Hakkokin Makusanta
  • Take: Hakkokin Makusanta
  • marubucin: Imam Aliyyu Assajjad a.s
  • Source:
  • Ranar Saki: 19:9:40 1-10-1403


Hakkin Matar Aure: "Kuma hakkin wacce kake kula da ita da mallakar aure shi ne ka san cewa Allah ya sanya ta mazauni, wurin hutu, wurin nutsuwa gareka, da kariya, kuma haka nan ya wajabta wa kowannenku gode wa Allah game da samun abokin zamansa, ya san cewa wannan ni'ima ce tasa daga gareshi, kuma ya wajaba ya kyautata zaman ni'imar Allah ya girmama ta ya tausasa mata, duk da kuwa hakkinka a kanta ya fi karfi, biyayyarta gareka ta fi lizimtuwa cikin abin da ta so da wanda ta ki matukar ba sabo ba ne, sannan tana da hakkin tausayawa da debe kewa, da wurin zama gareta, biyan bukatar jin dadin da babu wakawa da ita, wannan kuwa abu ne mai girma, Babu karfi sai da Allah".

Hakkin Bawa: "Kuma hakkin wanda kake mallaka shi ne ka sani cewa shi halittar ubangijinka ne, kuma dan uwanka ne na uba da uwa, kuma tsokarka da jininka ne, ba ka mallake shi domin kai ne ka halicce shi ba Allah ba!, kuma ba ka halitta masa ji ko gani ba, ba ka gudanar masa da arzikinsa ba, sai dai Allah ne ya isar maka da dukkan wannan da wanda ya hore maka shi ya ba ka amanarsa, ya ba ka ajiyarsa, domin ka kare shi, ka yi masa halayen da Allah yake yi (wa bayinsa), sai ka ciyar da shi daga abin da kake ci, ka sanya masa abin da kake sanyawa, kada ka dora masa abin da ba zai iya ba, idan kuwa ka ki shi, to sai ka (mayar da lamarinka) zuwa Allah ka bar shi (ka rabu da shi), ka canja wani da shi, kada ka azabtar da halittar Allah, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Uwa: "Ka sani hakkin babarka cewa ita ta dauki cikinka a inda babu wani mutum mai iya daukar wani, ta ciyar da kai daga cikin zuciyarta da abin da babu wani mutum mai ciyar da irinsa ga wani, ta zama lokacinka da jinta da ganinta, hannunta da kafarta, gashinta da fuskarta, da dukkan gabobinta, tana mai murna da farin ciki, tana mai jure duk wani abin kinta, da zoginta, da nauyinta, da bakin cikinta, har dai hannun kudura ya cire ka daga gareta, kuma ta fitar da kai zuwa duniya, sai ta yarda da koshinka ita ta ji yunwa, ta tufatar da kai ita kuwa ta tsaraita, ta kosar da kai ita kuwa ta yi kishi, ta sanya ka inuwa ita kuwa ta sha rana, ta ni'imantar da kai da wahalarta, da jiyar da kai dadin bacci da rashin baccinta, cikinta ya kasance wurin zama gareka, dakinta ya zamanto matattara gareka, kuma nononta ya zama salkar sha gunka, ranta kuma kariya ne gareka, tana shan zafin duniya da sanyinta don kare ka, to sai ka gode mata a kan wannan sai dai ba zaka iya ba sai da taimakon Allah da dacewarsa".

Hakkin Uba: "Kuma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan, babu karfi sai da Allah".

Hakkin Da: "Kuma hakkin danka shi ne ka san cewa shi daga gareka yake kuma abin rabawa zuwa gareka a wannan duniya da alherinsa da sharrinsa, kuma kai abin tambaya ne kan abin da ka koya masa na kyakkyawan ladabi da shiryarwa ga ubangijinsa mai girma da buwaya, da kuma taimaka masa kan biyayyarsa ga Allah game da kai da kanka, to kai abin ba wa lada ne kan hakan kuma abin yi wa ukuba (idan ka cutar da shi ko ka yi sakacin tarbiyyarsa). To sai ka yi aiki cikin umarninsa irin aikin mai kawata aikinsa ta hanyar kyautata tarbiyyarsa tun a nan duniya, aikin mai yanke uzuri wurin ubangijinsa da abin da yake tsakaninsa da shi ta hanyar kyautata kula da shi da karba masa daga gareshi, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Dan'uwa: "Kuma Hakkin Dan'uwanka shi ne ka sani cewa shi ne hannunka da kake shimfidawa, kuma bayanka da kake jingina da shi, kuma daukakarka da kake dogaro da ita, kuma karfinka da kake ijewa da shi, don haka kada ka rike shi makami a kan sabon Allah, ko ka sanya shi tanadi domin zaluntar halittar Allah, kuma kada ka bar taimakonsa da agaza masa kan makiyinsa, da shiga tsakaninsa da shaidancinsa, da ba shi nasiha, da fuskantuwa zuwa gareshi a tafarkin Allah, to idan ya karkatu zuwa ga ubangijinsa, (Ubangijin) ya kyautata amsa masa, in kuwa ba haka ba, to Allah ya kasance shi ne ya fi zabuwa gunka, kuma mafi girma gareka fiye da shi".

Hakkin Mai 'Yantawa: "Amma hakkin mai 'yanta ka, mai ni'imata maka, shi ne ka sani cewa ya ciyar da dukiyarsa kanka, ya fitar da kai daga kaskancin bauta da dimuwarsa zuwa ga izzar 'yanci da nutsuwarta, sai ya sake ka daga ribacewar mallaka, ya kwance ka daga kaidin bauta, ya fitar da kai daga gidan sarkar (bauta), ya samar maka da hutun izza, ya fitar da kai daga kurkukun rinjaya, ya kare maka tsanani, ya shimfida maka harshen adalci, ya halatta maka duniya dukkanta, ya mallaka maka kanka, ya kwance maka daurin ribacewa, ya ba ka damar bautar ubangijinka, ya jurewa tawayar dukiyarsa da wannan, to ka sani shi ne mafi cancantar halitta da kai bayan danginka na jini a rayuwarka da mutuwarka, kuma shi ya fi cancantar kowa da taimakonka da agajinka, da kariyarka a tafarkin Allah, don haka kada ka taba zabar kanka a kansa har abada matukar yana bukatar ka".

Hakkin 'Yantacce: "Amma hakkin wanda ka 'yanta shi wanda ni'imarka take kansa, shi ne ka sani cewa Allah madaukaki ya sanya ka mai kariya gareshi, mai garkuwa mai taimako mai dabaibayi gareshi, kuma ya sanya ka tsani da sababi tsakaninka da shi, to shi ya cancanci zama kariyarka daga wuta, sai ladanka saboda shi ya kasance daga gareshi a lahira, a duniya kuwa ya ba ka gadonsa idan ba shi da dangi na jini, sakamakon abin da ka ciyar na dukiyarka (a kansa), ka tsayu da shi na hakkinsa bayan ciyar da dukiyarka, idan kuwa ba ka tsayu da kula da hakkinsa ba, to ana jiye maka tsoron kada gadonsa ya yi maka dadi, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Mai Yin Alheri: "Amma hakkin wanda ya yi maka alheri shi ne ka gode masa, ka kuma ambace shi da alheri, ka samar masa da maganar (mutane) ta alheri (a kansa), ka tsarkake yi masa addu'a a tsakaninka da Allah mai girma da buwaya. Idan ka yi haka zai zama ka gode masa a boye da a sarari, sannan idan ka samu dama wata rana kai ma ka rama masa (alherin da ya yi maka), idan kuwa ba haka ba, to sai ka saurari damar da zaka (rama masa) kana mai sanya wa ranka wannan".

Hakkin Ladani: "Amma hakkim mai kiran sallah shi ne ka sani cewa shi mai tuna maka ubangijinka mai girma da daukaka ne, kuma mai kiran ka zuwa ga rabautarka, mafi girman mai taimakonka kan sauke wajibin Allah da yake kanka, sai ka gode masa a kan haka irin godiyar da kake yi wa masu kyautatawa. Idan kuwa ka kasance mai muhimmantar da gidanka ne (ta yadda ko ya yi kiran sai ka yi zamanka), to kai ba ka muhimmantar da lamarinsa na Allah ba, ka sani shi ni'imar Allah ce kanka babu kokwanto cikinta, to ka kyautata kasancewa tare da ita da godiyar Allah kanta a kowane hali, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Limami: "Amma hakkin limaminka a sallarka, shi ne ka sani cewa kai kana dora masa nauyin jakadancin tsakaninka da ubangijinka mai girma da buwaya ne, ya yi magana maimakonka kai ba ka yi magana mai makonsa ba, ya yi maka addu'a kai ba ka yi addu'a gareshi ba, kuma ya isar maka da tsoron tsayuwa gaban Allah mai girma da daukaka da yi maka rokonsa kai ba ka isar masa da wannan ba. Idan an samu wata tawaya tana kansa ban da kai, idan ya kasance mai sabo ne to kai ba ka yi tarayya da shi a cikinsa ba, kuma ba shi da wani fifiko a kanka (cikin alherin da ake samu), sai ya kare maka kanka da kansa, sallarka da sallarsa, to sai ka gode masa a kan hakan, kuma babu karfi da dubara sai da Allah".

Hakkin Abokin Zama: "Amma hakkin abokin zamanka sai ka tausasa masa dabi'arka, ka yi masa adalci a yin magana, kada ka kura masa idanuwa yayin da kake kallo, kuma ka yi nufin fahimtar da shi idan ka yi magana, idan kai ne ka zo wurin zamansa to kana da zabin tashi idan ka so, idan kuwa shi ne ya zo wurin zama gunka yana da zabi ya tashi amma kai ba ka da zabin tashi ka bar shi sai da izininsa, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Makoci: "Amma hakkin makocinka shi ne ka kiyaye shi idan ba ya nan, ka girmama shi idan yana nan, ka taimaka masa ka agaza masa a duka halayen biyu, kada ka bibiyi sirrinsa, kuma kada ka binciki wani mummunan abu nasa da ka sani, idan kuwa ka sani ba tare da ka bincika ba ko ka dora wa kanka neman sanin, to sai ka zama mai matukar katangewa mai matukar suturtawa, ta yadda da masuna zasu nemi kaiwa ga wani sirrin da ba su iya kaiwa ba saboda tsananin tattarewa gareshi, kada ka saurare shi (da satar jin me yake cewa) ta yadda bai sani ba. Kada ka sallama shi yayin tsanani, kada ka yi masa hassada yayin wata ni'ima, ka yafe masa kurakuransa, ka yafe masa laifinsa, kada ka bar yin hakuri da shi yayin da ya yi maka wauta, kuma kada ka fasa zama mai aminci gareshi, kada ka yi masa raddin zagi, ka kuma bata makircin mai zuwa (da sunan yi maka) nasiha (kansa), ka zauna da shi zaman mutunci, kuma babu dubara babu karfi sai da Allah".

Hakkin Aboki: "Amma hakkin aboki shi ne ka yi abota shi da fifita (shi) matukar ka samu damar yin hakan, idan kuwa ba ka yi ba to mafi karanci shi ne ka yi masa adalci, ka girmama shi kamar yadda yake girmama ka, ka kiyaye shi kamar yadda yake kiyaye ka, a tsakaninka da shi kada ka bar shi ya riga (ka) gaggawa zuwa ga wani alheri, idan kuwa ya riga (ka yin alheri) to sai ka saka masa, kada ka takaita masa abin da ya cancanta na kauna, ka dora wa kanka yi masa nasiha, da nuna masa hanya, da dora shi kan biyayyar ubangijinsa, da taimakonsa ga kare kansa cikin abin da ya yi nufi na sabon ubangijinsa, sannan ka kasance rahama gareshi, kada ka zama masa azaba, kuma babu karfi sai da Allah.".

Hakkin Abokin Tarayya: "Amma hakkin abokin tarayya (wanda kuka hada hannun cinikayya) shi ne idan ba ya nan sai ka kare shi, idan yana nan sai ka daidaita kanka da shi, kada ka yi wani hukunci sai da nasa hukuncin, kada ka yi aiki da ra'ayinka ba tare da tasa mahangar ba, ka kiyaye masa dukiyarsa, kada ka ha'ince shi cikin abin da yake babba ne ko karami, ka sani labari (daga manzon Allah) ya isar mana cewa; hannun Allah yana tare da hannayen masu tarayyar (hada hannun jari) matukar ba su ha'inci juna ba, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Dukiya: "Amma hakkin dukiyarka shi ne kada ka dauke ta sai ta hanyar halal dinta, kada ka ciyar da ita sai ta halal, kada ka karkatar da ita daga inda ta dace, kada ka juyar da ita daga hakkinta, kuma kada ka sanya ta ko'ina idan dai daga Allah take sai gareshi tsani zuwa gareshi, kada ka zabi kanka da ita a kan wanda tayiwu ba ya gode maka, ta yiwu (mai gadonka) ba zai kyautata gadon abin da ka bari ba, tayiwu ba zai yi biyayyar Allah da ita (dukiyar) ba sai ya zama kai ka taimaka masa a kan hakan, ko kuma ya zama ya kyautata gani ga kansa da abin da ya farar a dukiyarka sai ya yi biyayya ga Allah da ita, sai ya tafi da riba (ladan aikin alheri da ita) kai kuma ka koma (lahira) da zunubi (saboda tarin haram da ka yi) da hasara da nadama tare da tababbun (mutane), kuma babu karfi sai da Allah".

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, June 04, 2011