Hakkin Iyaye
  • Take: Hakkin Iyaye
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 19:52:43 1-10-1403

Hakkokin Iyaye

HAFIZ MUHAMMAD SA'ID hfazah@yahoo.com

Ayyukan 'Ya'ya
A bangare na farko na wannan littafin mun gabatar da hakkokin 'ya'ya a kan iyayensu saboda muhimmancin hakan, yanzu kuma zamu shiga bayanin hakkokin iyaye, kuma kamar yadda shari'a ta muhimmantar da hakkokin 'ya'ya a kan iyaye da cewa; iyayen su san wannan to ta fara da muhimmantar da hakkokin iyaye a kan 'ya'yansu ne, sannan mu sani cewa idan iyaye ba su bayar da tarbiyya mai kyau ga 'ya'yansu ba to kada su yi tsammanin cewa; za a samu wata kyakkyawar biyayya garesu ta bangaren 'ya'yansu.
Kuma tabbas idan iyaye ba su tarbiyyantar da 'ya'yansu kan koyarwar Ahlul Baiti (a.s) ba to lallai ta yiwu su fada cikin wani hali da ba a taba tsammaninsa ba, don haka ne ma zamu yi bincike kan hakkokin iyaye a cikin wasu fasaloli masu zuwa, da fatan samun tarbiyyantar da 'ya'ya domin su kiyaye su domin taka rawa babba ta samar da al'umma ta gari.
?
Muhimmancin Hakkokin Iyaye
Tun ranar farko da Allah madaukaki ya halicci mutum ya sanya jagorancin 'ya'ya a hannun iyaye wanda yake shi ne uba na farko Annabi Adam (a.s). Wadannan hakkokin an yi bayaninsu a wasu ayoyin na Kur'ani mai girma, aka kuma hada tauhidi da biyayya ga iyaye domin nuni zuwa ga girman wadannan hakkoki a fadinsa madaukaki; "Kuma yayin da muka riki alkawarin Banu Isra'ila da cewa; kada ku bauta wa kowa sai Allah kuma ku kyautata wa iyaye" .
Sannan har ilayau aka sake nuna matsayi babba da Annabi Yahaya ya kai saobda biyayya ga iyaye ana yabonsa da cewa:
"Ya kasance mai biyayya ga iyayensa bai kasance jabberi shakiyyi ba ". Kamar yadda Annabi Isa (a.s) yake fada da dukkan alfahari cewa: "Kuma mai biyayya ga mahaifiyata kuma bai sanya ni jabberi shakiyyi ba" .
Musulunci ya himmantu da nuni zuwa ga wannan matsayi na hakkin iyaye yayin da manzon rahama (s.a.w) yake shelanta cewa: "Aljanna tana karkashin tafin iyaye mata ne" . a wata ruwayar ya zo cewa; "Karkashin tafin iyaye mata, dausayi ne daga dausayin aljanna" .
Imam Ali Sajjad (a.s) yana siffanta irin wannan hakkokin da fadinsa: Ka sani hakkin babarka cewa; ta dauki cikinka wasu watanni tana ba ka abinci daga 'ya'yan itaciya da nononta, kuma ta bayar da gaba dayan rayuwarta domin kare ka, kuma ba ta yi sanyi ba tana mai yarda da kwana da yunwa amma kai ka koshi, ta zama da kishirwa kai ka koshi, ta kasance babu kyakkyawan tufafi kai kuma kana da tufafi, ta shiga rana kai kana inuwa, saboda ba ka nono tana rasa bacci ta jure wa rashin bacci, ta kare ka daga zafin lokacin zafi da kuma tsananin lokacin sanyi.
Kuma ta jurewa dukkan wata wahala domin kai, ka sani ba zaka iya gode wa ni'imar uwa ba, ba zaka iya sauke hakkinta ba, sai dai Allah ya yi maka taimako ya kuma ba ka dacewa .
Imam Sajjad haka ya kasance mai kiyaye hakkin uwa, an taba tambayarsa me ya sa ba ka cin abinci tare da babarka? sai ya ce: Ina jin tsoron kada in riga babata daukar wata loma da ita take so, sai ya kasance na saba wa abin da take so da wannan!
Imam Sadik (a.s) yana cewa; "Wani mutum ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) sai ya tambaye shi ya ma'aikin Allah! Wane makusancina ne zan yi wa alheri? Sai ya ce: Babarka. Ya sake tambaya: bayan nan? Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. Sai ya sake tambayaka a karo na uku. Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. A karo na hudu Sai ma'aikin Allah ya ce masa: Babanka .
Amma kada mu manta irin wannan girmamawa ba mai cancantar ta sai uwa da ta dauki nauyin shiryar da 'ya'yanta ta sha wahala wajen nuna musu hanyar daidai ba wacce ta wulakanta su ba ta watsar da su babu wani tausayi ko damuwa da abin da zasu iya kasancewa nan gaba.
Yaron da bai samu soyayya da kauna daga uwa ba, zai taso tabbas cikin matsalolin rayuwa iri-iri na tunani, kuma a nan gaba zai iya kasancewa daga cikin wadanda ba zasu iya fahimtar ma'anar tausayi ga iyaye ko al'ummarsu ba, don haka iyayen da suka yi masa irin wannan tarbiyya suna kawo wa al'ummarsu wani bala'i ne.
Game da girmama uba kuwa Imam Sajjad yana cewa: "Amma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babu karfi sai da Allah" .
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Addu'ar mutane uku tabbas abin amsawa ce;
1- Addu'ar wanda aka zalunta;
2- Addu'ar matafiyi;
3- Addu'ar Uba ga dansa ;
Sannan akwai fadin Ubangiji game da iyaye da cewa: Ya hukunta kada a bauta kowa sai shi kuma a kyautata wa iyaye, suna manya ne ko kuma dayansu, Ubangiji ya hana a ce musu tir ko kaico, sannan ya yi umarni da a gaya musu magana mai girma da girmamawa. Kuma akwai bayanai da suke nuni ga cewa; wadanda suke cutar da iyayensu suna nesa da rahamar Allah kuma suna cikin azaba a lahira.
Abu Walad Hannad ya tambayi Imam Sadik (a.s) game da ma'anar fadin Allah (s.w.t): "Ku kyautata wa iyaye"? sai Imam Sadik (a.s) ya amsa masa da cewa: "Kyautatawa a nan tana nufin ku yi musu kyakkyawar mu'amala, kada ku tilasta su su biya muku bukatunku koda kuwa masu kudi ne. Kuma ku kula da halayensu da matsalolinsu, shin Ubangiji madaukaki ba ya cewa ba zaku iya samun kyakkyawa ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so? Sannan sai Imam Sadik (a.s) ya ce: "Koda kuwa sun tsufa kada ka sake ka yi musu mafi kankantar wulakantawa, sannan kada ka daga murya a kansu, wato koda sun bata maka rai kada ka wulakanta su, idan suka dake ka to kada ka yi kara a kansu, kada ka fadi magana mai zafi, ka gaya musu magana ta girmamawa; wato ka yi musu magana mai taushi da nuna kauna kamar ka ce musu Allah ya ba ku hakuri, wannan shi ne fadin alheri.
Amma da Allah madaukaki yake cewa: Ka shimfida musu fukafukin rusunawa don tausayi da kauna, wato ka tausasa zukatansu da kallon tausasawa da tausayawa, kuma kada ka taba daga murya a kan tasu, kada ka sanya hannunka a kan nasu, kada ka shiga gabansu yayin tafiya" .
A wata ruwayar Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Me zai hana wani mutum musulmi ya kyautata wa iyayensa suna raye ne ko suna mace! Ya yi musu salla, ya bayar da sadaka don su, ya yi musu hajji da azumi, kuma ladan nan kamar yadda za a ba wa iyayensa shi ma fa haka nan za a ba shi, haka nan saboda wannan al'amari da yake ji na alheri ga iyaye Allah zai ba shi lada mai yawa.
Kaunar batattun iyaye
Mu'ammar dan Khallad ya tambayi Imam Ridha (a.s) cewa: Shin zai iya yi wa iyayen da ba bisa tafarkin gaskiya suke ba addu'a? Sai Imam ya ce: Ka yi musu addu'a kuma ka yi musu sadaka, kuma idan suna raye ba su san hanyar gaskiya ba to ka kyautata musu! Domin manzon Allah (s.a.w) ya ce: Ubangiji ya aiko ni da rahama ne da tausayawa, ba da tsanantawa da cutarwa da rashin kyautatawa ba .
Kyautata wa iyaye yana daga alamomin sanin Allah madaukaki da girmansa, domin babu wata ibada da take gaggauta kusantarwa zuwa ga Allah fiye da kyautatawa iyaye, domin hakkin iyaye reshe ne na hakkin Allah madaukaki. Amma da sharadin kada iyaye su kautar da 'ya'yansu daga tafarkin gaskiya da shiriya, su ba su tarbiyya sahihiya mai amfani da inganci, kuma ba su canja yakinin 'ya'yansu da kokwanto ba, ba su damfara su da duniya ba maimakon Allah (s.w.t) da gudun duniya.
Amma idan iyaye suka kauce wa tafarkin Allah madaukaki to saba musu zata kasance ibada ce, domin ba a saba wa Allah domin biyayya ga abin halitta, kamar dai yadda Allah madaukaki ya ce: "Idan suka tilasta maka ka yi shirka da ni da wani abu wanda ba ka san shi ba to kada ka yi biyayya garesu" .
Daga nan zamu iya fahimtar cewa girmama uwa da uba dole ne ya kasance ba a cikin abin da ya saba wa Allah ba, domin babu biyayya a kan bata da sabon mahalicci madaukaki, amma kuma duk da haka ba a yarda da yi musu wulakanci da mummunan halaye ba, dole ne kuma a girmama su ko suna da imani ko ba su da shi. Kuma Imam Bakir (a.s) a game da haka ya kawo mana magana mai gaskiya abin gaskatawa da cewa; Ubangiji madaukaki bai toge kowa ba game da abubuwa uku:
1- Kiyaye amana ga kowa koda kuwa kafiri ne;
2- Cika alkawari ga kowa koda kuwa ga mutumin banza;
3- Kyautata wa iyaye koda kuwa na gari ne ko batattu ;

A takaice muna iya fahimtar cewa; musulunci ya karfafa yin alaka da juna tsakanin 'yan'Adam kuma ta wannan hanyar ne zai kiyaye kasantuwar al'ummu a matsayin tsintsiya madauri daya, kuma ya samar da wata nau'in hadin kai tsakanin al'umma gaba daya da kara mata dogaro da juna.
Sabanin al'ummar da babu koyarwar addini a cikinta da dan'Adam ba shi da wata kima, a nan ana daukar dan'Adam kamar wani kaya ne da za a yi amfani da shi domin cimma burace-buracen duniya kawai, sannan kuma babu batun maganar kimar dan'Adam balle maganar dogaro da juna.
A irin wadannan wuraren babu maganar kimar kyawawan halaye kamar kyautata wa iyaye da sadaukar da kai, da zabar wani a kanmu, da kunya, da kame kai, da sadar da zumunci, da mutuntaka, da daukakar rai.

Sanin Hakkin Iyaye
Godiya ga wanda ya yi mana ni'ima wani al'amari ne na dabi'ar halittar mutum, kuma hankali ya karfafe shi, don haka ne ma Allah madaukaki ya umarci 'ya'ya da su yi godiya ga wahalhalun da iyaye suka yi na dawainiyarsu a fagage daban-daban, Allah madaukaki yana cewa: "Mun yi wasiyya ga mutum da iyayensa, babarsa ta dauki cikinsa cikin rauni a kan rauni, kuma yayensa cikin shekaru biyu, (don haka) ka gode mini da iyayenka zuwa gareni zaku koma" .
Kuma akwai aya mai tsawo a cikin Kur'ani da ta yi magana kan hakan a surar ahkaf wacce take nuni da wasiyyar da aka yi wa mutum na kyautata wa iyayensa, sakamakon irin wahalhalun da suka sha kansa.

Sanyaya Halaye Ga Iyaye
Kallon iyaye da tausayawa yana daya daga cikin abubuwan da shari'a take ganinsu a matsayin ibada, manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Kallon fuskar iyaye ibada ne .
A wani hadisin mai girma da daukaka yana cewa: Babu wani mutum da zai kalli iyayensa da soyayya da kauna da tausayawa sai Ubangiji ya ba shi ladan hajji karbabbe a kowane kallo da ya yi, sai aka tambayi manzon Allah (s.a.w)! Idan da mutum zai kalli fuskar iyaye sau dari yana da wannan ladan kuwa? Sai ya ce: Haka ne, idan ya yi hakan sau dari a rana yana da ladan hajji dari da zai samu .

Nisantar Tsanantawa
Ibrahim dan Mahzam yana cewa: Wata rana na fito daga wajen Imam Sadik (a.s) a madina na tafi gidana, babata tana rayuwa tare da ni, sai ta yi jayayya da ni kan wani al'amari kuma na gaya mata magana maras dadi da ba ta dace ba.
Wayewar garin wannan ranar bayan sallar asuba sai na sake zuwa wajensa (a.s). Yayin da nake shigowa ba tare da na ce komai ba sai Imam (a.s) ya ce da ni: Ya kai dan Mahzam! Daren jiya ka yi magana mai zafi mai kaushi ga babarka, shin ba ka sani ba cewa cikinta ne ya zama gidanka tsawon lokaci, da goyonka da ta yi, kirjinta ya zama abincinka, saboda me kake yi mata magana mai zafi, kada ka sake yin hakan !

Godiya Ga Iyaye
'Ya'ya na gari kodayaushe suna kokarin ganin sun gode wa iyayensu, kuma wannan aiki ne mai matukar muhimmanci da amfani. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Hutu a kan gado saboda hidima da kyautata wa iyaye wanda yake sanya su farin ciki, da kuma haduwa da su da fuska mai walwala ya fi yaki da takobi a tafarkin Allah… idan wani ya bakanta wa iyayensa to sallarsa ba za a karbe ta ba.
Haka nan Imam Sadik (a.s) ya ce: Idan kana son ka samu tsawon rayuwa to ka faranta wa iyayenka.

Kiyaye Mutuncin Iyaye
Kiyaye mutuncin iyaye yana daga cikin hakkokin iyaye kan 'ya'yansu, wani lokaci wasu 'ya'yan sukan yi aikin da zai sanya cin mutunci da zagi ga iyayensu a cikin mutane, kuma wannan yana jawo wa iyayen jin bakin ciki da zubar mutunci.
Don haka ne 'ya'ya su guji abin da zai kawo wulakanci ga iyayensu, a kan haka ne manzon rahama (s.a.w) yake cewa: Mutum ya zagi iyayensa yana daga manyan zunubai. Sai aka ce ya ma'aikin Allah (s.a.w) yanzu mutum ya zagi iyayensa? Sai ya ce: haka ne mana, idan mutum ya zagi iyayen wani, shi ma wancan sai ya zagi iyayensa .

Ba Wa Iyaye Dukiya
'Ya'ya na gari masu imani su ne wadanda suke sanya komai nasu a hannun iyayensu, kuma ba su taba fasa bayar da dukiyarsu ga iyayensu ba, komai nasu suke bukata sai su ba su.
Imam Ridha (a.s) yana fada a wata wasiyya mai hikima da ya yi ga 'ya'ya yana mai cewa: Farin ciki ya same ka idan ka yi biyayya ga babanka, ka kyautata masa, ka kaskan da kai a gabansa da girmama shi da darajanta shi, ka yi kokari kodayaushe muryarka ta yi kasa da tasa, saboda shi ne asalin samuwarka da dalilin zuwanka duniya, kuma kai reshe ne daga gareshi, idan da babanka ba ya nan da ba a same ka ba, don haka sai ka ba wa babanka da babarka dukiyarka.
A wata ruwayar an ruwaito daga manzon Allah (s.a.w) cewa; Da kai da dukiyarka duk na babanka ne .

Biyayya A Kan Tafarkin Gaskiya
A bisa koyarwar Kur'ani wani abu ne wajibi a yi biyayya ga iyaye, kamar yadda Imam Ali (a.s) yake fada cewa; "Hakkin uba a kan da shi ne ya bi shi a komai banda a sabon Allah madaukaki" . Kuma haka nan wani mutum daga kasar Yaman ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) domin ya tafi yaki tare da shi, sai Annabi (s.a.w) ya umarce shi da ya koma ya nemi izini da yardar iyayensa, "…idan sun bayar da izini ka yi yaki, idan ba haka ba to sai ka yi musu kyawawan halaye, ka sani wannan aikin gareka ya fi dukkan biyayya ga dukkan umarnin Allah bayan kadaita Allah" .
Kamar yadda dai muka yi nuni ne a baya cewa; kiyaye dukkan wadannan hakkokin yana kasancewa ne idan bai saba da keta hakkin wasu ba, don haka idan wani ya tauye hakkin 'ya'yansa da matarsa da 'yan'uwansa da sauran jama'a da sunan kare hakkin iyaye da biyayya garesu wannan bai dandani imani ba, kuma maimakon ya samu lada zai samu zunubi ne. Don haka ne ma muke karfafa cewa: Biyayya ga iyaye tana kasancewa ne banda inda ta saba wa Allah madaukaki da umarninsa.

Lokacin Tsufa
Wani babban bala'in da ya hau kan al'ummun da suke da'awar ci gaba a wanan duniya shi ne rashin kimanta tsofaffi, a wasu al'ummu idan iyaye sun tsufa sai a kai su gidan kula da raunana, sai iyaye su rasa samun mai nuna musu kauna a kusa alhalin suna bukatar haka daga 'ya'yansu kamar yadda 'ya'yansu suke bukata daga garesu yayin yarintarsu.
Haka nan zaka ga iyaye tsofaffi suna cikin dandana azabar rashin samun wannan tausasawa da tausayawa, kai akwai wanda na ga yana kuka a gidan irin wadannan raunana a talabijin yana cewa; yau shekara bakwai ke nan sai dai dansa ya aiko masa da kayan abinci amma bai gan shi da idanuwansa ba, har ma yana neman hukuma ta tiamaka masa dansa ya zo ya gan shi da idanuwansa.
Irin wannan rayuwa tana da daci matuka ga iyaye tsofaffi: Wannan abin takaici da yake wakana a wasu kasashen har na musulmi yana da zafi da zogi a zukata matuka, iyayen da suka dora dukkan rayuwarsu ga hidimar 'ya'ya da al'umma amma bayan duk wannan wahala sai sakamakonsu ya kasance tsarewa da kullewa kamar 'yan gidan yari, suna masu kirga kwanakin mutuwarsu har zuwa wafatinsu, a irin wannan duniya mai da'awar samun ci gaba da 'yancin dan'Adam.
Idan mun yi dubi zuwa ga abubuwan da muka kawo zamu ga yadda addinin musulunci ya yi umarni da girmama iyaye ta yadda ya haramta gaya musu mafi karancin kalmar da take nuni zuwa ga wulakanci . Ibrahim dan Shu'aib ya ce da Imam Sadik (a.s): Ina da uba wanda ya tsufa ya yi rauni matuka da gaske, ina goya shi, kuma ina kai shi waje domin ya biya bukatarsa. Sai Imam (a.s) ya ce masa: Duk yadda zaka iya ka yi wa babanka hidima, kai har ma ka dauki loma da hannunka ka sanya masa a bakinsa, wannan ne aikin da zai kasance sanadiyyar kubutarka daga wuta .

Hakkokin Iyaye Bayan Mutuwa
A mahangar musulunci hakkin iyaye kan 'ya'ya baya karewa da mutuwa, kamar yadda iyaye suke da hakki a lokacin da suke raye haka nan ma suna da hakki kan 'ya'ya bayan mutuwarsu. Wasu daga cikin irin wadannan hakkokin sun hada da:
1- Ziyarar kabarinsu;
2-Karanta musu Kur'ani;
3-Ba su ladan ayyukan alheri;
4-Biya musu basussukansu;
5-Yi musu hajji a ba su ladan;
6-Yi musu sadaka a ba su ladan;
7-Yi musu azumi a ba su ladan;
8-Ba su ladan 'yanta bayi;
9-Yi musu salla a ba su ladan;
10- Yi musu addu'a .

Sakamakon Kyautata Wa Iyaye
Idan mun koma zuwa ga hadisan imamai (a.s) zamu samu cewa sun yi nuni zuwa ga wani sakamako da za a samu sakamakon kyautata wa iyaye, kuma zamu yi nuni zuwa ga wasu daga cikinsu:

Aljanna
Wani mutum ya zo wajen Imam Sadik (a.s) ya ce: Ya kai dan manzon Allah! Babana ya tsufa kuma ni ina goya shi kuma ina kai shi ko'ina domin biyan bukatarsa. Sai Imam ya ce: Ka yi masa hidima iyakacin yadda zaka iya, ka sani wannan aikin shi zai kai ka aljanna ne .

Ladan Shahada
Wata rana manzon Allah (s.a.w) ya ga wani saurayi wanda ya shagaltu da neman abin rayuwarsa sai ya ce masa: "Ya kai saurayi! Shin kana kula da wani da wannan kudin da kake samu? Sai ya ce: E. Sai ya ce: Waye? Sai ya ce: Babata. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Kada ka daina yi mata hidima, don ka sani aljanna tana karkashin kafafunta".
Kuma Manzon Allah (s.a.w) ya kara da cewa: Da ladan shahada ya kasance ga wanda aka kashe a tafarkin Allah ne kawai da ke nan shahidan al'ummata 'yan kadan ne, sannan sai ya kawo mutane bakwai na musulmi da ake kirga su cikin shahidai kamar haka:
1-Wanda ya kone a wuta;
2-Wanda ya mutu a cikin matsatsin mutane;
3-Matar da mutum yayin haihuwa;
4-Wanda gini ya fado masa ya mutu;
5-Wanda ya nutse a ruwa ya mutu;
6-Musulmin da ata dabba ta cinye shi;
7-Da wanda yake kokarin ganin ya yalwata wa iyalinsa dai iyayensa;
Wadannan dukkaninsu suna cikin shahidai ;

Ya Fi Jihadi Lada
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Shugaban masu alheri ranar lahira shi ne wanda yake yi wa iyayensa abubuwan alheri bayan mutuwarsu. Imam Sadik (a.s) ya ce: Wani mutum ya zo wajen ma'aikin Allah (s.a.w) sai ya ce: Ya ma'aikin Allah! Ni zan yi maka bai'a kan yin hijira da yaki. Sai manzon Allah (s.a.w) ya tambaye shi: shin daya daga cikin iyayenka yana raye? Sai ya ce: E, duka biyun suna raye. Manzon Allah (s.a.w) ya sake tamaya: Shin kana son ladan lahira wajen Allah madaukaki? Sai ya ce; E. Sai manzon Allah ya ce: To ka koma wajen iyayenka, kuma ka kyautata musu.

Mafi Kyawun Aiki
Cikon annabawa (s.a.w) yana cewa: Duk wanda yake son ya samu tsawon rayuwa da yalwa a rayuwa da arziki, da kuma dukiya mai yawa, to ya kyautata wa iyayensa. Domin kuwa wannan aikin wani bangare ne na biyayya ga Allah madaukaki.
Wannan al'amari tabbas yana nuna mana cewa izzar duniya da lahira tana cikin biyayya ga iyaye ne.
Kuma ya zo a wata ruwaya cewa: Mansur dan Hazim ya tambayi Imam Sadik (a.s): Wane aiki ne ya fi sauran ayyuka. Sai Imam (a.s) ya ce: Salla a lokacinta, da biyayya ga iyaye, da jihadi a tafarkin Allah" .

Tsawon Rayuwa Da Samun Da Nagari
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya yi mini alkawarin kyawawan halaye ga iyayensa to ni ma zan lamunce masa dukiya mai yawa da tsawon rayuwa, da soyayya da kuma daukaka tsakanin iyalai da danginsa . Haka nan a wata ruwayar ya zo cewa; "Ku bi iyayenku sai 'ya'yanku su bi ku" .

Saukin Mutuwa
Imam Sadik (a.s) ya ba wa 'ya'yan da suke aikin alheri da kyautata wa iyaye ladan cewa: "Duk wanda yake son ya samu sauki a wajen Ubangijinsa yayin mutuwa to ya sadar da zumuncinsa, kuma ya kyauta wa iyayensa, idan ya yi haka to zai samu sauki yayin fitar ransa kuma ba zai samu talauci da miskinanci a rayuwarsa ta duniya ba.
Wani saurayi daga sahabban manzon Allah (s.a.w) da ya yi rashin lafiya aka kwantar da shi. Sai manzon Allah (s.a.w) ya tafi domin ya gai da shi. Ga halinsa ya yi tsanani kuma ga shi karshen rayuwarsa ne. sai manzon rahama ya umarce shi da ya fadi kalmar shahada, amma sai harshensa ya kasa kawo wannan kalma.
Sai manon Allah (s.a.w) ya tambayi wata mata da take wurin cewa: Shin wannan saurayi yana da uwa kuwa? Sai ya ta ce: E, ni ce babarsa. Sai ya ce: Shin kina fushi da shi ne? Sai ya ta ce: E, ya ma'aikin Allah. Sai manzon rahama (s.a.w) ya nemi ta yafe masa kurakuransa, sai ta ce: Ya ma'aikin Allah na yafe masa saboda kai.
A wannan lokacin sai manzon Allah ya sanar da wannan saurayi wannan addu'a: Ya man yakabalul yasira wa ya'afu anil kasir, ikbil minni alyasir wa'afu annil kasir, innaka antal afuwwul gafur. Sannan sai ya lakkana masa kalmar shahada, a wannan lokacin ne saurayi ya bude bakinsa cikin sauki ya fadi wannan kalma ta shahada" .

Ladan Hajji
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: babu wani da da zai kalli fuskar iyayensa da tausayawa da rahama sai Ubangiji ya rubuta masa ladan hajji kan kowane kallo da ya yi. Sai sahabban manzon Allah (s.a.w) suka ce: Ya ma'aikin Allah! Idan mutum ya kalli fuskar baban da babarsa a sau dari fa za a ba shi wannan ladan? Sai ya ce: Haka ne, koda kuwa ya kalla sau dari ne to za a ba shi ladan hajji sau dari. Ubangiji madaukaki mai iko ne ya ba shi lada sama da haka .

Shafe Zunubai
Samun gafarar zunubai yana daya daga cikin abubuwan da ake samu saboda kyautata wa iyaye. Imami na shida yana cewa; wata rana wani mutum ya zo wajen Annabi (s.a.w) sai ya ce: Ya ma'aikin Allah! Lokacin da na sami 'ya, sai na rene ta har ta balaga, har zuwa wata rana sai na sanya mata tufafi na yi mata ado, sannan sai na kawo ta wajen rijiya na jefa ta ciki.
Tana ihu tana neman taimakona, karshen abin da na ji a wurinta shi ne tana cewa da ni: Baba!! Ya ma'aikin Allah mene ne kaffarar wannan sabon? Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: Ya kai wannan mutum shin babarka tana raye? Sai ya ce: A'a. sai manzon Allah ya ce: Shin goggonka tana raye? Sai ya ce: E. Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: Ka tafi ka kyautata mata ka yi mata hidima domin ita tana matsayin babarka ce, kuma yi mata kyawawan halaye shi ne kaffarar wannan zunubin .
Imam Sadik (a.s) ya kara da cewa: A zamanin jahiliyya iyaye maza sun kasance suna kashe 'ya'yansu domin kada su fada a ribace su a wasu kabilun su haihu a can.

Samun Baban Matsayi
Annabi Musa (a.s) ya ga wani mutum mai matsayi babba a wajen Allah, mai daraja madaukakiya sai ya yi burin ya samu matsayinsa. Don haka sai ya tambayi Allah madaukaki ya Allah! Mene ne ya sa bawanka ya kai ga wannan matsayin? Sai Allah madaukaki ya ce: Ya kai Musa! Ya kasance mai kyautata wa iyayensa ne… .

Dacewa a Rayuwa
Hidima ga iyaye yana daga cikin mafi muhimmancin abubuwan da suke kawo dacewa a rayuwa a dukkan bangarorin rayuwar mutum, kuma da samun nutsuwar rayinsa. Cikon manzanni (s.a.w) ya yi nuni da wannan a fadinsa mai daraja: Ubangiji ya sanya ni'imomi hudu sakamakon ayyuka hudu:
1- Samun ilimi sakamakon girmama malami;
2- Tabbatar imani sakamakon girmama Allah madaukaki;
3- Jin dadin rayuwa sakamakon girmama iyaye; 4- Samun tsira daga jahannama sakamakon barin cutar da mutane.

Biyayya Ga Manzon Allah (s.a.w)
Wani mutum ya tambayi manzon Allah (s.a.w) game da wahalar da yake sha da iyaye. Sai manzon raham ya ce: Ka kyautata wa babarka, ka kyautata wa babarka, ka kyautata wa babanka, ka kyautata wa babanka, ka kyautata wa babanka.
Daga nan ne zamu ga cewa biyayya ga umarnin manzon Allah (s.a.w) yana cikin biyayya ga Allah ne wanda wannan shi ma yana da nasa ladan, kuma yana cikin gaskiya da cin nasara.
Ubangiji yana cewa: "Duk wanda ya bi Allah da manzonsa to hakika ya rabauta rabauta mai girma" . Don haka da nagari wanda yake kyautata wa iyayensa yana cikin biyayya ga manzon Allah (s.a.w) ne kuma zai samu darajar da Allah madaukaki ya yi alkawari.

Mummunan Sakamakon Saba Wa Iyaye
Kamar yadda biyayya ga iyaye take da kyakkyawan sakamakon duniya da lahira saboda biyayya ce ga Allah haka nan ma munana halaye ga iyaye yake da nasa munanan sakamako masu cutarwa, kuma zamu yi nuni da wasu daga cikinsu a nan kamar haka:
1- Korewa daga wurin Annabi (s.a.w) ;
2- Nisanta daga adalci ;
3- Rasa ni'imomin Ubangiji kamar aljanna ;
4- Matsaloli a duniya ;
5- Azabar rai mummuna ;
6- Fushin Allah ;
7- Gajarcin rayuwa ;
8- Hana shi hakkokin zamantakewa ;
9- Sabo ne babba .

Mai son samun cikakkun bayanai kan hanyar tarbiyyar yara a Musulunci, sai ya nemi littafinmu mai suna "Tarbiyyar Yara a Musulunci".
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012