Tarbiyyar Yara2
  • Take: Tarbiyyar Yara2
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 19:12:21 1-10-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Tarbiyyar Yara A Musulunci Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannan littafi mai suna "Tarbiyyar Yara A Musulunci" domin bayani game da yadda ya kamata a tarbiyyantar da yaro, an rubuta wannan littafi ne saboda bukatar da take cikin al'ummarmu ta ganin an kiyaye hakkin yara da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari ta Addini wanda wannan shi ne sirrin ci gaban kowace al'umma da kuma habakarta a fagage daban-daban, kuma hanya mafi dacewa wajan ilmantarwa. Domin idan yara suka gyaru suka ta so da Azama da Kishi da Ilimi da Tunani mai kyau wannan yana nufin al'umma zata ci gaba kuma zata kai ga cimma burinta da gaggawa ba tare da wani tsoro kan haka ba.
Tun da ya kasance hadafinmu shi ne gina gida na gari da al'umma saliha wacce zata zama ta daukaka Addinin musulunci da kyawawan dabi'u a cikin al'umma shi ya sa a wannan karon muka ga ya dace mu bayar da himma wurin bincike game da yadda ya kamata a reni manyan gobe, da fatan Allah ya sa wannan aiki ya zama karbabbe a wurinsa ya kuma karfafi Addinin musulunci da shi. Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Dan'uwana Ahmad Muhammad kuma ya haskaka kabarinsa da shi.

Magana kan yara wani abu ne da babu abin da ya kai shi muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam Saboda su ne manya a gobe, kuma idan ba a tarbiyyatar da su yadda ya kamata ba to wannan yana nufin rushewar al'adun al'umma da shafe kufan abin da ta gada kaka da kakanni. Shi ya sa ma a tarihin juyin juya hali na kowace al'umma zaka ga yana faruwa da Yara da Samari ne sannan ya yiwu, idan mun duba tarihin Annabawa (a.s) da Manzon Rahama (s.a.w) da ma juyin da ya faru a bayansu, za mu ga ya faru ne ta hannun samari da yaran al'ummu.
Duba ka gani yadda mushirikan Makka suke cewa: Manzo ya zo ya bata tunanin samarinsu sabaoda samari su suke karbar canji, amma tsohon jini da ya kafu a bisa wata Akida da ta kafu a kwakwalwarsa to wannan yana da wahala ya canja sai daidaiku, don haka ne ma Ku'rani ya bayar da muhimmaci a kan shekarun samartaka.
Don haka ne Malaman tarbiyya suke ganin cewa; Yana da wahala ga mutum ya canja da wuri bayan ya yi shekaru arba'in kan wani ra'ayi: Misali idan mutum ya kai shekara arba'in ba ya sallar dare to yana da wahala ya iya jurewa ya dage a kai, Shi ya sa idan saurayi ya dore a kan hanya ta gari to yana da wahala ya canja sai dai idan ya zama akwai wani sirri tsakaninsa da Allah da ba shi da kyau, ko kuma lallai zuciyarsa ba ta kama hanya ta gari ba, ko ba ta doru bisa mahanga sahihiya da Allah ya dora Addininsa a kai ta hannun Manzonsa (s.a.w) ba.
Haka ma idan ya zama yana da dauda a zuciya kamar hassada ko mugun kulli kan bayin Allah na gari to duk wannan yana iya tasiri wajan lalacewarsa koda yana ayyuka ta bangaren ibada a nan ba mamaki ba ne karshensa ya ki kyau. Duba Bil'am dan Ba'ur mana ka gani da malami ne shi amma saboda ya yi wa Annabi Musa (a.s) hassada sai ya lalace, haka ma Iblis yana daga mala'iku masu ilimi na koli, amma sai ya yi hassada, shi ke nan sai ya kaskanta, darajarsa ta yi kasa. Shi ya sa ya zo a wata ruwaya cewa: "Kada ku duba yawan sallarsu da azuminsu da yawan hajji da kyawawa da kuma sautinsu da dare, ku duba gaskiyar magana da rikon amana" . Wato; kada a duba yawan salla da ruku'u ko sujadar mutum, ta yiwu wata al'ada ce da ya saba da ita, idan ya bari sai ya ji babu dadi, amma a duba ayyukansa da mu'amalarsa, irin wadannan mutane suna kama da wanda ya saba da sallar jam'i ko ta dare ko azumin nafila amma ba sa tasiri a ayyukansu.
Haka ma yaro idan ya saba da wani abu haka zai taso da shi a matsayin saurayi, idan da ya saba da karatu sai ya zama saurayi to ba zai iya bari ba kuma haka zai manyanta, haka kuma zai tsufa matukar wani yanayi na tilas da lalura bai fado ba. Amma yaron da ya taso yana bin 'bata gari yaya zai taso? Don haka ne tarbiyyar yara da ta samarin al'umma da ilmantar da su domin a samu al'umma ta gari take bukatar hukuma, da iyaye, da 'yanuwa, da makwabta, da malamai, su sanya hannu:

Kur'ani mai girma ya himmantu da tarbiyyar yaro da kula da shi, don haka ne a ayoyi masu yawa ya yi magana game da 'ya'ya da hakkokinsu, da yadda ya kamata a kalle su, da zama da su, da zamu iya kawo su a dunkule kamar haka:
1- 'Ya'ya adon rayuwar duniya ne: Kahafi: 46.
2- 'Ya'ya su ne asasin jarrabawa daga Allah: Tagabun: 15.
3- Wasu daga 'ya'yanmu makiyanmu ne: Tagabun: 14.
4- Kada ku damu da nauyin 'ya'yanku a kanku: An'am: 151.
5- Kada ku yi alfahari da yawan 'ya'yanku: Saba': 35.
6- 'Ya'yan da ba na kirki ba, ba su da wani amfani a lahira: Mumtahannat: 3.
7- Kada 'ya'ya su hana tuna Allah: Munafikun: 9.
8- Wasu 'ya'yan nutsuwar rai ne kuma sanyin idanuwa ga mutum: Furkan: 74.
9- Yi wa 'ya'ya wa'azi da nasiha: Lukman: 13.
10- Yi wa 'ya'ya addu'a ta gari: Ibrahim: 35.
11- Yi wa 'ya'ya nasiha da wasiyya a karshen rayuwar iyaye kafin mutuwarsu: Bakara: 132 .

Daga cikin irin nasihohi da wasu littattafai suke tattare da su game da tarbiyyar 'ya'ya, musamman idan mun yi la'akari da cewa yaro yana daidai da farar takarda ce wacce duk wata tarbiyya da aka ba shi ita ce takan yi masa tasiri a rayuwarsa. Kuma yaro yana dauke da yiwuwar ya zama kamilin mutum wanda kyakkyawar tarbiyya ce zata iya daidaita shi, ko kuma ya samu mummunar tarbiyya ta rushe wannan karfin zama salihi na gari da yake kunshe da shi. Daga cikin irin wadannan matakai kuma hanyoyi masu muhimmanci akwai:
1- Dasa wa yaro jin nutsuwar zuci da rai, da kama hannunsa domin daukaka matsayinsa, wannan kuwa yana iya kasancewa ne ta hanyar rashin wulakanta shi, da sanya masa jin daukaka da kamala, ko rashin nuna masa gazawarsa. Don haka abin da ya kamata shi ne: a rika tattaunawa da shi, da neman shawararsa da nuna masa inda ya samu rauni, domin ya taso mutum mai dauke da jin cewa zai iya kasancewa jagora a kowane fage.
2- Rashin kallafa wa yaro abin da ya fi karfinsa, ko kuma ayyukan da ba ya son su, domin gudun kada ya gajiya ya kasa, wannan kuma yana iya janyo masa jin kasawa da rushe himmarsa.
3- Dada wa yaro kaimi domin ya zama wani babban mutum ta hanyar girmama masa manyan mutane da suka gabata ko rayayyu, da yi masa bayanin sirrin abin da ya sanya suka zama manyan mutane masu daraja da kuma hanyoyin da suka bi domin kai wa ga wannan matsayin.
4- Kula da yaro domin kada girman kai da ruduwa da kansa su same shi domin yana ganin ya fi sauran abokansa kokari a karatu, da koya masa siffofin dabi'u kyawawa da ya kamata ya siffantu da su, da nuna masa wadannan ni'imomi da yake da su daga Allah ne kuma shi zai godewa.
5- Yi wa yaro bayanin abin da al'ummarsa take ciki dalla-dalla da kuma yadda zai bayar da tasa gudummuwa domin kawo ci gaban al'ummarsa ta hanyar:
a. Samar masa akida ta gari da zai doru a kanta.
b. Bayanin gudummuwar da al'ummarsa ta bayar wajen ci gaban dan Adam.
c. Sanar da shi yadda zai fuskanci matsalolin da suka addabi al'ummar musulmi, da kuma sanya masa cewa yana da karfin da zai iya kawo karshensu.
d. Yi masa bayanin dalilan da suka sanya al'ummar musulmi ta samu ci baya da dulmiya cikin jahilci da mummunan halin da ta fada ciki, da kuma nuna masa shi zai iya kaucewa wannan kuma zai iya maganinsa.
e. Yi masa bayanin yiwuwar gyara da za a iya samarwa ta hanyar amfani da karfin da al'ummarsa take da shi.
f. Yi masa bayanin mummunan halin lalacewar kyawawan halaye da na zamantakewar al'umma da al'ummar da take da'awar ci gaba ta fada cikinsa, da sauran matsaloli da suke fama da su.
6- Sanya lura da karfafawa a kan babbar gudummuwar da telebishan, da radiyo, da mujallu, da kissoshi masu hoto, da labaru zasu iya bayarwa wajan tarbiyyar yara da gina su .
Don haka ne nake nasiha ga mutane da su yi duba zuwa ga Gidan Abrar wato Gidan Sayyidi Ali (a.s) da Fadima (a.s) da 'Ya'yansu Hasan da Husaini (a.s) a kuma a karanta kissarsu da ta zo a cikin surar Insani, da alwashin da suka yi na azumi, da kuma sadakar da suka yi da abincinsu a kwana uku: ga maraya, da miskini, da kuma ga ribataccen yaki , domin karanta irin wannan kissoshi zai sanya mana daukar ilimi da darussa masu yawa game da yadda ya kamata salihin gida mai tarbiyya ya kasance.

Rajab 1424