Tabbatar Kiyama
  • Take: Tabbatar Kiyama
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 21:19:40 1-10-1403

Hafiz Muhammad hfazah@yahoo.com Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Tashin Kabari Da Tashin Kiyama Mun yi imani da cewa Ubangiji zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawarinta, sai ya saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo, wannan al'amari ne da baki dayansa da abin da ya tattara na daga sauki, abu ne wanda dukkan shari'o'in da aka saukar daga sama da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai, kuma babu wata madogara ga musulmi sai dai ya yi imani da akidar Kur'ani mai girma wacce Annabinmu mai girma ya zo da ita, domin duk wanda ya yi imani da Allah imani yankakke, ya kuma yi imani da Muhammad manzo ne daga gare shi, wanda ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya, to babu makawa ya yi imani da abin da Kur'ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni'ima, da wuta da kuna, kuma Kur'ani ya bayyana haka a sarari, kuma ya yi nuni da shi a cikin abin da ya kai kusan ayoyi dubu.
Idan har shakku ya samu wani game da wannan, ba don komai ba ne sai domin yana shakku game da ma'abocin sakon, ko kuma game da samuwar mahaliccin halittu da kudurarsa, ba komai ba ne sai shakkun da yake bujuro masa game da asalin addinai dukkaninsu, da kuma ingancin shari'o'i gaba dayansu.

Tayar Da Mamata Tayar da mamata wani al'amari ne da yake larura daga laruran Addinin Musulunci, Kur'ani mai girma ya yi ishara game da shi: "Shin mutum yana tsammanin ba zamu tattara kasusuwansa ba ne. A'aha, Lalle mu masu iko a kan mu daidaita yatsunsa ne". Surau Alkiyama: 3. Da fadinsa: "Idan kayi al'ajabi to abin al'ajabi ce maganarsu cewa ashe idan muka mutu muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa". Ra'ad: 5. Da fadinsa: "Shin mun gajiya ne da halittar farko, sai dai su suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta". Surar Kaf: 14.
Tayar da mamata ba wani abu ba ne sai dawo da mutum ranar tashin kiyama da jikinsa bayan rididdigewa, da sake dawo da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge. Ba wajibi ba ne a yi imani da dalla-dallan tayar da mamata fiye da abin da Kur'ani ya ambata, ko sama da abin da ya fada na daga; Hisabi, da Siradi, da Auna ayyuka, da Aljana, da Wuta, da Sakamako, da Ukuba, daidai gwargwadon abin da bayaninsa ya zo a cikin Kur'ani mai girma.
"Bai wajaba ba sanin hakikar da babu mai iya kai wa gareta sai ma'abocin zurfin ilimi, kamar ilimin cewa shin jikin mamata zasu dawo ne da kan kansu ko wasu makamantansu ne? Kuma shin rayuka zasu rasu ne kamar jikin mamata ko kuwa zasu ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jikinsu yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanci mutum ne ko ya hada har da dukkan dabbobi ne? Kuma shin tashin a lokaci daya ne ko a sannu-sannu ne? Kuma idan yin imani da Aljanna da Wuta wajibi ne, amma bai zama dole a san cewa samammu ne a halin yanzu ba, ko kuma sanin cewa a sama suke ko a kasa, ko kuma sun saba. Haka nan idan sanin ma'auni ya zama wajibi, amma bai wajiba ba a san cewa ma'aunin na ma'ana ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu. Kuma ba dole ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri, ko kuwa daidaituwa a kan tafarki madaidaici ne. Hadafin wannan bayani shi ne, a musulunci ba a shardanta bincike domin sanin cewa wadannan abubuwa suna da jiki ne ko kuwa .
Wannan akidar ta tashin kiyamar da saukin nan nata ita ce wacce musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya wuce haka domin saninta dalla-dalla sama da abin da Kur'ani ya zo da ita domin ya gamsar da kansa, don kore shakkun da masu bincike da masu kokwanto ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali, ko bahasin dalili na zahiri, to yana wahalar da kansa ne, kuma zai fada a cikin mushkiloli da jayayya maras iyaka. A Addini, babu adinda yake tilasta wannan zurfafawar dalla-dalla da littattafan masana Akida da malaman falsafa suke cike da shi, kuma babu wata larurar Addini, ko ta zamantakewa, ko siyasa, da take tilasta irin wadannan rubuce-rubucen da makalolin da aka makale littattafai da su, haka nan babu wata fa'ida, wadannan abubuwan sun karar da karfi da kokari da lokuta da tunanin masu jayaya ba tare da fa'ida ba.
Gamsuwarmu game da gazawar mutum game da riskar wadannan al'amuran da suke boyayyu a gare mu, kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu, sun wadatar wajen raddin wadannan shubuhohi da shakkun da ake tayarwa game da wadancan bayanai. Tare da sanin cewa, Allah (S.W.T) mai iko ne a kan ya ba mu labarin hakikanin aukuwar Tashin kiyama da tashi daga kabari. Ilimin dan Adam da gwaje-gwajensa, da bincike-bincikensa, mustahili ne su iya samo wani abu da bai san shi ba, wanda ba ya kuma karkashin gwajinsa da bincikensa, da ba zai iya saninsa ba sai bayan mutuwarsa da ciratarsa daga wannan duniya zuwa wata duniyar daban, idan haka ne, yaya za a saurari ya yi hukunci da tabbatarwa ko kore wannan abu, balle ya shiga bayanansa dalla-dalla da abubuwan da suka kebanta da shi, sai dai idan ya dogara a kan bokanci, da zato, da mamaki, kamar yadda yake a dabi'ar dan Adam ya yi mamakin dukkan abin da bai saba da shi ba, kuma iliminsa da riskarsa ba su san shi ba, kamar mai fada da jahilcinsa yana mai mamakin tashi daga kabari da tashin kiyama: "Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu".
Ba komai ne ya sa shi mamakin ba sai rashin sabawa da ganin matacce rididdigagge an mayar masa da sabuwar rayuwa, sai dai mai wannan mamakin ya manta da yanda aka halicce shi tun farko alhalin da can ya kasance rasasshe, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu an hada su ne daga kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma sarari da abin ya tattaro, har ya zama mutum madaidaici mai hankali: "Shin mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya buga mana misali ya mance halittarsa, ya ce: Wanene zai rayar da kasusuwa alhalin suna rididdigaggu". Yasin: 77-78.
Ana gaya wa mai irin wannan maganar da ya mance kansa: "Ka ce; wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu".
Yasin: 79. Kuma a ce masa: Bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa, kuma ka san Manzo da abin da ya ba da labari game da shi, da gajiyawar iliminka hatta a gano sirrin halittarka da sirrin samuwarka, da yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon mani da ba ya jin komai, ba ya hankalta zuwa marhalolin da ke biye da aka harhada daga kwayoyin halitta manesanta, domin ka zamanto mutum madaidaici, mai hankali, mai tunani, mai riska da mariskai. Kuma a ce da shi: Yaya kake mamakin dawo maka da rayuwa sabuwa bayan ka zama rididdigagge, kana kokarin tsinkayar sanin abin da kwarewarka ka da iliminka ba zasu iya gano shi ba?
A kuma ce masa: Ba ka da wata mafita sai mika wuya kana mai ikrari da wannan hakika, wacce mai juya al'amuran halittu, masani, mai kudura, wanda ya samar da kai daga rashi. Kuma dukkan wani kokari na binciko abin da ba zai yiwu a gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne maras amfani, da rudani cikn dimuwa, da bude ido a cikin duhu mai dundum.
Duk da irin inda dan Adam ya kai gare shi na ilimi a wannan zamani, ya kago lantarki, da rada , da amfani da makamin kare dangi, da sauran kage-kagen da, da an yi magana game da su a shekarun baya da an kirga su a cikin mustahilan abubuwa ababan yi wa isgili, amma duk da haka mutum ya kasa gano hakikanin wutar lantarki, da sirrin kwayar zarra, ya kasa gano hatta hakikanin daya daga cikin siffofinta, to yaya zai ji kwadayin gano sirrin halitta da samuwa, sannan ya kara gaba yana son ya san sirrin Tashin kiyama da Tashi daga kabari.
Haka ne, ya kamata ga mutum bayan ya yi imani da musulunci ya nisanci bin son zuciya, kuma ya shagaltu da abin da zai gyara masa lahirarsa da duniyarsa, da kuma abin da zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abin da zai taimake shi a kansa, da kuma abin da zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan halarta a gaban Mai mulki, Mai yawan sani. "Kuma ku ji tsoron ranar da wata rai ba ta wadatar wa wata rai komai kuma ba a karbar ceto daga gareta, kuma ba a karbar fansa daga gareta, kuma ba a taimakon su". Bakara: 48

Ranar Sakamako Ranar sakamako; Ita ce ranar da za a tara aljanu da mutane domin saka musu da abin da suka aikata a wannan duniya na biyayya ko sabawa. Akwai dalilai masu yawa na hankali da na shari'a game da rananr sakamako, amma kasancewar kura'ani mai girma da ruwayoyin da suka zo daga Annabi (S.A.W) game da ranar alkiyama suna da yawan gaske, sannan imani da wannan rana bisa dogaro da su wani abu ne sananne gun musulmi gaba daya, don haka zamu yi nuni da wasu daga dalilan hankali game da haka:

Dalilin Adalci Kasancewar ubangiji wajibi ne ya siffantu da adalci, ya wajabta zuwan ranar alkiyama domin tsayar da adalci tsakanin mai zalunci da wanda aka zalunta. Idan adalci shi ne ba wa duk mai hakki hakkinsa, to wannan yana tilasta karbar hakki daga hannun azzalumi da mayar da shi hannun ma'abocinsa na ainihi. Don haka ne koton Allah mai hukunci da adalci zata zauna a wannan rana domin tsayar da adalci da sakamako da abin da bayi suka aikata na alheri da na sharri.
Haka nan kasancewar ubangiji mai hikima da adalci ya lizimta rashin daidaita tsakanin azzalumi da wanda aka zalunta a sakamakon, don haka dole ne a samu wata rana da za a karbi hakkin mai hakki a mayar da shi ga mai shi na asali.
Da yake zalunci bai takaita da abin da yake faruwa tsakanin bayi ba na danniya da fin karfi, don haka zalunci yana iya kasancewa cikin abin da ya shafi daidaita mai kyautatawa da mai munanawa, don haka tunda daidaita mai aikata alheri da mai aikata sharri a sakamako yana daga zalunci, don haka ya zama wajibi ga Allah ya zo da wata rana da zai ba wa kowanne daga cikinsu abin da ya cancance shi, domin rashin samar da wannan rana domin sakamako da abin da ya cancanta ga wadannan bangarori biyu, ya zama daidaita su a sakamako wanda ya gabata cewa yin hakan zalunci ne, shi kuwa ubangiji ya kubuta daga yin zalunci.

Dalilin Koruwar Wasa Mahangarmu game da ayyukan ubangiji madaukaki ita ce; cewa shi ba mai wasa ba ne, kuma wasa ya koru daga ayyukansa, saboda haka halittar duniya musamman halittun da suke da zabi a ayyukansu kamar 'yan Adam da aljanu duk ba domin wasa ba ne, don haka dole ne a samu wata rana da zasu taru wuri daya domin sakamakon abin da suka aiwatar da wanda suka aikta a wannan rayuwa ta duniya. Da halittar mutum da aljan ta takaita da duniya ne kawai da wannan ya lizimta wasa a ayyukan Allah (S.W.T) alhlin wasa ya koru gareshi madaukaki.

Dalilin Hadafi Akwai wasu jama'a daga Ash'ariyya da suka tafi a kan cewa; ayyukan Allah (S.W.T) ba su da hadafi, don haka mun saba da su a kan haka. Mahangarmu ita ce; ayyukan Allah suna da hadafi.
A bisa wannan dalilin ne muke cewa: tun da wasa ya koru ga Allah (S.W.T) kamar yadda ya gabata a dalili na sama, saboda haka wannan halitta da Allah ya yi tana da hadafi, kuma tunda mun ga wannan hadafin, na kamala ne ko na sakamako ba zai iya samuwa a wannan duniyar ba, don haka dole ne a samu wata duniyar daban da take da yanayin da ta cancanci tabbatar wannan hadafin a cikinta.

Hadafin Sakamakon Ayyuka Ubangiji madaukaki ya halicci mutum da aljan domin hadafi da yake son su kai zuwa gareshi na kamala, wannan ya sanya kallafawa bayi ayyuka da nauyi mai girma kamar wajabin salla, da zakka, da azumi, da hajji, da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Da kuma ayyukan da ya haramta kamar shan giya, da zina, da cin kudin riba, wannan duk domin su sami kaiwa zuwa ga wannan matsayi mai girma na kamala.
Amma bayi ba su zamanto daya ba a cikin karbar wannan sakon, acikinsu akwai; mai sabo da mai biyayya, don haka ya zama wajibi a samu wata rana da za a saka wa kowanne daga cikinsu da abin da ya cancanta da shi na kamala ko kaskanci sakamakon ayyukansu da karbarsu ga wannan takalifi da aka dora musu ko rashin karbarsu gareshi.

Hadafin Kamala Da Sa'ada Tunda ubangiji ya halicci mutum da aljan domin su samu kamala da sa'ada ne da suka cancance su, wannan kuwa ba mai samuwa ba ne a wannan duniya kamar yadda muke iya ganin halin duniya na canje-canje, da karewa, da wahala, da tsufa, da rauni, don haka ne dole a samu wata duniya daban ba wannan ba, da take da yanayin da ya dace da kamala da sa'adar da ta cancance su.