yana iya kasancewa mummuna ko kyakkyawa, sannan kuma yana iya kasancewa na samuwa ne da yake wakana ko kuma abu ne wanda Allah ya hana yin sa ko kuma ya yi umarni da a aiwatar da shi kamar na shari'a.
Don haka muna iya binciken wadannan kalmomi tukuna kafin mu shiga cikin bayanin hakikanin abin da ake nufi da wannan al'amari, sannan kuma sai mu yi bayanin tasirinsa a al'amuran da suka shafi al'umma da rayuwarta a ayyukanta na yau da kullum kuma ya dabaibaye cigabanta da ma samuwarta a matsayinta na al'umma mai hakki da 'yanci. Da farko muna iya binciken wadannan kalmomi na hukuncin Allah ko kaddarawarsa domin mu san me ake nufi da wadannan kalmomi a yadda al'ummarmu suke amfani da su da kuma yadda masana Allah suke ganinsu.
Kalmar Allah ya kaddara ko ya hukunta kalmomi ne da ake amfani da su da nufin al'amarin da ya wakana ya faru ko kuma abin da ya faru kuma ya samu: idan aka samu riba ko faduwa a kasuwanci ko aka kulla aure sai a ce Allah ya kaddara, haka nan idan aka samu haihuwa kamar aka samu namiji ko mace sai a ce; haka Allah ya hukunta ko ya kadddara ko kuma ya so ko kuma ya yi nufi. Wato da son Allah da kaddarawarsa da hukuntawarsa da nufinsa kai da yardarsa duk sai a yi amfani da su a kan al'amari daya. Koda yake ba kasafai bahaushe yake amfani da Allah ya yarda ba sai ga abin da yake na alheri ko na farin ciki da jin dadi, amma duk da haka idan da zaka ce Allah ya yarda yayin da ka fadi a ciniki ne ko kuma a jarabawar makaranta, ko a hasara kamar tadukiya, ko rashin lafiya, ko hadari, to suna komawa zuwa ga ma'anar cewa shi ne ya kaddara ya hukunta.
Idan muka duba mahangar ilimin sanin Allah muna iya ganin sun kawo ma'anar da suke amfani da ita game da kaddarawa da hukuntawa. Idan muka dauki kalmar kaddarawa "kadar" a larabci sun ba ta ma'anar da ta saba da ta hukuntawa ko zartarwa "kadhaa" a larabci. Yayin da zamu ga sun yi amfani da kalamr farko "kadar" a kan abin da ake auna shi ake kuma daidaita shi kamar dai mai dinki da yake auna yadi yake daidaita shi ta hanyar yankawa da hadawa da dinkawa domin samar da wando ko riga, ko kuma mai gini da yake kwaba yashi da sumunti kuma ya daidaita bulallika sannan sai ya daidaita tsakaninsu ya hada su domin samar da gini cikakke wanda zai iya ba mu gida cikakke gamamme shiryayye. Amma idan aka ce ya hukunta "kadhaa" to ya riga ya gama aikin kenan, wato ya zartar da aikin ya yi sitampin ya gama, kamar gida ne da aka gama gina shi, ko kuma riga da aka gama dinka ta, ko kuma wani rubutu da aka gama aka sanya sitampi a kan takarda, don haka sai a ce: ya zartar ko ya hukunta, ko ya gama.
A nan kenan muna iya ganin bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu duk da kuwa suna layi daya ne ba layuyyuka mabambanta ba. Abin da muke nufi a layi daya suke kamar mai yanka yadi da yake daidaita shi ai ba komai zai cimma ba kuma ba wata natija za a samu ba sakamakon yanka wannan yadin sai kaiwa ga samar da riga, don haka ne ma muna iya cewa; kaddarawa a nan wato yanka yadi da dinka shi, da kuma hukuntawa wato gama dinki abubuwa biyu ne da suke a layi daya. Amma da mun ce ba a layi daya suke ba, to sai mu ce kenan mai dinki yana kaiwa ne ga samar da gida da dinkin da yake yi, kamar yadda muna iya cewa kenan (idan da haka ne) mai gini yana dora bulo ya kwaba siminti da yashi domin daga karshe a samu riga da wando, don haka ne sai mu ce a layi daya suke kenan, amma ba haka ba ne, domin ba a layi dayan suke ba. Domin mai dinki kaddarawarsa da hukuntawarsa tana iya kaiwa ne kawai ga samar da riga da wando da hula d.s.s. kamar yadda mai gini kaddarawarsa da hukuntawarsa tana iya kai mu ne ga samar da gida. Don haka ne muna iya cewa: kaddarawa da hukuntawa a layi daya suke a ma'anarsu, sai dai kawai sai an wuce marhalar kaddarawa ne sai a kai ga hukuntawa (ko kuma gamawa ko zartarwa). Kuma bahaushe kana amfani da wadannan kalmomi sannan sai ka sanya musu ma'anar so da nufi da yarda, kuma hakan daidai ne idan muka lura da cewa sai an yi so da kauna da nufi sannan sai a kai ga kaddarawa da hukuntawa, don haka sai ka ambaci abu da sunan da ake kiran sababinsa a fadinka da cewa; haka Allah ya so, ko ya yarda. Sannan wannan kaddarawa da hukuntawa natijar so din ne, kuma suna iya kasancewa a ayyukan halittawa da samarwa ko shar'antawa, ko ayyukan bayi: to a nan ne fa aka samu badakala da cakudewa da yamutsewar tunani.
Sai dai akwai bahasin palsapa kan wannan al'amari da ya shafi kaddarawa da hukuntawar Allah a bahasin iliminsa amma ba zan tabo shi ba saboda kebantarsa da Allah amma yana amfani wajen kawo misalai a yanayin ma'anar wasu hadisai da ba su inganta ba, da kuma bayanin cewa; ilimin Allah da faruwar abu tun kafin faruwarsa ba ya sanya shi mai tilasta faruwar abun ta hanyar dankara shi kan bayi ba da zabinsu ba. Don haka ne zamu bayar da karfi kan mas'alar kamar yadda malaman sanin Allah suka yi bayani domin shi ne ya fi saukin fahimta sannan kuma ya fi amfani ga al'umma. Kodayake akwai dan bambanci a isdilahohi da suke amfani da su tsakanin imamiyya da mu'utazila da ash'ariyya abin da yake bahasi ne da ba zai amfane mu ba a irin wannan matsayin koda yake ba zai cutar ba.
Idan aka ce Allah ya halitta me ake nufi? Kuma me muke iya fahimta daga wannan magana? Tabbas na san masu amsa zasu bayar da jawabi kan cewa Allah ya samar da wani abu ne. A wannan fage muna da ma'anar halittawa da take nufin samarwa, wannan samarwa din ba ta hannun abin halittawa, kuma ba ta hannun abubuwan da suke a matsayin sabuba da aka yi amfani da su wajan wannan aiki na samarwa, sai dai wadannan abubuwan da suke sabuba suna iya yin tasiri cikin yanayin da aka yi halitta din.
Da wani bayani da ya fi sauki muna iya cewa; Ubangiji yana yin halitta, kuma saudayawa a wannan duniya da muke iya amfani da gani ko ji ko tabawa ko dandanawa ko shakawa domin rizkar abubuwa mabambanta a cikinsu da akwai abubuwan da Allah ya sanya su sabubba domin samar da halittun da suke cikinta wadanda suka hada da mutum da dabbobi da tsirrai d.s.s, sai dai cewa; wadannan sabuban duk da ba su suke yin halitta ba amma Allah ya sanya su masu tasiri cikin halitta din. Misalin zafi da muke iya ganin yana faruwa sakamakon kunna wuta, muna iya ganin wannan zafin da Allah ya samar da shi bai kawo shi haka nan ba batare da wani sababi ba, a nan muna iya ganin ya sanya sababin samar da zafi ita ce wuta, ko rana ko gas da sauransu, kamar kuma yadda yake samar da 'ya'ya ta hanyar iyaye ne. Kuma mazhabin Ahlul Baiti (A.S) ya saba da ash'arawa da suka cire tasirin wadannan sabuban suna masu ganin cewa Allah ne yake halittar zafi, kuma babu wata rawa da wadannan sabuban kamar wuta da rana suke iya takawa wajan samar da zafi.
Amma wannan magana ta ash'arawa tana da rauni idan muka duba zuwa ga samuwar tasirin wadannan abubuwan a zahiri ta yadda: furiji ko wata da yake sama ba zasu iya bayar da zafi ba, kuma wuta da rana ba zasu iya bayar da sanyi ba, kamar yadda maniyyin mutum ba ba zai iya bayar da kare ba, kuma kwan kaza ba zai iya bayar da shaho ba! Haka nan dai muke iya ganin tasiri tsakanin aububuwa mabambanta don haka ne ma ash'arawa suka kirkiro ra'ayinsu na "kasb" al'amarin da yake bai gushe ba cikin duhu, kuma wannan ne ma ya sanya Imamul Haramain ya yi kokarin gujewa daga wannan ra'ayi.
Sannan muna iya ganin cewa a wannan mahallin na halittawa babu wani abu da zai iya zabar yadda zai kasance, don haka Allah ya yi nufin su kasance kamar yadda yake so kuma haka nan ya kaddara ya hukunta. Da wannan ne muke sanin cewa idan aka haifi mutum to don Allah ya yarda ya yi shi ne, kuma ya hukunta ya lizimta ya tilasta ya kasance kamar yadda ya yi shi, babu wata rawa ta zabinsa da zai iya takawa kan wannan ko kadan, sai dai akwai rawar da sabubba suke iya takawa, kamar ana iya halittarsa nakasasshe ko tauyayye sakamakon buguwar cikin uwa ko nau'in yadda take kwanciya, ko kuma nau'in abincin da take ci, ko kuma nau'in yadda ake saduwa kamar shin a lokacin cikin bakin ciki ne ta samu cikin ko lokacin farin ciki ko razani ko rashin nutsuwa da makamantansu.
Sannan muna iya ganin nau'in halittun sun sassaba a yanayinsu, mafi girman kima da Allah ya yi wa mutane da mala'iku da aljanu shi ne; su suna iya sabawa idan suka ga dama, a yau idan mala'iku da mutane da aljanu suka ga dama suna iya yi wa Allah tawaye, amma sauran halittu sai aka yi su da wata dabi'a tabbatacciya da ba ta karbar canji sai dai amfana daga gareta domin samun wata habaka zuwa wani mikdari daidai gwargwado kamar yadda ake yi wa kare tarbiyyar gadi ko aike.
Halittarmu tana iya nuna mana cewa ba mu da zabi kan yadda za a samar da mu kuma wannan samuwar tana da marhaloli daban-daban, sannan muna iya ganin hakan a fili cewa da an tambayi wani mutumin me kake so ka kasance da ya ce ina son in kasance kamar yanayi kaza ko kuma shakali kaza ko kuma kamar wane. Ba wasa ba ne kuma ba rashin hadafi ne ya sanya ka ga mutane musamman wasu lokuta wasu mata suna yin shafe-shafe domin su gurje fatarsu ta koma irin wata kala, musamman ko daga baka zuwa fara, ko daga fara zuwa yalo da sauransu.
Sai kowa ya kasance yana da wani yanayi daban da na waninsa, kuma da an nemi shawararsa da an yi shi dan kabila kaza, ko launi kaza, ko kuma da ma an haife shi dan kasa kaza, da ma shi ne wane kaza! daidai gwargwadon ma'aunan da suke su ne ma'aunin kamala gunsa.
Sannan kuma ya halicce su ne bisa mafi tsarin halitta ta yadda tawaya da take faruwa a halittarsu take komawa zuwa ga sabubban samuwarsu ne da suke karbar tawaya da kamala domin mustahili ne wannan tawayar ta zo daga Allah madaukaki mai tsantsar kamala da babu wani kwarzanen tawaya gareshi. Duk da haka wannan ba zai sanya mu mantawa da cewa dukkan komai asalinsa ya gangaro daga Ubangiji madaukaki ne.
Sannan wannan sabubban suna da tasiri matuka, kuma wannan yana daga cikin abin da ya sanya ni tambayar malamina Allama Ayatullahi Sayyid Adil Alawi cewa; don me mutane suke ganin a halittar wasu mutane musamman mace a kan samu dalilin arzikinsu da kuma talaucinsu ta yadda za a ce tana da kashin tsiya ko kashin arziki. Sai ya ce: "Haka ne, kamar yadda mu ma a nan kasashenmu muna da irin wannan; akan ce wance tana da goshin tsiya ko goshin arziki sai dai wannan wani bangare ne na sababi da ana iya kawar da shi da addu'a da makamantan hakan". Al'amarin tasirin bayi a cikin ayyukan Allah da halittawarsa abu ne sananne da shari'a ta zo da shi, kuma muna iya ganin wannan misalin a hadisan da suka yi bayanin ajalin da aka hukunta wa mutum amma sai a canja shi. Misali ya zo cewa: Allah yana kaddara wa wani mutum zai mutum nan da kwanaki 3 amma sai ya yi sadaka ko sadar da zumunci sai Allah ya mayar da shi shekaru 30. Don haka mu mun saba da yahudawa da suka ce an yi wa hannayen Allah kukumi; ya riga ya gama komai ba zai iya canja wani abu ba.
A takaice muna iya cewa; babu wani zabi da muke da shi a kan al'amarin halittawa, sai dai muna iya tasarrufi cikin sabuban halittawa, ko kuma mu yi wani abu da Allah zai canja mana wani abu da ya kaddara shi a kanmu. Kuma tasarrufi cikin sabuban samarwa wani abu ne wanda aka samu iliminsa a likitanci a wannan zamani kuma shari'a ba ta kore shi ba kamar yadda tun farko shari'a ba ta yi musun sa ba.

Ayyukan Mutane Da Kaddara
Haka nan matakan da dan Adam yake dauka ana kirga su cikin kaddarawar Allah ne: kamar dai shan magani ne ga marasa lafiya, ko yawaita istigfari ga mai son ya yi arziki, ko saukar ni'imar Allah ga al'umma idan ta yi imani ta yi takawa. Kuma muna iya ganin wannan a koyarwar musulunci a ruwayar Saduk a littafinsa "Attauhid" shafi na 369, yayin da imam Ali (A.S) yana tafiya ya kauce daga kusa da wani bango da ya karkace kamar zai fado, sai wani ya ce; masa: Ya Amirul muminin shin kana gudun kaddarar Allah ne? sai imam Ali (A.S) ya ce: "Ina gudu daga kaddarar Allah ne zuwa ga kaddarar Allah"! Shi ya sa muka ga ruwayar da take magana game da mutane biyar wadanda ba a karbar addu'arsu ya hada da wanda ya ga garu ya karkata zai fado bai kauce ba har ya fado masa (wannan yana kama da mai addu'a ne a kan wani al'amari amma bai dauki matakin da ya dace da shi ba, ba yadda za a yi ya ga kyakkyawar natija).
Kuma a wata ruwayar muna iya ganin yadda imam Ali (A.S) ya ba wa wani mutum amsa game da cewa; yakin da suke yi da kaddarawar Allah ne ba tare da Allah ya tilasta su ba, sai dai wani abu ne wanda suke zuwa da zabinsu, kuma ba don wannan zabin da Allah ya ba su ba, to da babu ma'anar aiko manzanni da aikin lada ko na sabo ko kuma umarni da hani ko sakamakon aljanna da wuta. Don haka ne ma ya zo daga imam Ridha (A.S) cewa: Duk wanda bai yi imani da kaddara ba to ya kafirta.
Saudayawa wasu suna cakudawa tsakanin kaddarawar shar'antawa da kuma ta samarwa, sannan sai su tashi wata natija mai ban mamaki da zata kai su ga imani da tilascin ayyuka da rashin zabin kansu, don haka sai su jingina wa Allah ayyukansu da wani lokaci sukan iya kasancewa na sabo ko na zalunci da munana kai tsaye. Wani lokaci kuma suna cire tasirin kansu a matsayinsu na masu zabi suna masu kaddarawa cewa; kaddarar Allah tana cire musu zabin da ya ba su: muna iya ganin irin wannan al'amari kamar haka:
Abdullahi dan umar ya ruwaito daga Abubakar halifa na farko (a cikin tarihin hulafa, na suyudi) cewa: wani mutum ya zo wajen Abubakar sai ya ce masa: shin kana ganin zina kaddarawar Allah ce? sai ya ce: E. Sai mutumin ya ce: Kana ganin Allah ya kaddara mini sannan sai ya azabtar da ni? Sai halifa Abubakar ya ce: Ya kai dan kaskantacce da akwai wani mutum a kusa da ni da na umarce shi ya fasa maka hanci.
AyatulLahi Subhani yana cewa: "Wannan mutumin ya fahimci cewa; kaddarar Allah da kuma sakamakon azaba a kan aiki ba su dace da adalcin Allah madaukaki ba, kuma wannan yana nuna kenan dole ne a jefar da daya daga ciki, kuma Halifa da ya kasa bayar da amsa mai gamsarwa a wannan mas'ala ga wannan mutumin sai ya yi gargadi da barazana kawai, kuma wannan yana nuna mana a fili cewa: a kwakwalen wasu mutane kaddarar Allah tana daidai da tilastawarsa ne". (Ilahiyyat shafi: 509).
Idan mun duba zamu ga wannan mutumin yana ganin Allah ya kaddara masa yin zina a ayyukansa wanda wannan al'amari ne da yake komawa zuwa samuwarsa, sannan kuma sai ya kaddara masa kuma ya hukunta masa haramcinta wanda al'amari ne da yake na shar'antawarsa, sannan kuma sai ya azabtar da shi idan ya yi, wanda yake komawa ga ayyukan Ubangiji na samarwa.
Kuma muna iya ganin wannan a fili yayin da Umar dan Khaddabi halifa na biyu ya gudu a yakin Hunain, sai Ummul Haris al'ansariyya ta gan shi yana gudu sai ta tambaye shi lafiya dai?! Sai ya ce: Al'amarin Allah ne: wato kaddarawar Allah ce. (Almagazi na alwakidi). A nan muna iya gani a fili yake cewa; Allah ya shar'anta wa musulmi su kare kansu daga sharrin makiya kuma al'amari ne na shar'ia, amma halifa kuma ya danganta gudunsa wanda yake abu ne na samarwa da yake komawa zuwa ga ayyukansa da cewa shi ma kaddarawar Allah ce. Sai ya kasance Ubangiji ya kaddara masa ya je yaki a ayyukansa, kuma ya shar'anta masa tafiya yakin, sannan kuma sai ya kaddara masa ya gudu.
Banu umayya su ne farkon wadanda suka karfafi wannan al'amari a kwakwalen mutane domin su ci karensu ba babbaka, su yi zalunci yadda suka so sai kuma su danganta shi ga Allah, wannan al'amari yana da bayanai masu yawa a tarihi da ba zamu iya kawo su a nan ba.
Ayyukan mutum kai tsaye sun saba da maganar halittawa, a nan ne ya kasance mahallin da dan Adam ba shi da tilasci daga Allah, da wannan ne muke iya sanya mutum tsakanin kolum biyu da shi da mala'ika da aljani domin su ne mahallin maganar Allah a wannan wurin, kuma su ne wadanda suke iya sabawa ko su yi biyayya. Da mala'ika ko aljani ko mutum ya ga dama yana iya bin Allah ko kuma ya saba masa bisa daidai ikonsa da zabinsa da Allah ne ya halitta shi da shi, kuma haka Allah da hikimarsa maras iyaka da misali ya hukunta.
A nan ne mahallin da ake cewa Allah ya hukunta amma ba ana nufin bisa tilasci ba, kamar yadda ake cewa ya hukunta amma ba ana nufin ba shi da hannu a ciki ba, a nan Allah bai yi duka biyun ba, bai tilasta ba, kuma bai cire hannunsa ba, domin idan ka ce ya cire hannunsa to a nan ka bi ra'ayin mu'utazilawa, kamar yadda idan ka ce ya tilasta ka bi ra'ayin mujbira da ash'arawa da kuma ma'abota sufanci.
A nan ne Ahlul Baiti (A.S) suke karfafawar cewa: al'amarin tsakanin wadannan abubuwa biyu ne: Idan ka ce Allah ya hukunta ko kuma ya kaddara ko kuma ya so ko ya zartar da cewa; a haife ka bahaushe ko bature ko balarabe to wannan yana komawa ne zuwa ga na farko wato halittawa da ba ka da iko a kai sai yadda ya yi ka, ya sanya ka da ga bahaushe ko ba'amurike ko bature, ko balarabe, ko makamancin hakan. To a nan yana nufin ya tilasta ka tayadda ba ka da wani zabi, daidai kake da wanda aka daure hannayensa aka jefa ruwa, a nan ko ka ki ko ka so dole ne ka jike.
Amma idan ka fadi cewa; Allah ya hukunta ko kuma ya kaddara ko kuma ya so ko ya zartar da cewa ka kasance musulmi ko kirista ko bayahude ko arne ko bamajuse to a nan ya saba da fadin ka na sama, domin a nan yana nufin Allah ya umarce ka da ka bi hanyarsa sai ka bi ko ka ki bi, don haka sai ka bi shi ka kasance musulmi ko kuma ka ki bin sa sai ka kasance bayahude ko kirista ko arne ko kuma bamajuse. A nan ne muke cewa da ya tilasta ka, da aiko manzanni da sako da sanya wasiyyai domin shiryar da dan adam ya zama wasa kenan, da hadafin aiko sako ya kasance barna da wasa. Don haka wannan ya faru ne da zabika, kuma a kan haka ne mazhabin Ahlul Baiti (A.S) ya saba da mujabbira da asha'arawa da kuma kirista da yahudawa da masu sufanci (sufancin da ya saba wa koyarwar tafarkin Ahlul Baiti (A.S).
Kai yahudawa sun zurfafa a kan cewa; ba ma kawai ya yi wa dan Adam tilas ba, shi kansa ya yi wa kansa tilas ba zai iya canja abin da ya dora wa kansa ba kamar yadda suke cewa; "hannayen Allah abin yi wa kukumi ne", wato ya riga ya zartar dole ne a kansa ya yi kaza kuma ba zai iya iya canjawa ba, wannan kuwa ya yi tasiri har a shari'arsu da suke cewa mustahili ne a samu shafaffen hukunci domin an riga an gama.
Kamar yadda muna iya ganin munin hakan ya sanya mu'utazila gudu daga wannan ra'ayi, amma sai suka fada cikin mummuna irinsa ko kuma sama da hakan ma muni, suka ce babu hannun Allah sam a ayyukan bayi, sun yi tsammanin wannan zai iya warware matsalar da suka yi gudu, amma sai suka gujewa tarkon farko suka fada wa na biyu, sai suka gujewa tarkon butulcewa Allah suka fada na gwama shi da waninsa; yayin da suka sanya mutum a matsayin mai tasiri kan ayyukansa mai zaman kansa ba tare da wani hannu da Allah mahaliccinsa yake da shi a kai ba.
A nan ne imamai (A.S) suka karfafa da cewa duk wanda ya yi furuci da tilascin Allah ga bayi to ya butulce masa, wanda kuwa ya tafi a kan ganin damar mutum (cire hannun Allah daga ikon ayyukan dan Adam) to ya gwama shi da waninsa. Kuma muna iya ganin yadda Allah yakan canja mana wani mataki ko ya ba mu wata kariya, ko kuma ya hana mu wata tafiya ko ya shiga tsakaninmu da wani abu da muke so a wasu lokuta, kuma wannan yana nuni da cewa; ashe bai cire hannayensa daga ayyukanmu ba.
A kan haka ne muke iya cewa; akwai hannun Allah a ayyukanmu duk da kuwa bai tilasta mu ba, wato da Ubangiji bai ba mu ilimi da hankali da karfi da iko da nufi da lafiya ba, da ba mu iya yin wadannan ayyukan ba, don haka akwai hannunsa a cikin ayyukanmu, amma kuma bai tilasta mu ba saboda ya halicce mu tare da zabi, domin ba ma'ana ya ce mu yi sannan sai ya tilasta mu kan yi ko kan kin yi, ko kuma ya ce mu bari sannan sai ya tilasta mu kan bari ko rashin bari, domin idan ya yi hakan sannan sai ya azabtar da masu yi ko masu bari sabanin umarninsa ko haninsa kuma ya ni'imtar da masu yi ko masu bari bisa dacewa da umarninsa ko haninsa, to wannan ya saba da hikimarsa kuma tambaya ta hankali ba zata gushe ba tana ganin zaluncinsa (Allah ya daukaka daga aikata haka, tsarki ya tabbata gareshi).
Don haka ne muke cewa; akwai hannun Allah a cikin ayyukanmu amma kuma bai tilasta mu ba, kuma Allah ya shiryar da kowane mutum da ma'anar aiko sako, sannan kuma ya shiryar da wasu da ma'anar sun yi riko da ni'imar da ya yi musu ta hankali sai suka bi shi, kuma ya batar da wasu mutanen da ma'anar sun ki riko da ni'imar da ya yi musu ta hankali sai suka saba masa.
A nan muke cewa; idan mutum ya ga dama yana iya shiryuwa, kuma da ya ga dama yana iya bacewa, sai shari'a ta dangana bata gareshi domin ya ki amfani da hankalinsa ya ki biyayya ga umarnin Allah, kuma shari'a ta dangana shiryarwa ga Allah saboda shi madaukaki shi ya ba shi hankali da karfi da nufi da gabobin da ya yi amfani da su da duk wani abu da ya yi riko da shi kai har ma da sakon wahayi da aka yi da aiko annabi da shiriya da ya amfana da su wajen samun shiriya, karshe ma hatta da shi samuwar kansa.
Don haka a nan idan mutum ya ga dama ta hanyar riko da sabuban hakan yana iya dacewa ga shiriya, kuma wannan shi ne ma'anar kaddarawa da Allah ya yi a wannan al'amarin. Kuma muna iya ganin wadannan al'amuran matsayai da darajoji ba sun takaita da lahira ba ne, ko abin da ya shafe ta, har ma da duniyar mutum suna shafa: don haka idan mutum ya ga dama ta hanyar rikon sabubai yana iya cewa; ni ina son zama likita ko injiniya ko malamin addini ko shugaban garinmu ko kuma mai labarai ko makamancin wannan kuma idan ya samu yin riko da sabuban hakan yana iya kaiwa ga hakan da taimakon Allah da ya shirya masa kuma ya yalwata masa wadannan sabubai masu yawa a wannan duniya tasa.
Don haka ne kakan ga wani ya tashi tsaye yana son ya kasance daga waliyyan Allah ko kuma masu kawo gyara ko kuma masu shiryar da mutane zuwa ga Allah ko masu bauta wa Allah, da makamanta hakan, kuma matukar ya yi riko da hanyar yin hakan to sai a samu dacewa da wannan yalwatawar da Allah ya yi masa.
Kamar yadda idan ya dauki hanya sahihiya ta yin hakan ya kan iya kaiwa ga kololuwar hadafinsa, haka nan idan ya yi riko da sabuban hakan kan al'amuransa na wannan duniya -wadanda a bisa hakika su ma suna komawa ne zuwa ga al'amuran lahirarsa- a wannan duniyar yakan iya kaiwa ga kololuwar hadafinsa, kuma haka nan kuskure wajen rikon hanya sahihiya a duka biyun yakan iya kaiwa ga rashin dacewa.

A kan wannan al'amari ne muzaffar mai littafin akidojin imamiyya yake cewa: "Mujabbira sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan halittu, sai ya zamanto ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, kuma ya tilasta su a kan aikata abin da ya yi umarni tare da haka ya ba su lada, domin sun tafi a kan cewa ayyukansu tabbas ayyukanSa ne, ana dai danganta ayyukan ne garesu saboda rangwame domin su ne mahallin ayyukan Ubangiji. Asalin wannan kuwa domin su sun yi inkarin sababi na dabi'a tsakanin abubuwa , suna ganin Allah madaukaki ne yake aikata komai bisa hakika.
Sun yi musun wannan sababi ne saboda tsammanin cewa hakan shi ne ma'anar kasancewar Ubangiji mahalicci, Wanda ba Shi da abokin tarayya, amma duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa ya tsarkaka daga hakan.
Mufawwada kuma sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, da la'akari da cewa; danganta ayyukan gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi ne, kuma halittu suna da nasu sababan na musamman duk da cewa dukkansu suna tukewa ne zuwa sababi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T). Duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa, hakika ya fitar da Allah daga mulkinSa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa.
Abin da muka yi imani da shi a nan muna masu biyayya ga abin da ya zo daga lmamanmu tsarkaka da suke cewa al'amari ne tsakanin al'amura biyu, al'amarin da irin wadannan masu jayayya daga malaman ilimin sanin Allah suka kasa fahimtarsa, wasu kuma suka takaita, wasu kuma suka zurfafa, babu wani daga cikin masana ilimi da ma'abuta falsafa da ya fahimce shi sai bayan karnoni masu yawa.
Ba abin mamaki ba ne ga wanda bai tsinkayi hikimar Imamai (A.S) dangane da al'amari tsakanin al'amura biyu ba, ya yi tsammanin cewa wannan magana ta al'amari ne tsakanin al'umara biyu tana daga abin da malaman falsafa na turai na wannan zamani suka gano, alhali kuwa Imamanmu sun rigaye su tun kafin karnoni goma da suka wuce.
Imam Sadik (A.S) ya fada yana mai bayanin hanyar nan matsakaiciya da cewa: "Babu Tilastawa kuma babu fawwalawa sai dai al'amari ne tsakanin al'amuran guda biyu.
Wannan kalma ta girmama! Ma'anarta ta zurfafa! A takaice abin nufi shi ne; hakika ayyukanmu a bangare guda ayyukanmu ne bisa hakika kuma mu ne sababinsu na dabi'a kuma suna karkashin ikonmu da zabinmu, a daya bangaren kuma suna karkashin kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin mulkinsa, domin Shi ne mai ba da samuwa mai bayar da ita, bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana ya zama ya zalunce mu idan ya yi mana azaba a kan sabo, domin muna da iko da kuma zabi a kan abin da muke aikatawa. Kuma bai fawwala mana samar da ayyukanmu ba ballantana ya zamanto ya fitar da su daga karkashin ikonsa ba, al'amarin halittawa da hukuntawa da umarni duka nasa ne, kuma shi mai iko ne a kan komai kuma masani da bayinsa.
Ta kowane hali, imaninmu shi ne hukuncin Allah da kaddarawarsa sirri ne daga asiran Allah (S.W.T) duk wanda ya iya fahimtarsa yadda ya dace ba tare wuce gona da iri ba ko kuma takaitawa ba, to wannan ya yi, in ba haka ba, bai wajaba a kansa ba ya kallafawa kansa fahimta da zurfafawa a cikinsa ba, domin gudun kada ya bata, akidarsa ta lalace, domin wannan yana daga al'amura masu zurfi, kai yana daga mafi zurfin bahasosin falsafa wadanda ba mai gane so sai daidaikun mutane, kuma duga-dugan da yawa daga malaman ilimin akida sun zame, kallafa wa kai fahimtarsa, kallafa wa mutum maras ilimi mai zurfi ne da abin da yake sama da ikonsa.
Saboda haka ya wadatar mutum ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga fadin Imamai tsarkaka (A.S) cewa; shi wani al'amari ne tsakanin al'amura biyu, babu tilastawa babu kuma fawwalawa a cikinsa, kuma shi ba ya daga cikin shika-shikan akida ballantana kudurcewa da shi dalla-dalla da zurfafawa su zama wajibi ko ta halin kaka" .

Sakamakon Bincike
Dogaro da abubuwan da suka gabata muna iya cewa: kaddarawa da hukuntawa sun kasu gida shida ne kamar haka: Na ilimin Allah (S.W.T) Wannan kuwa mun riga mun yi nuni da cewa ba zamu yi magana kansa ba musamman da yake ya danganta da Palsapa, Na shar'antawa wanda shi ma ba mahallin maganarmu ba ne sai dai mun yi nuni a kai, Sai na uku: na ayyukan bayi da ubangiji a abubuwan da suke faruwa suke wakana, wannan kuwa shi ne mahallin jayayya sosai, kuma a nan ne kafafuwa suke zamewa.
A sha'anin samarwa da fararwa da halittawa a fadinmu cewa; Allah (S.W.T) ya halitta, abin nufi a nan ubangiji ne ya kaddara hakan a matsayin samarwa domin cika halitta yadda ya so, kamar ka ce; Allah ya kaddara abin da yake cikin mahaifa ya kasance namiji ne, ko Allah ya kaddara babu yadda za a yi mu ga wani abu sai ta cikin kaloli. Saudayawa ana amfani da wannan a wurare masu yawa; akan ce; Allah ya kaddara dai sai an samu haihuwa tsakanin wance da wane, da nufin cewa; halittawa dai na Allah ne, kuma shi ne yake bayar da haihuwa ga wanda ya so, kuma ya hana wanda ya so, kuma haka nan ne yake tsarawa a samarwa.
Amma batun cewa akwai tasirin wasu halittu da idan an kawar da wannan tasirin za a iya haihuwa ko kuma idan aka dauki wani mataki na musamman zai canza yanayin kwayoyin halittar mace domin ta samu ciki wannan ba ya cikin abin da muke nufi a wannan bahasin namu domin yana komawa zuwa ga tasirin sabubban da ake da su kan wasunsu ne, al'amarin da yake nuna mana tasirin da yake tsakanin samammu.
Kamar yadda a fadinmu cewa; Allah madaukaki ya hukunta hakan; a nan ana nufin ya riga ya tsara kuma ya kammala halitta din, kamar takarda ce da aka rubuta ta kuma aka sanya hannu kuma aka yi mata sitampin. Don haka idan muka ce: hukuncin Allah haka yake a maganar samun da namiji tsakanin uwaye biyu, to muna nufin ya riga ya zartar kuma ya samar da shi bayan wucewar marhalar tsarawa da daidaita halittarsa a ciki da kuma kammala samuwarsa da cika ta.
Saudayawa a hukuncin Allah ko kaddarawarsa a halittawarsa a harshen hausa a kan yi amfani da kowanne a mahallin kowanne musamman da yake mutane sun fi bayanin abin aka riga aka kammala shi, tayiwu a wasu wurare su yi amfani da wadannan kalmomi kan a bin da ba a kammala shi ba, kamar yadda wani zai ga mai babur yana gudu sabanin ka'ida kuma a can gaba ga wata mota ta gindaya zata tsallaka, sannan sai ya ji karar jan burkin mashin din nan da sauti mai karfi, sai ya ce; Allah ya kaddara! ko ya hukunta!: Yana mai nufin cewa; a bisa abin da ya auna kuma ya kiyasta akwai sharuddan yin hatsari da suka kammala da suka hada da gudun da ya wuce misali da gindayawar mota da jan burki, wannan kuwa shi ne ma'anar kaddarawa. Amma kuma bayan an riga an yi hatsari to wannan aukuwar da faruwan tasa ta kasance an hukunta kenan.
Komadai wane irin abu ne muke nufi a kaddarawa da hukuntawa -kamar yadda muka ce bahaushe yana amfani da su da ma'ana daya- ba komai ba ne sai samarwa da halittawa da Allah yake yi, kuma muna iya karawa da cewa; wannan yana kama da fadinmu ne cewa; Allah ya kaddara wa rana ta rika juyawa tana motsawa a wurinta, kuma ya kaddarawa duniya ta rika motsawa tana juyawa a wurinta a lokaci guda kuma tana tafiya tana kewaye rana a shekara sau daya, wannan al'amarin yana kaddara samuwar dare da rana. Amma kuma bayan samun dare ko rana to wannan yana nufin an riga an hukunta hakan an riga an gama kamar yadda aka yi wa takarda da aka rubuta sitampin .
A cikin wadannan mas'alolin da suka shafi ayyukan bayi ne kafafu suka zame, don haka sai wasu jama'a suka tafi a kan tilasci kamar yadda ya gabata. Sai ka ga wani ya yi sata sai wasu su ce; an kaddara masa hakan ne, ko kuma ya ki daukar mataki da ya dace kan abu har ya faru sai a ce: an kaddara, ko kuma a ki canza wani abu da yana iya canzuwa kamar wani mutum ya zo ya take hakkin mutane sai ka ji an ce Allah ne ya kaddara hakan, kana iya ganin an yi magudi a zame sai kawai ka ji wani ya ce: Allah ya kaddara hakan ya ba wane mulki don haka sai saura su yi hakuri da hakan!
Idan muka ce Allah ne ya yi hakan kamar yadda mujabbira suke nufi cewa; shi ne ya yi hakan kai tsaye kamar yadda wuka take a hannun mai yanka to wannan yana iya komawa zuwa ga jingina wa Allah madaukaki tawaya da zalunci da aikata fasikanci da dukkan wasu ayyuka munana kamar kashe annabawa da salihan bayi -Allah ya nisanta daga haka-.
Don haka masu cewa; Allah ya kaddara mana wane ya kasance shugaba da ma'anar da mujabbira suke nufi, to sun jingina dukkan munana da zalunci ga Allah ne, kuma Allah ya barranta daga muradinsu da manufarsu da suke nufi suke jingina masa ita. Amma idan suna nufin Allah ya kaddara da ma'anar cewa ya tabar da ayyukan bayi da suka ki daukar mataki don haka sai ya ki kawo musu canji suka fada cikin bala'i yana gani ya kyale duk da zai iya canjawa amma ya sanya sharadin canjin shi ne su tashi tukuna, kuma ba zai gyara su ba sakamakon sakacin da suka yi suka bar hakkokinsu har ma wani mutum ya haye karagar mulki yana dandana masu kuda da azaba to wannan gaskiya ne kuma daidai ne, kuma muna iya cewa Allah ya kaddara kuma ya batar da wannan al'ummar idan dai suna nufin ya jingina su ga kawukansu kuma ya ki sanya rahama a cikinsu. Wannan kuwa yana komawa ne ga dokar Allah ta cewa; sai wanda ya yi kokarin neman shiriyarsa da datarwarsa ne yake taimaka, domin ba ya kawo canji sai mutane sun nemi canjin sannan sai ya kawo dauki.
Ra'ayoyin mujbira da ash'arawa da sufaye (sufayen da ba bisa tafarkin Ahlul Baiti (A.S) suke ba) suka samu ya taso ne daga musun sabuban da suke tsakatsaki wajen samar da halitta ko aiwatar da ayyukan halitta, domin idan muka duba zamu ga wanda ya yi kisa da wuka shi ne ake jingina wa kisa kuma shi ne ake hukuntawa, amma kwamandan da ya bayar da umarni aka yi kisa to ana iya jingina masa kisa kuma a jingina wa sojojinsa kisan domin suna da zabi kuma shi ma yana zabi. A wannan misalin da wani zai ce ayyukan nan na sojoji aiki ne na kwamanda kai tsaye kamar yadda wuka take a hannun mai kisa to ya yi kuskure, kuma a nan ne kafafun wadannan mutane da muka ambata suka zame, a nan ne suka sha kasa suka fadi warwas.
Don haka magana ta gaskiya muna iya cewa: kwamanda ya yi kisa kuma a hukunta shi kuma a ce sojoji sun yi kisa su ma a hukunta su, wannan kuma shi ne sahihin ra'ayi domin ba duk iri daya sabuba suke ba, sabuba suna da bambanci tsakaninsu domin akwai masu zabi kuma akwai marasa zabi, a nan muna iya ganin bayi suna da zabi kuma suna iya yi ko kuma su ki yi.
Kamar mai fadi ne (a wata waka ta Farisawa) da yake cewa: Dole ne ya sha giya, domin idan bai sha giya ba to ilimin Allah zai zama jahilci: yana nufin Allah ya kaddara masa dole sai ya sha giya, kuma sai ya dauki giya ya sha kuma ya kira wannan da cewa Allah ne ya kaddara. A nan muna iya cewa Allah ya halicci giya ta hanyar halittar tsabar da ake hadawa a yi giya kuma ya halicci tasiri tsakanin abubuwa da sinadirai kuma ya sanya tasiri cikin abubuwan da ake sarrafawa, don haka ne ma idan wani ya hada giya aka sha to za a iya buguwa sakamakon tasirin da Allah ya kaddara ya sanya a cikin wannan hade, wannan a batun halittawa kenan. Amma a game da shan wannan giya da hada ta da wannan ma'ana ba zai karbu ba domin shanta bisa zabi ne, kuma a fili yake cewa ba Allah ne ya yi shan bayi ba don haka ne ma bai yarda da shi ba kuma ya yi gargadin ukuba a kai, don haka ne ma idan wani ya sha giya sai aka ce Allah ya kaddara ya sha wannan giyar sai mu ce: idan ana nufin ya halitta giya sakamakon shi ne ya samar da wadannan sinadirai da tsirrai to haka ne amma idan kana nufin shi ya hada ta da kansa ya sha sai dai kawai ya yi amfani da wannan bawa ne wajen hada ta da shanta a nan sai mu ce; ka zo da wani abu mai muni kuma Allah ya barranta daga hakan. Haka nan idan ana nufin ya kaddara da ma'anar ya yi umarni da a sha a shar'ance sai mu ce wannan ma ya yi muni kwarai domin kage ne ga Allah kuma ba mu samu wani daga musulmi ya yi da'awar hakan ba, kamar yadda idan aka ce ai shi ya dauka ya sanya ta bakin mai sha kuma shi ya hadiyar masa da ita kamar yadda yake gun mujabbira, sai mu ce tir da wannan kauli da ya jingina dukkan nakasu da tawaya ga Allah madaukaki. Amma idan ana nufi ya kaddara da ma'anar ya tabar da wanda ya sha wannan giya ya kyale shi da halinsa kuma ya saka masa da mummunan aikinsa ta yadda ya yi tambele ko ya fada rami ko ya bige kansa ya ji ciwo to wannan haka ne. Haka nan idan aka ce: Allah ya kaddara wa wane ko su wane bata ko ya batar da al'umma kaza ko kuma ya shiryar da ita da cewa ba don Allah ya kaddara musu shiriya ba, da ba su shiriya ba, ko kuma ba don Allah ya kaddara musu bata ba, da ba su bata ba, wannan duka daidai ne idan aka cire tilasci a ciki.
Kuma muna iya ganin yadda Allah madaukaki ya ce; ya shiryar da Samudawa, a fadinsa madaukaki: "amma Samudawa sai muka shiryar da su, amma sai suka zabi makanta a kan shiriya" (fusilat: 17) a nan kalmar makanta tana nufin bata. Sannan kuma a fadin Allah madaukaki "mun shiryar da su" da zaka tambaya shin Samudawa sun shiryu sai a ce maka ba su shiryu ba, amma kenan shin Allah ya fadi sabanin gaskiya ne, sai mu ce; Allah ya barranta daga fadin sabanin gaskiya, to don me ya ce: ya shiryar da su!.
Idan aka ce: Allah ya kaddarawa Samudawa bata: ana nufin ya tabar da ayyukansu bai karba daga garesu ba kuma ya jingina su da kawukansu domin ba ya batar da mutane sai ya yi musun bayanin abin da zai tseratar da su (tauba: 115), wato Allah yana shiryar da mutane ne sannan kuma idan suka ki shiryuwa sakamakon zabinsu sai kuma ya batar da su, wato; idan ba su karba ba sai ya batar da su ya bar su da zabinsu, don haka muna iya cewa; ya batar da Samudawa. Saboda Allah yana cewa: "ba yadda za a yi Allah ya batar da mutane har sai ya yi musu bayanin abin da zasu ji tsoronsa" . Kuma a fili yake a zahiri sai da Allah ya yi wa Samudawa gargadi ya shiryar da su sannan kuma sai ya batar da su sakamakon hanyar da suka zaba. A nan muna iya ganin shiriya kala uku ce; shiriya takwiniyya, da tashri'iyya kuma Allah ya yi wa Samudawa da dukkan al'ummar duniya wadannan. Sai kuma shiriya taufikiyya wacce Allah bai bayar da ita ba sai ga wanda ya karbi wadannan na farko ya yi amfani da su kamar yadda Allah ya so, amma bayaninsu zai iya kawar da mu daga abin da muke magana yanzu.
Idan ka ce: Allah ya shiryar da Samudawa wato; ana nufin ya kaddara musu shiriya a shar'ance kenan domin aiko musu annabi (A.S) da ya isar musu da sako. Haka nan ya yalwata musu rayuwa ya tanadar musu duk wani abu da zai kai su ga shiriya ya ba su hankali da zabi da nufi da iko wannan kuwa yana nufin ya kaddara musu shiriya a nau'in halittarsu kenan.
Ya Ubangijin Muhammad da Ali! Ubangijinmu! girmanka ya daukaka, daukakarak kuwa ba shi da iyaka! kai kadai ne kake iya hada wadannan siffofi, don haka ka shiryar da mu kada ka batar da mu, ka hada siffofin da azahiri ba sa haduwa kuma duka daya ne kuma gaskiya ne, ka batar da adawa kuma ka shiryar da su a lokaci guda! Kuma wannan ayoyi suna nuna mana babban sirrin da yake cikin cewa Allah ba ya tilasta bayinsa kuma suna da zabin kansu. A irin wannan muna iya ganin an samu wani wanda ya hada tanakudin kur'ani a sama da tsawon shekaru ashirin -domin ya nuna yadda Allah madaukaki ya yi ta tanakudi a littafinsa- domin ya rusa sakon Allah, sai ga shi a rana daya ya hadu da imami (A.S), kuma wannan haduwar ta sanya shi ya tuba ya yaga dukkan abin da ya tara kusan rabin karni guda saboda ganin cewa; shi ne bai fahinci maganar Allah ba mai cike da hikima da kamala.

Shin Tilasci Ga Bayi Ya Inganta?
Sai dai mun samu wasu hadisai da suka zo suna nuna cewa Allah ya tilasta bayi a ayyukansu ta yadda ba su da wani zabi kamar ruwayoyi masu cewa: Alkalami ya bushe da abin da zai same ka. (buhari daga abu huraira j 8, shafi 44, bugun alkahira). Da hadisan da suka yi nuni da rubuta komai na ajali da arziki a cikin mahaifiya, ta yadda koda saura zira'i daya ne ya mutu sai ya yi aikin 'yan'wuta sai ya shige ta. (Buhari, j 8, babin kaddara, shafi: 122). Da hadisan da suke nuna kowane mutum ya yi aiki, domin kowanne an saukake masa abin da aka halitta shi dominsa ne. (Muslim, j 8, shafi: 44). Akwai hadisai masu yawa da suke nuni da hakan, kana iya duba (jami'ul usul, j 10, babin kaddara, hadisi na 7555, shafi: 513. Da ruwayoyi masu cewa: Ubangiji madaukaki ya ce: wadannan suna wuta ba ruwana, wadannan kuma suna aljanna babu ruwana.
Muna iya cewa da an fassara wadannan ruwayoyi da kasancewar wannan a ilimin Allah ne to da sai bahasin ya koma na palsapa sai dai akwai tambayoyi da zasu iya zama a kwakwale kamar cewa; don me wannan ya kebanta da cikin mahaifiya! hada da cewa masu kawo ruwayoyin da masu bayaninsu duk sun fassara shi da fassarar da ba ta nuni da ilimin Allah. Kuma tayiwu wani ya ce: kalmar ciki a nan tana nufin faruwar bawa ta yadda babu ma'ana ga kebantar wannan da ciki, sai kenan ma'anar ciki ta kasance tana nuna mahallin samuwar mutum ne da yana iya kasancewa duniyar barzahu ta farko wato duniyar ZARR (ko kuma duniyar barzahu a gangarowar samuwar rayukan mutane kafin su zo duniya wacce ta saba da ta biyu wacce take a lokacin komawar rayuka zuwa ga Allah madaukaki) ga wanda ya yi imani da ita kenan, domin ilimin Allah bai takaita da ciki ba.
Amma idan muka duba abin da wannan hadisai suke nufi kamar yadda muka yi nuni suna duba ne kai tsaye ga ayyukan Allah mahallici ta yadda zai kai ga tilascin ayyuka da cire wa dan Adam zabinsa da muka yi nuni da cewa hukuncin Allah da kaddarawarsa ba sa cire wa mutum zabin kansa, to sai mu ga wadannan hadisai sun yi hannun riga da koyarwar musulunci da ta tabbata ta ingantacciyar hanya, hada da cewa manyan malamai masana Allah (S.W.T) sun rushe su daga inganci.
AyatulLahi ja'afar subhani yana fada (Ilahiyyat, shafi 551). "Kai kace kaddara wani abu ne mai hukunci mai kekasar zuci mai wauta maras rahama mai mugun kulli a kan bayi don haka babu wata damar samun rahamarsa madaukaki da kyautatawarsa". A dai wannan shafin yana fada cewa: "Wadannan ruwayoyin sun saba da abin da ya zo a kur'ani da sunna domin littafin kur'ani yana nuna dan Adam a matsayin wani halitta ne mai zabin kansa, kuma shiriyarsa da batansa suna wuyansa". Sannan sai ya kawo ayoyi kamar fadinsa madaukaki:
"Mu mun shiryar da shi tafarki, imma dai ya kasance mai godiya ko mai yawan butulcewa". Insani (Dahari: 3). Da fadinsa madaukaki: "Ka ce idan na bata kawai ina fatar da kaina ne, idan kuma na shiriya to sakamakon abin da Ubangijina yake yi mini wahayinsa ne, hakika shi mai ji ne makusanci". (Saba': 50). Da fadinsa madaukaki: "Hakika hasken shiriya sun zo muku daga Ubangijinku, duk wanda ya ga hanya (shiriya) to ga kansa ne (amfanin yake) wanda kuwa ya makance (ya bata) to yana kansa ne…" (An'am: 140).
Ina ganin akwai maganganu masu yawa game da wannan da magana kan su yake tsawaita, kuma a cikin abin da muka kawo a takaice akwai isarwa ga wanda ya kasance yana neman tunatarwa, ko kuma wanda yake da zuciyar lura ya sanya idanuwansa da kunnuwansa na basira. Allah ka taimaka mana shiriyar kanmu kada ka tabar da mu da batan kanmu.