Hakkokin Jagorori
  • Take: Hakkokin Jagorori
  • marubucin: Imam Aliyyu Assajjad a.s
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:44:2 1-10-1403


Hakkin Jagora: "Amma hakkin jagora shi ne ka san cewa shi jarrabawa ce gareka, kuma shi abin jarrabawa ne game da kai saboda abin da aka sanya a hannunsa a kanka na iko, kuma ka tsarkake masa nasiha, kada ka yi gogayya da shi, ka ga ke nan ka sanya shi ya sanya hannunsa a kanka sai ka kasance dalilin halakarka da halakarsa. Ka kaskan da kai da tausasawa domin ba shi yarda da kai da abin da zai kame shi daga gareka, kuma ba zai cutar da addininka ba, sai kuma ka nemi taimakon Allah a kansa a cikin dukkan wannan. Kuma kada ka yi masa takama ko ka yi gaba da shi, domin idan ka yi haka to sai ka sanya shi saba wa Allah da saba maka, sai ka sanya ranka ta fuskanci abin da kake ki, sai ka jefa shi halaka saboda kai (domin idan ya zalunce ka, zai fada halaka kuma kai ma zaka cutu), kuma kai ne ke nan ka zama mai taimaka masa a kanka, kuma mai tarayya da shi a abin da ya yi maka na mummuna (domin duk wanda ya taimaka wurin jagora ya yi masa ukuba, to ya yi tarayya da jagoran wurin cutar da kansa), kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Ilimi: "Kuma hakkin mai tarbiyyantar da kai da ilimi )mai ilmantar da kai) shi ne ka girmama shi, ka kuma karrama majalisinsa, da kyautata sauraronsa, da fuskantowa zuwa gareshi, da taimaka masa a kanka cikin abin da ba ka wadatuwa da shi na daga ilimi ta hanyar bayar da hankalinka, da halarto da fahimtarka, da tsarkake masa [zuciyarka] da bayyana masa ganinka ta hanyar barin jin dadi, da gudun sha'awa (domin idan ka zama nagari, to duk sa'adda ya gan ka zai ji dadin ganinka a matsayin yana da dalibi nagari), kuma ka san cewa duk abin da yake sanar da kai, sakonsa ne zuwa ga duk wanda ya hadu da kai daga jahilai, to sai ka lizimci kyakkyawar isarwa daga gareshi zuwa garesu, kada ka ha'ince shi wurin bayar da sakonsa, da kula da (isar da wannan sakon da ka samu) daga gareshi idan ka dauki nauyin yin hakan, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Ubangida: "Amma hakkin mai mulki da kai yana kama da mai mulki da kai a jagoranci, sai dai wannan -jagora- ba ya mallakar abin da wancan -mai bawa- yake mallaka. Don haka haka biyayyarsa ta zama wajibi a kanka a cikin komai karami da babba, sai dai idan wani abu ne da zai fitar da kai daga biyayyar hakkin Allah, wanda zai hana ka biyan hakkinsa (ubangiji) da hakkokin sauran halittu, idan ka gama da hakkinsa (ubangiji) sannan sai ka shagaltu da hakkinsa (ubangida), kuma babu karfi sai da Allah".

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, June 04, 2011