Kadaitar Ubangiji
  • Take: Kadaitar Ubangiji
  • marubucin: Allama Muhammad Muzaffar
  • Source:
  • Ranar Saki: 21:35:36 1-10-1403

Wallafar: Mujaddadi Sheikh Ridha Muzaffar Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Imam Mahadi (A.S) yana cewa: “Kuma Kowane mutum daga cikinku ya yi aiki da abin da zai kusanta da shi zuwa ga soyayyarmu, kuma ya nisanci abin da zai kusantar da shi ga kinmu da fushinmu” Biharul Anwar: 53, shafi 126.

1-Sani Da Nazari Kan Samuwar Allah Mun yi imanin cewa saboda baiwar da Allah ya yi mana ta karfin tunani da kuma kyautar hankali, to ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Za mu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya ne”. Surar Fussilat: 53
Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai ba”. (Surar Bakara: 170)
Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zato”. Surar An’am: 116
A hakika mu abin da muke yin imani da shi shi ne cewa: Hankulanmu su ne suke wajabta mana yin tuntuntuni kan halittu da sanin mahallicin duniya, kamar yadda suke wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da’awar annabta da kuma mu’uijzarsa. Kuma bai inganta ba -a hankalce- a yi koyi da wani a cikin wadannan al’amuran komai matsayinsa da darajarsa. Abin da ya zo a cikin Alkur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali da ra’ayoyin ma’abota hankali suka ginu akansu, ya kuma zo ne don fadakar da mutane abin da aka halitta su a kansa na sani da hankaltuwa da tunani da kuma fadada tunani da fuskantarwa zuwa ga abin da hankula suke hukunci da shi. Ba daidai ba ne -a irin wannan hali- mutum ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane masu tarbiyyantarwa kan wata akida ko wasu mutanen daban. A’a ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa[4] wadanda ake kira shika-shikan Addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne: Tauhidi -Kadaita Allah-, da Annabci, da Imamanci, da kuma Tashin kiyama. Duk wanda ya yi koyi da iyayensa ko kuma wasunsu a imani da wadannan shika-shikan to lalle ya ketare iyaka ya fandare daga hanya madaidaiciya, kuma ba zai taba zama abin yi wa uzuri ba har abada.
A takaice dai mu muna da’awar abubuwa biyu ne:
Na Farko: Wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba.
Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne na hankali kafin ya zamanto na shari’a, wato saninsa bai samo asali daga nassosin Addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi. Kuma ba komai ake nufi da ma’anar wajabcin hankali ba sai riskar hankali ga larurar sani da kuma lizimtar yin tunani da kokarin bincike a cikin shika-shikan Addini.

2- Koyi Da Wani A Rassan Addini Amma rassan al’amuran Addini su ne hukunce-hukuncen shari’a wadanda suka shafi ayyuka, su bai wajaba ba a yi nazari da ijtihadi a kansu ba, wajibi ne a cikin rassan hukunce-hukucen addini idan ba laruran Addini ne ba ne kamar wajabcin salla, da zakka, da azumi, da hajji, mukallafi ya yi dayan al’amura uku a cikinsu:- Ko ya yi ijtihadi[5] ya yi bincike a kan dalilan hukunce-hukunce idan yana cikin masu iya yin hakan, ko kuma ya zama mai ihtiyadi idan zai iya yin ihtiyadi[6], Ko kuma ya yi koyi da Mujtahidin da ya cika sharruda. Ya kasance wanda zai yi takalidi da shi mai hankali ne, Adali, mai kare kansa, mai kiyaye Addininsa, mai saba wa son ransa, mai bin umarnin Ubangijinsa. Duk wanda ba Mujtahidi ba ne, kuma ba mai yin ihtiyadi ba, kuma bai yi koyi da mujtahidin da ya cika sharudda ba, to dukkan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, ko da kuwa ya yi salla, ya yi azumi, ya yi ibada duk tsayin rayuwarsa, sai dai idan aikinsa ya dace da ra’ayin wanda yake yi wa takalidi kuma ya yi sa’ar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah (S.W.T).

3- Ijtihadi Mun yi Imanin cewa: ljtihadi a rassan hukunce-hukuncen shari’a wajibi ne kifa’i[7] da ya doru a kan dukkan musulmi a zamanin boyuwar Imam, wato ya wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Sai dai idan wadanda suka wadatar sun dauki nauyin yi, to ya saraya daga kan sauran musulmai, sai su wadatu da wanda ya dauki nauyin yin hakan kuma ya kai ga matsayin ijtihadi kuma ya cika sharuddan, sai su yi masa takalidi, su koma masa a cikin al’amuran hukunce-hukuncen Addininsu.
A kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami wanda ya sadaukar da kansa a tsakaninsu ya kai ga matsayin Ijtihadi wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo, kuma ya kasance ya cika sharuddan da ya cancanci a yi masa takalidi, sai su wadatu da shi su yi masa takalidi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen Addininsu. Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to ya wajaba a kan kowane daya daga cikinsu ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya wanda zai dukufa domin kai wa ga wannan matsayi a tsakaninsu, tunda ba zai yiwu ba dukkansu su dukufa domin neman wannan al’amari ko kuma zai yi wahala, Kuma bai halatta ba su yi takalidi da wanda ya mutu na daga cikin Mujtahidai.
Ijtihadi: Shi ne nazarin dalilan shari’a domin samun sanin hukunce-hukuncen shari’ar da shugaban Manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta sakewa ko canzawa da canzawar zamani da kuma halaye. “Halal din Muhammad (S.A.W) halal ne har zuwa ranar Tashin Kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa Ranar Tashin Kiyama.
Dalilan shari’a su ne: Alkur’ani mai girma, da Sunna, da Ijma’i, da Hankali kamar yadda yake dalla-dalla a littattafan Usulul Fikhi.
Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar sani mai yawa da ilimi wandanda ba sa samuwa sai ga wanda ya dage ya yi kokari ya cire nauye-nauyen da suke a kansa ya bayar da kokarinsa domin samunsa.

4- Mujtahidi Abin da muka yi imani da shi game da mujtahidi wanda ya cika sharudda cewa shi wakilin Imami (A.S) ne a halin boyuwarsa, kuma mai hukunci, shugaba cikakke, abin da yake ga Imami (A.S) na koma wa zuwa gareshi a al’amura da hukunci a tsakanin mutane yana gare shi kuma duk wanda ya ya yi raddi gareshi tamkar mai raddi ne ga Imam (A.S) wanda kuma ya yi wa imami raddi to ya yi wa Allah, wannan kuma yana matsayin shirka da Allah ne kamar yadda ya zo a hadisi daga Imam Sadik (A.S).
Shi Mujtahidin da ya cika sharruda ba wai makoma ba ne na mutane a fatawa kawai ba, a’a yana da jagoranci na gaba daya, sai a koma zuwa gare shi a hukunci da raba gardama da shari’a, wannan duk yana daga cikin abubuwan da suka kebance shi, bai halatta ba ga wani ya dauki nauyinsu sai da izininsa, kamar yadda bai halatta ba a yi haddi ko ladadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa. Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebance shi. Wannan matsayin ko shugabanci na gaba daya imami ne ya bayar da shi ga Mujtahidin da ya cika sharudda domin ya zama wakilinsa mai maye gurbinsa a lokacin fakuwarsa, shi ya sa ma ake cewa da shi “Na’ibin Imam”.


FASALI NA FARKO 5- Ubangiji Madaukaki Mun yi imani cewa Allah Madaukaki daya ne makadaici babu wani abu kamarsa, magabaci ne bai gushe ba kuma ba ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai Hikima, Adali, Rayayye, Mai Iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jauhar[8] ba ne kuma ba ard[9] ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi. Gannai ba sa riskarSa Shi kuwa yana riskar gannai.
Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (A.S), mamakin kyawun wannan bayani mai hikima! Mamakin wannan abin nema na ilimi mai zurfi!` .
Haka nan ana kirga duk wanda ya ce yana nuna kansa ga halittunsa ranar Kiyama a cikin kafirai[10] koda kuwa ya kore masa kamantawa da jiki, batun baka ne kawai, kuma irin masu wannan da’awa sun sandare ne a kan zahirin laffuzan Kur’ani ko hadisai, kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su, suka kuma kasa yin amfani da aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai da ka’idojin aron kalma, da kuma ka’idojin aron ma’anar kalma suke.

6- Kadaita Allah (S.W.T) Mun yi imani cewa ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, kuma mun yi imani da cewa shi kadai ne a zatinsa da wajabcin samuwarsa, kamar yadda muka yi imani da kadaita shi a siffofi da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan. Mun kuma yi imani da cewa ba shi da kama da shi a siffofinsa, shi a ilimi da kudura ba shi da tamka, a halittawa da arzutawa ba shi da abokin tarayya, a cikin kowace kamala ba shi da kini. Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (S.W.T), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu.
Amma ziyartar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi’a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin al’amarin, shi ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (S.W.T) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar ‘yan’uwa na Addini, da kuma taimakon talaka. Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (S.W.T) ko kuma shirka a bautarSa. Haka nan sauran kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda suka hada da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da kai janaza da kuma ziyartar ‘yan’uwa.
Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan Addini suna daga kyawawan ayyuka a shari’a wannan al’amari ne da ya tabbata a fikihu, ba nan ne wajan tabbatar da shi ba. Abin da muke so mu yi bayani a nan shi ne; gudanar da irin wadannan ayyuka ba ya daga cikin irin nau’o’in shirka da Allah kamar yadda wasu suke rayawa, ba kuma bautar imamai ba ne, sai dai abin da ake nufi shi ne raya al’amuransu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “wannan, duk wanda Ya girmama alamomin Addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukata”. Surar Hajj: 32.

7- Siffofin Ubangiji (S.W.T) Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa akwai siffofi tabbatattu na hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi, da iko, da wadata, da irada -nufi-, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne da suke kari a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala. Na’am siffofinsa sun sassaba a ma’anoninsu ne ba a hakikaninsu da samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.
Tabbatattun siffofi na idafa[11] kuwa, kamar halittawa, da arzutawa, da gabatuwa, da kuma samarwa, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da kuma la’akari daban-daban.
Amma siffofin da ake kira salbiyya -korarru- wadanda ake kiransu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore kasancewarsa mai yiwuwar samuwa[12] ba wajibin samuwa ba, abin da yake nufin kore jiki, da sura, da sura, da motsi, da rashin motsi, da nauyi, da rashin nauyi, da makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa. Sannan kuma kore kasancewarsa ba wajibin samuwa ba yana tabbatar da kasancewarsa wajibin samuwa, wajabcin samuwa kuwa yana daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah (S.W.T) kuwa Makadaici ne ta kowace fuska, babu yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawa a hakikaninsa makadaici sidif.
Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra’ayin cewa siffofi tabbatttu suna komawa ne zuwa ga siffofi salbiyya, saboda ya kasa gane cewa siffofin Allah su ne ainihin zatinsa, sai ya yi tsammanin cewa siffofi tabbatattu suna komawa zuwa korewa ne domin ya samu nutsuwar imani da kadaitakar zati da rashin kididdigarsa, amma sai ya fada cikin abin da yake mafi muni saboda sanya ainihin zati wanda shi ne ainihin samuwa, kuma tsantsar samuwa wanda ba shi da wata nakasa ko wata fuska ta siffar yiwuwar samuwa. Sai ya sanya shi ya zama aininin rashi kuma tsantsar korarre[13], Allah ya kiyaye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma zamewar duga-dugai. Kamar yadda mamaki ba ya karewa ga wanda yake da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya -tabbatattu- kari ne a kan zatinSa, ya yi imani da kididdigar zatin Allah wajibin samuwa, da samuwar ababan tarayya[14] gareshi, ko kuma wannan magana tasa ta kai shi ga imani da hauhawar zatinsa madaukakin sarki. Shugabanmu Amirul Muminin (A.S) ya ce:
Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi[15], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuma ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya gididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: Akan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin[16].

8- Adalcin Allah Mun yi imani cewa yana daga siffofin Allah madaukaki tabbatattu na kamala cewa shi adali ne ba azzalumi ba, ba ya take hakki a shari’arsa ba ya zalunci a hukuncinsa, yana saka wa masu biyayya kuma yana da hakkin hukunta masu sabo, ba ya kallafawa bayinsa abin da ba zasu iya ba, kuma ba ya yi musu ukuba fiye da abin da suka cancanta.
Kuma mun yi imani cewa Ubangiji ba ya barin aikata abu mai kyau matukar ba wani abin da zai hana aikata shi, kuma ba ya aikata mummuna saboda Shi mai kudura ne a kan ya aikata kyakkyawa ko ya bar mummuna, tare da cewa yana da sani game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna, da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan, babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balle ya bar shi, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarsa balle ya aikata shi, tare da cewa shi mai hikima ne ba makawa aikinsa ya kasance ya dace da hikima kuma a bisa tsari mafi kamala.
Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki to da al’amarin hakan ba zai rabu da daya daga cikin surorin nan hudu ba:
1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa mummuna ba ne.
2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma gajiya ga barin aikata shi.
3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma gajiya ga barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa.
4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya takaita ke nan a kan cewa aikisa ya zama bisa sha’awa da wasa.
Dukkan wadannan surori sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna.
Sai dai kuma wasu sashen musulmi sun halatta wa Allah (S.W.T) aikata mummuna, suka halatta cewa zai iya azabtar da masu biyayya, ya kuma shigar da masu sabo aljanna kai hatta kafirai ma, kuma suka halatta cewa yana iya dora wa bayinsa abin da ya fi karfinsu da abin da ba zasu iya ba, tare da haka kuma ya azabtar da su a kan ba su aikata ba. Kuma suka halatta zalunci da danne hakki, da karya da yaudara ga Allah madaukaki, da kuma aikata aikin da babu wata hikima, da manufa, da maslaha, da fa’ida, da hujjar cewa shi: “Ba a tambayar sa a kan abin da yake aikatawa amma su ana tambayar su”. Surar Anbiya: 23. Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan Akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, Ja’iri, mai wauta, mai wasa, makaryaci, mai yaudara, da yake aikata mummunan aiki yana barin kyakkyawa, Allah ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa[17]. Kuma Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
“Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayi”. Surar Mumin: 23.
“Kuma Allah ba ya son barna”. Surar Bakara: 31
“Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu muna Masu wasa ba”. Surar Dukhan: 205.
“Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini”. Surar Zariyat: 56. Da sauran ayoyi masu girma, tsarki ya tabbata gareka ba ka halicci wannan don barna -rashin manufa- ba.

9- Hawan Hukunci A Kan Baligi Mun yi imani cewa Allah (S.W.T) ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani.
Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
Kuma mun yi imani cewa: Babu makawa Allah madaukaki ya kallafa wa bayinsa ayyuka ya kuma sanya musu shari’o’in abin da yake na maslaharsu da alherinsu da rabautarsu ta har abada, ya kuma gargade su ga barin abin da yake akwai barna da cutuwa a kansu da mummunan karshe gare su, ko da kuwa ya san cewa su ba zasu bi Shi ba, domin wannan tausasawa ce da kuma rahama ga bayinSa domin su suna jahiltar mafi yawancin maslaharsu da hanyoyin samunta a nan duniya da kuma lahira. Suna kuma jahiltar da yawan abubuwan da zasu jawo musu cutarwa da tabewa, Shi kuwa Ubangiji Shi ne Mai Rahama mai Jin kai, kuma Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa da yake mustahili ne ya rabu da shi har abada.
Ba ya janye wannan tausasawa da wannan rahama domin kasancewar bayinsa sun bujire wa bin sa, sun ki bin abubuwan da ya yi umarni da abubuwan da ya hana.

10- Hukuncin Allah Da Kaddara Mujabbira[18] sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan halittu, sai ya zamanto ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, kuma ya tilasta su a kan aikata abin da ya yi umarni tare da haka ya ba su lada, domin sun tafi akan cewa ayyukansu tabbas ayyukanSa ne, ana dai danganta ayyukan ne garesu saboda rangwame domin su ne mahallin ayyukan Ubangiji. Asalin wannan kuwa domin su sun yi inkarin sababi na dabi’a tsakanin abubuwa[19], suna ganin Allah madaukaki ne yake aikata komai bisa hakika. Sun yi musun wannan sababi ne saboda tsammanin cewa hakan shi ne ma’anar kasancewar Ubangiji mahalicci, da ba Shi da abokin tarayya, amma duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa ya tsarkaka daga hakan.
Mufawwada[20] kuma sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, da la’akari da cewa; danganta ayyukan gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi ne, kuma halittu suna da nasu sababan na musamman duk da cewa dukkansu suna tukewa ne zuwa sababi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T). Duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa, hakika ya fitar da Allah daga mulkinSa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa.
Abin da muka yi imani da shi a nan muna masu biyayya ga abin da ya zo daga lmamanmu tsarkaka da suke cewa al’amari ne tsakanin al’amura biyu, al’amarin da irin wadannan masu jayayya daga malaman ilimin sanin Allah suka kasa fahimtarsa, wasu kuma suka takaita, wasu kuma suka zurfafa, babu wani daga cikin masana ilimi da ma’abuta falsafa da ya fahimce shi sai bayan karnoni masu yawa. Ba abin mamaki ba ne ga wanda bai tsinkayi hikimar Imamai (A.S) dangane da al’amari tsakanin al’amura biyu ba, ya yi tsammanin cewa wannan magana ta al’amari ne tsakanin al’umara biyu tana daga abin da malaman falsafa na turai na wannan zamani suka gano, alhali kuwa Imamanmu sun rigaye su tun kafin karnoni goma da suka wuce.
Imam Sadik (A.S) ya fada yana mai bayanin hanyar nan matsakaiciya da cewa: “Babu Tilastawa kuma babu fawwalawa sai dai al’amari ne tsakanin al’amuran guda biyu.
Wannan kalma ta girmama! Ma’anarta ta zurfafa! A takaice abin nufi shi ne; Hakika ayyukanmu a bangare guda ayyukanmu ne bisa hakika kuma mu ne sababinsu na dabi’a kuma suna karkashin ikonmu da zabinmu, a daya bangaren kuma suna karkashin kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin mulkinsa, domin Shi ne mai ba da samuwa mai bayar da ita, bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana ya zama ya zalunce mu idan ya yi mana azaba a kan sabo, domin muna da iko da kuma zabi a kan abin da muke aikatawa. Kuma bai fawwala mana samar da ayyukanmu ba ballantana ya zamanto ya fitar da su daga karkashin ikonsa ba, al’amarin halittawa da hukuntawa da umarni duka nasa ne, kuma shi mai iko ne a kan komai kuma masani da bayinsa.
Ta kowane hali, imaninmu shi ne hukuncin Allah da kaddarawarSa sirri ne daga asiran Allah (S.W.T) duk wanda ya iya fahimtarsa yadda ya dace ba tare wuce gona da iri ba ko kuma takaitawa ba, to wannan ya yi, in ba haka ba, bai wajaba a kansa ba ya kallafawa kansa fahimta da zurfafawa a cikinsa ba, domin gudun kada ya bata, akidarsa ta lalace, domin wannan yana daga al’amura masu zurfi, kai yana daga mafi zurfin bahasosin falsafa wadanda ba mai gane so sai daidaikun mutane, kuma duga-dugan da yawa daga malaman ilimin akida sun zame, kallafa wa kai fahimtarsa, kallafa wa mutum maras ilimi mai zurfi ne da abin da yake sama da ikonsa.
Saboda haka ya wadatar mutum ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga fadin Imamai tsarkaka (A.S) cewa; shi wani al’amari ne tsakanin al’amura biyu, babu tilastawa babu kuma fawwalawa a cikinsa, kuma shi ba ya daga cikin shika-shikan akida ballantana kudurcewa da shi dalla-dalla da zurfafawa su zama wajibi ko ta halin kaka.

11- Bada'in Allah Madaukaki “Bada” ga mutum; shi ne wani sabon ra’ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra’ayin ba, wato ya canja niyyarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi domin faruwar wani abu gareshi da zai sanya canji a ra’ayinsa da saninsa, sai ya canja niyya sai ya bar aikata shi bayan da can yana nufin ya aiwatar da shi, wannan kuwa ya faru ne sakamakon jahiltar maslaha da kuma yin nadama a kan abin da ya gabata. “Bada” da wannan ma’anar mustahili ne ga Allah (S.W.T) domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa, wannan kuwa ya koru ga Ubangiji, kuma Shi’a Imamiyya ba su yarda da shi ba. Imam Sadik (A.S) ya ce: “Wanda ya yi da’awar cewa canji cikin wani abu ya faru ga Allah (S.W.T) game da wani abu canji irin na nadama, to a gurinmu wannan ya kafirta da Allah mai girma”. Kuma ya ce: “Wanda ya raya cewa wani abu na canjin ra’ayi ya faru ga Allah wanda ya kasance bai san shi ba jiya to ka barranta daga gareshi”.
Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kusan nuni da ma’anar “Bada” kamar yadda ta gabata, kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (A.S) cewa: “Wani abu bai taba bayyana ba ga Allah kamar yadda ya bayyana gareshi game da Isma’ila dana”. Don haka ne wadansu daga marubutan musulmi suka danganta Bada ga Shi’a Imamiyya da waccan ma’ana domin suka ga mazhaba kuma tafarki na Ahlul Baiti (AS), suka sanya wannan daya daga abubuwan da suke suka da aibata shi’a da shi. Sahihiyar magana a nan ita ce, mu muna fadi kamar yadda ubangiji ya fada a littafinsa ne cewa:
“Allah yana shafe abin da ya so kuma yana tabbarwa kuma Ummul kitab a gunsa take ”. Surar Ra’ad: 39.
Abin nufi shi ne cewa Allah (S.W.T) na iya bayyanar da wani abu ta harshen Annabinsa ko waliyyinSa ko kuma a zahiri saboda wata maslaha da ta sanya bayyanawar, sa’annan daga baya sai ya shafe shi ya zama ba abin da ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma’il (A.S) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S) Ya ga yana yanka shi a mafarki. A nan sai ma’anar maganar Imam Sadik (A.S) ta zama cewa: Babu wani abu da ya bayyana ga Allah (S.W.T) a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma’ila dansa yayin da ya dauki ransa kafin rasuwar Imam Sadik (A.S) domin mutane su san cewa shi Isma’ila ba Imami ba ne, bayan a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.
Wani abu da yake kusa da ma’anar “Bada” shi ne shafe hukunce-hukuncen shari’o’in da suka gabata da shari’ar Annabinmu Muhammadu (S.A.W) da kuma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen da Annabinmu (S.A.W) ya zo da su.

12- Hukunce-Hukuncen Addini Mun yi imani cewa Ubangiji ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ayyukansu, abin da maslaharsa ta zama tilas sai ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da take tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa a garemu ta zama mai rinjaye ya soyar da shi - mustahabbi- a garemu.
Wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa, kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hukuncin Allah a kansa koda kuwa hanyar saninsa ta toshe garemu. Kuma hakika yana daga mummuna ya zama ya yi umarni da abin da yake akwai barna a cikinsa, ko kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Sai dai wasu daga daga cikin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne abin da Ubangiji ya hana kawai, kyakkyawa kuwa shi ne abin da ya yi umarni da shi, babu wata maslaha ko cutuwa a cikin ayyukan su a kan-kansu, wannan magana kuwa ta saba wa hukuncin hankali.
Kamar yadda suka halatta wa Allah ya aikata mummuna ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Hakika ya gabata cewa wannan magana akwai ketare iyaka -sabo- mai girma a cikinta, ba domin komai ba sai domin lizimta danganta jahilci da gazawa ga Allah (S.W.T).
A takaice dai abin da yake ingantacce a yi imani da shi, shi ne : Ubangiji madaukaki ba shi da wata maslaha ko amfani a cikin kallafa mana wajibai da hana mu aikata haram, maslahar wannan duk tana komawa zuwa garemu ne, babu wata ma’ana wajen kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni da su ko hani ga barin su, domin Allah ba ya hani kara zube don wasa, kuma shi mawadaci ne ga barin bayinsa.