Neman Tabarruki2
  • Take: Neman Tabarruki2
  • marubucin: Sheikh Subhani
  • Source:
  • Ranar Saki: 19:37:10 1-9-1403

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI


Neman Tabarruki Da Manzo Da Abin Da Ya Bari 2

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Abin Da Yake Janyo A Nemi Tabarruki
Abin da yake janyo a nemi tabarruki daya daga cikin abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Kwararowar ni'imar Ubangiji wacce wani lokaci take samuwa ta hanyar da ba ita aka saba da ita ba, dangane da wannan mun kawo misalai a baya.
2-Soyayya da kaunar iyalan gidan manzanci, da sahabban Manzo, wannan kuwa yana daga cikin umurnin Kur'ani mai girma, babu shakka kuwa so da kauna suna bukatar inda za a bayyanar da su, wurin da za a bayyanar da wannan soyayya kuwa a wurinsu yayin da suke a raye, kamar yadda ya kasance wasu mabiyasu na gaskiya sun aikata hakan. Amma lokacin da ba su raye tare da mu kuwa akwai wuraren da ya kamata a nuna wannan soyayya gare su, kamar tunawa ta ranar haihuwarsu, sannan yin bakin ciki da tuna ranar wafatinsu, sannan yayin da mutum ya je a kaburburansu ya sumbaci bangaye da kofofin kabarinsu, dukkan yana samun tushe ne daga soyayya gare su, wacce take tun tsawon tarihi a cikin zukatan musulmai. A hakikanin gaskiya wannan gungun mutane wadanda suke sumbatar kabarin annabi da nuna kauna ga duk wani abu da ya shafe shi, wannan duk suna nuna soyayyarsu ne ga shi kansa Manzo, amma yanzu hannunsu ba zai iya isa zuwa gare shi ba, saboda haka ne suke nuna soyayyarsu ga duk abin da ya bari ko kuma a ka jingina shi zuwa gare shi.
Wuraren zayara duk da cewa a zahiri bai wuce dutse da katakai ba, amma soyayyarmu garesu tana nuna tsananin yadda muke son wanda yake a ciki wato manzon Allah (s.a.w) da A'immatu Ahlul bait (a.s) kuma jingina wadannan duwatsu ga annabi ko imamai ya sanya suka samu wata daraja da tsarki na musamman. Lokacin da zuciya ta zama gidan soyayyar wani masoyi, ma'abucin wannan zuciya yana farin ciki da jin sunan ko ya ga, tufafi, hankici, takalmi, garin masoyi ko tunawa da duk wani abin da ya shafi wannan masoyi na shi, sannan kuma yana ganin wannan masoyin cikin wadannan abubuwan.
Musulmai sakamakon soyayyar da suke da ita ga manzon Allah, idan suka ji labari cewa ga wani wuri inda sawun Ahmad Mahmud (s.a.w) yake, zasu ta fi cikin shauki domin su gane wa idanunsu wannan alama ta shi.
Abubuwan da suka shafi wannan a cikin tarihin rayuwar Manzo (s.a.w) suna da yawa ta yadda a zamu iya kawo su duka ba a nan, amma zamu kawo wasu daga cikinsu a matsayin misali kamar haka:
1-Sahabbai Suna Kawo Jariransu Ga Manzo
Duk lokacin da aka haifi wani yaro a Madina sahabban Manzo sun kasance suna kawo shi wajen Manzo kafin ya fara cin komai domin neman albarka, sai Manzo ya sanya masa wannan jariri dabino a bakinsa a matsayin ya buda masa bakinsa kenan, kuma sai Manzo ya yi wa wannan yaro addu'a. Ibn Hajar yana cewa: Duk yaron da aka Haifa a Madina bayan hijira tabbas Manzo ya gan shi, domin kuwa sahabbai sun dora wa kanzu cewa duk lkacin da aka haifar musu jariri sai sun kawo wajen Manzo domin ya bude masa bakinsa. A'isha tana cewa: Ana kawo yara wajen Manzo domin neman tabarruki. Abdurrahman Bn Auf yana cewa: Ba za a haifar wa wani sahabi jariri ba face ya kawo shi wajen Manzo (s.a.w) domin ya yi masa addu'a. Lokacin da aka haifi Abdullahi Bn Abbas Manzo da Ahlul baitinsa sun kasance a sha'abi Abi Dalib inda Manzo ya bude masa baki da yawunsa.
2-Neman tabarruki ta hanyar Manzo ya shafi kawunan sahabbai
Ba kawai jarirai 'ya'yan sahabbai ba ne ake kai wa man zo domin ya shafi kawunansu a matsayin neman tabarruki, har sahabbai da kansu sun kasance suna zuwa wajen Manzo domin ya shafi kansu don neman albarka. Ziyad Bn Abdullah yana daga cikin wadanda Manzo ya yi wa addu'a sannan ya shafi kansa. A wannan lokaci ya shafi kansa har zuwa hancinsa. A kan haka ne mawaki yayin da yake yabon bin ziyad inda yake cewa:
Ya kai dan wanda Manzo ya shafi kansa,
Kuma ya yi masa addu'ar alheri a masallaci.
2-Neman Tabarruki Da Ruwan Alwalar Manzo Da Na Wankansa
Daya daga cikin abubuwan da suka shahara a zamanin rayuwar Manzo shi ne, sahabbai sun kasance suna neman tabarruki da ruwan alwala da na wankan Manzo (s.a.w) ta yadda sam ba su bari digon ruwan alwallarsa ya fadi a kasa, idan har ya kasance mai yawa sai su shanye shi, idan kuwa ba shi da yawa sai su shafa ga fuskarsu.
Urwa Bn Mas'ud Sakafi wanda ya kasance wakilin kuraishawa a sulhun Hudaibiyya, ya ga wannan al'amari yayin da ya koma ya gaya wa kuraishawa inda yake cewa: Sahabban Muhammad domin su samu ruwan alwallarsa sukan yi buge-buge, ya ci gaba da cewa ba wai kawai ruwan alwallarsa da wanka ba, har da ruwa da abincin da ya rage, ko kuwa kwanon da ya ci abinci ko rijiyar da ya sha ruwa sukan nemi tabarruki da ita.

Neman Tabarruki Da Kabarin Manoz (s.a.w)
A- Marwan Bn Hakam ya shiga masallaci, sai ya ga wani mutum ya kafa fuskarsa bisa kabarin Manzo (s.a.w) sai Marwan ya dago kansa ya jawo shi baya ya ce masa: "Ka san abin da kake yi kuwa? Sai wannan mutum ya dago kansa, sai khalifa ya gane cewa Abu Ayyub Ansari ne wanda yake daya daga cikin manyan sahabban Manzo (s.a.w) kuma wanda ya sauki Manzo yayin da ya zo a Madina. Abu Ayyub sai bai wa Marwan amsa, ga abin da yake cewa: Ni ban zo nan ba sabo da dutse, na zo ne saboda manzon Allah, Ya kai Marwan na ji daga Manzo yana cewa: Zuwa lokacin da mutanen kirki suke jagorantar musulunci kada ku yi kuka a kan haka, amma ku yi kuka yayin da ya zamana wadanda ba su cancanta ba suke shugabancin musulunci, wato kai da gidan Amawi. Wannan bangare na tarihi, Hakim Nishaburi ya kawo shi a cikin Mustadrikul sahihaini yana nuna mana yadda ya kasance manyan sahabban Manzo suke neman tabarruki da kabarin Manzo a lokacin rayuwarsu. Sannan yana nuna mana kiyayyar wasu daga cikin wadanda ba su da soyayyar Manzo a cikin zuciyarsu kamar irinsu marwan a kan yin wannan al'amari na neman tabarruki.
B-Bilal Habashi wanda yake shi ma daya daga cikin manyan sahabban Manzo wanda bayan rasuwar Manzo ya zabi ya yi rayuwa a wani wuri daban sabanin Madina, wata rana ya yi mafarki da Manzo yana ce masa, wannan rashin kula har ina? Lokacin da ya farka daga barci, sai ya yi tunanin ya tafi domin ya ziyarci Manzo, domin kuwa tun lokacin da ya baro Madina bai sake zuwanta ba, don haka goben wannan rana sai ya tafi Madina, lokacin da ya shiga garin Madina, sai ya zauna gefen kabarin Manzo ya yi kuka mai yawa yana goga fuskarsa ga kabarin Manzo (s.a.w) lokacin da ya ga HAsan da Husain (a.s) sai ya rungume su yana sumbatarsu, sannan suka neme shi da ya je inda yake kiran salla a zamanin Manzo domin ya kira salla haka kuwa ya yi kamar yadda muka kawo a baya.
C- A lokacin da Manzo ya yi wafati bayan an rufe Fadima (a.s) 'yar Manzo (s.a.w) ta je wajen kabarinsa ta yi kuka sannan ta debo kasar kabarinsa ta shafa a fuskarta, Ga abin da take cewa a wasu baituka na waka: Me zai faru ga wanda ya shaki kasar kabarin Ahmad, Don bai shaki turare mai tsada ba a tsawon rayuwarsa. Masifa ta sauka gareni, wacce idan da rana ta saukar wa zata koma dare.
A nan zamu wadatu da wadannan misali da muka kawo daga cikin gomomin misalai da suke tabbatar da neman tabarruki daga Manzo, amma idan aka koma zuwa ga manyan Littattafan hadisi zamu ga yadda wannan al'amari na neman tabarruki ya kasance mutawatir.
Sakamakon Bahsin
Bincike a kan tarihin musulunci yana tabbatar mana da cewa batun neman tabarruki da Manzo ko wani abu wanda aka jingina shi zuwa ga Manzo wani abu wanda ya zama al'adar musulmi a duk tsawon tarihi, sannan manufarsa a kan hakan yana daga cikin dayan biyu:
1-Neman tabarruki da wadannan abubuwan da nufin cewa ni'imar Ubangiji tana biyowa ta nan ne zuwa gare su, kamar yadda ya kasance ni'imar Ubangiji zuwa ga annabi Yakub ta biyo ta hanyar rigar annabi Yusuf (a.s)
2-Soyayyar al'ummar musulmi ga Manzo shi ya sanya duk wani abu da ya shafi shi manzon suke girmama shi, don haka ne ya sanya duk kankantar wani abu da ya bari wanda ya hada daga takobi, hula, takalmi gashi, farce, da abin da ya sha ruwa a cikinsa, da abin da yake zuba ruwa a cikinsa, da rijiyar da Manzo ya sha ruwa a cikinta, duk sun kasance suna kiyaye su suna kuma girmama wadannan abubuwa, haka nan suna neman tabarruki da tufafin Manzo da makamancinsa, sanann ya kasance zoben Manzo yana zagaya a tsakanin yatsun sahabbai.
Daga karshe zamu yi tunatarwa da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Ahmad Bn ham Hambal shugaban mazhabar Hambaliyya wanda yake da girma a tsakanin 'yan Sunna, ya ksance yana da ra'ayoyi masu yawa dangane da abin da ya shafi neman tabarruki, a nan zamu kawo wasu daga cikin maganganunsa a matsayin misali:
A-Dan Abdullah yana cewa: Na tambayi babana a kan cewa na ga wani mutum yana dora hannunsa a kan mimbarin Manzo da nufin ya neman tabrruki kuma yana sumbatarsa, sannan ya yi hakan ne ga kabarin Manzo da nufin neman lada, sai babansa ya amsa masa da cewa: babu laifi.
Ahmad Bn Muhammad makarri Maliki (ya rasu 1041) a cikin littafinsa mai suna fathul muta'al yana ruwaitowa daga waliyyuddin Iraki yana cewa, Ustaz Abu Sa'id ya ruwaito daga wani littafi dadadde wanda Ibn Nasir ya rubuta ga abin da yake cewa: Na tambayi Imam Ahmad dangane da sumbatar kabari, sai ya amsa mini da cewa babu laifi.
Ibn Nasir ya kara da cewa, na nuna wa Ibn Taimiyya wannan littafi, sai ya kasance ya yi tsananin mamaki daga maganar Imam Ahmad, sai na ce masa ai babu mamaki a cikin wannan magana, Imam Ahmad shi ne wanda ya kasance ya sha ruwan da aka wanke rigar Shafi'i da shi . Idan har Ahmad dangane da malamansa yana yin haka to ina ga wadanda suke samansu har zuwa abin da yake daga manzon Allah (s.a.w) .
Abu na biyu kuwa shi ne a shekarun baya an rubuta wasu litattafai guda biyu a kan neman tabarruki wanda daya daga ciki malamin sunni ya rubuta daya kuwa malamin Shi'a ya rubuta shi, sannan dukkan su biyun sun yi bayani da kyau kamar yadda ya dace. A nan zamu gabatar da wadannan litattafai guda biyu ga masu karatu kamar haka:
1-Ta barrukus sahaba bi asararir rasul (s.a.w) wanda babban malamin nan kuma masanin tarihi wato Allama Muhammad Tahir Bn Abdulkadir Bn Mahmud Maliki ya rubuta, kuma an rubuta wannan littafi a shekara ta 1385 a Alkahira a madaba'a ta madni.
2-Attabarruk: Wanda muhakkik Ayatullahi Ali Ahmadi Miyanji ya rubuta (1385-1421) wanda ya koma ga rahamar Allaha shakarun da suka gabata, a cikin wannan littafi na sa ya yi bincike da kyau dangane da wannan magana ta hanyar hadisai da tarihi, ta yadda ya tabbatar da tarihin musulmi a kan hakan. Ta yadda babu sauran shakku dangane da wannan al'amari.
Daga karshe zamu iya daukar sakamako cewa abin da yake faruwa a yau kuma muke gani a kabarin Manzo ta yadda wasu gungu a karkashin "yan amru bil ma'aruf da hani da mummuna, suke daukar duk wani nau'i na nuna kauna da soyayyar Manzo a matsayin bidi'a da shirka, wani zunubi ne wanda ba za a yafe shi ba, wanda ya samo asali da rashin fahimtar hakikanin addinin musulunci, idan da wadannan masu wannan aiki zasu amince da shirya tarukan karawa juna ilimi, da gaskiya ta bayyana daga cikin duhu, ta yadda kafirtawa ko fasikanta al'ummar musulmi yakau, ta yadda soyayyar muslunci ta maye gurbin gaba da kiyayya.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012