Yin Kuka
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Kuka A Kan Rabuwa Da Masoya
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Bakin ciki kuwa yayin da mutum ya rasa wani nasa ko abokansa, wani abu ne wanda yake kunshe a cikin halittar mutum. A lokacin da wani yake cikin musibar rashin wani nasa ko wanda ya sani, mutum zai kasance cikin bakin ciki, ba tare da ya sani ba hawaye zasu zubo daga idanunsa. Zuwa yanzu ba a samu wanda yake inkarin wannan hakikar ba ta yadda ya zamana mutum da gaske yake yana inkarin hakan. Babu shakka a bayyane yake cewa musulunci addini ne wanda yake ya dace da fitra da halittar mutum, sannan ba tare da sabawa halittar mutum ba ya tsara masa hanyar rayuwa: "Ka tsayar da fuskarka ga addini tsarkake na Ubangiji, halittace wacce Allah ya halatta mutum a kanta" .
Babu shakka ba zai yiwu ba ya zamana addinin da yake na duniya ya zo kuma ya hana mutane kuka yayin da suka rasa wani nasu, matukar dai ba zai haifar da hushin ubangijin ba yin hakan.
Bincike a kan tarihi ya tabbatar mana da cewa Manzo (s.a.w) da sahabbansa da tabi'ai dukkan sun yi rayuwarsu ne a kan dabi'a ta "yan adamtaka. A nan zamu kawo wasu abubu na tarihi a matsayin sheda a kan abin da muka fada kamar haka:
Manzo (s.a.w) yayin da dansa Ibarahim ya rasu ya yi kuka a kan rashinsa, yana mai cewa: Idanuwa suna kuka zuciya tana konewa, babu abin da zamu fada sai abin da yake neman yardar Allah ne, ya Ibarahim mun yi bakin ciki a kan rabuwa da kai"!
Masu tarihi sun rubuta cewa: Lokacin da Ibrahim dan manzo yake cikin magagin mutuwa, sai Manzo ya shigo cikin gida, ya gan shi bisa cinyoyin mamarsa a rungume,. Sai Manzo ya karbe shi, ya kwantar da shi bisa cinyarsa sai ya ce:
"Ya Ibrahim ba zamu wadatar da kai komai ba a wajen Allah, Sai kwalla suka cika masa idanunsa, sai ya ce lallai Ibarahim muna tsananin bakin ciki akanka, idanuwa suna kuka zuciya tana konewa saboda bakin ciki, ba zamu fadi abin da zai fusata Ubangiji ba, ba dan mutuwa ta kasance gaskiya ba, kuma alkawari wanda ba ya canzawa ba, kuma wata hanya ce wacce dole kowa ya tafi, da bakin cikimmu na rashinka ya nunka wannan sau daruruwa.
A wannan lokacin sai Abdurrahaman Bn Auf ya ce wa manzon Allah: Ashe ba kai dakanka ka yi hani a kan kukan mutuwa ba? Sai Manzo ya bayar da amsar cewa: ba haka ba ne na yi hani ne a kan kukan da sauti guda biyu, wato kara da kuwwa a lokacin da mutum wata musiba ta same shi, sannan da yagar fuska da keta tufafi, da karar kuka wanda ake rera shi daga cikin makoshi, wanda yake wannan aikin shaidan ne, ko kuwa ayi shi da yanayin waka ta haram. Amma wannan kukan nawa ya samo asali daga tausai da kauna, Sannan duk wanda bai tausaya ba, ba za a tausaya masa ba .
Wannan misali na sama ba shi kadaiba ne misali wanda Manzo ya yi kuka a kan rasa wani nasa. Manzo a lokacin dansa Tahir ya rasu ya yi kuka kuma yana cewa: "Idanuwa suna kuka zuciya tana konewa saboda bakin ciki amma ba zamu yi sabon Allah ba" .
Allama amini a cikin littafinsa mai dimbin daraja "Al-gadir" ya kawo a wurare da dama inda Manzo ya yi kuka sakakamon rasa wani nasa da ya yi. Misalan da zamu kawo a kasa suna daga cikin misalan da Allama Amini ya kawo:
1-Lokacin da Hamza Allah ya jikansa ya yi shahada a yakin Uhd, Safiyya diyar Abdul Mutallib ta tafi tana neman Manzo lokacin da ta ga Manzo, sai Manzo ya shiga tsakaninta da Ansar ya ce: ku kyale ta da abin da ya dame ta, Safiyya ta zauna kusa da gawar Hamzata yi kuka. Duk lokacin da muryar kukanta ta yi sama, sai Manzo shi ma kukansa ya yi sama, idan ta yi kuka a hankali sai Manzo shi ma ya yi a hankali. Haka nan Fadima (a.s) 'yar Manzo ta kasance tana kuka Manzo shi ma yana kuka tare da ita, yana cewa: Babu wanda musiba zata taba shafa kamar ki.
2- Bayan yakin Uhd Manzo ya dawo Madina, sai ya samu labarin cewa matan Madina suna yin kuka a kan danginsu da suka yi shahada a Uhd, sai Manzo ya ce: Shi Hamza bashi da mai yi masa kuka? Lokacin da Ansar suka ji wannan kalami na Manzo, sai suka cewa matansu: Duk wanda yake so ya yi kuka a kan shahidinsa ya fara yin kuka a kan Hamza baffan Manzo. (Kamar yadda mai littafin "Zawayid yake cewa har yanzu wannan abin haka yake duk lokacin da wani zai yi wa mamacinsa kuka sai ya fara da yi wa Hamzakuka".
3-Lokacin da labarin shahadar Ja'afar, Zaid Bn Harisa da Abdullahi Bn Rawaha ya iso wa manzon Allah, kwalla sun zubo daga idanun Manzo.
Lokacin da Manzo ya je ziyarar Mahaifiyarsa ya yi kuka kwarai da gaske, sakamakon wannan kukan nasa ne wadanda suke tare da shi suka fashe da kuka.
4-Lokacin da Usman Bn maz'un ya rasu, wanda yake daya daga cikin sahabban Manzo (s.a.w) Manzo ya sumbaci gawarsa kuma ya yi kuka, ta yadda kwallansa suka gudana bisa kuncinsa.
5-Lokacin da wani daga cikin 'ya'yan 'yar Manzo ya rasu ya yi kuka, sai Ubada Bn Samit ya tambaye shi me ya sa yake kuka? Sai Manzo ya ba shi amsa da cewa: Kuka rahama ce wacce Allah ya bai wa 'yan Adam, Allah madaukai zai ji kan bayinsa wadanda suke da tausayi.
6-Sayyida Zahara (a.s) bayan rasuwar Manzo ta yi kuka kwarai da gaske, tana cewa: Ya kai babana! Ka kusanci ubangijnka, kuma ka karba kiransa, ya baba masoyina, muna isar da labarin rasuwarka zuwa ga Jibrilu, kuma aljannar Firdausi ita ce makomarka .
7-'Yar Manzo Fadima (a.s) ta tsaya a kan kabarin babanta, ta debi kasar kabarin a cikin hannunta, ta dora a kan idanunta tana kuka tana cewa a cikin waka:
"Me zai faru ga mutum idan ya shaki kasar kabarin Ahmad,
Don bai shaki turare mai tsada ba a duk tsawon rayuwarsa.
Musiba ta sauka a kaina wacce idan da
Ta sauka ne a kan yini zai koma dare.
A yakin Uhud gwaggon Jabir Bn Abdullah ta kasance tana kuka a kan dan'uwanta Abdullah Bn Umar da aka kashe.
Sai Jabir ya ce ina kuka mutane suna hana ni yin kuka, amma Manzo bai hane ni da yin kuka ba. Sai Manzo ya ce: "Ka yi kuka a wajen zaman makokinsa domin kuwa ka rasa masoyi, kuma kada ka yi kuka domin kuwa, ina rantsuwa da Allah zuwa lokacin da aka rufe shi a cikin kabari mala'iku sun yi masa inuwa da fika-fikansu".
Amma dangane da ruwayar da ta zo daga Umar da dansa Abdullah Bn Umar cewa Manzo ya ce: "Lallai ana azabtar da mamaci a kan kukan danginsa".
A ra'ayimmu zahirin wannan hadisi ya yi karo da yadda tarihin rayuwar khalifa na biyu, wannan kuwa ya hada da:
1-Lokacin da labarin mutuwar nu'uman Bn mukarrin ya iso wa Umar, lokacin da umar ya fito daga gida ya hau kan mimbari ya isar da wannan labari ga mutane, a wannan lokaci sai ya dora hannunsa a bisa kai ya yi kuka.
2-Lokacin da Khalid Bn Walid ya rasu, Umar ya yi kuka a wajen zaman makokinsa, lokacin da labari ya iso masa cewa wasu sun hana mata su yi kuka sai ya ce: Idan har kukan ba suna daga murya suna kakari ba ne, babu wani laifi a kansa.
3-Lokacin da dan'uwan Umar ya rasu, sai wani abokinsa daga kabilar bani Ka'ab ya zo Madina, da Umar ya ga wannan abokin dan'uwansa, sai kwalla suka kwararo daga idanunsa ya ce: Zuwanka ya tuna mini Zaid!
Wannan kuka na khalifa Umar a wurare masu yawa, zai fahimtar da mu cewa ma'anar wannan hadisi koda kuwa danganensa ya inganta to yana nufin wani abu daban ne. Sannan bugu da kari idan har muka amince da zahirin wannan hadisi, to zai yi karo ne da ayar Kur'ani. Domin kuwa aya tana cewa: "Babu wani wanda zai dauki zunubin wani". Don haka idan aka azabtar da wani mamaci sakamakon kukan da danginsa suka yi, me zai kasance ma'anar wannan kenan?
Bincike Dangane Da Ma'anar Hadisin
Abubuwan da muka fada a baya zasu fahimtar da mu cewa idan har danganen wannan hadisi ya inganta, to ma'anarsa zata zama sabanin zahirin abin da yake nunawa, domin kuwa hadisin yana cewa ne "ana azabatar da mamaci sakamakon kukan da danginsa suke yi". Saboda haka muna ganin cewa wannan hadisi akwai wasu alamu da suke nuni da wani abu, yayin da aka ruwaito shi, ba a ruwaito da wadannan alamomi ba, sakamakon haka ne wasu suka fahimci cewa kukan mutuwa ya haramta, alhalin an rabkana daga ma'anarsa ta hakika.
A cikin Sahih Muslim, an ruwaito daga Hisham Bn Urwa shi kuma daga babansa cewa, an ruwaito daga A'isha ta hanyar Ibn Umar cewa: Ana yi wa mamaci azaba sakamakon kukan da danginsa suke yi". Sai A'isha ta ce: Allah ya rahamshe da baban Abdurrahaman, domin ya ji wani abu amma bai iya rike shi ba. Hakikanin al'amarin shi ne wata rana an wuce ta wajen Manzo da gawar wani bayahude, sai mutanensa suna yi masa kuka, sai Manzo ya ce: "Kuna yi masa kuka alhali shi yana cikin azaba".
Abu Dawud a cikin littafin sunan dinsa, ya ruwaito ta hanyar Urwa shi kuma daga Ibn Umar yana cewa: Wannan jumla da take cewa "Ana azabtar da mamaci sakamakon kukan danginsa". Daga manzon Allah take. Lokacin da wannan labari ya kai wa A'isha sai ta ce: Lokacin da Manzo zai gitta kabarin wani bayahude sai ya ce: Mai wannan kabarin yana cikin azaba, alhalin danginsa suna yi masa kuka. "Sai ya karanta wannan aya: "Babu wani mai zunubi da zai dauki zunubin wani".
Imam Shafi'i yana cewa: Abin da A'isha ta ruwaito dangane da wannan magana tare da amfani da abin da Kur'ani da Sunna suke koyarwa ya fi kama da maganar Manzo a kan abin da Ibn Umar yake fada. Idan kuwa kuka ce menene dalilinku a kan haka daga Kur'ani to zamu kawo wannan ayar kamar haka:
"Ba mai zunubi wanda zai dauki zunubin wani, mutum ba shi da wani abu sai abin da ya aikata". Duk wanda ya aikata aikin alheri daidai da kwarar zarra zai samu abinsa. Kuma duk wanda ya aikata sharri dai-dai da kwarar zarra zai sami abinsa . Domin a saka wa kowa abin da abin da ya yi kokari an kansa".
Sannan idan kuka ce menene dalilinku daga Sunna? sai mu ambaci wannan ruwayar kamar haka:
Manzo (s.a.w) ya tambayi wani mutum cewa: Shin wannan danka ne? sai mutumin ya bayar da amsa cewa: E.
Sai Manzo ya ce: "Bai kamata ba ya cutar da kai haka nan kai ma bai kamata ba ka cutar da shi". Manzo (s.a.w) a cikin wannan jumla yana so ya isar da abin da Kur'ani yake cewa: Babu wanda zai cutar da wani ta hanyar zunubinsa, duk abin da mutum ya aikata yana bisakansa, wato ba zai cutar da kowa da zunubinsa ba sai kansa. Haka nan idan aikin kwarai ne zai amfanar da kansa ne.
Haka nan a cikin Sahih Muslim ta hanayr Ibn Abbas, an ruwaito hadisi cewa Manzo (s.a.w) ya ce: Lallai mamaci ana yi masa azaba da kukan danginsa". Sannan Ibn Abbas yana karawa da cewa: Lokacin da Umar ya rasu an hakaito wannan hadisi a wurin A'isha, sai ta ce: Allah ya jikan Umar, ina rantsuwa da Allah sam Manzo bai ce ba Allah zai yi wa mumini azaba sakamakon kukan wani! Amma ya ce Allah zai kara wa kafiri azaba sakamakon kukan da danginsa suke yi a kansa. Sannan wannan ayar ta wadatar da ku inda Allah yake cewa: "Babu wani mai zunubi wanda zai dauki zunubin wani" .
Ya dace mu yi tunatarwa a kan wani abu kamar haka cewa, Hadisin da Sahih Muslim ya ruwaito ta hanyar Hisham Bn Urwa wanda muka yi nuni da shi farkon wannan Bahasi ya inganta kuma karbabbe ne, Amma wannan hadisin da aka ruwaito daga Ibn Abbas ba ya inganta, domin kuwa kara wa kafiri azaba sakamakon kukan da danginsa suke yi bai dace da ayar Kur'ani ba.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012