Sakamakon Ayyuka2
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Ayyuka Da Kyakkyawan Sakamako 2
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Nazarin Malaman AhlusSunna
Domin mu karasa kammala bahsin, a nan zamu cika da maganganun wasu daga cikin manyan malaman Sunna guda biyu kamar haka:
1-Khalidi a cikin litttafinsa (Sulhul Ikhwan) yana rubuta cewa: Yin bakance yana bisa ma'aunin niyyar da masu bakancen suka yi, domin kuwa "dukkan ayyuka suna tare da niyya" wato abin da mai bakance ya yi nufi. Idan ya zamana don neman kusanci ne ga mamacin to babu shakka wannan bai halatta ba. Amma idan mutum yana nufin neman kusanci ne zuwa ga Allah, amma da nufin ladar ta je wa wani mamaci wanda ya nufa da hakan, ba wai kawai ya halatta ba idan mutum ya yi alkwari zai yi hakan wajibi ne ya cika wannan alkawarin.
2-Izami a cikin littafin (furkanul Kur'ani) ya kawo cewa: Idan mutum ya yi bincike dangane da alwakrin yanka da suke yi domin annabawa da salihan bayi, zai samu sakamakon cewa, ba su da wata manufa wacce ta wuce yin hakan amatsayin sadakarwa ko kyautar ladar wannan aiki zuwa ga ruhinsu. Sannan malaman AhlusSunna sun hadu a kan cewa yin sadaka zuwa ga ruhin wadanda suka riga mu daga wadanda suke raye, wani abu ne mai yi musu amfani kuma ladar zata isa zuwa garesu. Sannan ruwayoyin da suka zo dangane da hakan ingantattu ne kuma mashahurai ne.
Abu Dawud tare da dangane zuwa ga Mai muna ya ruwaito cewa: Babana ya tamabayi Manzo (s.a.w) yana cewa ya manzon Allah! Na yi bakance (alkawari) cewa idan Allah ya ba ni da namiji, zan yanaka raguna a (Bawana) sunan wani wuri ne, sai yake cewa ban fahimta ba da kyau, amma mai muna yana magana ne a kan raguna guda 50.
Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Akwai gumaka a wannan wurin Sai baban Maimuna ya ce babu gumaka.
Sai Manzo (s.a.w) ya ce to cika alwakrin da ka yi wa Allah .
Kamar yadda muka gani a sama Manzo yana karfafawa dangane da cewa shin akwai gumaka inda za a yi wannan yankan, wannan yana nuna cewa kawai bakancen da aka yi saboda gumaka shi ne haram, domin kuwa al'adar mutanen jahiliyya ta tafi a kan wannan.
"…. Abin da kuka yanka don gumaka…. fasikanci ne" .
Duk mutumin da ya kula da kyau dangane da wadanda suke zuwa ziyara a wurare masu tsarki zai ga cewa, suna yin bakance ne domin samun yardar Allah a wadannan wurare, sannan suna yin yankansu ne da sunan Allah, sannan manufarsu a kan wannan shi ne, wanda aka rufe a wannan wuri ya amfana da ladar wannan abin da suka yanka, sannan mabukata su amfana da naman da aka yanka.
Fatawowin Malaman AhlusSunna
Kamar yadda ya kasance wannan al'amari wani abu ne da ya shafi fikhu, idan muka san fatawowin malam AhlusSunna dangane da wannan magana zai iya taimaka mana wajen fahimtar al'amarin, sun kasance sun kasa wannan magana zuwa gida biyu kamar haka:
Aö-Duk lokacin da mamaci ya yi wasiyya a kan aiwatar da wani abu dukkan shugabannin mazhabobi guda hudu sun hadu a kan wajibcin aiwatar da wannan abin, kuma suna cewa mamaci yana amfana daga ayyukan wadanda suke raye.
B-Idan mutum bai yi wasiyya a kan wani abu ba, amma 'ya'yansa ko wani na kusa da shi suna so su gabatar da wani aikin lada zuwa gare shi, dukkan malaman fikihu ban da malikiyya sun hadu a kan ingancin hakan.
1-Malaman Hambaliyya suna cewa: Duk wanda ya mutu kafin ya gabatar da hajji na wajibi, koda yana da uzuri ko kuwa ba shi da uzuri dangane da hakan, dole ne a yi masa hajji daga dukiyarsa koda kuwa bai yi wasiyya ba.
2-Malaman Hanafiyya suna cewa: Idan mutum bai yi wasiyya ba sai ya rasu, sai wani daga cikin magadansa ya yi masa hajji, aikinsa zai karbu da izinin Allah.
3-Shafi'iyya suna cewa: Duk lokacin da mutum ya kasa gabatar da aikin hajji, bayan mutuwarsa wani yana iya yi masa a madadinsa.
Idan muna so mu kawo ra'ayoyin dukkan malaman fikihu na AhlusSunna dangane da wannan al'amari ne zamu tsawaita magana ne a kansa, don haka zamu wadatu da abin da muka ambata a sama, abin da kawai ya yi saura a nan shi ne mu yi bayani a kan wasu kalubale da wasu suka kawo dangane da hakan.
Kalubale Na Farko
Masu kalu balantar wannan al'amari suna cewa Kur'ani mai girma yana nuna cewa mutum kawai zai iya amfana da abin da ya aikata ne, kamar inda yake cewa: "Mutum ba shi da wani abu sai abin da ya aikata" .
Saboda haka ta yaya zai zamana ayyukan da wasu zasu yi don mamaci ya amfana da su, alhalin babu wani kokari da ya yi wajen aiwatar da hakan.
Amsa
Amsar wannan kalubale kuwa a fili yake, da sharadin cewa mu fahimci ma'anar wannan aya da kyau:
Na farko: Wannan aya tana magana ne a kan sakamakon da azaba, wato duk wanda aka kama shi sakamakon ayyukansa, ba wai an kama shi ba ne sakamakon aikin wani daban, sannan wannan aya sam ba ta da alaka da bayar da lada, tare da dalilin cewa:
"Shin ba ka ga mutumin da ya juya baya ba? ya bayar da kadan ya hana mai yawa, shin yana da ilimin gaibu ne wanda yake gani da shi, ko kuwa ba shi da masaniya dangane da sahifar Musa? Da kuma rubuce-rubucen Ibrahim wanda ya cika alwkari da su. Babu wani wanda zai dauki nauyin wani. Sannan mutum ba shi da wani abu sai abin da ya aikata. Dukkan wani kokarinsa za a gan shi. Sannan za a saka masa da duk abin da ya dace. Sannan makura tana ga Ubangijinka".
Tare da kula da abin da muka yi bayani a sama zamu fahimci cewa mutum zai samu duk abin da ya cancance shi ne sakamakon ayyukansa na zunubi. Domin a cikin adabin larabci daya daga cikin ma'anonin "lamun" kamar irin wanda ya zo cikin kalmar "Lil insan" yana nuna cancanta ne, kamar yadda ya zo a cikin ayar da take cewa "Wailun lil mudaffifin" wato azaba da banu sun tabbata ga masu tauye ma'auni, domin cancantarsu da hakan sakamakon ayyukansu. Don haka wannan aya ba ta da alaka da bayar da lada, tana magana ne dangane da azaba.
Na biyu: Idan mun dauka ma cewa wannan aya tana nuni ne a kan lada da azaba, a nan akwai abubuwa guda biyu wadanda bai kamata a cakuda su wuri guda ba:
1-Rahama da azabar mutum duk sun rataye ne ga aikinsa, idan mutum ya aikata aikin kwarai zai kasance ya rabauta, idan kuwa ya zamana ya aikata mummuna zai zamana ya shiga azabar Allah. Wannan wata ka'ida ce ta Kur'ani wacce ta zo a cikin ayoyi da dama, kamae inda yake cewa: "Duk wanda ya aikata kyakkyawa don kansa, wanda kuwa ya aikata mummuna don kansa".
2- Idan mutum ya aikata kyakkyawan aiki sannan ya bayar da ladar wannan aikin zuwa ga wani wanda ya rasu, wannan mamaci zai amfana da wannan ladar.
Wannan asali guda biyu sam ba su karo da juna, ka'ida ta farko ta hade kowane mutum kuma tana magana ne yayin da mutum yake raye a duniya, sannan tana bayani ne akana bin da zai sanya mutum ya samu babban rabo a lahira ko kuwa ya tabe, amma ka'ida ta biyu kuwa tana magana ne dangane da wani abu wanda yake ya kebanci wasu ne, amma bambancin da yake tsakaninsu da kuma rashin karonsu da juna zai bayyana a cikin misalin da zamu kawo.
Mahaifi yana yi wa dansa nasiha yana cewa: Rayuwarka mai kyau da rashin kyanta yana kunshe da kokari da ka yi a cikin rayuwa, don haka fatan rayuwa mai kyau ba tare da aiki ba aikin banza ne kuma wawanci ne. Amma wannan ba yana nufin cewa ba idan wani ya ba shi kyautar wani abu kada ya karba ba, ta yadda idan ya karbi abin da aka ba shi matsayin kayauta ya kuma yi amfani da ita kamar ya saba wa maganar mahaifinsa ne, domin kuwa maganar mahaifinsa wata ka'ida ce a cikin rayuwa, amma amfana daga aikin wani mutum wani abu ne wanda yakan faru ne amma ba kodayaushe ba. Mahaifinsa yana yi masa nuni ne da ya dogara da kansa domin kuwa jin dadin rayuwa ba ya samuwa tare da ragganci da kasala. Amma wannan ba yana nufin cewa ba wani lokaci idan ta kama kada mutum ya amfana da aikin wani mutum daban ba.
Kalubale Na Biyu
Hadisin da duka bangarori guda biyu suka ruwaito yana nuni ne da cewa, yayin da mutum ya mutu littafin ayyukansa zai kulle, sai kawai ta hanyoyi guda uku:
1-Sadakatu jariya
2-Aikin ilimi da mutum ya yi wanda wasu suke amfana da shi.
3-Idan mutum ya haifi dan kwarai wanda zai rika yi masa addu'a.
Don haka mutum zai iya amfana da wasu abubuwa bayan ya mutu ta wadannan hanyoyi guda. Alhalin kuwa amfanuwa da ayyukan wasu bayan mutuwa ba ya daya daga cikin wadannan guda ukkun.
Amsa
Wannan hadisi da aka ambata yana magana ne a kan ayyukan da mutum da kansa ya aikata, saboda haka a nan da sauran magana wato idan mutum ya mutu duk wani aiki wanda shi ne da kansa ya yi sanadinsa zai yanke sai abubwa guda uku wadanda aka ambata wadanda su ne zasu dawwama, sakamakon mutuwar mutum ba zasu yanke ba. Saboda haka wannan hadisi ba shi da alaka da ladar da mutum zai samu sakamakon ayyukan wasu da suka yi saboda shi.
Saboda haka wannan hadisi kai tsaye yana magana ne dangane da ayyukan da mutum ya aikata da kansa ne, wadanda duk zasu yanke bayan mutuwarsa, sai kawai wadannan ayyuka guda uku wadanda zai ci gaba da amfana da su. Don haka wannan shi ne batun da ake magana a kansa a cikin wannan hadisi, saboda haka sam ba shi da alaka da abin da mutum zai samu na lada ta fuskar ayyukan wasu.
Kalubale Na Uku
Ayyuka sun kasu zuwa gida biyu, wadansu ana iya yinsu a madadin wani (kamar hajji da sadaka) wadan su kuwa ba za a iya yinsu ba a madadin wani mutum daban ba (Kamar azumi da salla), saboda haka ta yaya ne wani zai iya yin wadannan ayyukan a madadin wani, alhalin ba a wakiltar wani a cikin wadan ayyukan!
Amsa
Dangane da ayyukan da ake iya wakiltar wani da wadanda ba za a iya wakiltar wani ba, dole su samo asali daga shari'a, misali karbar musulunci ba ya daga cikin abin da za a iya yi a madadin wani, idan da mutum zai yi kalmar shahada sau dari a madadin kafiri, wannan kafiri yananan a matsayinsa na kafiri ba tare da wani canji ba, amma azumi kamar yadda ya zo a cikin ruwaya ana iya wakiltar wani a cikinsa.
Manzo (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya mutu ana binsa azumi sai waliyyinsa ya yi a madadinsa".
Da makamantan wannan ruwayar kamar yadda muka ambata a farkon wannan Bahasi, sannan ta yaya ne wannan mutum zai ce ba a wakiltar mutum a wajen yin salla, amma ya amince da ana iya wakiltar mutum a wajen hajji, domin kuwa dawafi a wajen aikin hajji yana tattare da yin salla, idan har abu ya zamana a wani wuri ana iya wakiltar wani to ai babu bambanci a ko'ina ana iya wakiltar mutum a wajen wannan aikin.
Hakim ya ruwaito a cikin Mustadrak dinsa daga Manzo (s.a.w) yana cewa: Yasin zuciyar Kur'ani ce, babu wanda zai karanta ta alhalin yana neman gafarar Allah face sai Allah ya gafarta masa, don haka ku karanta ta ga mamatanku.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012