Bidi'a Cikin Addini
  • Take: Bidi'a Cikin Addini
  • marubucin: Ayatul-Lahi Subhani
  • Source:
  • Ranar Saki: 21:9:15 10-10-1403

Bidi'a A Cikin Addini

 
 
Ayatullahi Ja'afar Subhani
 
Kur'ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
 
Bidi'a A Cikin Addini
Tauhidin Annabi Ibrahim wanda yake shi ne tushen duk wani addini da yazo daga sama, yana da matakai daban-daban wadanda masu ilimin kalam suka yi cikakken bayani a kansu, sannan su yi rubutu da dama a kan hakan.
Daya daga cikin wadannan matakai kuwa shi ne (kadaita Allah a cikin kafa doka da hukunci) wato Allah ne kawai yake da hakkin kafa doka da bayar da umarni ga halittunsa. Sannan babu wani wanda yake da hakkin ya kafa wa wata al'umma doka sannan ya tilastawa mutane a kan su yi aiki da wannan dokar, ta yadda zai takaita 'yancin mutane. wajibi ne kuma tilas ne ga kowane mai kadaita Allah ya yi imani da cewa babu wanda zai kafa doka ko shari'a sai Allah madaukaki. Kuma shi kadai ne yake da iko a kan mutane da dukiyoyinsu. Sannan shi yake da iko a kan umarni da hani.
Wannan al'amari kuwa ana iya tabbatar da shi ta hanyoyi guda biyu wato ta hanyar hankali da shari'a, a nan zamu fara tabbatar da hakan ne ta hanyar hankali.
Takaita kafa doka ga Allah kawai bai zamo sakamakon karamin tunani ba ne, domin kafa doka ingantacciya yana da sharudda na shi na kansa, wannan sharudda kuwa ba za a iya samun su ba a ko'ina sai wurin Allah madaukaki. Wadannan sharudda kuwa su ne kamar haka:
1- Dole ne wanda zai kafa doka ya zamana ya san mutum hakikanin sani.
2-Sannan kada ya zamana akwai wani amfanin da zai dawo zuwa ga mai kafa dokar.
3-Ya zamana ya tsarkaka daga duk wani neman matsayi ko daga wani bangarenci na wata kungiya.
Wadannan sharudda kuwa sakamakon bahsin da zamu yi nan gaba zamu ga cewa babu wanda yake da su sai Allah shi kadai mawadaci. Domin kuwa:
A-Mai kafa doka dole ya zamana yana da cikakkiyar masaniya dangane da mutum ta yadda zai san duk abin da yake damunsa da abin da yake bukata. Ta yadda sakamakon haka sai ya kafa dokokin da zasu daidaita shi su kuma shiryar da shi.
Sannan mai kafa doka dole ne ya san rayuwar zamantakewa tare da al'umma, ta yadda zai san ayyukan da ya kamata kowane mutum guda zai aiwatar a cikin al'umma, sannan ya san wanene a cikin ayyukansu zai amfanar da shi da kuma abin da zai cutar da shi a matsayin rayuwarsa ta zaman tare. Wannan kuwa babu wanda ya san hakan sai wanda ya halicci mutum ya san bukatunsa da matsalolinsa, shi ne wanda ya halicci mutum ya kuma san abin da yake bukata. A kan haka ne Kur'ani yake cewa: "Shin Allah bai san abin da ya halitta ba da kayau, alhali kuwa shi ne wanda ya san sirrin abin da ya halitta". Allah shi ne mahaliccin kwayoyin halitta da gabobin da suka hadu suka yi mutum, tabbas wanda yake haka shi ne ya fii kowa sanin abin da zai amfanar da cutar da mutum.
Shi ne sakamakon cikakken iliminsa ya san duk wani abin da zai gyara alakar da ke a tsakanin mutane, sannan ya san abin da kowa ya kamata ya aikata domin tabbatuwar laka mai kyau a tsakanin al'ummasannan ya san duk wani hakki na kowane mutum a cikin la'umma.
B-Sanin hakinin al'amura da kiyaye abin da zai amfanar da mutane yakan wajabta wa mai kafa doka ya tsarkaka daga duk wani neman amfanin kansa ko son kai wajen kafa doka. Domin kuwa siffar son kai nemar wa kai amfani takan sanya wani hijabi mai karfi tsakanin mai kafa doka da hakikanin al'amari, domin kuwa mai kafa doka duk yadda ya kasance mai son adalci mai son gaskiya to zai kasance cikin tarkon son zuciya idan har ya kasance yana da wannan siffar.
C-Kwadayi da kula da wasu manyan mutane da suke a wata kungiya mai karfi a cikin al'umma yakan sanya mai kafa doka ya kauce wa ka'ida wajen kafa doka ta yadda zai kafa doka ba tare da nuna bambanci ba. Sannan wannan zai hana shi ya zamana ya kafa doka kawai domin amfanin dukkan al'umma, wato duk abin da yake shi ne mafi alheri ga al'umma shi zai kafa doka a kansa.
Sannan tsoro da damuwa daga dokokin wasu masu karfi wannan kuwa daidaikun mutane ne ko kuwa wata kungiya ce, takan kasance kamar wata takobi a kan mai kafa doka ta yadda zata yi tasiri a kansa wajen kafa doka. Musamman sakamakon matsalolin rayuwar zamantakewa, wannan yakan sanya mai kafa doka ya zamana ya dace da guguwar masu karfi ta siyasa ce ko kuwa ta akida, wato ya zamana ya bayar da wuya ga wannan guguwar mai karfi da yake fuskanta. Idan kuwa ba haka ba dole ya yi shirin fuskantar matsaloli wadanda suka da dauri da makamantansa, ta yadda zai kauce wa wannan matsayi na kafa doka wasu su maye gurbinsa. Domin kuwa idan ma bai mika wuya ba to lallai ba shi da karfin da zai yi fito na fito da wannan barazanar da take fuskantarsa.
A nan ma Allah ne kawai wanda yake madaukaki mai kudra wanda ba ya jin tsoro ko shakkun wani ko kuma ya ji kwadayin wani abu, dimin dukkan sun koru daga gareshi (S.W.T), Saboda haka shi kadai ne yake iya kafa dokar da zata dace da abin da zai amfanar da mutane da kuma abin da zai iya cutar da su, sai ya kafa dokar da ta cancanta.
Abin jin dadi a nan wasu daga cikin masanan yammacin duniya sun fahimci wannan sharudda na sama Sakamkon haka ne John Jak a cikin littafinsa (dokin zaman tare) ga abin da yake cewa:
Wajen gane dokokin da zasu yi wa al'ummu amfani, dole hankali na gaba daya ya kula da duk bukatocin mutane amma ba tare da ya kalli shi kansa ba, sannan ya zamana ba shi da wata alaka da wannan duniya ta dabi'a (nature) Amma kuma yana da cikakkiyar masaniya a kanta, Sannan dacewa ko cin nasararsa ba ta da alaka da mu, amma a shirye yake ya taimake mu domin mu ci nasarar rayuwarmu. Kawai abin da zai wadatar da shi, shi ne alfaharinsa wanda sakamkon wucewar zamani ne zai bayyana, wato mai yiwuwa ya yi hidima a cikin karni guda amma sai a wani karnin ne sakamako zai bayyana.
A nan sakamakon ka'idojin na hankali mun ga yadda kafa doka ta takaita kwai ga Allah madaukaki. Abin da ya rage a nan shi ne mu ga me Kur'ani yake cewa dangane da haka:
Dangane da wannan magana kuwa Kur'ani shi ma ya karfafa hukuncin da hankali ya yi ne domin kuwa shi ma ya tabbatar da cewa babu wani wanda yake da hakkin kafa doka sai Allah madaukaki. Ayoyi da dama ne kuwa suka bayyanar da wannan magana, a nan dmin mu takaita kawai zamu kawo wasu ne daga cikin wadanda suke yin magana a kan hakan:
1-"Babu hukunci sai ga Allah, kuma ya yi umrni da cewa kada a bauta kowa sai shi kuma wannan shi ne addini tsayayye".
Jumlar da take cewa "babu hukunci sai ga Allah"tana bayyanar da cewa duk wani nau;in hukunci ya kebanta da Allah ne kawai. Sakamakon cewa shi kadai ne yake da wannan ikon don haka ya ce shi kawai za a bauta wa.
2-Ahlul kitab Sun dauki malamansu da Annabi Isa a matsayin ubangijinsu, sabanin Allah madaukaki .
Wannan aya tana bayyanar da yadda Ahlul kitab suka dauki hakkin da Allah ne kawai yake da shi suka mika wa malamansu, mai makon su koma zuwa ga Littattafan da aka aiko musu wajen samun hukunce-hukunce, sai su koma zuwa ga malamansu batattu, duk da kuwa sun san cewa wani lokaci sakamakon wasu dalilai suka halatta abin da Allah ya haramta su kuma haramta abin da Allah ya halatta, sakamakon haka ne ta bangaren kadaita Allah a wajen kafa doka suka kasance mushrikai.
Addi Bn Hatim ya kasance kirista yana cewa: Yayin da shigo wajen mazon Allah a lokacin yana karanta wannan ayar wacce ma'anar ita ce "Kiristoci da yahudawa sun kasance sun dauki malamansu a matsayin ubangijinsu". Sai na cewa Manzo wannan al'amari ba shi da inganci. Sai Manzo ya ce: Sukan halatta haram su kuma haramta halas, sannan kuma kuna yi musu biyayya ko ba haka ba ne? Sai na ce haka ne. Sai ya ce: to wannan kawai ya wadatar ya zamana kun dauke su matsayin ubangijinku .
Tare da la'akari da abin da muka fada a sama a cikin wannan Bahasi zamu fahimta cewa kafa doka kawai ya takaita ne ga Allah mai tsarki. Sannan ayyukan annabawa da imamai ne suke kawai bayyanar da wadannan doki na Allah madaukaki, sannan ba su da ikon sanya hannu a cikin kafa dokokin Ubangiji.
A nan amsar wata tambaya guda daya kawai ya rage wannan kuwa ita ce, idan hakkin kafa doka kawai ya takaita ga Allah ne, to a jamhuriyar musulunci menene matsayin kafa dokar da 'yan majalisa suke yi?
Amsar wannan tambaya kuwa ita ce, aikin 'yan majalisa shi ne shirya ayyuka a karkashin dokokin na baki daya da musulunci ya zo da su, don haka ba suna kafa dokoki sababbi ba ne. Sannan babu wata kasa duk yadda ta kai wajen ci gaba wajen dokoki ta zamana ta wadatu da shirya abin da ya kamata ta yi (programs) Saboda haka a hakikanin gaskiya Majalisa wani wuri ne na shirye-shiryen abin da ya kamata gwammanati ta aiwatar karkashin dokokin addinim musulunci. Sannan ta nuna yadda ya kamata a aiwatar da wadannan dokokin acikinrayuwar dan Adam ta yau da kullum.

Bidi'a A Cikin Addini
Kamar yadda yake kafa doka hakki ne kawai na Allah madaukaki sannan babu wani wanda yake da wannan hakkin ta yadda zai kafa wa wani mutum kowata al'umma doka. Haka nan babu wani wanda yake da ikon ya kara ko ya rage wani abu a cikin dokokin da Allah a saukar ta hanyar wahayi. Saboda haka sanya hannu a cikin dokokin da Allah ya saukar ta hanyar ragi ne ko kari, wannan shi ne ake kira da "Bidi'a" a cikin addini. Saboda haka mutumin da ya yi haka ya yi bidi'a a cikin kadaita Allah a cikin kafa doka wanda muka yi maganarsa a sama.
Sakamakon barnar da ke akwai wajen (bidi'a) ko sanya hannu wajen kafa doka ya zamana daya daga manyan zunubbai wanda wannan bahsin da muke cikinsa yake dauke da cikakkiyar ma'anar "Bidi'a" wanda yake daya daga cikin muhimman abubuwan da zamu yi magana a kai nan gaba.
Ma'anar Bidi'a a harshen larabci shi ne, yin wani abu sabo wanda yake da ba a yinsa. Saboda haka duk wani sabon abu wanda yake da ba a yinsa ana kiransa "bidi'a".
Dabi'ar Mafi yawan mutane Suna son sabon abu, sannan ba su son rayuwar da take da yanayi iri guda babu canji. Sakamkon haka ne ya sanya masana ginin gidaje a kodayaushe suke kokari wajen samar da zane da nau'oi'in gidaje kala daban-daban, sannan kalar tufafin da mutane suke sanyawa kullum yana samun canji, dukkan wadannan ta fuskar lugga ana kiran su da Bidi'a. A kan haka ne ma Kur'ani mai girma yake ambatar Allah madaukaki da "Mai kirkiro sammai da kassai" . Domin kuwa shi ne ya kirkiro sammai da kasai ba tare da ya ga makamantansu ba kafin nan, Wani abu ne sabo wanda a da bai gabata ba.
Amma a nan akwai wani abu wanda ba mu fada ba dangane da 'bidi'a' domin kuwa bidi'a da wannan ma'ana ba ita ce ba ce muka yi magana ba a kanta a bahsin mu na baya wacce take an haramta kamar yadda muka yi bayani.
Domin kuwa musulunci ba ya hani a kan sababbin abubuwa a cikin rayuwar daidaiku da zaman tare. A yau dan Adam dangane da yanayin rayuwrsa yana da abubuwa sababbi wadanda ba a taba yinsu a tarihi, kamar abin da ya shafi gine-gine da tufafi da dai makamantansu. Duk da cewa wadannan a mahangar ma'ana ta kalmar 'Bidi'a' suna iya shiga a ciki amma ba su daga cikin bidi'a wacce ake magana wacce take daya daga cikin manyan zunubbai.
A cikin tarihi ana rubutawa cewa farkon bid'ar da sahabbai suka zo da ita bayan wafatin Manzo shi ne tankade garin alkama, wannan al'amari ne wanda yake sabo kuma da ba a yinsa, amma wannan ba ya daga cikin bid'ar da malamn fikihu suke cewa tana daga cikin manyan zunubbai. Saboda haka dole a bayyanar da cikakkiyar ma'anar bida'r da ake magana a cikin shari'a.
Amma bid'ar da malaman fikihu da akida suke magana a kanta kuma take daya daga cikin manyan zunubbai ita ce shigo da wani abu a cikin addini ta hanyar rage wani abu ko kuwa kara wani a cikin addini wanda bai zo ba daga Allah. Misali kamar yadda a kara wani abu a cikin kalmomin kiran salla ko kuma rage wani abu daga ciki. Ko kuma kara lokaci ko rage shi a cikin lokacin azumi sabanin yadda adini ya zo da shi wato daga bulluwar alfijr zuwa faduwar rana.
Amma masana suna bayyanar da ma'anar bidi'a kamar haka:
A-Bidi'a ita ce kari ko rage wani abu a cikin addini, sannan a dauki wannan abin daya daga cikin addini.
B-Bidi'a ita ce kawo wani abu sabo a cikin addini alhali babu dalilin shari'a a kan halarcinsa. Amma idan wannan kawo sabon abin yana da asali a cikin shari'a to ba 'bidi'a' ba ce.
C-Bidi'a ita ce farar da wani abu sabo a cikin addini. Tare sharadin cewa babu wani dalili ko asali daga addini da yake nuna halascin abin, ana kiran wannan bidi'a a cikin addini a tsakanin musulmi .
Muna iya wadatuwa da wadannan ma'anoni guda uku. Sannan mu manta da sauran ma'anonin da ba su da ma wani muhimmin bambanci da wadannan. Saboda haka daga wadannan ma'anoni zamu iya fahimtar cewa bidi'a tana da wasu rukunnai guda uku wadanda suke raba ta da 'Sunna'.

1-Sanya wani abu a cikin addini
Duk wani kari ko ragi a cikin addini wanda zai sanya addini ya samu wani canji sakamakon hakan, sannan kuma a danganta wannan zuwa ga Allah ko manzonsa. Amma sabunta wani abu wanda zai sanya mutum ya samu wani canji a ruhinsa, ba a kiransa bidi'a. Amma mai yiwuwa ya kasance bai halatta ba amma ba a kiran sa bidi'a da wannan ma'anar.
Daga wannannan bayani zamu iya fahimtar cewa akwai wasu ayyuka daga cikin ayyukammu wadanda mai yiwuwa su zama halas ko haram, amma ba a kiransu bidi'a, kamar misalin kwallon kafa ko wani nau'i na wasanni. Irin wadannan sababbin abuwa a cikin rayuwa, sakamkon kasantuwarsu ba shigar da wani abu ba ne a cikin addini ba a kiransu da bidi'a.
A yau ga wadanda suka samu tasiri daga turawa al'adar hada maza da mata a taruka wani abu wanda ya zama ruwan dare, amma tunda masu yin wannan aiki ba su danganta shi zuwa ga Allah ba, don haka ba a kiran wannan bidi'a, duk da cewa a mahangar musulunci ya haramta.
Saboda haka zamu iya daukar sakamako a kan cewa 'bidi'a tana kunshe da sanya wani abu a cikin addini. Saboda haka idan wani abu sabo ba a shigar da shi cikin addini ba wato ba da sunnan addini ake yinsa ba, ta yadda ba a jibinta shi zuwa ga Allah ko Manzonsa ba, wannan ba a kiransa bidi'a. Wannan kuwa babu bambanci ya kasance a mahangar shari'a ya halatta ne (kamar kwallon kafa) ko kuwa bai halatta ba kamar cakudar maza da mata.
2-Ya Kasance Ba Shi Da Asali Daga Kur'ani Da Sunna
Sharadin na biyu a cikin abubuwan da suke mai da abu ya zama bidi'a shi ne ya zamana wannan abin da aka sanya a cikin addini ba shi da tushe daga Kur'ani da sunnar Ma'aiki, ta yadda zai zama shi ne madogara wajen yin wannan sabon abin. Domin kuwa idan ya zamana yana da madogara daga Kur'ani ko Sunna to ba a kiransa bidi'a a cikin addini sai dai a ce zuwa da wani abu wanda yake a cikin shari'a wanda aka manta da shi yanzu kuma aka gano shi ya bayyana.
Wannan sharadi kuwa yazo a bayyane a cikin ma'anar bidi'a sannan kuma an kara karfafa shi a ilimince. Ta yadda suke cewa: "Bidi'a ita ce zuwa da wani abu a cikin addini wanda ba shi da madogara a cikin addinin, amma idan ba haka ba bai zama bidi'a ba".
Saboda haka bisa ga dogaro ga wannan sharadi na sama da aka ambata zamu iya gane cewa da yawa daga cikin sababbin abubuwa wadanda suke a cikin rayuwa mutane a yau ba'bidi'a ba ce, duk da cewa ana dangana su zuwa ga addini. Domin kuwa wadannan sababbi abubuwa suna da tushe daga addini, saboda haka suna samun inganci ta fuskar samo asalinsu ne daga addini'duk da cewa ba a fili suka zo ba amma an fitar da su ne daga Kur'ani da Sunna.
A matsayin misali a yau sojojin duniya da na jamhuriyar musulinci ta Iran suna da manyan makamai domin kare kansu. Wannan al'amari na tanadar makamai bayan yana kara dora sojojin a kan makiyansu, kuma wani umarni ne na Allah madaukaki inda yake cewa a cikin Kur'ani mai girma: "Ku yi musu tanaji daga kayan yaki iya iyawarku, sannan ku tanaji dawakai masu kaifi ta yadda zaku tsoratar da makiyanku" .
A cikin wannan umarni guda biyu ne ya zo ta yadda daya daga cikinsu yake nuni da abu kebantacce da na gaba daya kamar haka:
1-Umarni na gaba daya: Shi ne iya yadda kuke iyawa ku tanaji karfi (duk wani nau'i na kayan yaki.
2-Umarni na biyu kuwa shi ne yana nuni ne ga tanadar dawaki masu karfi domin filin daga (a nan kuwa ya yi nuni ne ga wani nau'i na makami)
Saboda haka sayen duk wani nauyin makamin yaki na zamani, aiwatar da umarni ne na farko wanda yake nuna a yi wa sojoji tanajin manyan makamai na zamani. Saboda haka tare da la'akari da wannan aya muna iya danganta tanajin da muke wa sojoji da kayan yaki na zamani zuwa ga shari'a da addini, sannan kuma aikimmu ba zai zama bidi'a ba. Domin kuwa ba a ambaci wadannan makamai da nau'o'insu ba, amma bangaren umurnin aya ta farko yana nuni da tanajin wadannan makamai. Saboda haka samun irin wannan tushe daga addini yana tabbatar da ingancin hakan a addini.
3-Ya zamana ya yadu cikin al'umma: Daya daga cikin sharuddan kasancewar sabon abu ya zama bidi'a shi ne, ya zama ya yadu a cikin mutane. Duk da cewa wannan sharadi bai zo a wajen bayyana ma'anar 'bidi'a' ba amma hakikanin 'bidi'a' yana kunshe da shi. Sannan akwai abubuwa da yawa da suke nuni a kan hakan.
Misali ya zo a cikin ruwayoyin inda suke nuni a kan fito na fito da 'bidi'a' masu yin bidi'a babu shakka wadannan ruwayoyin sakamakon yaduwar wannan bidi'o'i ne a tsakanin al'umma ta hanyar masu yin wannan aiki.
Manzo mai tsira yana cewa: "Duk wanda ya zo da bidi'a a cikin wannan addinin zunubbin wadanda suka bi shi a kan hakan yana a kansa" . Wannan ruwaya da makamanciyarta suna nuni ne a kan cewa tunanin kari ko ragi a cikin addini matukar bai wuce matsayin tunani ba wato bai kai ga aiki ba ta yadda kawai ya tsaya ne ga mai shi, wato bai yadu zuwa ga sauran mutane ba, to a nan haramun ne kawai amma ba bidi'a ba ce.
Tare da kula da wadannan sharudda da muka ambata na bidi'a muna iya fahimtar hakikanin ma'anar bidi'a sannan mu fahimci iyakokinta ta yadda zamu iya gane abin da ba ita ba.

Haramcin Bidi'a A Cikin Kur'ani Da Sunna
Bidi'a wani nau'i ne na shiga a cikin hakkin tafiyar da al'amura (rububiyya) domin kuwa al'amarin kafa doka ya kebanci Allah ne kawai, saboda haka duk wani nau'i na shiga a cikin tafiyar da al'amura yana da hukunci shiga cikin hakkin Allah madaukaki. Sannan jingina abin da ba shi da asali daga addinin zuwa ga Allah ko manzanninsa, yana daga cikin kirkira wa Allah da manzanninsa wani abu wanda ba daga garesu yake ba (Iftira).
Sakamakon haka ne Kur'ani yake Allah wadai da bidi'a. Misali dangane da mushrikai inda suka raba ranakun Allah ba tare da wani dalili ba, ta yadda suka sanya wasu ranaku halas wasu kuwa haram, sannan suka jingina wannan aiki nasu zuwa ga Allah, a kan haka ne Kur'ani yake cewa: "Shin Allah ne ya yi muku izini a hakan ko kuwa kuna kirkirawa ne ku dangana shi zuwa ga Allah?" .
Sannan yana cewa: "Kada ku ce wannan halas ne wannan haram ne daga abin da kuke fada na karya daga bakunanku, domin ku kirkirawa Allah karya, tabbas wadanda suke kirkirawa Allah karya ba zasu rabauta ba" .
Zargin da Allah yake wa masu bidi'a a cikin wannan ya kasance ne sakamakon yadda suka shiga cikin hakkin Allah na kafa doka sannan suka dangana shi zuwa ga Allah. Wato ta yadda suke halastawa ko suke haramtawa ba tare da izinin Allah ba, kuma su jingina abin zuwa ga Allah.
Sannan Kur'ani yana Allah-wadai da yahudawa da nasara yayin da suka rubuta wasu abubuwa da hannayensu sannan suka jingina shi zuwa ga Allah don isa zuwa ga wasu gurikan na abin duniya. Ga abin da yake cewa a kan hakan: "Banu ya tabbata ga wadanda suke rubuta littafi da hannayensu sannan su ce wannan daga Allah yake, domin su sayar da shi da kudaden 'yan kadan, to banu ya tabbata a garesu a kan abin da suka rubuta da hannayensu, sannan banu ya tabbata garesu dangane da abin da suke kasuwanci da shi".
Mun ga Matsayin Kur'ani dangane da wadanda suke bidi'a a cikin addini da kuma wadanda suke canza wani abu daga cikin addini a matsayin masu yin wasa da hukuncin Ubangiji. Sannan dole ne a nan mu fadakar a kan cewa matsayin ruwayoyi kuwa a bidi'a kamar matsayin Kur'ani ne a kan hakan: Manzo da Shugabannin musulunci sun kasance suna tir da bidi'a da masu yin bidi'a wato masu yin wani abu a cikin wanda ba shi da tushe daga addinin, suna ambatarsu da masu bidi'a kuma batattu. Yana da kyau a nan mu tunatar a kan wani hadisi wanda malaman addinin musulunci suka ruwaito daga Manzo, sannan sukan yawan karanta shi a cikin hadubar sallar jumu'ar manzo a cikin daya daga cikin hudubobinsa yana cewa:
"Fiyayyen abu shi ne littafin Allah, sannan fiyayyar shiriya ita ce shiriyar Muhammad (S.A.W), Sannan mafi sharrin abu shi ne abin da a ka kirkira, Sannan duk abin da yake bidi'a bata ne".
Bugu da kari ma a kan haka, hankali ma yana Allah-wadai da yin bidi'a a cikin addini, domin kuwa yin hakan ketara iyaka ne zuwa ga hakkin da ya kebanta ga Allah kawai madaukaki. Sannan kuma tare da yin karya da kirkira wa Allah abin da ba daga gare shi yake ba, saboda haka muni da haramcin yin hakan a fili yake ba shi da bukatar bayani da yawa a kan kan hakan.
Bayanin Bahasin Da Ya Gabata A Takaice
1-Muna iya samun sakamako dangane da bahsimmu da ya gabata kamar haka:
Kafa doka hakki ne na musamman wanda ya kebanci Allah shi kadai, saboda haka duk wani nau'i ne na shigar shugula ga hakkin da ya kebanci Allah. Saboda haka wani abu ne wanda yake mummuna a mahangar hankali da shari'a kuma wani abu ne wanda aka yi hani a kansa kuma haramun.
2-Kebantuwar Kafa doka ga Allah kuwa ya kasance ne sakamakon cewa kafa doka yana bukatuwa zuwa ga wasu abubuwa kamar haka:
1-Cikakkiyar masaniya dangane da mutum.
2-Rashin duk wani amfani ga kafa dokar dangane da wanda yake kafa dokar.
3-Rashin la'akari da wata kungiya ko wasu masu karfi a cikin al'umma. Wadannan siffofin guda uku babu wanda yake da su kamar yadda ya dace Sai Allah madaukaki.
Majalisar dokoki kuwa da take jamhuriyar musulunci rawar da take takawa bai wuce fito da hukunce-hukunce ba daga tushensu ko kuma mu ce shirya abin da ya kamata a aiwatar a cikin hukuma.
3-Duk wani ketare iyaka wanda ya shafi kafa doka wani abu ne wanda aka yi hani a kansa, koda kuwa da ma'anar canza wani abu ne. Saboda haka kari ko rage wani abu a cikin addinin Allah haramun ne kuma ana kirga shi daga cikin bidi'a.
4- Kalmar bidi'a tana tabbatuwa yayin da ya kasance sabon abu ya kunshi wadannan siffofi da zamu ambata a kasa.
A-Wani aiki wanda yake sabo sannan da sunan addini ya kuma zama wani abu cikin addinin.
B-Rashin samun tushen wannan abin daga cikin Kur'ani ko Sunna ko hankali.
C-Yaduwar wannan abin a cikin al'umma a masatyin wani abu na addini.
5-Kur'ani mai girma yana daukar bidi'a wani nau'i na kirkira abu da dangana shi zuwa ga Allah, ta yadda ya zamana mushrikai suna halittawa kuma suna haramtawa su kuma jingina shi zuwa ga Allah, sakamakon haka ne aka yi Allah-wadai da su. Haka nan ma Kur'ani yake zargin yahudu da nasara a kan canza wani abu da suke daga cikin littafin Allah.
Haka nan hadisin manzoma ya nuna cewa bidi'a daya daga cikin mafi munin abubuwa ce, sannan tana kaiwa zuwa ga halaka kuma ta kai mutum zuwa ga fushi da zabar Allah.
6-Hankali ma yana karfafa wannan tir da Allah wadai da shari'a take yi wa bidi'a. Zuwa nan mun fahimci ma'nar "bidi'a" a lugga da ma'anar a shari'a, a nan zamu yi nuni da wasu abubuwa na gefe kamar haka.
Kashe-Kshen Bidi'a Zuwa Gida Biyu
Daya daga cikin kashe-kashen da ake yi wa bidi'a shi ne a kan kasa ta zuwa bidi'a mai kyau da marar kyau (hasana da sayyi'a).
Asalin wannan kasa bidi'a zuwa mai kyau da marar kyawu kuwa yana komawa ne zuwa ga halifa na biyu (Umar Bn Khattab). Saboda mutanen har zuwa shekara 14 bayan hijira, sun san cewa ana yin sallar nafila ta watan azumi a daidaiku ne (Sallar tarawihi). Amma sakamakon wasu dalilai a zamaninsa aka yi wannan salla a cikin jam'i da limanci Ubaiyu Bn Ka'ab a cikin masallacin Manzo. Lokacin da halifa na biyu ya ga wannan al'amari sai ya ce "Madalla da wannan bidi'a".
A nan ba zamu shiga cikin maganar cewa shin wannan sallar nafila a daidaiku ne za a yi ta ko kuwa a cikin jam'i ba, kawai a nan muna magana ne dangane da kasa bidi'a zuwa mai kyau da marar kyau wanda ya samo asali ne daga halifa na biyu.
A bayanimmu na baya mun ga cewa ma'anar bidi'a ita ce zuwa da wani sabon abu a cikin addini wanda babu shi, sannan babu wani dalili na shari'a da yake nuni a kan hakan. A kan haka ne bidi'a ba zata taba zama wani abu daban ba sai marar kyau, saboda haka kasa bidi'a zuwa mai kyau da marar kayu sam ba shi da wata ma'ana.
Koda yake da mutane zasu kawo wani abu sabo a cikin yanayin rayuwarsu amma ba su dangana shi ba zuwa ga Allah to wannan abin zai iya daukar ma'anar lugga ta kalmar bidi'a, sannan za a iya kasa ta zuwa gida biyu mai kyau da marar kyau. Wato; al'adun da suke bullowa a cikin al'ummu daban-daban suna iya kasuwa zuwa masu kyau da marasa kyau. Domin kuwa da yawa daga cikinsu suna iya zama masu amfani ko kuma su zamo mararsa amfani. Amma bidi'a a shari'a guda daya ce kuma dukkanta marar kyau ce kuma ba ta halatta. (Wato kirkiro wani abu sabo a cikin addini wanda babu shi, sannan kuma babu wani dalili na shari'a a kan yin hakan).
Dalilan Canza Wasu Abubuwa A Cikin Addini
Duk da cewa hakikanin musulunci ba wani abu ba ne sai kawai mika wuya ga Allah, sannan wasu daga cikin akidu na aikace sun samo asali ne daga wannan mika wuyan, saboda haka ta yaya ne mutum musulmi zai iya canza wani abu a cikin addini, Sannan menene nufinsa da dalilinsa a kan yin hakan?
A nan kasa zamu bayyana wasu daga cikin dalilan da suke sanya yin hakan, wadanda dukkansu suna karkashin bayyana ra'yi ne a kan 'nassi"
1-Girmama abu ba tare da dalili ba
Da yawa daga cikin mutane tare da amfani da wasu ra'ayoyi nakansu suna ganin bidi'a a cikin addini wani nau'i ne na girmamawa, misali hukuncin musulunci ya nuna cewa haramun ne yin azumi ga matafiyi. Lokacin da Manzo ya yi tafiya domin bude garin Makka ya kasance a cikin watan Ramadan ne, sakamakon haka lokacin da ya isa wani wuri sai ya yi umarni da a kawo masa ruwa ya sha. Amma wasu daga cikin musulmi da tunanin girmama abu ba tare da wani tunani ba sai suka saba wa Manzo a kan hakan sai ba su sha azuminsu ba. Domin kuwa sun yi tunanin cewa idan suka yi yaki tare da azumi zai fi lada. lokacin wannan labari ya je ga kunnen Manzo Sai ya kira su da masu sabo kuma masu zunubi.
2-Bin zabin abin da mutum yake sha'awa
Kowane abu a cikin musulunci yana da hukunci guda daya ne. Mafi yawa daga cikin sabanin da ke akwai tsakanin musulmi dangane da hukunce-hukunce ya samu asali ne daga bin son zuciya. Da wani kalamin domin girmamawa muna iya cewa ya samu tushe ne daga bin abin da mutum yake sha'awa. Imam Ali (A.S) a cikin maganganunsa yana nuni da wannan al'amari kamar haka: "Yaku mutane kodayaushe fitinu suna faruwa ne daga bin son zuciya ta yadda mutum zai bi abin da yake so sabanin abin da Kur'ani ya zo da shi".
Ana iya samun sheda da yawa a cikin tarihi a kan ire-iren wannan bidi'a, saboda haka a nan muna iya wadatuwa da misalai guda biyu daga cikinsu:
A: Daya daga cikin kashe-kashen hajji ita ce hajjin "tamattu". Wannan wani nauyi ne da ya hau kan kowane musulmin da yake rayuwa mil 48 daga Makka ko fiye da haka, saboda haka wanda hajjin tamattu ya hau kansa, dole ne bayan ya gabatar da umura sai ya fita daga cikin harami, sannan a wannan lokaci duk wani abu wanda ya haramta gareshi banda farauta ya halatta gareshi, har zuwa ranar 9 ga Zulhajji inda zai sake yin harami domin gabatar da sauran ayyukan hajji.
Tarihi yana rubuta cewa a zamanin Manzo wani daga cikin sahabban Manzo bai yi na'am ba da wannan hajji ta tamattu domin kuwa bai yi masa dadi ba a kan cewa yaya za a yi mutum ya zo aikin hajji tsakanin umura da hajji ya iya saduwa da iyalinsa ko kuma a lokacin da ruwan wanka (janaba) yake sakkowa daga fuskarsa kuma ya yi haramin aikin hajji, ta haka ne lokacin da ya zama halifa sai ya hana musulmi wannan hajji ta tamattu, alhalin wannan ya sabawa umurnin Allah da manzonsa. Saboda haka yana daya daga cikin bidi'a a cikin addini, wanda yake ba wani abu ne sai binson zuciya da abin da mutum yake ganin shi ne ya fi a kan kansa. Amma abin farin cikin wannan hani da halifa na biyu ya yi ya kasance na wani lokaci ne, inda yanzu da yawa daga cikin musulmi 'yan Sunna kamar yanda 'yan Shi'a suke yin hajji tamattu suma suna wannan nau'i na hajji.
B: Malik shugaban mazhabar Malikiyya yana ruwaitowa cewa: mai kiran salla ya zo wajen Umar Bn Khattab domin ya sanar da shi cewa lokacin salla ya yi, sai ya samu khalifa yana barci, domin ya tayar da khalifa daga barci sai ya ce: "Assalatu khairum minan naum". Wato salla tafi barci. Sai khalifa ya ji dadin wannan jumla sai ya karanta a cikin kiran sallar asubahi".
3-Ta'assubanci marar dalili
Daya daga cikin abubuwan da suka kawo bidi'a a cikin addini shi ne, ta'assubanci (riko da abu) marar dalili a kan al'adun iyaye da kakanni, da kuma al'adun da mutum ya tashi a cikinsu. Tsananin soyuwar da mutum yake da shi dangane da wadannan abubuwan yakan sanya shi ya yi nesa da fahimtar gaskiyar addini ta yadda zai mai da bata a mai makons gaskiya.
Tarihi yana nuna cewa: Mutanen Da'ifa sun aiko mutane zuwa ga Manzo domin su wakilce su domin su su bayyana wa Manzo shirinsu domin karbar addinin musulunci, amma sai suka sanya wa musulunci sharudda guda kamar haka:
1-Ya zamana ya halasta musu riba.
2-Ya halasta musu kusantar matan banza.
3-Wuraren bautar gumakansu su kasance har zuwa shekaru uku masu zuwa.
Lokacin da Manzo ya samu labarin wadannan sharudda nasu sai ya nuna tsananin damuwarsa kuma ya nuna rashin amincewar da ko daya daga cikinsu.
Idan da mutanen Da'ifa sun kasance musulmii na hakika, to dole ne su mika wuyansu ga hukuncin Ubangiji, ba wai su gabatar da son zuciyarsu ba a kan musulunci. Wannan a fili yake sakamakon manufofinsu daban-daban ya sanya suka sanya wa addinin wadannan sharudda. Daga cikin neman da suka yi kuwa na ci gaba da bautar gumaka, wannan kuwa duk ya faru ne sakamakon ta'assubanci marar dalili.
Wadannan dalilai guda uku na sama da wadansu makamantansu su ne tushen bidi'o'i a cikin addini. Sannan akwai wasu dalilai ma bayan wadannan amma saboda karancin damar da muke da ita zamu takaita a nan.

Fito Na Fiton Addini A Kan Hana Bayyanar Bidi'a
Malamai da masana da addinin musulunci kowane lokaci sun kasance suna kokari a kan hana shigowar bidi'a a cikin addini, sannan wannan ya wajaba a kansu domin kula da abin da wasu wadanda wasu daga cikin masu magana da yawon addini da marubuta, ta yadda zasu kula da abin da suke fada domin sukan yi amfani da kalmomi masu jan hankali domin su shigo da sabbin abubuwa a cikin addini. Sannan wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi kariya a kan addini duk inda yake, ta yadda addini zai kasance kamar yadda ya zo daga Allah madaukaki ba tare da wani canji ba. Kamar yadda ya zo daga Manzo kuma dukkan Sunna da Shi'a sun tafi a kan hakan cewa: Manzo ya ce wa al'umma da su koma zuwa ga Kur'ani da koyarwar Ahlul baiti (A.S) idan suka yi riko da wadannan abubuwa guda biyu, ba zasu taba bata ba daga hanyar daidai, inda yake cewa: "Na bar muku nauyi guda biyu littafin Allah da Ahlul baiti wadanda idan kuka yi riko da su ba zaku halaka ba har sai kun koma zuwa wurina a bakin tafki".
Sannan a wani hadisin an siffanta iyalan Manzo ne da jirgin annabi nuhu da cewa duk wanda ya shige shi ya tsira wanda kuwa bai shiga ba ya halaka domin zai nutse". Duk lokacin da al'ummar musulmi suka karbi addininsu daga iyalan Manzo tabbas zasu samu cikakkiyar shiriyar Ubangiji, sannan zasu tsira daga duk wata bidi'a da bin masu bidi'a.
Zuwa nan mun fahimci ma'anar bidi'a kuma mun gane bambancinta da sunnar Ma'aiki (S.A.W) sannan wannan bahsin zai zame mana matsayin mabudi domin yin amfani da shi a bahsoshimmu na gaba.