Sunan Bauta ga Wani
  • Take: Sunan Bauta ga Wani
  • marubucin: Ayatul-Lahi Subhani
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:25:0 1-10-1403

Ayatullahi Ja'afar Subhani
Kur'ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Sanya Wa 'Ya'ya Sunan Da Ya Fara Da "Abd" Wani lokaci sakamakon soyayyar mutum ga wani yakan kirakansa da sunan bawansa, wato "Abd ko Gulam", manufar wannan kuwa shi ne nuna karanta ga wannan mutum da kake girmamawa.
Wani lokaci wasu mutane masu tsarkin zuciya suna tsananin kaunar annabawa da waliyya Allah, sakamakon haka ne suke sanya wa 'ya'yansu sunan wannan bawan Allah da suke kauna tare da sanya kalmar "Abd" ko "Gulam" a farkon sunan, wato kamar su sanya wa dansu suna da "Gulam Husain" ko "Abudul Husain". Irin wannan sanya sunan ba shi da wani hadafi wanda ya wuce nuna soyayya ga iyalan gidan manzanci, sannan fahimtar hakan ga wadanda suke da tsarkin zuciya wani abu ne mai sauki kwarai da gaske.
Tare da kula da wannan gajeruwar gabatarwa zamu yi nuni ne da wasu maganganun da wasu masu kiyayya da yin hakan suke cewa kamar haka:
Suna cewa; Ba zai yiwu ba mutum ya zama bawan wani sabanin Allah. Kamar yadda Allah yake cewa: "Lallai duk abin da yake sama da kasa sai ya zo wa Allah mai rahama yana matsayin bawa".
Tare da lura da cewa mutum kawai zai iya zama bawan Allah ne, don haka irin wannan sanya suna a kira mutum da sunan bawan wani kamar "Abdul Husain" bai halatta ba domin kuwa wannan yana bayar da kanshi na shirka ne!
Wajen bayar da wannan amsa zamu yi tunatarwa da cewa: Farko dole ne mu fahimci ma'aunin da zai sanya a zama bawa, sannan sai mu zo mu yi magana a kan kebantarsa da rashin hakan, da wata ma'ana kasantuwar bauta ta halatta tana cakude da halittar dan Adam ce, ya bambanta da bauta ta doka wacce wani lokaci ana iya cire ta daga mutum, a nan ne za a fahimci rashin tabbatuwar wannan kalu bale da suke yi.
Duk lokacin da ya zamana ma'aunin bauta shi ne ta hanyar halitta da samar da mutum ne, ta wannan fuskar dukkan mutanen duniya bayin Allah ne, sannan babu wani wanda suke bayinsa bayan shi. Idan annabi Isa (A.S) yana kiran kansa da "Abdullahi" ko kuwa Allah yana amfani da kalmar "Ibadullhi" yayin da yake magana da bayin Allah muminai kamar inda yake cewa: "Ka ce yaku bayin Allah wadanda suka yi imani, ku ji tsoron ubangijinku" , dukkan wannan ta fuskar wannan ma'aunin ne na cewa shi ne ya halatta su.
Wannan nau'i na bauta yana tattare da kowane mutum, sannan ba zai iya rabuwa da shi ba, don haka ta wannan ma'ana ne mutum bawan Allah ne kawai, sannan shi ne ya bauta masa. Amma idan ya zamana bauta wani nau'i ne wanda mutane su dakansu suka ayyana ko kuma ta hanyar shari'ar Ubangiji da ya sanya, ta wannan fuskar mutum ba kawai bawan Allah ne ba, domin kuwa mutum wani lokaci yakan iya zama bawan wani mutum daban, a nan zamu yi nuni da misalan duka guda biyun kamar haka:
1-Masu karfi da iko a duk tsawon tarihi suna daukar raunana a matsayin bayinsu, ta yadda suke amfani da su wajen saye da sayarwa da kuma amfani da su domin samu 'ya'ya har zuwa wani lokaci ba mai nisa ba. Wannan ya kasance a na yinsa a kasashen tuarai da Amerika, sannan har zuwa yanzu bakaken fata da suke a kasar Amerika 'ya'yan wadanda aka kama ne da karfi daga kasashen Afrika a matsayin bayi zuwa Amerika. Irin wannan nau'i na bauta musulunci ya yi Allah-wadai da shi, kawai ya halatta nau'in bauta ne yayin da aka kama fursunoni a wajen yaki, wannan shi ma domin kiyaye rayuwakan wadanda aka Kaman ne, bayanin wannan kuwa ya zo a cikin babin jihadi a cikin Littattafan fikihu.
2- Kur'ani ya kasa mutane zuwa gida biyu yana cewa: Da yana mai makon da, haka nan bawa yana mai makon bawa, wato 'yantacce yana daidai da 'yantacce, bawa kuma yana daidai da bawa a wajen yin kisasi. Abin da kuwa ake nufi da bawa a cikin wannan aya ba ana nufin bawa na halitta ba ne, domin kuwa wannan nau'in bauatar ba ta kebanci wasu mutane ba sabanin wasunsu, domin kuwa Allah ne ya halicci kowane mutum don haka kowa bawansa ne. Don haka abin da ake nufi da bawa a cikin wannan aya wanda yake sabanin yantacce wanda ba bawa ba. Saboda haka a nan sai mu lura cewa bayin su wanene wadanda Allah yake kira da bayi a cikin wannan aya? Babu shakka bayin wadanda suka mallake su ne kamar yadda dokokin musulunci suka ayyana shugabancinsu a kansu.
Sannan Allah madaukaki dangane da aure yana magana a kan auren wadanda suke bayi da wadanda ba su ba, inda yake cewa: "Ku auri marasa aure daga cikin maza da mata da na kwarai daga cikin bayinku" .
A nan abin tamabaya shi ne su wadannan bayin maza da mata da Allah yake magana a kansu na wane ne, babu mai su sai wanda ya mallake su ta hanyar doka kamar yadda ta ayyana ya mallake su.
Saboda haka daga nan zamu iya gane cewa zama bawa wanda ya samo asali ta hanyar halitta, babu wanda zai zama bawan wani sai na Allah domin kuwa shi ne wanda ya halicci kowane mutum, amma bautar da ta samu asali ta hanyar dokar Ubangiji ana iya jingina ta zuwa wanda ba Allah ba, ta yadda za a iya cewa Zaid bawan Manzo ne ko kuma Bilal bawan Abubakar ne, haka nan Kumbur bawan Ali ne, wanda daga baya aka 'yanta su.
Tare da kula da wannan nau'in na zama bawa guda biyu muna iya tunatarwa da cewa: Bauta ta hanyar doka tana sanyawa bawa ya yi biyayya ga ubangijinsa, don haka bayi maza da mata dole ne su yi biyayya ga ubangijinsu. Sannan hukunce-hukuncen wannan bauta sun zo a cikin Littattafan fikhu, don haka manufar sanya wa 'ya'ya suna da misalign "Abdun nabiy" ko "Abdul Husain" ya yi kama ne da zama bawa na doka ba wai bawa na halitta ba, wato a hakikanin gaskiya yana nuni ne zuwa ga yin biyayya, wato kamar yadda bayin doka suke biyayya ga ubangijinsu haka nan wadanda aka sanya wa wannan suna suna matsayin bayin Manzo ne ko bayin Imam Husain (A.S) haka nan kuma suna masu yin biyayya ne gare su.
Da wata ma'ana kuwa a nan kalmar "Abd" tana nufin mai biyayya ne. kuma a cikin harshen larabci daya daga cikin ma'anoninta shi ne mai biyayya. Sannan musulmi tare da aiki da ayar da take cewa: "Ku bi Allah da manzonsa da ma'abuta al'amura" . Don haka musulmi suna masu biyayya ne ga Allah da Manzo da ma'abuta al'amura (Ahlul baiti (A.S).
Amma abin mamaki a nan shi ne, wadanda suke soke-soke a kan batun sanya wa 'ya'ya irin wadannan sunayen, suna kiran azzaluman sarakuna wadanda suke tsananin girmamawa kamar su bauta musu da sunan Amirul mumininn!
Bayan cire sarki Sa'ud Bn Abdul Aziz daga karagar mulki sai dan'uwansa Faisal ya hau kujerar mulkin Saudiyya, a wani zama na musamman mai fatawa wanda ya gabata (Bin Baz) na kasar saudiyya ya kira Faisal da suna Amirul muminin. Wannan al'amari mai ban tsoro wanda har ya sanya shi kan shi Sarki Faisal ya nemi uzuri daga al'umma a kan wannan suna da aka kira shi da shi, wato yadda shi kansa yana ganin kansa bai cancanci a kira shi da sunan Amirul mumininn ba.
Wannan al'amari da ya faru kuwa duk an rubuta shi a cikin jaridu na kasar saudiyya wanda kansa marubucin wannan littafin da kansa ya karanta wannan a cikin jaridu da mujallun kasar.