Yin Takiyya
  • Take: Yin Takiyya
  • marubucin: Allama Muhammad Muzaffar
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:52:45 13-9-1403

Wallafar: Allama Muzaffar Fassarar: Hafiz Muhammad
Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Bahasin Takiyya An ruwaito daga Imam Sadik (A.S) a sahihin hadisi cewa: "Takiyya addinina ce kuma addinin iyayena ce". Da kuma "Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi". Haka nan takiyya ta kasance taken Ahlul Baiti (A.S) wajen kare kai daga cutar da su da kuma mabiyansu, da kare jininsu, da kawo gyara ga halin da musulmi suke ciki, da kuma hada kansu. Takiyya ba ta gushe ba a matsayin alama da ake sanin shi'a da ita tsakanin sauran bangarori na al'ummu, kuma dukkan mutum idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yarda da abin da ya yi imani da shi, ko kuma bayyanar da shi a sarari, to babu makawa ya boye, ya kiyaye a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi'ar hankali take hukunci da shi. Kuma sannanen abu ne cewa Shi'a da lmamansu sun sha nau'o'in jarrabawa da matsa lamba na tsawon zamani da babu wata jama'a da ta sha irinta. Wannan al'amari ya tilasta su a mafi yawan lokutansu su yi amfani da takiyya, suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyanarwa, da suturta akidunsa, da ayyukan da suka kebanta da su, saboda abin da yake biyo bayan hakan na daga cutuwa a addini da duniya, wannan shi ne ya sanya suka bambanta da takiyya, aka kuma san su da ita.
Takiyya tana da hukunce-hukunce ta fuskacin wajabcinta da rashin wajabcinta daidai gwargwado sassabawar wuraren tsoron cutuwa da aka ambata a babobinta a littattafan fikihu. Ita ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya zama halal, ko saba mata ya zama wajabi ne a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga Addini, da hidima ga Musulunci, da jihadi a tafarkinsa, to a wannan hali dukiya ba komai ba ce, kuma ba za a fifita rai ba. Takiyya tana iya zama haram a ayyukan da sukan iya kai wa ga kashe rayuka masu alfarma, ko yada karya, ko barna a Addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su, ko kuma yada zalunci da ketare haddi a tsakaninsu.
A kowane hali dai, takiyya a gun Shi'a ba ta mayar da su wata kungiyar asiri, domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi'a marasa fahimtar al'amura suke surantawa, kuma suka ki dora wa kansu nauyin fahimtar ra'ayi ingantacce. Kamar yadda ba ta sanya Addini da hukunce-hukuncensa su zama wani sirri daga asiran da bai halatta a bayyana su ga wanda ba ya imani da su ba, al'amarin bai zama haka ba, alhalin littattafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu na fikihu, da hukunce-hukunce, da bahasosin akida, sun cika gabas da yamma, sun ma wuce yadda ake tsammani daga kowace al'umma da take da wani addini.
Wadanda suke son aibata shi'a sun samu damar amfani da akidarmu ta takiyya, suka sanya ta daga abubuwan da suke sukan su da ita, kamar dai ba sa iya kashe kishirwar gabarsu sai da fille wuyayensu da takubba, da tumbuke asalinsu gaba dayansu a wadancan zamunan da suka gabata, da ya isa a ce wannan dan shi'a ne ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Baiti (A.S) na daga Umayyawa, da Abbasawa, da kuma Usmaniyawa. ldan sukan mai son suka ya dogara ne da abin da yake raya rashin shar'ancinsa a addini, to mu sai mu ce masa:
Na Farko: Mu masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S) kuma muna bin shiriyarsu ne, kuma su ne suka umarce mu da ita suka wajabta ta a kanmu a lokacin bukata, ita tana daga addini a wajensu, kuma ka ji fadin Imam Sadik (A.S) da yake cewa: "Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi."
Na biyu: Shar'anta ta kuma ya zo a Kur'ani mai girma, da fadarsa madaukaki: "Sai dai wanda aka tilasta shi alhalin zuciyarsa kuwa tana nutse da imani". Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar Dan Yasir da ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan Musulunci. Da kuma fadinsa madaukaki: "Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya". Surar Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa: "Kuma wani mutum daga mutanen fir'auna yana mai boye Imaninsa Ya ce". Surar Gafir: 28.